Littafan Hausa Novels

Auren Zobe Hausa Novel Complete

Auren Zobe Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Auren zobe

Sadiya Musa Rimi

1

Cikin yanayin lullumi na shigowar daminar wannan shekarar,motar mulmulalliya Mai azabar kyau da ta dauko gudunta tun daga cikin garin Abuja har zuwa nan birnin Kanon dabo,bata kuma tsaya a koina ba har zuwa lokacin da motar ta yanke daga cikin garin har zuwa Kan babban titin Maiduguri road inda ta miqe sambal tana kwarara gudu har zuwa Kan titin Takai dake nan Kan babban titin na maiduri road din.

A hankali motar ta sauka daga Kan babban titin ta karya kwana daga Kan titin Takai zuwa Kan titin daya dauka daga nan har cikin garin Rimi,tun daga nan Suka Fara daga hannuwa suna gaisawa da jama’a cike da Jin dadi da annashuwa, “there’s no place like home”matashin saurayin dake tuqin ya fada cikin muryarsa Mai dadi da nutsuwa.

Daga nan bakin reka ya tsayar da motar suka gaggaisa da jama’a ana mishi barka da zuwa daga nan Kuma ya miqa da motar zuwa cikin gari suna tafe a slow duk inda Suka wuce sai sun gaisa da jama’a rumfa rumfa yake bin mutane suna gaisawa har zuwa qofar Arewa nan cikin kankare.

Rumfar nan ta Baba Sarki ta dame da dattijai an futo anyi zaman la’asar ga wanzan nan a kusa Kamar yadda ya Saba Koda yaushe Baba Sarki Yana ajiyeshi sabida samari masu tatin Suma a kansu ko yara qanana,kowa yasan da zamanshi babu saurayin daya Isa yayi kankarekansa da suna yanzun nan kaji Baba Sarki ya kirashi an saka wanzan yasauke Mai gashin Kan Baki dayanshi.

Sanadin Yarenah Hausa Novel Complete

Kankaran nan ya cika tatil da matasa tamkar wani dan siyasa ya sauka haka matasa Suka taso,cike da farin cikin Malam Basiru yace “dan halak kaqi ambato,ana maganarshi sai gashi ya sauka”

Murna da farin ciki a zuciyar sarkin noma Kamar ya taka Kan Dan mutum,qaunarshi da Yusuf din daban ceaduk cikin yaranshi,Yusuf ya futo daga cikin motar dogon saurayi sankacece kyakkyawan daya gaji da haduwa,Kuma aka gogeda ilimi na zamani da nagartar data hadu da tarbiya irin ta manyan iyayenmu na karkata, sai Mahmud daya bude daya bangaran shima ya futo,ingarman namiji gogaggen bakatsine tsayinsu da Yusuf Kamar an suna da tip kafin a sasu abota da juna.

Cikin matasan Yusif din yatsaya,cikin yanayin shigar shi ta shadda gezner dinkin matasan birni Wanda suke sanye dashi dashi da Mahmud din kala daya kamaryadda Suka Saba,a tsakiyar matasan ya tsaya suna gaisawa Mahmud ko rumfarsu Baba Sarki ya nufa fuskarshi dauke da murmushi.

Gaba daya suke amsa sallamar Mahmud din Baba Sarkin ke cewa cikin barkwanci, “kowa yaga Zara zai ga wata,ga hanta da Jinin baba Sarki sun sauka lafiya a gida”bariya Baki dayan datyijan sukesuda Mahmud din da tluake kallan Baba Sarkin tamkar mahaifinsa.

Da haka Mahmud din ya risina yana gaidasu, Baba Sarki ya danqe hannunsa cike da qauna suna gaisawa yace “bamu saka rai da ganinku ba ganin yau Talata sai gaku Kuma Kun shigo Mana”.

Mahmud din da murmushin sa yace “wallahi Baba hutu muka dan samu shine mukace gara mu shigo gida a gaisa tun da mun kwana biyu bamu shigo ba”.

