Jinkirin Aure na Oum Hairan Hausa Novel
_JINKIRIN AURE_*
*_Ƙalubale ga ƴammata_*
*By*
*Oum Hairan*
*Dedicated to*
Dr Mass Agadas son so for ever.
*P 1-2*
Iska ce ke kaɗawa ta damuna me cikakken sanyi da sanya zuciyar da take cikin kwanciyar hankali a nishaɗi, yayin da zuciyoyin da suke cike da zullumin damuwa suke kasancewa da sassaucin yanayi.
Saidai a gurinta itan wannan yanayi yafi mata kowanne yanayi zafi, rayuwarta ta ƙuntata hawayenta ya yawaita ƙuncin zuciyarta ya ƙaru a yayin data keɓance kanta ita kaɗai a madaidaicin office ɗin nata me ɗauke da table me kujera ɗaya, gabanta cike yake da files-files na petiant ɗinta na yau data gani inda gabadayan hankalinta yabar gangar jikinta a zaune saman kujerar lokaci zuwa lokaci hawayenta ba diga saman takardar dake gabanta.
Yar Jami’a Hausa Novel Complete
Ƙwankwasa ƙofar akayi har karo uku dake hankalinta baya jikinta batasan anayi ba, jin shirun ne yasa me neman izinin turo ƙofar tare da sallama ta shigo cikin office ɗin ta tsaya ta zubawa Mamallakiyar office ɗin idanu tana mamakin abinda yake sanyata shiga matsananciyar damuwar da har hankalinta yake gushewa haka.
Dukan Table ɗin Dr Zaheera tayi abinda ya dawo da wadda ke zaunen cikin nutsuwarta tayi saurin sa handcap ta share idanunta ta ɗagosu ta zubasu kan Dr Zaheera itama ita take kallo harta isa ga wata kujerar ta zauna suna facing ɗin juna.
Dr Zahira ce ta kawar da shirun da cewa “Kullum kin kasance cikin damuwa kin takuri kanki kin tsawwala kanki Dr Madinah meye yasa hakan ne? Meyesa kike mantawa duk abinda ba’a fareshi akanka ba bazaa ƙare shi akanki ba?”
Manyan fararen idanunta ta lumshe ta kwantar da kanta saman kujerar da take kai hawaye na tsiyaya daga kwarmin idanunta tasa tisue ta goge dogo hancinta
“Meye ne matsalata meye ne aibina meye yasa kyawuna ya kasa samar min da mijin aure, meyesa kullum al’umma basamin adalci suke ganin cewar nice naƙi aure bayan Nima nafi kowa son na ganni cikin dausayin sunnar ma’aikin Allah???
Tambayar da kullum nakewa kaina kenan”
Cewar Dr Madinah dake ɗagowa tana zuba idanunta akan ƙawarta Dr Zahira, shiru Dr Zahira tayi na ɗan lokaci sannan ta buɗe baki tace.
“Dr Madinah ba jama’ar gari da suke ganinki daga nesa ba ni kaina da nake da kusanci dake lamarinki yana bani mamaki gani da sani a damuwa da tunanin meye dalili? Madinah kyawunki yakai ace kina juya ragamar maza a hannunki sai kuma ya kasance maza sune ƙaddararki, ta yaya zan yarda ace mu da bamu kai ba maza na zumuɗi akanmu ke da kika wucce kice babu wanda ya taɓa cewa yana sonki?”
Murmushi me ciwo Madinah tayi tana kai dubanta ga agogo ta miƙe ta fara harhaɗa files ɗin ta sanyasu wajen adanasu ta ɗauki jakarta ta dubi Dr Zahira tayi gaba tana cewa “duk sanda na tsaya tuntuntunin abinda kike tunani yanzu Zuciyata zafi takeyi Zahira ni kaina na fara tsoron kaina ina tunanin to ko wani abune ke gareni abin gudu da Ni na kasa ganewa, Zahira shekaruna sun fara tafiya a matsayina na ɗiya mace ba namiji ba ace na zubar da shekaru talatin da biyu batare da aure ba wannan abu da cin rai yake…..”
Isa sukayi bakin titin suka tari ɗan sahu suka hau ya fara sauke Zahira a kwanar unguwar su sannan ya wuce da Madinah tasu unguwar ya sauke ta ta fito tana gyara mayafin data yafa saman uniform ɗinta na aiki ta nufi unguwar tasu lokaci zuwa lokaci suna gaisawa da dattijan unguwar dake zaune a ƙofar gidajensu.
