Littafan Hausa Novels

Ciwon Ya Mace Hausa Novel Complete

Ciwon Ya Mace Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

CIWON ‘YA MACE

 

By

Fadila Lamido

 

ADABI WRITER’S ASSOCIATION

 

GARGADI

Aguji daukan Labarin nan a daurashi a kowacce irin kafa batare da iziniba.

 

PAGE 1-2

 

BISMILLAHI RAHAMANIR RAHIM.

 

Hakika da na sani keya ce. Ko ma mene ne ni ce na jawo ma kaina da kaina. Gashi yanzu na rasa kwanciyar hankalina. Ko kofar gida ba na kaunar fita bare na je makaranta. Cikin gidan ma babu dadi komai ya da me ya lalace.

Dumin ruwan hawayen da ya sauka a kumatunta shi ya dawo da ita cikin hayyacinta, har ma ta samu damar sa hanun ta share hawaye. Kodayaushe cikin yaba tarbiyan gidansu ta ke, duk irin tsaurara tsaron gidansu ba ta kallon shi a matsayin takura, ahali ma sai hakan ya ke zamar mata abin alfahari.

Ajiyan zuciya ta yi mai karfi, sannan ta shiga tuna lokacin da ta yi ta ba wa Rahma damar sanar da ita duk wani zance komai muninsa da dacinsa.

Hawaye ta sa ke sharewa a karo na biyu, ta na me tuna furucin ta ga Rahma, “Zaman tare be ce haka ba Rahma. Domin ni duk abin da zan ji an fada a kan ki da ‘yan gidan ku sai na fada mi ki.”

“Yanzu me ki ka ga an yi ban fada miki ba? Ni ma din ai haka ne, babu wani abun da zan boye miki.”

Ni”imatullah Hausa Novel Complete

“Na gani a cikin kwayar idaniyarku wallahi. Na fa dago na ga irin kallon da ku ke mini, idan su za su mini haka bai da ce ace hardake ba. Amma ba komai.”

Yunkurawa ta yi da nufin mikewa Rahma ta yi saurin riko ta ta na cewa, “Shikenan na ji, da ga yanzu komai na ji zan dinga fada miki. Amma karkiji haushina.” Cikin sauri ta sa hannunta ta dafe kumatunta tare da runtse idonta ta na me jin zafi har cikin tsakiyar kan ta, dalilin tuna marin da ya zazzabga mata daren jiya.

Ji take kamar ta na jin a zabar marin har yanzu, dan haka hawaye su ka zobo mata.

Hannu ta mika ta share, sannan ta yi saurin mikewa cikin yanayi irin na mai tunani, komawa ta yi ta jingina bayanta da bango tare da kara yin zurfi cikin tunani, zuwa can ta shiga fadi afili, “Bansan yadda zan yi ba ne, domin ya na sama da ni, sosai na ke jin bakin cikin marin nan da yayi mini, a can baya ina amsan kowanni irin hukunci da ga gareshi, banajin zafi sam, saidai ma abin ya zamar min abin alfahari. Me yasa wannan karon ya sauya? Jiya da safe da hannun sa ya miko mini sakon Mamy, fuskar sa cike da walwala, zuwa dare komai ya sauya, saidai bana bakin cikin sauyarwa ta shi, domin yadda ya ke ji na a ranshi inajin shi fiye da haka a kasan zuciyata, domin da ina da dama ba marin biyu kawai zan mishi ba, saina mishi doka da ko lada aka bashi bazai iya mikewa ba, amman Kash sai daman yazo a hannun shi.” Nisawa ta yi a daidai lokacin da ta ji kiran da Mamy ta ke kwala ma ta, cikin yar karamar muryanta da bata fita sosai ta amsa, sannan ta fice ba tare da walwala ba.

“Nur! Lokacin fa yana kurewa, kizo karki makara.”

“Mamy ni gaskiya a canza min makaranta.” Wani irin kallo Mimy ta mata da mamaki akan fuskarta, sannan ta ce “Lallai Nur kina da aiki, idan an canza miki makarantar kofar gida ma zaki daina fita ne? Ko kuwa jama’ar unguwan ma zakibar haduwa da su ne?

Shirun da taga Nur ta yi yasa taci gaba da cewa “Bana son irin wannan, maza kizo ki wuce.” Cikin dakin ta juya batare da ta ce komai ba, a cikin kankanin lokaci ta fito fuskarta babu walwala.

