Littafan Hausa Novels

Bakar Kaddara Hausa Novel Complete

Bakar Kaddara Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

BAK’AR K’ADDARA

 

 

 

NA RUMAISA ALIYU INUWA

 

 

 

*ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION*

{R.S.W.A}

 

https://www.facebook.com/Royal-Star-Writers-Association-101607075594165/?ref=py_c

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

 

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

 

 

 

 

 

*77-78*

___________________Kamar yadda tayi a farkon fitowarta gida haka wannan karan ma,tafiya take bata sanin inda take jefa k’afarta,tin bayan Magriba take tafiya har zuwa isha bata zauna ta huta ba,sai ma ji taka kamar ana janta,tin tana bin hanyar da mutane suke kai kawo har ya zamto ta shiga wata hanya wadda da alamu bayan gari ne,dan babu koma sai motsin halittun da sai dare suke karakaina,

Bakar Mace Hausa Novel Complete

Abar tausayi ga duk wani mai zuciyar imani idan yaga BAHIJJA saiya tausaya mata,tana so ta huta amma babu hali da tayi yunk’urin zama ko fad’uwa sai taji kamar an taro ta ana ingizata,yunwa kuwa da k’ishin ruwa sun mata dafifi.

 

 

 

In tak’aice muku dai BAHIJJA cikin daji ta nufa babu gida gaba babu gida baya,sai da tayi tafiyar Awa biyar sannan ta yanke jiki ya fad’i a cikin ciyayi,ko motsi bata iyawa sai nishi sama-sama,a haka garin Allah ya waye mata tana sume,saida iskar Asbahi ya kad’a sannan BAHIJJA ta farfad’o daga suman wahala,abin tausayi k’ara mik’ewa tayi taci gaba da tafiyar cikin galabaitar k’ishi da yunwa.

 

 

Allah sarki baiwar Allah BAHIJJA,Allah ya saka miki.

 

 

 

Su Gwoggo kuwa haka suka k’ara yini ba tare da anji labarin BAHIJJA ba,jami’ai suna iya bakin k’ok’arin su akan wannan case d’in,amma shuru babu labarin wanda ma ya ganta balle a tambaye shi inda yaga ta nufa.

 

 

Gwoggo ta rame lokaci guda,ta zama abar tausayi,kukanma yanzu baya fita sa bo da babu hawayen,sai dai kukan zuci.

 

 

Sady Baby kuwa Allah-Allah take gobe tayi ta nufi garin Abuja,dan bata raba d’ayan biyu Hajiya Zina zata iya sawa a sato mata BAHIJJA,dan ita kad’aice abar zarginta.

 

 

 

Baba kuwa Sallah ce kawai take tsayar dashi ga neman d’iyarsa dan baya fidda ran idan ya fita zai iya ganinta,ya zama wani iri lokaci guda,sai hango fara’arta da yadda take shagwab’a idan suna tare,k’wallar idonsa yake gogewa lokaci zuwa lokaci,yana mata Addu’ar kariya a duk inda ta samu kanta.

 

 

 

Rayhan kuwa sai 12:00 na dare ya dawo yayi wujiga-wujiga da shi,dan ko abinci baici ba tin safen nan,ko yunwarma baya ji,dan burinsa kawai yaga BAHIJJA,haka ya dawo gida,ya taradda Mami zaune tana zulumin inda ya tafi,aikuwa tana ganinsa ta saki ajiyar zuciya,inda take ya zo ya zauna,

 

“Rayhan ina ka tafi?” Mami ta tambaya.

 

 

“Mami neman BAHIJJA na tafi,amma ban ganta ba” ya fad’a cikin rauni.

 

 

“Rayhan muyi mata Addu’a za’a ganta da izinin Ubangiji,komai zai zo da sauk’i,yanzu bari na sama maka Abinci kaci kafin ka kwanta”.

 

“A’a Mami bana jin yunwa”.