Dai dai nan Yusuf din ya qaraso shima ya shiga gaisawa dasu baki daya,gudan Jinin na Baba Sarki abin sone Wajen kowa.

Tare Suka shiga cikin gidan ko kafin su Isa tuni labari ya isar ma su Goggo,dakin Hajiya Asabe Suka Fara Shiga Kamar Koda yaushe,Hajiyan tana musu sannu da zuwa tana ajiye musu fura da ruwa a kwanansha daban dana Mai haqorin Hajiya nan suka zauna ana gaisawa yayin da yara duka Suka hadu Suka baibaibayesu suna kallo kamar sun Sami gidan zoo.

“Hala wani sha’ani ake a gidan haka naga duka gidan yau jama’ar cikinsa sun dadu?”,Mahmud din yake tambayar Hajiyan Yana duban gaiyar yaran da suka shigo,da yawansu duk ga majina nan ta danqare a hancinsu sai Daman yage musu baki suke

Hajiyan tace “matar wannan yarance ta haihu jiya aka share suna shine fa kaga gidan da jama’a haka sabida mutanan qauyuka duka basu koma ba,an sami Zainabu wallahi Malam ne yace ba sai an fada muku ba hidima da wani abu ko babu yi kukeyi dan haka a daina qoqarin ko wanne abu ya taso sai an fada muku shiyasa ko a waya Saminu Blbai fada muku ba”.

Yusif din yace “haba Hajiya to ai komai aka fada Mana dolen mune,idan ba’a fadar abubuwa da yawa da ya kamata Musa ka hannun a cikinsu zasuyi ta zuwa suna wucewa ba tareda mun San dasu har ya Zama a mun taimaka ba”.

“Sosai hakan dai za’a ci gaba da fada Mana dukka wani abu daya dace mu shiga ciki Hajiya a daina biyewa Baba Sarki a irin wannan gabar”Mahmud ya fada shima.

Kusan minti talatin sukaci sannan Suka miqe suka zagaya sauran dakunan matan na Baba Sarki a qarshe Suka dire a dakin Goggo.

Nuratu ke ta qoqarin ganin ta kimtsa dakin tunda akace sunzo,sabida duk lokacin da ake wani sha’ani a gidan dakin Goggon Kanfi na kowa baci a dalilin duka sirikan gidan nan suke zaman su suyi dabdalarsu dasu da ‘ya’yansu ko a yanzu rake ne da gyada Suka zauna bayan an gama suyar nama duka yara da manya Suka Sha ana Sha ana hira,dan haka wani daro da suke kwashe shara dashi a cike dan Nuratun ta cika shi da bawan rake da gyada.

Goggo kyakkyawar bafulatana kamanninta da yusif kamar an tsaga Kara,cike da kunya wadda take yiwa yusif din a matsayinshi na dan fari ta zauna nan suke gaisawa dasu.

Ya shigo Yana murnaa ya zauna shima Suka gaisa sannan ya karbo mukullin mota zai kwashe kayan da suka kawo sannan ya kai musu kayansu ai nahin gidan Yusuf din dake bayan gari nan wajan kotu,sosai Suka zage suna hira a falon Goggon yayin da take tambayar Mahmud wajan Inna Mahmud din yace “lafiya Lau suke,zuwa jibi zamu wuce can din insha Allahu ta can Kuma sai mu juya wajan aikinmu”.

A kunyace Goggon tace “kudai Kuna jin dadin zamanku a hakannan kuyita neman kudi Kuna tarawa tare da kashema dangi amma ku ajiye iyali wajan da za’a riqa kashe kudin a sami lada Kun gagara.

Mahmud din ya shafa Kai a hankali Yana dariya,a tsakanin Goggo da Inna bai san Wanda yafi wani son yaga sunyi aure ba,wancan zuwan da sukayi har cewa Inna tayi Baba sarki ke daure musu gindi inda ya matsa suyi aure da tuni sun tsaya sunyin,amma ya barsu dasu sai su ke faman Yi musu zancen auren a Koda yaushe,tace taraku kawai nake amma insha Allah da dai dai da dai Zan baku mamaki,Kuna zaune zaku ga Mata na Sanya an wanke an kawo muku.