Kallon ta Mamy ta sake yi a karo na biyu sannan ta ce “To ki saki ran mana, me zaisa ki takurawa zuciyarki bayan ke ce auta mowar ‘ya’ya” Murmushi ne ya subuce mata, duk yadda taso ta daure ta kasa, dariya ta yi kadan sannan ta hade fuska tare da cewa “Na tafi”

“Adawo lafiya Allah ya tsare. Kuma daga yanzu sai ki dinga kiyaye bakin ki, shi mai tarkon tsuntsaye baya É—aga kara. Kome zakiji karki tanka.”

Jin furucin Mamy ya kara tada hankalinta, cike da bacin rai tabar gidan.

Bayan ta dauki hanyar ma tafe take tana waiwayen bayanta har ta kawo kofar wani dandasheshen gida, duk unguwar gidan ne ya haska layin sabo da kyan sa da tsarin shi, karamar kofar da ke jikin get din gidan ta nufa, kai tsaye ta tura kofar ta shiga, mai gadin gidan ta gaida, sannan ta wuce ciki, a harabar gidan ta tsaya cikin daga murya tace, “Helen!” Batare data rufe baki ba wata buduwar yariya ta fito yar kimanin shekara goma sha 16. Baka ce amman ba can ba, kyakyawa ce sosai, uniform ne a jikinta riga da siket daidai guiwa, kanta babu dankwali yasha kananan kitsu, hannu suka sha da Nur da ke tsaye itama cikin uniform din ta ke, saidai akwai banbanci domin ita Nur siket dinta ya wuce guiwa, kuma bayan dankwalin dake kanta akwai dan karamin hijjabi, bayan sun sha hannu da Helen su ka juya suka fice a gidan.

Da alama gaba dayan su cikin damuwa su ke, domin gaba dayan su tafe suke suna tunani, suna daf da barin layin wata zungureriyar mota da ta fito da ga bayan su ta faka a gaban su. Tun kafin sukai ga inda motar ta faka Helen ta ce, “Poul ne”

Kallon motar Nur ta yi domin sai a yanzun ta dan ji nutsuwa tazo mata tun fitowanta gida, ita ko Helen da saurin ta ta karasa gaban motar, lokacin da Nur ta iso gurin yayi daidai da lokacin da yake mikawa Helen kudi. Kallonshi Nur ta yi ya na zaune a mazaunin driver, kyakyawa ne na gaske, domin sabo da kyanshi baka iya yi masa kallo daya ka cire Ido, sai dai akwai tarin jin kai tsiya a tattare dashi. Shigarshi akodayaushe kamar ta cikekken bahaushe, daker Nur ta iya dauke idon ta a kanshi badan ta gaji da kallonshiba sai dan kar ya fahimci tana kallonshi. Kasa ta yi da murya sannan ta ce ta ce “Ina kwana? ” Kawar da kai ta yi tare da runtse ido, sai dai harta bude idon be tankataba. Duk cewa Tasan yaji sarai amman be amsa ba. Bata ji mamakiba dan tun da ta ke gaidashi be ta ba amsawa ba bare ya dago idon sa ya dobe ta, saidai hakan be taba damun ta ba, kuma bata taba jin kyashin gaidashi ba aduk lokacin da zata ganshi. Wajen ta bari bayan ta kara gaba ta tsaye jiran Helen.

Wucewan motar ya sa ta waigowa ta kalli Helen, ita kanta fuskanta babu walwala, dan haka ta ce “Helen Duk da kyautan kudin da aka baki banga kinji dadi ba, kuma da alama ya bakine dan ranki yayi fari tunda har ya biyoki hanya ya baki, ni ai dauka nake ko ke baya iya gane ki, dan bantaba ganin ya kalleki ba bare yayi magana da ke, ni fa wallahi ada da farko na dauka kurma ne, sai ranar da nazo na ji yana balbala balaki a cikin gida, kuma har yau bantaba jin sa yana maganar arziki ba, idan har zakaji muryansa to fadane kawai.”

Murmusawa Helen ta yi tare da cewa, “Ko maganar arzikin ma yake haka zakijita kamar yaki, maganar sa babu yawa kuma babu dadi” Itama Nur dariya ta yi sannan su ka ci gaba da tafiya, bayan sunyi tafiya me tsawo Nur ta sake kallon Helen, rashin kwanciyar hankali karara akan fuskanta dan haka ta zungureta tare da cewa, “Helen wai me ke damun ki ne haka?”