Gidansu ta shiga da sallamarta babu kowa a tsakar gidan hakan ya bata damar nufar ɗakin mahaifiyarta ta daga labulen tana cewa “Ammi sannu da gida” Ammi dake zaune a tsakar ɗakin ta ɗago tana duban tilon ɗiyar tata mace tace “Yawwa Munau Jaɓɓama” guri ta samu ta zauna tana yage mayafinta tace “Yau na gaji da yawa Ammi me kuka girka mana?” Numfashi ta sauke tace “Abinda kika tsana” dafe kirji tayi tace “Nashi na Ammi don Allah meye yasa kukayi alale?” Tana maganar tana kwalawa me aikinsu kira Bintalo ta ta rusuna a gabanta tace “meye kikeyi Binta?” Tana wasa da yatsunta tace “bsbu abinda nakeyi Uwarɗakina” fasali taja tace “ki samamin abinda zanci insjin yunwa gashi ku kun tashi kunyiwa mutane Alele” miƙewa Bintalo tayi ta fita bata jima ba ta dawo ɗauke da tire shaƙare da kwanuka ta ajiye mata a gabanta ta fara budewa tayi murmushi tace “wato wanani Ammi kikayi niyyar yi ashe ma My Favorite kukayi” murmushi Ammi tayi ta zuba mata ido tana kallon yanda take cin abincin a nutse da alama yunwa ta yini da ita yau.
“Munau” Ammi ta kira sunanta ta ɗago tana ajiye cokalin ta mayar da hankalinta ga mahaifiyar tasu Ammi tace “Wato Madinah kullum da wannan tunanin nake kwana nake tashi kullum da tunanin lokacin aurenki nake bacci nake tashi Madinah kullum shekarunki tafiya sukeyi girma ƙara sauko Miki yakeyi ke kuma abinda yake aranki shi kikeyi baki tunanin gobenki kin kasa tsayar da hankalinki ki samarwa kanki abokin rayuwa ki inganta kanki, Munau meye ne a gabanki daya danni sunnar ma’aikin Allah da tunaninki baya baki dacewa da cancantarki na kiyi ta? Aure shine martaba da mutuncin kowacce ƴa mace aure shine daraja da ƙimar kowacce mace ke ba iya mace ba hatta namiji aure shine ƙimarsa”
Idanunta da suke tsiyayar da hawaye ta sadda ƙasa taci gaba da kukanta me tafasa zuciya, wannan ya tashi hankalin Ammi tace “Ina mamakin yanda da zaran nayi Miki magana akan ingancin rayuwarki kike sanyani a gaba kinamin kuka Munau idan har maganar da nakeyi Miki ce bakiso zan iya tattarawa na daina amma ki sani da gaske ganinki a gabana bayamun daɗi kamar kowacce uwa Nima nafison ki rinƙa zuwar min da yawo kina komawa ɗakinki”
Hannu tasa ta tsane hawayenta ta ɗago cikin raunin murya tace “Wlh Ammi kullum ina addu’a mafarki da fatan zuwan wannan ranar amma taƙi zuwa, Ammi ya zanyi wannan rana tazone? Nima na zama matar aure cikakkiyar mace me ƴanci sannan me ji da alfarmar aure, Ammi ki daina ganin laifina kiyimin addu’a don Allah kema gani kikeyi kamar nice banason aure bayan auren ne yaƙi zaɓata Ammi kinsani tun kafin wannan lokacin wallahi tallahi bansan wani namiji ɗaya daya taɓa tarata ya buɗe baki yacemin yana sona koda wasa ba bare da aure, wai Ammi ya akeyi ake samun mijin auren nan ne Nima nayi ko na samu ki daina kallo na a me laifi….”
Ta ƙarashe maganar tana sakin wani kuka me gunji tare da kifa kanta a kafaɗar Ammi, cike da tausayawa Ammi ta shiga bubbuga bayanta da sanyin yanayi na mahaifiyar da taga ɗanta cikin halin tsanani tace “Shikenan Munau na fahimceki ki daina kukan haka Allah yanaji yana gani zai kawo mana mafita da yardarsa zanci gaba da yimiki addu’a kema karki gajiya wannan ita ce ƙaddarar mu, yawwa ɗazu baffan ku Sunusi yazomin da maganar haɗin aurenki da ɗan uwanki Khamal…”
A firgice ta ɗago tace “Ni kuma Ammi habadai Khamal kin manta waye Khamal Ammi ƙungurmin ɗan taba sannan ɓarawon kaji da awakin unguwa ace shine mijina? A’a nikam wannan zaɓin baimin ba nidai a tayani da addu’a nasan Allah bai manta dani ba Ammi”
[6/2, 9:15 PM] AM OUM HAIRAN: *_JINKIRIN AURE_**_Ƙalubale ga ƴammata_*
*By*
*Oum Hairan*
*Dedicated to*
Dr. Mass @gadas son so for ever.