“Aure lokacine idan lokacin yinshi yayi zamuyi ne Goggo ku kwantar da hankalinku,akwai shirye shiryen hakan aqasa insha Allahu yusif din ya fada yana dubanta.

Nan Suka zauna har dare sai da Suka ci abinci sannan bayan sunyi hira dasu Baba sarki suka wuce kyakkyawan gidan Yusif din da bazaka taba zatan cewa a qauye yake cikin qaramin gari Kamar Rimi ba.

Kwanan su uku a garin kamar yadda sukayi niya,duk wani alheri da Yusif ya Saba ma matasa da tsoffi idan damina ta matso na raban taki da kudade duka yayi musucikin kwanaki ukunnan,an canzama Baba Sarki taractocin nomanshi baki daya,ranar alhamis da safe duka suna dakin Baba sarkin a zaune da shirin su na wucewa Dandume.

Da fara’arsa sosai Kamar Koda yaushe yake dubansu,”ku turawan gwamnatin har yanzu baku fara Shirin ajiye iyali ba ne?”.

Baba sarkin ya tambayasu “Muna nan muna dubawa Baba in Allah ya yadda kwanan nan zakuji kyakkyawan labari”,yusif din ya fada da murmushi.

Hakane Allah to ya tabbatar da alkairi,aci gaba da kulawa da lura da amanar da aka dora muku ta wajan aikinku da Kuma ta kayuwanku gaba daya,Koda yaushe mutum ya Sanya tsoron Allah a gaba Kuma kada jin dadin duniya ya taba sawa mutum ya manta daga asalin inda ya fita har ya yada nagartar gidansu,ubangiji ya muku albarka ya duba muku lamurranki.

Da haka Suka futo daga gabanshi Suka sake shigewa cikin gidan wajan su Goggo Suka sake musu sallama yadda motar ta shiga haka Suka futo jama’a suna ta faman miqa gaisuwa da Allah kiyaye Kamar wasu ‘yan shiyasa.

Auren zobe

Sadiya Musa Rimi

2

Kamar yadda sukayi ma Rimi shigar la’asar haka sukai ma garin na Dandume Inna suna zaune da Yaya Mariya a cikin babbar rumfarta wasu atamfofi ne da basu wuce qwaya goma ba sai leshi biyu suke jerawa a cikin wata jaka iron ta Kai kayan amare ,Innan ta kalli Yaya mariya data dafe baki tana dubansu da dariya a fuskarta tana dariya.

Hannayanta ta ware tana dagawa sama tace”wallahi Inna babu ruwana ban kirasu ba,Allah ne dai ya dubi maraicinsu ya CeCe su sukazo ayi dasu”.

Shiga cikin rumfar sukayi da dariyarsu nan kusa Yaya Mariya suka zauna Yusif ya fara daga kayan Yana tsokanarta “yayarmu ‘yar kasuwar duniya,bana Kuma nan Kika dawo ko dan Kinga azimi ya matso?”.

Da dariyarta ta dubi Inna data cune fuska tana hararsu dukansu tace “lefen kune Allah yayi zaku gani yau za’a miqashi ranar Asabar daurin aure nan gidan Kawu Mu’azu a Futuwa”.

Ido Suka ware baki daya suna duban ta yayin da Mahmud din ya matsa da sauri ya Kama hannun Innan ya riqe yace “da Wasa dai amma Yaya Mariya take Ko Inna?,zolayace irin wadda ta Saba ko?”.

Innan ta amshe hannunta tace “Allah ya nufa kusani shiyasa kuka iso kafin ayi, diyar Kawunka Ummu na nema maka Kuma bai watsa min qasa a Ido ba ya bani,komai na wahala ya yafe wannan ma Yayarka ta matsa ba za’ayi hakan ba sai an Mata ko yayane shiyasa aka hado wannan lefen akai musu,tunda ba ita kadai za’a yima auren ba da ‘yan uwanta duka sun an kawo musu nasu, su uku zai aurar.