“Badan mun yi nisa da gida ba da na koma na bawa Mama wannan kudin”

Lumshe Ido Nur ta yi, domin dama tatsuniyar gizo bata wuce ta koki, cigaba ta yi da tafiya tana cewa, “Ki boye idan kin koma sai ki bata.” wannan karon Helen ba ta ce komai ba, tun da ga lokacin har suka isa makarantar babu me ma wani magana.

Haka har suka tashi daga ita har Helen din basu da wani walwala, wadda duk wadda ya san su yana iya fahimtan hakan.

Helen ce ta fara shigewa gida sannan Nur ta isa na su gidan. Tana saka kafa a falon ta hangi shi zaune ya daura kafa daya kan daya; tare da ware hannun shi duk biyun a saman kujira. Tsoro ne ya so dirar mata, saidai wata zuciyar nacewa karki sake kiji tsoron sa, dan haka ta dake ta shiga kwalawa Mamy kira. Har sau uku ta kira bata amsa ba dan haka ta tabbatarwa kanta cewa Mamy bata cikin gida nan. Duk kokarin ta wajen ganin ta dake saida gabanta ya shiga faduwa, daki ta nufa saidai tana daf da shiga dakin ta ji ya kirayi sunan ta cikin kausarsiyar murya, “Ke Nur!”

Juyowa tayi ta na kallon shi, Ido cikin Ido suke kallon Juna tsawon lokaci, zuwa can ya fesar da numfashi cikin sanyin murya ya ce “Idan Mamy ta dawo ki tabbatar kin gyara abin da kika bata, idan ba haka ba kuwa zaman gidanan zai gagare ki.

Har ya gama zancen bata cire idonta akan nashi ba, ganin haka yasa shi kara kafeta da ido “Au kin tsaya ne kin kafe ni da ido? Na lura baki san waye ni ba, ni mugu ne ki bar gani na haka, Kuma karki yi abin da na gaya din ki gani. Me yasa zaki min haka? Nasan har yanzun zaki iya tuna lokacin da nake goya ki a bayan nan nawa na kaiki kitso. Idan an gama haka zan goyoki har mu dawo gida kina min kuka, rigana haka ya ke baci da hawaye da majinar ki, har yanzun ina mamakin ta yadda akayi irin wannan maganar ya fito daga bakin ki, basan baki da kunya ba sai jiya. Ashe ke din fitsarriya ce, ni sa’an kine ko nataba wasa dake ne?”

Tunda ya fara magana a wannan karon tai kasa da kanta, bata sake dagowa ba har yazun da yake mata tambayan, tana jin yadda yake kallon ta tsayon lokaci,acikin ranta take jin kamar bata kauta ba duk da cewa ba shirri ta mishiba sai dan girmanshi da mutuncin sa da take gani, muryan shi ta ji ya ci gaba da cewa “Ina jin ki? Me na miki kika tsane ni?”

Can kasa ta yi da murya sannan ta ce “Ni ban tsane ka ba kafin jiya”

Kafar sa da ya daura kan daya ya sauke, sannan ya mike tsaye ya fara takowa inda ta ke, tsoro ne ke son mamaye Nur, saidai tana ta kokarin ta na jawo ma zuciyarta dakiya, a gabanta ya tsaya sannan ya ce “Kafin jiya baki tsaneni ba? A cikin mu waye zai sha wuya da daya ya tsana daya?” Kafada ya daga batare da ya jira amsantaba ya ci gaba da cewa Wannan matsalar ki ce, amman ina son in san dalilin da ya sa kika min haka?”

Kasa ta kara yi da kanta yayin da jikinta ya fara rawa. Tuna azabar marin da ya yan-yan ka mata a jiya, a kuma gaban Mamy, yau Kuma gashi babu Mamy daga shi sai ita. Ganin yana matsowa ta fara ja da baya cikin muryan mai Shirin yin kuka ta ce “Yaya Abdallah karka mare ni, hannun ka akwai zafi.”

“Haba? Ashe akwai zafi? To kinajina? Da zaran Mamy ta dawo ki gyara abin da kika bata jiya.”