*Free P 3-4*
_Normal 300 VIP 600 PC 1k acct details 3184512451 Fauziyya Tasiu First bank._
Tashi tayi ta nufi ɗakinta ta cire kayanta ta nufi bayi ta watsa ruwa tayi alwala tayi sallar magrib ta zauna tana karatun Kur’ani tana sharar hawaye, a wannan yanayi taji an buɗe ƙofar dakin nata an shigo an nemi guri an zauna bata ɗago ba Saida takai aya sannan ta rufe Kur’anin ta shafa addu’arta ta juyo tare dayin kasa da muryarta cikin girmamawa tace “Yaya Mus’ab kaine a daren nan ga gari yanata cida alamun ruwa zai sauka”
Fasali yaja yana cire hularsa yace “To ya zanyi Madinah kece kinƙi barinmu mu huta Baffa Sunusi ne yaje ya dameni da maganar aurenki da Khamal kuma yacemin lallai kafin azumin bana sukeson ayi komi a gama shiyasa nazo naji meye kike ganin zai yuwu?”
Tunda ya fara maganar take kallonsa tana girgiza kai batare da ta katseshi ba har ya gama sannan tace “Yanzu Yaya Mus’ab wannan shirmen maganar har takai ka hana kanka kwanciya cikin iyalinka ka fito da wannan tsohon daren?”
Murmushi yayi yace “Kullum ke raayinki bambam yakesha da mutane Ni abinda yasa naga dacewar nazo mu tattauna naga ba duka abinda rai keso take samu ba musamman a wannan bigiran Madinah kinsani ni bana cikin mutanen da zasu kawo Miki mafita domin cutarwa a gareki, nayi ɗawainiya da rayuwarki tun yarinta kawo lokacin da kika zama mutum kike iya yiwa kanki abubuwa da suka shafi rayuwarki.
Inason ki tsaya ki ɗauko hankalinki ki tattarashi waje guda ki duba yanda rayuwar take tafiya kiyi hƙr ki karɓi wannan zaɓin kiyi addu’a wata ƙila shine alkhairin daya hana wani zuwa ke kuma kikaƙi karbarsa tun kina ƙarama”
Idanunta ta ɗago daya ciko da kwalla tace “Shikenan ashe dama idan Allah ya jarabci bawa da wata ƙaddara saiya manta da faɗin ma’aiki (S.A.W) da yake horonmu da mu zaɓawa ƴaƴanmu iyaye na kwarai, Yaya Mus’ab wanne ɓangare zan nuna idan na karɓi Khamal a matsayin miji nace shine alfahari na? Please Yaya Mus’ab na rokeka a matsayinka na gatan daka tsayawa rayuwata kayiwa girman Allah ka shigemin gaba wajen bijirewa auren Khamal baiyimin ba bayan haka Nima banyi masa ba Yaya Mus’ab abinda Khamal yake faɗa min kullum shine shifa duk da lalacewarsa yanaji a ransa taimakona zaiyi idan ya aureni saboda naje na zubar da darajata irin mazan da nakeso na tsaya ruwan idanu nayi musu tsufa bazasu iya aurena ba Yaya Mus’ab kullum haka yake faɗamin Ni ban kalleshi da aibinsa ba sai shine yake cusguna min da naƙasun da bani nayiwa kaina ba….”