Qwandalarka ba a nema ba balle kace baka shirya ba,aure ne za’a daura ranar asabar watanni uku Suka rage Mata ta kammala diplomarta idan ta kammala ayi dha’anin biki,ba dani za kuyi daqiqin wannan zaman zangeramar ba,na fahimci so kake sai qasa tarufe idona tukunna daka ajiye Iyali da Malam Yana na ai baka Isa kakai haka ba iyaliba,”sai Kuma ta Sanya kuka.

Duka su ukun sukayi kanta suna bata baki shi dai Mahmuda san ranshi abar batun auren, shi Ummun ma ba gane ta zayayi ba a cikin ‘yan matan gidan ;amma a yadda Innan ta hasalo yabita a hankali ko dagawane ya samu ayi shi yafi.

Shiko Yusif da ya samu Innan tayi haquri da kukan sai yajaYaya Mariya suka fice suka bar Mahmud din da Inna Yana ta faman kawo Mata qabli da ba’adi.

Cikin garin Katsina ya dauki Yaya Mariyan Suka tafi,lefe na ‘yar gata ya hadowa Ummun kayane na garari na gani na fada akwaiti seti biyu har sai da Yaya Mariya tayi kuka sabida jinjina qaunar dake a tsakanin Mahmud din da Yusif din.

Nan ko gida Dandume Inna ta rantse tasake Maya rantsuwa aure ranar asabar babu fashi,sosai Mahmud din yai laushi Yana kallan maqota da matan Baffaninshi suna ta zuwa ganin lefen da Yaya Mariya ta hado a wata jaka guda daya da za’a hada kayan a ciki.

Yana nan Baffanshi Salihu ya shigo nan Suka zauna shida Baffa Sani Suka tisashi a gaba da nasiha akan auren da nuna mishi muhimmancin auren da gatan da akayi Mai,qwarai Jikin shi yai sanyi da yadda Suka riqa danganta rashin auren shi da rashin mahaifinshi a duniya su Kuma bai maidasu komai ba shiya sanya suka riqa fada shi Kuma Yana jin kamar kida sukeyi a kufai.

Itako Inna aurene dai ta fada babu fashi Ummul khairi ta roqa mai diyar qaninta Bashir dake can gida Funtuwa,yarinyace da bata wuce Sha takwas ba ‘yan uwantane ma manemansu suka futo shine da yazo fadama Innan ta roqama Mahmud Ummulkairin shima.

Bayan sallar magariba Yaya Mariya da Yusif suka dawo,zuwa lokacine Innan ta cika tayi dam tana tunanin saban salone yusif din ya bullo dashi ya dauke mariyan sabida kada akai kayan a ranar

Nan tsakar gida suke zaune da Mahmud din yana ta faman dan yada Kai yaqi sake jiki suyi hira Kamar yadda Suka Saba,shiko sai salalo salalo yake Mata duk dan ya samu ta sauko daga fishin da take.

A nitse tabi yaran da Suka Fara shigo da manyan akwatinan da kallo tana jiyo karadin Yaya Mariya daga waje.

Innan ta dafe baki tana bin yaran da kallo nan Kan tabarmar da suke aka jibge jakunkunan da qatuwar birgami da aka zubo takalma da jaka a ciki guda goma Sha shida.

Ita kadai tashigo gidan tana faman dariya da kallan Inna “Inna kin ganmu ko?wallahi ninlma bansan Ina zamujeba sai da muka fita yace Katsina zamuyi mu hado lefen amarya Inyaso gobe sai mukai kayan shima goben zaya shiga funtuwan yaji irin shirye shiryen da ummun ta hada,tun muna hanya yake Kiran mutanansu Yana fada musu auren nan wallahi”.