Kallo ya bita shi tsayon lokaci bata ce komai ba illa bugun zuciyarta da ke tsananta bugu, “Zaki yi abun da na ce ko baza ki yi ba?”

Mutsi ta fara da bakinta tsayon lokaci amman ta gaza furta komi, kula da hakan da yayi ya sa shi cewa “ina jin ki?”

“Yaya Abdallah cewa na yi Kaine ya kamata ka gyara ai”

Lumshe Ido ya yi zuwa can ya bude sannan ya ce “Shikenan, kijira abin da zai biyu baya, da kanki zaki gane maida ruwan rijiya ba barna ba ne, Kuma ke kin yi kadan ki ja dani, ki shirya ganin azaba, ukuba, zalinci, daga gare ni”

Zalinci Kuma? Nur ta yi tambayan tana me bude idonta a kanshi. Sosai take mamakin sauyarshi lokaci guda. Ayanzun gani take kamar wani ne aka sako ba waccen wadda ta sani a baya ba. Katseta yayi da cewa “Tambaya ki ke yi?”

Yadda ya zaro ido ya sata lumshe ido sannan ta ce “Yunwa nake ji zanje inci abinci.”

Hannunsa ya mika ya dungure mata goshi, kasancewar ta yi dafda bango hakan ya haddasa mata kumewa da keya, koda ya ga kanta ya hade da bango ta baya be hanashi kara dannan goshin nata ba, yana kara gurza mata kai da jikin bango, kokarin rike hannun shi ta ke amman ya ki ba ta daman yin hakan. Yana kara dannan kannata yana fadin, “Kin yi kadan ki dagula min lissafi, idan har kina son ki zauna lafiya a gidan nan kibini sauda kafa, ki kuma gaggauta yin abun da na fada miki, idan ba haka saina bata miki jikin ki da tabban duka, kuma wallahi saina saki kinyi nadamar zuwan ki duniya, sai kin fada da bakin ki ince ina ma ba’a haliccekiba.”

“Wayyo Yaya Abdallah ka sa ke min wuya na zan mutu.”

Kara danna kannata ya yi yana fadin, Da na yi farin ciki, me ake da irin ki, ki mutu mana, bana son in karajin maganar ki anan gurin. Hannun sa ya sauke a goshinta sannan ya d’ana mata shi a baki, ya bada sautin d’ass, cikin sauri ta runtse idonta, zafin da taji har cikin tsakiyar kwanyan kanta, har yanzun bata iya dawo da kanta ba, saboda wuyanta da ya kage, dan haka tai saurin sa hannunta ta dafe bakin tare da son taji ko hakorin wanni bangaren ne ya fita.

Hannun da ta dafe bakin yai saurin rikewa ya juyashi zuwa bayanta, sannan ya kamo dayan ya juya shi ya bada sautin kas, a wannan karon ta gama barma zuciyarta ta karye kawai. Hakorinta kuma ya fita, ga wuyanta da ya makale, zufane kawai ke yanko mata ko ta ina, bata sake wani yunkuri ba domin zuwa wannan lokacin sama sama ta ke jiyo azabar da ya ke gana mata. Yana murdeta yana aika mata tambayan zakiyi abinda nace ko bazakiyi ba, saidai ita ba sosai take jiyoshi ba.

Zuwa can taji yayi saurin sakin ta, galabaita da rashin karfin jiki yasata zubewa a kasa, cak ta ji ya dagata a tunaninta jifa zai da ita, amman ga mamakinta sai tajita kwance saman lallausan katifa.

[19/02, 7:04 pm] +234 806 396 6973: CIWON ‘YA MACE

By

Fadila Lamido

 

ADABI WRITER’S ASSOCIATION

 

 

PAGE 3-4

 

Muryarsa taji a saman kanta yana cewa, “Saura naga kafarki a falo”

Lumshe ido ta yi tana me jin kamar a wannan lokacin ne jinin jikinta ke sakowa, karan kofa ta ji sannan ta shiga jin muryan Mamy tana kwada mata kira, har sau uku ta ji ta kirata da ganan kuma ba ta sake jin kiran ba, bazata iya tantance iya adadin da ta dauka a wurin ba, bayan wani tsayon lokaci ta fara jiyo muryar mutanan gidan a falo, kanta dake mata nauyi ta dafe, daker ta iya daurewa ta tashi zaune, duk da cewa duk wuraren da ya yi mata mugunta radadi suke mata. Runtse idonta ta yi sannan ta mike tsaye, tun da ta mike bata kara sanin me take ciki ba, sai-dai jinta kawai ta yi rike gam a hannun mutum. Waigawa ta yi domin tasan waye ya ke rike da ita, Mamy ta gani tsaye, saidai tun kafin ta kai ga karantar fuskar Mamy ta jiyo muryar Abban su cikin fada sosai ya na cewa, “Mai ya yi zafi haka? Kina hauka ne? Ko tarbiyar da mu ka baki kenan?”