 

Bata kula shi ba ta shige kitchen ta zubo Abinci ta kawo masa,da taga ba zaici ba IATA ta dinga bashi,har saida yaci rabi sannan ya ce mata ya k’oshi,Lemon exotic ta tsiyaya masa ta bashi yasha,sannan ta umarce shi da yaje yayi wanka ya kwanta,amsa mata yayi ya tashi ya shige side d’in sa,sai da yayi wanka sannan ya kwanta,amma fafur bacci yak’i zuwa masa sai tunanin rabuwarsu da ita yake,bayan ta sanar masa tana son shi sannan zatai nesa dashi,bayan ya k’wallafa rai akanta,”to ko dama akwai masu bibiyar rayuwarta ne?”, ya fad’a a fili ,gyara kwanciya yayi ya kalli saman bedroom d’in,hango murmushin fuskarta yake,yana hango yadda take komai cikin nutsuwarta, “kina ina Bahy?” ya fad’a yana jin suya a ransa,ranar dai bacci b’arawo ne sace Rayhan.

 

 

 

 

B’angaren Amarya Khad kuwa an kaita tamfatsetsan gidanta dake garin Abuja,su Mommy da Ameera ne suka tarbesu,dan dama tun safe suka nufo gidan Khad d’in dan tarbarsu,sun dafo abinci mai rai da lafiya dan ‘yan kawo Amarya,lokacin da aka kai Khad tana ganin Ameera ta tafi ta rumgume ta tare da sakin kuka mai tsuma rai,ita dai Ameera tasan Amare suna kuka,amma ba irin wannan ba,sai dai idan da wani abin,ko Amaryar bata son Mijin dole akai mata,kuka take sosai tana rik’e da Ameera,ita ma Ameeran kukan ta saki dan bata san me zata ce ba,Mommy kuwa tunaninta kukan rabuwa da gida kawai Ameera take,sai da taga su kansu ‘yan kawo Amaryar jikinsu a sanyaye yake sannan ta fahimci ba lafiya ba,kamo Khad tayi ta zaunar da ita sannan kowa ya zauna,Mommy ce ta kalli K’anwar Mami wato Aunty Yana ta ce “Yana wai lafiyarku kuwa?,naga duk kunyi wani iri”.

 

“Mommyn Meera Wallahi muna cikin alhinin b’atan K’awar Khadija ne,tin jiya har muka tawo babu labarinta,shine take ta kuka tin jiya” cewar Aunty Yana.

 

 

Sai a lokacin Ameera ta kalli ko ina ta ga babu BAHIJJA babu Adabiyya kallon Khad tayi ta ce “Khad ina su BAHIJJA da Adabiyya?,naga basu zo ba,kuma wacce K’awar taki ce ta b’ata?” Ameera ta jero wad’annan tambayoyin cike da tsoron kar ace mata d’aya daga cikin su BAHIJJA ko Adabiyya ce,ai bata gama adana tunaninta ba taji kamar almara ance “to ai BAHIJJA ita ce aka nema aka rasa” cewar wata daga cikin masu kawo Khad.

 

 

“Innalillahi wa’inna ilaihirrajiun” cewar Mommy,yayinda Ameera kuma ta mik’e tsaye tana jujjuya kai ” BAHIJJA fa,Bahijja kuke nufin ba’a gani ba” ta fad’a tana d’ora hannu aka.

 

 

Dawowa tayi kusa da Khad ta dafa ta tace “Khad ki fad’an gaskiya da gaske BAHIJJA ce ta b’ata ?” Da alama Ameera a rud’e take dan abin ya doke ta sosai.

 

Kai Khad ta a gyad’a mata,aikuwa nan ta durk’ushe ta sanya kuka mai tsananin cin rai,wanda Mommy da kanta sai da tayi mamaki,ta san dai Ameera tana da tausayi,amma taga damuwarta akan b’atan Yarinyar yana da girma,nan fa aka dawo bawa Ameera baki,fad’i take ” yanzu ina BAHIJJA take?, shin wane ya sace ta?,me tayi musu?, Wallahi na tabbata wasu ne suka sace ta” fad’a take tana kuka,kowa sai da yaji tausayin Ameera.

 

 

Labarin yadda abin ya faru suka bawa Mommy,yadda Gwoggo ta sanar musu haka suka sanarwa Mommy,abin ya tab’a Mommy sosai,haka akai jugun-jugun sai da Mommy ta k’arfafa musu gwiwa akan cewar za’a ganta da yardar Ubangiji,Ameera kuwa lokaci guda tayi sanyi k’alau,Khad ma haka,haka suka k’ara shirya Khad sannan suka bata shawarar yadda zata rayu da Mijinta cikin ilimi da tarairayarsa,sai k’arfe biyar na yamma suka barota tana ta kuka,gidan su Ameera suka nufa dan anan zasu kwana washe gari su koma Kaduna.