Ɗaganta hannu Yaya Mus’ab yayi yace “Shikenan ya isa Madinah Allah yayi zaɓi na alkhairi yanzu ya batun komawarki karatun? Dr Shafi’u abokina yace akwai wata jami’a a Rasha da suke bada horo na musamman akan duk wata matsala data shafi ƙwaƙwalwa to ke kuma naga kinada interested akan wannan ɓangare shiyasa nace zanyi Miki magana ko zakije ki ƙara samun gogewa”
Ƴar ƙaramar dariya tayi tace “Shiyasa nake sonka Yayana duk abinda da zai kawowa rayuwata haske shine burinka Yaya Mus’ab Allah yaja kwana ya ƙara arziki, ka bincika min shi abinda tafiyar zataci da inason na biya kudin aikin hajji amma tunda hakane bari na tura gaba tunda dai Ammi tayi Ni daga baya naje nayi, Yaya nifa Research kawai akan abinda ya shafi brain yana mugun sani nishaɗi”
Dariya Mus’ab yayi yace “Autar Ammi kenan waye zaiƙi farin cikin Ammi ai dole mu ƙarfafa Miki gwiwa munyi waya ma da Khamis shima ya bada goyon baya Salees ne dai da Aminu suke ƙorafin wai mune mukeja ake zaginmu ana cewa mun ɗaure Miki gindi kina yawo da sunan karatu ni wani lokacin gwiwata har sanyi takeyi”
Kwantar da kanta tayi jikin bedside tace “kuyi hƙr No condition is permanent Ya Mus’ab wata rana sai labari Allah shaida ne bana aikata abinda mutane suke zargina dashi Yaya duk wata mace da wannan ƙaddarar ta faɗa mata dama sociaty dinmu kallon ƴar iska gantalalliya watsattsa sukeyi mata hatta da Allah ya hukunta zai aureta bayajin a ransa budurwa zai aura, nifa da wannan surutun da nakeja muku wlh ko za’a bani sadakin bazawara indai nagartar mijin takai gara na karɓa indai yayi albarka Shikenan”
Murmushi yayi ya miƙe cike da tausayin ƙanwar tasa yace “Insha Allahu komai zai wucce ki kwanta goma ta wucce gashi gobe talata” fatan alkhairi tayi masa ya fice tare da ja mata ƙofar ta miƙe tayi mata key ta shiga bayi ta dauro alwata ta kwanta daidai lokacin da aka kece da wani ruwa me ƙarfi ta kunna MP tana sauraron ƙira’a tare da tsunduma duniyar tunanin rayuwar baya.
Kamar yanda ta saba yauma ganin zata raba dare bacci yakasa ɗaukarta tana hasaso lkcn da zata kwanta kusa da mijinta ta tayi matashin kai da ƙirjinsa ta shafa sumarsa taja gemunsa, wannan rana ji takeyi dama zata iya kissimo irin nishaɗin da zata kasance dama tazo mata nan kusa dama zata buɗe idanu taga ba ita ce Madinan da abu ɗaya ya zamewa tsaiko cikin rayuwarta ba.
To wai meyene abinda ya zame mata katanga da samun abokin rayuwa ne? Tambayar da kullum takewa kanta da makusantanta kenan amma ta kasa samun amsa saidai ace mata tayi hƙr lokaci ne idan ta hƙr ta cire komai a ranta kuma sune waɗanda zasu fara cewa da ita “Madinah wai yaushe zakiyi aure ne?” Wannan tambaya tana dagula lissafin ta da ace mutanen duniya zasusan ƙuncin da take shiga a dalilin wannan tambaya da sun daina yi mata ita.
Zuwa yanzu abubuwa sun fara yi mata nauyi sha’awar kasancewa da namiji abokin ɗebe kewa tana yawan bijiro mata takan raba tsayin dare bata iya bacci ba saboda ciwon mara idan abin ya ta’azzara har fita takeyi daga hayyacinta sai likita ya tsaya a kanta sannan take dawowa daidai.
Sai bayan sallar asuba sannan ta koma ta kwanta bacci me nauyi ya dauketa dake yau ba itane da dutyn safe ba tanada isasshen lokacin bacci ba ita ta farka ba sai 12:21pm ta farka shima tashinta akayi ta buɗe idanunta kan Ƙawar tata kuma abokiyar aikinta Dr. Zahira murmushi sukayiwa juna Zahira tace “Tunda nayita kiran wayar ki najita a kashe nasan kinanan kina sana’ar saiki tashi mu fita inaso zaki rakani unguwa”
Miƙa tayi tare da salati ta diro a katifar Zahira tabita da kallo tana cewa “Kaga manyan mata masu manyan kaya matan me rabo wato Dr. Komanki abin sone ga kowanne lafiyayyen namiji wlh Ni kaina da nake mace halittarki na birgeni an baje fasaha wajen ƙeraki ke gani kin zamewa mazaje ƙwalele ya Allah karka kasheni sai naga wannan me rabo da zai huta da jikin nan”
“Amin ta amsa dashi tana shigewa bathroom ta sakarwa kanta ruwa ta sulla wankanta ta ɗauro towel ta fito ta tsaya jikin mirror tana shafa ta bata kusan rabin awa wajen shafa mai fesa turare gyara gira sannan ta koma ta ɗauki wata baƙar atamfa tasa abinka da kyakkyawar nandanan ta ƙara wani kyau na musamman ta ɗauki mayafi Milk kalar zanen jikin atamfar da takalminta da jakarta duk kalar mayafin ne ta dauki system nata da wayoyinta suka fice.