Jin irin furucin Abba yasa ta waiga ta kalli falon, fasassun kwalabe ta ci karo dashi barbaje afalon, yayin da Abba da Yaya Bashir suke binta da kallon mamaki, da ga can gefe ta hangi Yaya Abdallah zaune babu riga ajikin shi, yana ta duba damtsen hannunshi yayin da fuskarshi ke bayyanar da yana cikin tsananin bacin rai, muryan Abba ta sake ji yana cewa “Da ke na ke magana, wanne irin rashin d’a a ne wannan?”

Nan danan Nur ta kara rikecewa, cikin yanayi mai cike da nadama ta ce “Abba ka yi hakuri, bansan lokacin da nafito ba, a nan gurin kawai na ganni.”

Kallon sosai Abban ya kare mata, sannan ya ce, “Ko da wasa kada irin wannan ya sake faruwa.” hawayen da ya zubo mata tasa hannun ta share sannan ta ce “Toh Abba”

Hannu Abba ya daga mata alamar dakatarwa tare da cewa “Zo ki tsuguna ki bashi hakuri”

“Basai ta bashi hakuri ba domin nasan da abun da yai mata” Mamy ta fada ta na wa Abdallah kallon tuhuma.

Abba katse Mamy ya yi cike da fushi ya daga hannunshi yana cewa “Wannan be zama hujjaba, gaskiyar daya ce, ko an kita sai an bita za’a zauna lafiya.” Cikin gamsuwa da maganar Abba Mamy ta saki hannun Nur, ahankali Nur ta fara takawa harta isa gaban Yaya Abdallah ta tsuguna, hade hannunta ta yi wuri guda tare da fadin, “Dan Allah ka yi hakuri.”

Kamar jira ya ke ya mike tsaye batare da ya ce komai ba, rigarshi da ke gefen kujera ya dauka ya maida ita jikinshi sannan ya nufi hanyar dakinshi. Har yanzun Nur na tsugune bata motsa ba.

Ganin yana kokarin wucewa Abba ya ce, “Babana Nur ta na baka hakuri” Waigowa ya yi tare da sunkuyar da kanshi ya ce, “Bakomai Abba ya wuce”

Ya na shigewa hanyar da zata sadashi da dakinshi Abba da Yaya bashir ma suka fita, Nur kuwa zamewa ta yi tai zaman dirshen a wajen. Muryan Mamy ta ji ta ce “Tashi kije kicire kayan makarantar ki yi sallah sai kici abinci” Mikewa ta yi da sauri ta nufi daki kamar yadda Mamy ta ce haka ta yi, abincinne kawai ta ji sam bata sha’awarshi. Dan haka ta koma gado ta kwanta ruf da ciki, sai a yanzu ta cigaba da jin rikewar wuyanta da duk wani guri da Yaya Abdallah yai mata mugunta, da ga bisani ta shiga tuna irin fadan da Abba yai mata a yau, be taba mata hakan ba, a cikin ranta ta ce, ban kyauta ba sam. Hakan ba daidai bane, be dace ace ina fada dashi ba, kuma ba yau ya fara min hukunci ba. Mai ya sa zan mishi haka? Yana rike mutuncin shi, ko kadan bebar wata kafar da wani zai rainashiba, Yamin duk wani abu da ya kamata dan uwa yayiwa yar uwanshi, kafin jiya Ina alfari da Yaya Abdallah, da wuya ya taba lafiyar jikina kafin jiya, mai yasa zan mishi haka? Duka na kai mishi ko jifanshi na yi ne ban sani ba. Tunawa da ta yi da lokacin da ya mike ya na maida rigar shi ya maido da ita da ga tunanin da ta tafi, afili ta ce, Dole Yaya Abdallah yayi fushi, dole ya kasa magana, abin akwai mamaki.” Motsin da ta ji ya sa ta rike bakinta tare da kallon kofar, “Au kwanciya ki ka yi ba zaki fito kici abincin ba?” Mamy ta fada tana mika mata wayar hannun ta; tare da cewa Rahma ce”

Hannun Nur na rawa ta amsa kafin tasa wayar a kunnenta sai da ta ambaci Allah domin tun da Mamy ta ambaci Rahma gabanta ya yanke ya fadi.