 

 

 

 

 

Rabi Tifa sai da suka gama tantil batetensu sannan suka saduda,bayan ta sallami farkan nata,wajen karfe 10:30 na dare sannan ta tuna tabar Yarinyar mutane a D’aki babu abinci,aikuwa tana fita ta shige D’akin abin mamaki ko k’urar Yarinyar bata gani ba,tsoro ne ya kamata ko Gaye ya sad’ad’o ya d’auke ‘yar mutane yaje ya b’ata mata rayuwa,nan ta fito nemanta take kamar me,tana cikin dube-dube Gaye ya shigo, “ke kuma lafiyarki sai dube-dube kike a tsohon daren nan?”.

 

 

“Gaye ina kaki ‘yar mutane?” abinda Tifa ta fad’a kenan tana masa kallon tuhuma.

 

 

“Wace kuma mai wannan sunan wai ‘yar mutane,dama akwai masu wannan sunan?” Shima ya jefo mata wannan tambaya.

 

 

“Gaye duk abinda kake ji dashi kasan na fita,wallahi koka je ka dawo min da Yarinyar nan ko kuma nayi maka rashin mutunci wallahi,kai baka duka halin da take ciki,ba tada lafiya fa,gata k’aramar Yarinya ce,dan dai kawai tana da jikin girma ne,amma sa bo da rashin tsoron Allah shine zaka d’auketa kaje ka keta mata mutunci”.

 

 

“Ke dallah fita dani daga wannan haukar taki,kinsha ta miki karo shine zaki juye rashin mutuncinki a kaina,to Wallahi zan miki hauka,haka siddan kizo kinai miki zancen bara kaci wake,ban san me kike magana a kaiba,to ki bani hanya kona fasa miki tumbi da wannan bagobirar billahillazi” ya fad’a yana zare ido.

 

 

Nan ta tabbatar bai d’auki BAHIJJA ba,dan daya aikata to bazaiyi shayin fad’a mata ba,haka ta matsa masa ya wuce yana harare-harare,fita Rabi tayi saida ta duba ko ina ba taga BAHIJJA ba sannan ta dawo duk jikinta ba dad’i,dan taso ta cigaba da taimakonta har zuwa sanda zata dawo hankalinta.

 

 

 

Allah ya baki ladan niyya Rabi Tifa.

 

 

 

 

Adabiyya bayan ta koma gida ta sanarwa Iyayenta nan suke sanar mata sungani a tv,suka yanke shawarar gobe zasu je suyiwa Iyayen BAHIJJA jaje,haka Adabiyya ta kasance cikin rashin kwanciyar hankali na b’atan K’awarta kuma Aminiyarta.

 

 

 

Ubangiji ya had’amu da Aminai na hak’ik’a wanda zasu damu da damuwarmu,su tayamu kuka,sannan su taya mu farin ciki,allah kayi mana nesa da k’awayen da ba sa bo da Allah suke tare damu ba,sai dan wata baiwa tamu ko kuma dan su dinga yi mana zagon k’asa,ubangiji ya hadamu da Aminai shak’ik’ai ameen🤲🏻

 

 

 

*BAHIJJA*

Daji take ta kurd’awa ga zafin rana da yunwa da k’ishirwa,tana matuk’ar shan wahala sai k’iran ruwa take amma babu halin tsayawa ta sha dan ta wuce k’oramu da yawa amma sai dai ta wuce bata san ya zatai ta tsaya ba,can bayan lafawar rana ta shiga wani waje da fili ne fetal,sai dai da alama akwai mutane a wajen,tana cikin tafiya wata murya garjejiya ta buga tsawar da saida BAHIJJA ta fad’i k’asa,wasu mutane ne suka duddurgo daga saman bishiyu,kina ganinsu sai kin saki fitsari,dan timb’ir suke sai ganye da suka rufe al’aurarsu da ita,zagayeta sukai suna zazzare ido suna wani irin ihu,tare da wani irin yare wanda ban tab’a jin irinsa ba,haka suka zagayeta suna maganganunsu masu kama da ihu,ita dai tana kwance inda ta fad’i tsoronsu ya sanya ta k’ara sumewa.

 

 

 

Wannan kenan

 

*Alk’alaminmu’Yancinmu*

 

 

*(By Rumy)*

Add Comment

Click here to post a comment