A tsakar gida suka ishe Ammi tana gyaran ƙumba ta dubesu tace “Ai dake kece kinga ta fito Zahira ni tun asuba rabona da Munau tanacan tana sana’ar bacci kamar kasa” dariya tayi har Saida dimpli ɗinta ya lotsa tace “Ayyah Ammi wlh banyi bacci da wuri ba jiya don Ni a yanda na kwanta ma sai biyu zan fita a gdannan to wannan uwar ƙwarzabar tazo ta tasheni wai zataje unguwa kuma saina rakata”
Tsugunnawa tayi tace “Ammi na tuba wlh na horu a taimakeni da key ɗin motar Allah bazan kuma bige kowa ba” harararta tayi zatayi magana tace “Wlh Ammi tsautsayi ne bazan kuma ba da abin hawan kafi kwarjini kinsan yanayin aikin mu…..”
Cilla mata mukullin tayi tana cewa “Yar ƙaniya jeki nikam Allah nunamin ranar aurenku na daina ganinku kuna shigemin gaba” addu’a ce Ammi tayi amma Saida ta sanyaya mata jiki, har suka isa kango jikin gidan nasu dake dama tun jiya tace da maigadin ya wanke mata motar shiga kawai sukayi ta sallameshi suka fice suka dauki hanyar asibitin da suke aiki.
Dr. Zahira ce ta kawar da shirun da cewa “Na fahimci kinsa damuwa kwana biyu a ranki Dr. Meye yasa Ni da nake bazawara bana damuwa kamar yanda kike damun kanki?” Dr. Madinah akwai arhar hawaye nandanan suka shiga zarya a idanunta ta buɗe ƙaramin bakinta tace “Saboda ke kin taɓa yi kinada yaranki ko yanzu kika mutu kinada masu ɗaga hannu suce Allah ya jiƙan Umman mu Dr. Ni banyi ba banida kowa sai Ammi, kwana biyun nan ta matsa da maganar aurena sai nakejin dama zan iya aurar kaina kodan na faranta zuciyar mahaifiyata”
Cikin tausayawa Dr. Zahira tace “Dole zata damu Dr. Ko kinsan yanzu a unguwar nan taku shafinki aka buɗe jiya Husain ƙanina yazo yake cemin wai ke meye ya hanaki aure ne? Na dubeshi da mamaki shine yake cemin yaji a majalissar Bala me Youghut anata zaginki wai karuwanci kikeyi har wani dillali yana cewa shi yama taɓa kaiki gurin wani mai gidansa…..”
[6/3, 7:14 PM] AM OUM HAIRAN: *_JINKIRIN AURE_**_(Ƙalubale ga ƴammata)_*
*By*
*Oum Hairan*
*Dedicated to*
Dr. Mass @gadas son so for ever.
*Free P 5-6*
_Normal 300 VIP 600 PC 1k acct details 3184512451 Fauziyya Tasiu First bank. Shaidar payment ta wannan number 09013718241_
Murmushi takeyi wanda da ka gansa kasan na ciwo ne irin wadannan ƙananun sharrikan suna damunta amma yanzu sun rage yi mata zugi a zuciya ta saduda tunda ita dai ta tabbatar da bata taɓa aikata abinda mutane suke kallonta dashi ba, ta sani Allah zai wanketa tsaf idan lokacin wankewar yayi.
Da wannan suka isa sukayi parking bata iya cewa komai ba suka fito kowacce ta wucce office ɗinta da wuri tayi ƴan aikace-aikacenta ta sallami petiant ɗinta yawanci duk waɗanda zasu ƙara karɓar magani ne da kuma ganin yanayin jiki dake azumi ta ɗauka yau ɗin sai uku ta fito daga nata office ɗin ita dama Dr. Zahira ta jima da tashi a aiki suka kuma ficewa, lalle sukaje da kitso Zahira aka yima kitso Madinah ba ma’abociyar kitso bace tafi ganewa ta gyara sumarta ta daure dake Allah yayi mata baiwar sumar.
Biyar suka ɗauki hanya wannan karon Zahira ke jan motar suka shiga unguwannin cikin gari ƙofar nasarawa sukaje wani gida Zahira ce ta kira wata number bugu biyu aka ɗaga suka gaisa ta sanar dashi suna ƙofar gidan yayi musu izinin shiga Madinah na mita tana cewa ta gaji da yawon zuwa gurin ƴan tsubbu da Zahira ke sata ita ta barta taji da damuwarta basai ta ƙara mata wata ba.