Tana amsan wayar Mamy tafita tana cewa, “Ki na gamawa ki fito”

Wayar Nur tasa a kunnenta sai dai tsawon lokaci ta kasa cewa komai, acikin zuciyarta take ayyana sunan wadda za’a kira mata yau kuma, daker ta iya cewa,”Hello Rahma” Da ga can cikin wayar aka ce ce, “Yauwa Nur kinajina?”

Ajiyan zuciya Nur ta yi sannan ta ce “inajin ki”

“A cikin yan gidan ku waye baya gida?”

Wanni irin mummunan faduwan gaba ne ya sameta dan haka tasa hannunta ta dafe kirjinta tare da fadin, “Rahma mene ne kuma?”

“Ya na ga kamar a firgice ki ke?” Rahma ta fada ta na kallon cikin idon Nur.

“Bawai na firgita bane Yaya Bashir da Abba ne suka fita, su kadaine basa gida yanzu”

“Yauwa, zaki iya fitowa yanzun?”

“In fito in yi me? Rahma idan wani abu ki kajiyo a kan su kawai ki gayamini.”

“A’a kizo dai kikagani da idonki shi zaifi”

“Kina ina yanzu?”

“Ina cikin gari yanzu haka, ke kadai nake jira”

Cikin rike cewa Nur ta ce, “Ai ya yi nisa bazan iya zuwa ba Rahma, Mamy bazata barniba, tun da ga nan Kabala har cikin gari? Tafiyan akwai nisa ki gaya min kawai mene ne?”

“Nur toh zan taho ki yi kokari mu hadu a makabarta yanzun nan”

Sauke wayar ta yi batare da ta iya amsawa ba, saukowa ta yi a gadon ta na tunanin yadda zata yi tabar gidan, hijjabin sallah ta dauka ta sanya sannan ta fito falon gidan, wata zuciyar ke bata shawaran ta fice kawai wata kila har ta je ta dawo Mamy ba ta fito ba, saidai ta kasa yin hakan sabo da rashin sabawa da fita ba’a sani ba, juyawa ta yi ta nufi dakin Mamy, ta na tura kofar ta gansu ita da Aunty Saratu da alama wata mgn su ke mai mahimmancin domin su na jin an turo kofar suka yi shiru tare da waigowa suka kalli kofar.

Cikin dakin ta karasa tare da kirkiro murmushi ta ce, “Mamy zanje gidan su Rahma in amso littafina”

“Zaki gidansu Rahma ku je gidan su Helen zakice mini, Kinga Nur ku raba kan ku da gidan yaron nan, domin wallahi miskili yafi mahaukaci banhaushi, na san ku gani ku ke besan me ku ke ba, toh bari kiji, na gaya miki ko be kalle ku ba ya na kare mu ku kallo ta gafen idonshi, ranar da ya gama raina wayonku, zakusha mamakinshi.

Duk da cewa Nur ta na cikin damuwa sai da ta yi dariya sannan ta ce, “Ba abun da zai mana Mamy, aishi jarabar shi akan Mama da Helen yake sauke ta, ko muna cikin gidan be ma kallon inda muke.”

Aunty Saratu ce ta ce “Waye dama ya ce miki zai kalleku, shi da be kalli babba bare yara, ai Poul be da mutunci ko kadan, yaron da be wuce sa’an Bashir ba amman jira ya ke ka gaidashi.”

Karaf Nur ta ce, “Aunty ko kin gaidashi ma baxai amsa ba, karake mgnr ta yi tana kallon Mamy sannan taci gaba da cewa “Mamy na tafi yanzu zan dawo” Mamy nabin bayanta da kallo ta ce “Ku dai bi ahankali wallahi.