Inna ta dafe baki cike da farin ciki da jimami idanta har yayi taruwar ruwa tace “Kuma banda danyan kai Mariya yaro ya kwararo doguwar tafiya ki barshi ko ruwa bai shaba kidada dibga Mai wata,tun da Danna ya shigo bai huta ba yanxu Yana Ina kenan?”.

Yaya Mariyan tace “wallahi Inna nima bansan Katsina zaya daukeni muje ba sai da muka damqi titi,kudi sunyi kukan a wajan nan Inna,jikina har sanyi yayi wallahi,Mahmud kaga abinda Yusif yayi kuwa?ta fada tana janyo jakar atamfofi ta kwantarwa zata Fara budewa.

Dariya kawai mahmud din yayi Yaya Mariyan na ganin damuwa kwance a fuskarshi,yace Yusif zaiyi yafi hakama,hakan nan yake kudi basu Mai wahalar fita sai dai ku Yi ta binmu da addu’a Allah ya tsare ya qara budi kawai.

“Ni Ina Kika baromin shine yazo ya sanya wani abu acikin sa baki fada Ina yaje ba kina Nlneman Fara bude Kaya” Innan tafada.

Ya shige masallaci ko magariba fa bamu samu Yi ba Inna inajin kuma ya tsaya ne sai yayi isha’i sannan ya shigo,Goggo ma suna bisa hanya gobe dasu Hajiya Asabe bakiga yadda ta riqa murna ba tana jinjinawa namijin qoqarin da mukayi”taqarashe tana duban fuskar Mahmud daya faki idan Inna ya mele baki ya harari Yaya Mariyan Yana miqewa tsaye yace “ki zauna kallan Kaya dai magariba ta jima da wucewa maganar isha’i ake a yanzu dai”,daga ita har Inna Suka bishi da kallo sai da ya fice tukunna ta miqe yana duban Inna tace ‘a Kira su Baba Sani suga kayan nan Inna,yaran nan ko uwa daya uba daya Suka futo sai Mai qarfin zumunci zai kashe kudi haka.

To cikin daran nan haka dangi da abokan arziqi suka cika gidan Innan suna kallan Kaya kowa Yana jinjina qaunar mahmud din da Yusif,Inna har kuka tayi haka Malam Sani duk saida sukayi qwalla,abune da su kamata suyi amma dake qarfinsu bai Kai ba shi kuma mai auran dake da sukunin yin ba auren ne a gaban shi ba sai suka ga girman abin da Yusif din yayi sosai a idansu da zuciyarsu.

Suko su Mahmud sabida yawan mutane dole suka koma gidanshi dake nan ba’yan gidan Innan yayin da aka saka yara Suka bisu da kayan abinsucan.

Ko kadan Yusif din bai huta ba mutane kawai yake kira Yana ta faman fada musu auren Mahmud din da za’a daura funtuwan

Mahmud tun Yana Mai qorafi har ya rabu dashi ya ci abincinshi yayi Kwanciyarshi, kuwa aka tashi da Shirin Kai lefe yayin da yusif ya dada daukar Yaya Mariya da zata gwada mishi gidan su Ummun a Funtuwa ita kuma xata tsaya a gidan ta ta yima masu kawo lefen abinci gidanta sai sun fara sauka a gidanta sai suwuce tare.

Yammacin ranar Saminu yakawo su Goggo da niqiniqi na gudunmawar abinci daga Baba Sarki,bikin da aka shirya yinshi lami sai gashi nan da nan biki na sosai ya tashi a gidan na Innan,baqin matasan ‘yan boko sai isowa sukeyi dagaAbuja da porthercout.

Kowa yaji mahmud dandume zaiyi aure sai yasha mamaki yayin da wasu daga cikin abokansu suke ganin shiya Sanya suka taho gida tun a talata dan su shiryama abin.

Sosai garin na Dandume ya dinke da baqin ‘yan Boko duk da sunji tarewar Amarya sai Nan da watanni uku,Sada Mamman zariya shiya taho musu da manyan Kaya kamar yadda Yusif ya tsara Mai.