Da wannan suka shiga cikin gidan a aljihun zauren suka ishe babban mutumin malami ne babba da tarin littafai a gabansa yana duba wani littafi a hannunsa ya dago ya amsa sallamarsu tare da nuna musu gurin zama suka zauna da gaisawa Zahira ta fara yi masa bayani tace “Mal wannan ita ce Dr. Madinah wacce jiya na fara baka labari wato Mal wani abune me bam mamaki da ɗaure kai yake faruwa nikam abin yana bani mamaki matuƙa, Mal babu muni babu matsalar tarbiyya babu jahilci babu gigita ta talauci amma rayuwar taƙi tayi haske kullum cikin damuwa take hatta Ni kaina abin ya fara sani a damuwa, Mal mijin aure ya gagara ga Dr. Madinah gashi shekaru har sun fara nauyi kullum abu sai ƙara nisa yakeyi Ni raina ya fara faɗamin anya babu sa hannu ko na mutum ko na shaiɗanu?”
Zubawa Dr. Idanu yayi kanta na ƙasa tana wasa da yatsunta can ya numfasa yace “Allah ya shiga lamarin Madinah” shiru ta tsawaita can ya dago yace “Babu matsalar jinnu cikin lamarin nan kuma babu sa hannun kowa Madinah kawai lokacine baiyi ba amma insha Allahu zamu duƙufa tayaki addu’a Allah ya jinkirta zama ya kawo abokin rayuwa na kwarai yanzu abinda nakeso daku ga wata addu’a da zan baki yau daren Laraba ƙarfe biyu ki tashi kiyi alwala kiyi sallah raka’a huɗu kowacce ki karanta mata fatiha ƙafa ɗaya da kulhuwallahu 40 kowacce raka’a har ki idar kiyi istigfari adadin 100 kiyi salatin annabi ƙafa ɗari shima kina me tawassali ga Annabi Muhammad (S.A.W) bayan kin gama ki faɗi bukatar ki ta zaɓin miji na kwarai abin alfaharin kowacce mace sai ki rufe da istigfari 100 salati 100 saiki tashi ki koma ki kwanta kiyi haka na tsayin kwanaki bakwai bijahi Rasulullah sai Allah ya waiwayi lamarinki domin kin haɗa shi da wanda bazai iya juya baya ga bukatar wanda yaje masa dashi ba wato Muhammadur Rasulullah, Madinah idan kinyi haka duk abinda alƙibla ta nuna to dole ki karɓe shi koda kuwa ɗan uwan naki Khamalu ne idan kuma akasinshi ne to dama fatan da mukeyi kenan, aje a dage Allah zai duba buƙata”
Gdy tayi masa sosai suka ajiye masa sadakar Naira dubu goma suka tafi hakanan taji malamin ya kwanta mata domin a kalaminsa akwai tawali’u sosai cikin lamarinsa, suna tafe ne tafiya irin ta kurame can Madinah tace “Dole zan bar ƙasar nan cikin yan kwanaki Dr. Saurin cin birki tayi tace “What happen Dr. Madinah da zakice zakibar ƙasa bayan kinsan yanayin da muke ciki yanzun?” Numfashi ta sauke tace.
“Shine dalilin da zaisa nabar ƙasar Dr. Zahira yau ina zaune a office Baba Sunusi ya kirani zagin da yayimin akan nace banada ra’ayin aure da Khamal ko karen gidansa baitaɓa waba har yana kirana ƴar matsiyata taka hayen arziki……” Kukane yaci ƙarfinta ta rushe da kuka tace “Wai meye laifina ne da Alƙasim ya haifeni da Adiyyah? Dubanta Zahira tayi tace.
“Na dade da fahimtar family ɗinku kuna rayuwa a cikinsu ne kawai amma basa kaunarku Dr. Don Allah yau dai ki bani labarinki ko a takaice ne wala Allah ta yiwu inada rawar takawa Dr tun muna school of nursing na fahimci halin da kuke ciki amma abin baiyi tsamari irin yanzu ba don Allah Please Dr. Ba’a ɓoyewa abokin kuka mutuwa”
Ajiyar zuciya ta rinƙa jerawa sannan tace zan baki labari na Zahira kiyi hƙr tun a baya ba rashin cancanta ce tasa nake basarwa ba rashin lokaci ne yanzu kuma inada lokacin da zamuyi amfani dashi yanzu muje gidan Mama mu ɗauki izini saimu kwana a gdanmu”
Haka akayi gidansu Zahira suka fara zuwa Mama bata hanasu ba don tasan shakuwarsu musamman da sukace zasuyi wani aiki ne suka dungumo suka taho Sheka lokacin Ammi ta gama haɗawa autarta kayan shan ruwa suka baje a tsakar gida suka huta lokacin sallah yayi sukayi Saida sukayi Isha sukayiwa Ammi sallama sukayi shirin kwanciya dake katifar ta Dr Madinah babba ce by six ce me tudu, duban Dr Zahira tayi tace “kin shirya jin labari na?” Jinjina kai tayi Madinah tayi murmushi tace “kin shirya zubar da hawaye kenan zan baki labari kamar yanda kika buƙata amma idan bukata ta samu zan tashi” amincewar Dr Zahira yasa Madinah gyara zamanta ta kurɓi coffee ɗin hannunta ta fara da cewa.
