Rashin Mahaifiya Page 46 Hausa Novel
RASHIN MAHAIFIYA
*STORY & WRITING*
*BY ZAINAB KABIR*
*JAEN*
*🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟*
{R.S.W.A}
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
Page 40to50
*_______________* Cikin fusata ya kuma murd’e mata hannu k’ara tasa ta ce “Please Yaya kabari” dayake duk haka suke kiransa, sakinta yayi ya ce “gobe ma ki k’ara” cewa “tayi mugu kawai” sannan ta kwasa da gudu tayi cikin gida murmushi yayi ya ce “zan kamaki ne”.
Ni’ima ce taje tasamu Yaryarta ta fad’a mata yanda sukayi da Abbie k’arami Anty Lantana bak’aramin farinciki tayi ba ta ce “saina fi kowa farinciki in hakan ta kasance zan sanar ba da Abban yara da ita Amran” ta ce “to Anty” nan suka zauna suka cigaba da shawar warinsu bayan tafiyar Ni’ima Amran ta dawo gida nan Anty Lantana ta fad’a mata yanda sukayi da Ni’ima ce wa tayi “Mommah ni gaskiya bana son shi kwata-kwata shekara nawa yabani ya auri su Samha man sai yace sai ni ” cikin fad’a Anty Lantana ta ce “wallahi Amra matuk’ar nina haifeki ban yarda ki bijirewa auren nan ba in ba haka saina tsine miki!” ta fad’a cikin ‘bacin rai hankalin Amra ne ya tashi ma Mahaifiyarta bata ta’ba mata kalamai masu zafi haka rik’e hannun Mommah tayi ta ce “Mommah kiyi hak’uri Dan Allah wallahi na aminci zan bi umarnin ki amma kar kiyi fushi dani” cikin sanyin murya ta ce ma ‘Yar tata ” Amra hak’ik’a duk duniya bani da kamar Mommyn ku domin yanzu ita kad’ai nake da ita, yin auren nan shine farinciki na Dan Allah ki aminci ‘yata nasan zakiyi alfahari da auren nan gaba” ta ce “insha Allah Mommah”.ta tashi ta shiga d’akin ta ta fad’a kan gado tasa kuka yaza’ayi ta auri mutumin datasan ba k’aunarta yake yi ba,yayi hakane Dan ya cika wani k’udiri nasa amma bayanda zatayi kodan farincikin mahaifiyar ta dole ta amince.
Jerin Sunayen Hausa Novels List Da Download Link Nasu
To shirye-shiryen biki ya kankama ta kowa ne ‘bangare suna farinciki da had’a wannan auren Amarya ce kad’ai bata farinciki saboda ita gani take Angon ba sonta yake ba ranar biki anyi shagali na musamman aka kai Amarya gidan ta saidai mu ce (Allah ya basu zaman lafiya).
Ta Fita Zakkah Hausa Novel Complete
Tunda aka kawota bata kula Abbie k’arami inya mata magana saita sa masa kuka yarasa me yake damunsa bayason ya ganta cikin damuwa yau yazo d’akin ta ya sameta ya ce ” K’anwata nazone muyi magana dake” shiru tayi masa, dama bai tunanin zata amsa masa ba ya cigaba “Amra bawai na aureki Dan na k’untata miki bane na aureki ne don ina sonki kuma ni ba had’a ni akayi dake ba nina samu Mommy na fad’a mata ina sonki,amma in kinga bazaki iya zama dani zan iya sauwaqe miki kodan saboda farincikin ki, Dan Allah karki ‘boyemin ina jinki” a gaskiya inta ce bata son Abbie k’arami tayi k’arya tunda yana sonta zata zauna da Mijin ta lfy.
Tundaga wannan ranar suke zaune da Mijin ta lafiya yanzu wannan a halin basuda damuwar komai farinciki ya yawaice su Na’im yazama attajirin mai kud’i haka baffa da Habib da Abbie k’arami yanzu sun had’a Kansu sun zama tsintsiya ma d’aurinki d’aya.
Alhamdullillah a yau na kawo k’arshen wannan littafi nawa mai suna RASHIN MAHAIFIYA ina addu’a duk kurkuren da muka yi a cikin littafin Allah ya yafe mana abinda mukayi dai-dai kuma Allah yabamu ikon yin amfani dashi masoya ku biyoni a sabon littafinna zai zo muku nan bada dad’e wa ba.
Ina yiwa ‘yan k’ungiyata ta Royal star fatan alkhairi da kuma d’aukacin masoyana
Ina yiwa fans na RASHIN MAHAIFIYA godiya ubangiji ya bar k’auna
Taku har kullum
ZAINAB KABIR JAEN
{GARKUWAR💪ROYAL STAR🌟}.
[…] Rashin Mahaifiya Page 46 Hausa Novel […]