Nan gidansu su Ummu ko da bata shirya yin komai ba sabida a yadda bikin nata zayazo Mata,’yan uwanta su Zabba’u nata faman shiri itan jikinta a sanyaye ita da mahaifiyarta,gwalla gwaso kala kala kishiyoyi nata Yi musu sabida ganin kamar sadakace za’a bada ita a mutumin da bai nema ba sai Kuma gaYaya mariya tazo tace da abokin ango suke Yana San ganin Ummun sabida shirye shiryen biki sai kuma kawo lefen Ummun dake nan zuwa da azahar.

A nan zauren gidan Suka tsaya yarinya Mai kunya,Yusif din kawai ta gani duk saita gaza sakewa,akwai alamun rashin magana da qarancin wayewa tare da ita,a hankali ya riqa janta da Hira har ya samu jin abinda ‘yan uwanta Suka shiryayi,sai ya fada Mata su zasu qara da lunching wanda zasuyi anan cikin garin Katsina sabida mutanansu Kuma yanasan ta fada sauran amaren da anqwayan ma suna iya zuwa su zasu zo da motoci a Debi mutane insha Allahu kafin dare sun dawo da kowa.

Sosai auren na Mahmud ya qayatar,duk da ba tarewa amarua zatayi ba Amma mutane da dama daga cikin aboka shi sunji dadin bikin,simple abu babu wani dogon kashe kashen kudi da yawa,sai dai Kuma da yawa daga cikin abokanan nasu sunata faman qorafi akan qanqantar Ummun a wayewa irin tasu wanda suka saba goguwa da ganin manyan mata kawai suke ganin hakan a cikin idaniyarsu.

Lahadi su Yusif suka bar dandume sukabi gaiyar abokansu suka juya Abuja da zuwan sai bayan watanni uku Kuma kamar yadda aka ajiye lokacin da za’ayi ainahin biki itama Ummun ta tare a dakinta.

 

Auren zobe

Sadiya Musa Rimi

3

Dare sosai wajan Sha biyu da rabi ya gama abinda yake ya nemo Lili a waya,sai da ta jima tana ringing kamar koda yaushe ta daga a hankali da muryar ta Mai dadin sauraro, Yusif din ya dafe wayar a kunnanshi tare da sake juyi akan faffadan gadan nashi qirar qasar Italy.

“Babban abokin ango har Kun share bikin Kun dawo kenan” ta fada a hankali da sakaltacciyar muryarta Mai dadi,Yusif din ya dada dafe wayar sosai a kunnanshi tare da sake juyi yace “ai daurin sure ne kawai akayi biki sai nan da wata uku tukunna ta hada diploma dinta sai ayi.

Uhimmm ta sake wata ajiyar zuciya daga can bangaranta, “Lili! Ya Kira sunanta, Uhimmm man ya yayane, “Lili ki bari Mana na turo manya na ayi maganar Alauren mu uhimmm!Ina tsoron abinda ya faru da Mahmud fa nima ya faru dani.

“Wai man me yake damun kane? Uhimmm aure fa rayuwar kace Kaine zaka zauna a cikin abinka ba wani ne zai zauna maka ba,to dan meye wani zai shiga rayuwarka yace ga abinda yakeson kayi bayan Kaine da Auren Kuma rayuwarka ce?”

Ya danne wayar ya sake narke murya ta sake sanyi sosai yace “ki gane abinda nake nufi Lili!rayuwarkace Amma iyayenka suna da ruwa da tsakai a cikinta, uhimmm ki duba abinda akayiwa Mahmud,da Allah bai kaimu gida a wannan time din ba sai dai kawai mu Samu an daura mashi aure bai sani ba Kuma..

“Ku wadanne irin gidadawan ne iyayenku da ba zasu bar mutum yayi rayuwarshi ba sai sunyi katsalandan a cikinta?”ta fada da sauri hadda miqewa zaune daga kwancen da take acan bangaranta.