*** *** *** ***
Madinah Alƙasim, shine cikakken sunana Wadda a yanzu duniyar likitoci musamman wanda suka shafi ƙwaƙwalwa a ƙasata Nigeria sukafi sani da Dr. Deenah, Mal Buba shine wanda yayi silar tsatsona domin shine ya samar da Alƙasim da ƴan uwansa Sunusi Nuhu da Kabir sai mata biyu Gwaggo Hajara da Yakumbo Harira, Baffana Wato Alƙasim shine daban a cikin biyar ɗinnan kuma shine ɗa na uku a wajen Mal Buba ya kasance Sunusi da Nuhu sune kawai a samanshi sauran duk ƙasanshi ne.
Mahaifina ya taso da rangwamen gata saboda mahaifiyarsa ta rasu ne tun yana shekara uku a dalilin haihuwar ƙanwarsa inda suka tafi tare ita da jaririyar data haifa, saiya kasance ruƙon Kasim ya koma hannu Inna Mai koko wadda ita ce uwar su Sunusi. Inna mai koko batason Kasim ko kaɗan hakan yasa suma yaranta suka taso da aƙidar ƙiyayyar Kasim inda shi kuma Mal Buba ganin yanda suke nunawa ɗan marayan zakin nasa kyara da tsangwama yasa ya ɗauki kulawa da soyayyar duniya ya ɗora masa.
Sai ya kasance duk inda zasuje tare suke zuwa dake Mal Buba bafulatanin Gwangola ne dake cikin taraba a yanzu ya taso da yawon kiyo da fatauci har kawo lokacin da girma ya fara riskarsa, yaso ya ɗora Babban ɗansa Sunusi akan wannan tafarki amma sai Innan mai koko tayi tsalle ta dire tace ƴaƴanta karatun boko zasuyi ba gantali ba shima da yake ya jima da zare lissafinsa akansu yasa yaci gaba da rainon Kasim akan harkarsa har Kasim ya saba fita kasashen Afirka shine Chadi Ghana Cameron Mali Senegal Togo kai dama kasashe da yawa na Afrika irinsu Rwanda da dai sauransu.
Daga baya ne kuma karatun bokon yaƙi ga ƴaƴan Inna taso su koma harkar fatauci abin ya faskara domin ba’a rainesu a cikinta ba Baffa Kabir ne kawai ya ɗan yi abin arziki lokacin da Mal Buba ya dawo ya zauna su kuma sukaci gaba da fafatawa a zahiri Kabir ba irin zuciyar yan’uwansa ne dashi ba shi yanason Kasim musamman yanzu da kusancinsu yake ƙaruwa suke yawon kasashe tare.
Kasim baiyi ilimin boko mai zurfi ba iyakarsa Firamare irin ta wancan lokacin bata yanzu ba amma yanada ilimin muhammadiyya fiye da yan uwansa dalilin da yasa komansa ya zama cikin nutsuwa da dattako, Wata shekara harkar kasuwancinsu takaisu Ethiopia a hanyarsu ta shiga garin Ethiopia ne sukayi kicibis da wani ayari na ƴammata sun dauko ruwa dake suna kusa da wani ƙauye ne.
Nan suka isa garesu suka rokesu su sammasu ruwa su sha su wanke fuska kasancewar tafiyar Sahel ga rana duk sun galaɓaita, sai waɗannan ƴammata sukaƙi basu wannan ruwa guda ɗaya cikinsu da tafi kowacce kyau ita ce ta tsaya bayan yan’ uwanta sun tafi ta basu ruwan nata sukasha sukayi alwala suka bata tulun ta juya ta koma.