“Cikin d’aga murya Nur ta ce “Mamy wallahi bacan zamu ba”

Aharabar gidan ta ga motar da Yaya Abdallah ya ke hawa, amma babu motar Abba kuma tare da Yaya Bashir suka fita, cikin sauri take tafiya, acikin zuciyarta take cewa,”Yau Kuma me zan gani da idona bayan jiya na ji mummunan labari da ga Rahma, a jiya na yi mugun ji yau Kuma zan yi mugun gani kenan? Koma mene ne nasan ba abun Alheri ba ne, idan ina ganin laifin Yaya Abdallah Yaya zan yi kuma idan idona ya gano min aibun wani bayan Yaya Abdallah, tsayawa ta yi cak ta na kallon gidan na su tsayon lokaci sannan ta ce “Me za’ayi agidan nan anjima bayan naje na dawo? In je ne ko kada na je? Rasa wadda zai amsa mata yasa ta kara kallon gidan sannan ta fice da saurinta.

Tana isowa bakin layin su ta tare me mashin tahau, saidai har suka dauki hanya kirjinta bebar dukan uku-uku ba, da ke mashi ne nan danan ta fara hango makabartan, dan haka ta shiga raba ido, a wannan lokacin duk ta manta da wani ciwo da jikinta ke mata, da ga can gefen makabartan ta hangi Rahma tsaye, tun da ga nesa take kare ma wajen kallo babu kowa tsaye a wajen sai Rahma sai tarin motocin da mashinnan dake wucewa. Agogon da ke daure a tsintsiyar hannunta ta duba, karfe 04:45pm ta gani, dago kanta yayi daidai da isowan su inda Rahma ke tsaye dan haka ta tsayar da me mashin din.

Sauka ta yi akan mashin din, sannan ta biya kudin, in da Rahma ke tsaye ta nufa tana me cewa, “Rahma men ene?”

“Ni yau sai na ga duk a firgice kike Nur, inason in kara nuna miki abu nagaba ne bayan wadda na gaya miki jiya, in dai kin amince da hakan?”

“Hmm na amince mana Rahma, ai ni tun da kika gaya min jiya na yadda, saidai na yi tsananin mamaki dan ba ma ni ba har Mamy ta yi mamaki sosai. Kuma ta yi mai fada sosai, ina sa rai hakan bazai sake faruwa ba, dan ya ji kunya sosai, harma ya rasa bakin magana, Sannan ciwon Mamy ya tashi adaren, hakan ya kara mishi damuwa sosai, abun na damun shi har yau, nasan zai gyara in sha Allah.”

Lumshe Ido Rahma ta yi sannan ta ce “Yanzun kina son ki gannin ma idon ki ko kuwa?

Me zan gani?, Kina son kice min bayan Yaya Abdallah akwai Kuma wani me yin abun dabe dace ba agidanmu?

“Bance ba, ina magana ne akan shi Yaya Abdallah din.”

“Me zaki nuna min to akan shi? Kin ga Rahma karki raina min hankali, abin ya isa haka, Yaya Abdallah kamilin mutun ne duk jama’ar unguwarmu zasu iya bada shaida akan haka, waccen ma ina kyautata zaton akasi aka samu, duk gidanmu bayan Abba babu me kamun kanshi, idan an kamashi da wani laifi bashi zai baki daman da zaki dinga yi kowanni irin magana akanshi ba.”

Jikin Rahma a sanyaye ta ce “Ki yi hakuri Nur sabo da gudun irin wannan ya hana tun farko na gaya miki, yanzu ma dan na ga kin nuna kina son ki sani ne, Kuma ke kika bani damar sanar dake duk wani abu da zanji akan gidanku, Dan haka nasan wani abu kan Abdallah, amma tun da kince haka shikenan mubar kaza cikin gashin ta.”

Baki Nur ta lashe sannan ta ce “A’a inajin ki?”

“Idan kin amince kizo muje naf club ki gani…”

“Ina ne haka?” Nur ta tambaya bayan ta tsurawa Rahma ido.

Daya ne da ga cikin wuraren shakatawa mafi kyawun otal a kaduna, naf club ya na da wurin shakatawa. Dakunan suna da kyau saidai suna kusa da mashaya, waje ne wanda wani lokacin ya ke zama da hayaniya musamman da daddare, abincin gurin na da kyau, akwai dakin motsa jiki, da filin wasan. Akwai zauren taro. kuma wurin gabaÉ—aya yana raye komai dare…”

“Ina ruwana da kyawun gurin ko rashin kyawunshi, ni kawai ki gaya min me zamuyo acan din?”