Yusif ya dafe Kai zuciyarshi cike da qunci a hankali yace “iyayen mu ne gidadawa Lili? iyayen da Suka haifemu?”.

Likin ta yarfe hannu Kamar Yana ganinta tace “to dafa heart!Ina ruwansu da duk lokacin ma da kukaga zakuyi aure da zasu shiga ciki suce sai sun Zaba muku mace haba da Allah “Likinta fada cikin fishi.

Yusif yayi shiru Yana hadiye wani abu daya tokare Mai maqogwaranshi,a duniya Lili ce kawai take iya taba Mai iyaye ya kasa komai akai,itan Kuma Yana Mata uziri ne sabida Lili rainon turai ce a tunaninshi dalili kenan da duk maganar da tazo bakinta bata iya ajiyeta kawai sai ta furta,amma a zahirin gaskiya ga duk mutumin da ya zauna tare dashi ko ya kusance yasan wani irin jarababben sone daya wuce kima da misalin Allah ya jarrabi yusif din dashi na Lili.

Ko Mahmud na fada Ysif namijine, Kuma jarimi rauni guda da Allah ya jarrabeshi dashi shine soyayyar Lili.

Hailala da salatin annabi yake tayi har ya samu zuciyarshi tayi sanyi sannan ya sauke ajiyar zuciya ya maida hankalinshi Kan wayar Wanda zuwa wannan lokacin tuni ita lilin ma ta ajiye ta Kuma kashe wayar baki daya ta kwanta baccinta.

Sai kawai yayi saqare Yana duba wayar yayi Imani ko yasake dialing number ta Lili na iya qin dauka tace bacci ne takeji ko kuma ma baccin baki daya tama yishi ta manta dashi.

Sai ya ajiye wayar jikinsa a sanyaye ya juya kwanciyar rigingine ya Sanya hannunshi daya ta qasan kanshi daya Kuma ya dora a qirjinshi.

Wani irin kurmanso yake yima lilin dake azabtar da zuciyarsa,kwanciyar hankalinsa yaga lilin a cikin dakinsa,ya Kuma Yi Imani da Allah iko iron na ubangiji ne kawai zai bashi lilin ba dan Wai shi din isarsa takai isar da zaya nemo aurenta ba sai dan kawai yayi Imani da Allah ne ya qulla so da qauna a tsakaninsu,kuma shi dinne zaya mallaka Mai ita albarkacin soyayyarsa shi yake da yaqinin tana yimai yayin da jama’a ke ganin shi ke Sonta kuma shike bauta mata.

Qarfe biyu dai dai ya gaji da juyi a gado,ga wahalar daya Sha ta tafiya gaba daya garuruwa biyin da yaje babu Wanda ya samu ya huta nan din Kuma daya dawo damuwar Lili da fargabar matakin da shima nashi iyayen zasu iya dauka a kanshi ta hana mashi bacci sai kawai ya miqe ya Shiga bandaki ya sake saban wanka ya zira jallabiya sabuwa dal bayan ya feshe ta da turare ya fuskanci gabas ya tada da sallah,duk sujudar qarshe ta raka’a Yana roqon yalwar arziqi aljanna akanshi da iyayenshi zuri’a ta gari sai Kuma yayi ma Allah kirarida kursiyunsa da suna yan shi tsarkaka ya roqi ya mallaka Mai Lili.

Yana zaune dungurgur har akayi Kiran sallah a masallacin dake layin nasu ya miqe ya sake fesa turare a jikinsa ya fice masallacin ya futo daga get din gidansa shima Mahmud ya futo Suka hadu Kamar yadda suka Saba Suka Shiga masallacin tare cikin qamshidl da yauqi.