Kasim ne ya dubi Kabir yace “Bantaba zuwa garinnan ba amma naji labarin abinda ke faruwa mubi yarinyar nan kada matasa su keta mata haddi” babu musu sukabi bayanta ilai kuwa batayi nisa ba wasu matasa su biyu suka fito cikin rairayin Sahel suka tareta sunayi mata dariya ɗaya cikinsu yakai hannu ya dumbuli nononta aikuwa ta ƙanƙame jikinta yana rawa tanayi musu magiya da yanayin tashin hankali kamota ɗayan yayi daidai lokacin da Kasim ya iso da sauri yakai hannu zai ƙwaceta suka kama kokowa da matasan har suna yankarsa daƙyar ya ƙwaceta a hannunsu y haɗata da Kabir shi kuma yaje ya ɗebo mata ruwan ya dawo ya ishe su tana ganinsa ta rinƙa murmushi da kanta tayi musu jagora har gdansu mahaifinta tsoho ne sosai shi kaɗai ne a bukkar tasu sai wata bukkar dake rufe a gefe.
Da mamakinsu sukaji yayi musu magana da fullanci suka amsa masa yayi musu tambayoyi suna bashi amsa can ya dago yace musu “Adiyyah tayi miji yau zan daura maka aure da matarka ka dauketa ku tafi” Saida gaban Kasim ya faɗi ya ɗago zaiyi magana ya ɗaga masa hannu yace “yaro tsayin lkc ina jiran zuwan mijin Adiyyah baizo ba sai yanzu ka bayyana tabbas kaine zabin da Allah yayi mata kayi hkr ka karɓi al’adarmu a yanda tazo maka zakaji dadi kuma zakayi alfahari da auren Adiyyah gatanan na baka ita halak malak bayan Ni baka da wani gata saikai daga bayyana yanzu”
Kasim baiso karbar wannan aure ba haka Kabir ya rarrasheshi aka ɗaura wannan aure Adiyyah tayi murna shikam Kasim sama-sama ce murnar shi a ranar kaka Hakeem ya bawa Kasim wannan bukka dake rufe wai ya kwana da matarsa shi kuma zasu kwana da Kabir, wannan shine asalin haɗuwar Kasim da mahaifiyarmu Ammi kenan.
Cikin ikon Allah watansu biyu a wannan ƙauye suna shiga cikin gari suyi sarinsu har suka gama ana saura kwana uku zasu tafi ne ciwon ajali ya riski tsoho Hakeem a daren ya rasu sarai Adiyyah taji mutuwar mahaifinta maiyi mata gata dake su can ba kamar mu ba basa zaman makoki kwana biyu da rasuwar suka dauko hanyar Nigeria birnin Kano kasancewar kasuwanci ya jima da dawo da Mal Buba Kano ganinsu da baƙuwar fuska yasa bayan Oyoyo akayi cirko-cirko ana jiran aji abinda suka zo dashi Kabir ne yayi masu bayanin komai Mal Buba ya jinjina lamarin ubangiji shi nan har yayiwa Kasim mata a can Gwangola ashe matarsa tana Ethiopia, shikam baija da lamarin ba Inna me koko ce dai a lokacin ta rinƙa faɗa tana cewa wannan ai irin tsiya da masifa aka dauko musu ƙasar da akace da karuwanci suke samun kuɗin shiga shine zaaje a kwaso musu don a lalata musu nasaba.
Shi kuwa Sunusi baƙin ciki ne kawai na ganin zukekiyar matar da ƙaninsa ya samu a sadaka yasashi ƙyashi da baƙin ciki gashi shi ya bige da yar tallan shinkafa da wake. Gidan da Mal Buba ya ginawa Baffa Sunusi nan yasa aka gyarawa mahaifina da mahaifiyata Mal Buba da kansa yaje kasuwar Rimi ya siyo musu katifa da pillow da duk wani abu da yasan zasu buƙata, aka fara rayuwa a wannan gida Jamila matar Baffa Sunusi da Indo matar Baffa Nuhu suka hadewa Ammi na kai ya zamana ko fitsari a dole Ammi na take fitowa girki kuwa kafin ta gama tayi kuka yakai sau nawa don sun rinƙa kallonta suna zundenta suna mata habaici tare da dariya suna cewa da ita karuwa matar cushe ko kuma su rinƙa cewa da ita yar cirani kayy har mayyah sunsha ce mata wai kyawun banza kyan ɗan maciji…..
[6/7, 8:29 AM] AM OUM HAIRAN: *_JINKIRIN AURE_**_(Ƙalubale ga ƴammata)_*
[…] Jinkirin Aure na Oum Hairan Hausa Novel […]