“Yaya Abdallah zan nuna miki.”

“Rahma Yaya Abdallah ya na gida be je ko ina ba wallahi, can na baroshi a gida, bashi ki ka gani ba. Dan a gidama na same shi Kuma har na fito dinan ya na gida.”

“Shine Nur, baya gida, kuma idan kinzo munje zaki tabbatar da hakan.”

“Shikenan muje” Nur ta fada tare da tare me keke, shiga suka yi tare da gayawa mai keken in da za su, Ko da suka kama hanya babu me ma wani magana.

Misalin karfe 05:10pm su ka sauka agaban shararren Otal din, Rahma ce agaba Nur na binta a baya, tafe take tana waige-waige sabo da rashin sabo da shiga irin wannan wajen, Rahma ko ajikinta ta kama hanya tiryen-tiryen ya yin da Nur ke daura kafarta a in da Rahma ta cire tata, bayan sun shiga harabar wajen ne kuma suka rasa hanyar da zasu bi, da ga can babban kofar da tazamo nanne mashigar gurin suka hango maza da mata suna fitowa, dan haka Rahma taja Nur su ka boye a bayan wata mota, cigaba suka yi da kallon masu fitowa da ga ciki tsayon lokaci domin gudun cin karo da idon sani, ganin kowa na harkokin shi wasu na shiga wasu na fita ya sa suka fito daga bayan motar.

Nur ce tabi wajen da kallo sosai, tun da ta ke bata taba zuwa irin wannan wajen ba, tsoro ne karara akan fuskarta yayin da yanayin ta gaba daya yake cike da daburcewa, musamman ganin da ta yi ita kadaice aduk wurin take sanye da zunbulelen hijjabi har kasa, kallon Rahma ta yi gyale ne ajikinta, haka duk mutanen da suke wajen ko kusa babu me shiga irin tata, dagowa tayi ta kalli Rahma ta ce, “Rahma mubar wajen nan be dace damu ba”

“Ki Bari mu shiga ciki ki gani.”

Gaskiya ni bazan iya shiga ciki ba, hannunta ta dago ta kalli agogon batare da ta ce komi ba ta fara tafiya ta nufa hanyan ficewa daga Otal din, sauri take yayin da Rahma tabi bayanta tana Kira “Nur! Ki tsaya mana.”

Jin wata murya ta kira yi sunanta wadda ba na Rahma ba yasa ta ja ta tsaya cak, namiji ne ya kirayi sunan nata sai dai ta rasa gane ko wanene dan haka ta waigo da sauri.

Ido hudu suka yi da Auwal, abokin Yaya Abdallah ne kut da kut, kallo take kare mishi kamar yadda shima yake kare mata kallo, ganin yadda ya ke kallon ta ya sa tai saurin kallon jikinta.

“Me kike anan gurin Nur?”

Cike da kidemewa ta ce, “Babu komai” tafiya ta fara dan haka ya ce, “Zonan!”

Nur na jin haka ta cire takalmanta ta kwasa a guje, ganin haka Rahma ta rufa mata baya tana me kiran sunanta, saidai ko da wasa Nur bata tsaya ba. Aguje ta nufa titin tana kokarin tsallakawa, shiko Auwal kiran sunan Nur ya ke tare da bata Umarni tsayawa, amman ina Nur gudu kawai take.

Tsintan kanta ta yi dirshen zaune akasa, a wani layi me shiru sosai wadda bata iya banbance ko inane, layin ta kalla babu kowa sai gidaje masu dan karan kyau, cikin sauri ta mike ta fara tafiya, banda haushin karnuka babu abun da take jiyowa cikin unguwar, dan haka hakalinta ya kara tashi, kokarinta kawai ta ga titi domin ta samu motar unguwar su, ganin ta yi tafiya me tsayo bata samu babban titin da zataga motocin haya ba ta fara zubar da hawayen dana sani. Da ga bayanta ta ji tahowan wata mota da mugun gudu, cikinta ne ya kara murdawa domin ko tantama ba ta yi ita ake bi da motar, yin wannan tunanin ya kara sata diriricewa tare da ja da baya tana kallon motar domin daf take da ta isowa gareta.

2 Comments

Click here to post a comment