Matasan na da birgewa rayuwarsu gwanin sha’awa mutane da dama musamman manya maqotansu suna qaunarsu sosai,rayuwarsu Sam ba irin ta mutanan abujan bace suna bawa maqotaka haqqinta hatta da imam Yana yabawa sosai da irin gudunmawar da suke bama addini,an Kuma Yi musu shaida ta gari babu ruwansu da irin sharholiyar nan ta matasa duk da daudar duniya da Allah ya buda musu.

Sun futo masallacin bayan sun gaggaisa da jama’a nan qofar gidan Yusif din dake shine jere da hannun masallacin Suka tsaya.

Qarfe nawa zamu fita office ne?naga kamar ma baka Sami bacvi ba ko?Hala waya ka tsaya Yi kaga idanuwanka kuwa yadda suke nuna gajiya da bacci?.

Yusif din ya shafa kanshi a hankali yace “kaina ke ciwo kawai ba wani abu bane,Ina ganin ba tare zamu wuce office ba kayi gaba kawai na sameka,Ina son zan tsaya a wajan Lili,gara ta bani ranar da Zan turo manya su gana da iyayenta,idan Baba Sarki ya waiwayo kaina abin ba zai min kyau ba nima.

Mahmud din ya dafa kafadarshi da murmushi yace ” Bababsarki nada fahimta,banajin zai maka aure ba tare da ka Kai mai matar ba,sai dai Kai maganarta na tsaye har yanzu a Kan Lilin ko”.

Yusif ya daga Mai Ido cike da alamun tambaya a fuskarshi,Mahmud din ya shafa Kai yace “kasan Sarai me nake nufi,ya kamata ka sake dubawa à Kan maganarka da Lili broh,iyaye irin namu basu cika jituwa da mata irin su Lili ba, kamar yadda itama nayi Imani ba zata iya Shan inuwa daya da iyayenmu ba,shi Kuma rayuwar aure baki dayanta kwanciyar hankali ake nema a cikinta,Kai a Karan kanka banajin zaka Sami irin kwanciyar hankalin da ake samu a cikin aure idan har ka zabi Lili a matsayin abokiyar rayuwa,Kai Kuma ka kasa tsayawa ka fahimci abin duk da ake hanga maka”.

Yusif din ya cune fuska,ya rasa dalilin da kowa ya kasa fahintar sa akan Lili,dan haka ya juyar da fuskar shi cike da qosawa da maganar yace “Amma ai kasan bani na sawa kaina Sonya a cikin zuciyata ba ko?”.

Mahmud din shima yayi saurin tare shi yace “eh na sani baka sama zuciyarka soyayyarta ba Allah ne yasa maka amma Kuma ana roqon alkairi a komai ma na rayuwa Yusif,ya kamata ace zuwa yanzu ka dage da roqon Allah idan Lili alkairi ce awajan ka Allah ya baka ikon canza tsarin rayuwarta ya Zama dai dai da irin tsarin da addini ya dora,idan Kuma ba alkairi bace a wajan ka Allah ya musan ya maka da wadda ta fita”.

Da tsantsar bacin rai yace “lilince ba alkairi ba a wajena kake nufi kome?” Mahmud ya Sanya hannayansa duka biyun a aljihun jallabiyar shi ya daina kallan Yusid din ya juya Yana kallan gidanshi dake fuskantar na Yusif din yace “a dai yanzu a yadda take a yadda kakeson ka dauko ta ka shigo da ita cikin rayuwarka wannan yarinyar ba alkairi bace a rayuwarka Yusif”.

Wani irin tuquqin bacin rai ya sake Kama Yusifbdin fes ya dubi mahmud din yace “naji!ai dai rayuwa tace zata shigo ko?ko a Yaya take Ina son ta haka zanji da ita idan ta shigo,an gyara wadanda suke lalatattu ma balle ita,ya na kaiwa nan ya juya ya shige cikin get din gida shi yabar Mahmud din tsaye anan Yana duban bayanshi.

Allah ya gajarce maka wahala ya ganar dakai gaskiya isuhu,Mahmud din ya fada shima Yana juyawa cikin nashi gidan dan Shirin fita office.

Add Comment

Click here to post a comment