Littafan Hausa Novels

Ni da Yaya Ahmad Hausa Novel Complete

Ni da Yaya Ahmad Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

Ni da Yaya Ahmad Hausa Novel Complete

01…..page*

 

Karfe 01:30 am na dare kenan lkc da kowa ke hutawa ma’ana bacci amma lkc wasu suke jin daɗin yin abinda sukayi niyya.

 

Motace kiran BMW tayi parking a sabon unguwar g.r.a dake garin bauchi.

 

Wata matashiya budurwa ce ta fito da wata kawarta ta rakota suna rike da hannun juna kawar ta kalle kawarta cikin wani irin murya irinta yan maye tace ” *Subraty* sai yaushe kinga kin ɓatawa Elman show kuma kink’i kibashi hakuri me a ciki dan yana son kuyi rayuwar jin daɗi kin waye fa karki manta ke yar jami’a ce fa haba my dear Babanshi tsoho ambassada ne kuma yanzun senator ne kuma nasan koda yayi disvirg ɗinki shi zai aureki baki ga yanda muke da Aseem ba hiliss my dear ki bashi haɗin kai mana. ”

In Ba Ni Hausa Novel Complete

Fincike hannunta tayi bayan ta watsar mata harara kafin ta juya cike da yanga ta taka ramin block ɗin jikin gidansu ta haura ko sake bintakan kawarta bayi ba ta diri cikin gidansu tana sauka me gadin yana zuwa ya ɗaga abinda ta sauka akai ta shige ta baya tayi wani part na cikin gidan.

 

Tana zuwa tashiga da sallama yana kan abin sallah ta shige ɗakinta ta rufe kofarta ta kwanta ko cire kayan jikinta batayi ba.

 

Duk abinda ke faruwa akan idonsa cike da taikaci ya naushe iska yace ” na tsaneki Subra bana kaunar ganinki kin rabani da Surayya hankalinki yan kwanta ta tafi tabarni da bakin ciki idan ina raye sai kin zama abar tausayi kAmar yanda kika rabani da matata sai na rabaki da kowa har farin cikinki har shi kakan dake ɗaure miki gidin kiyi abinda kike so”

 

 

 

fita yayi daga ɗakin ya sauko kasa yafita zuwa gidan da *Subra* tashiga bakaɗa kofar yayi dai dai lkc Alhaji Bappa yana naɗe abin sallahnsa ya shigo ko kallon arziki Alhaji Bappa baiyi masa ba yaci gaba da naɗe abin sallahrsa.

 

Dai daita tsayuwarsa yayi yace ” Kaka Ina karuwar gidan nan take dan naga dawowarta.”

Shiru ma akace magana ne.

 

 

Dake da karfi yayi maganar tana kwance taji abinda ya fada mikewa tayi ta rufe ɗakinta sannan ta leko ta windo tace ” Idan ni karuwa ce kai me sunanka auù ashe kai ba namiji bane shi yasa ka kasa aure Allah sarki Adda Surayya kin azabdatu da y’ar uwanki mace gwara tun wuri ka nemi magani domin babu yar da zata zauna dai ga Namiji har namiji amma babu ƙkatabuss”

 

 

Tana faɗan haka ta kwanta abinta ko ba kome ta faɗa masa magana marar daɗi itama tsaki tayi ta gyara kwanciyarta wasu sirara hawaye ne ke zuba daga iɗanunta tace ” kucigaba da aibantani Allah yana nan nima fitan danake bansan me yasa haka yake faruwa dani ba amma daga *Ya Moha har Mama*

Kallon karuwa suke min” kuka ne ya kwace mata

 

 

 

Cike da takaice ya zabura zuwa kofar ɗakin Kaka ne ya dakatar da shi yace” Muh’ad fita min a gida tun kafin naci mutunci Ubanka”

 

 

Ba musu yafita yana me jin haushin maganar da *subra*

 

ta faɗa masa shiru yayi yana msi maita maganar shi ba namiji bane shafa kansa yayi yashige gidansu yana shiga ya faɗa gado yarufe idonsa.

 

 

 

*�?…�?…�?…�?…�?*

 

Washi gari da safe kowa yafito da niyyar karyawa yan mata da samarin gidan wanda akala zasu kai goma sha bakwai ban da iyayensu maza da mata ga yan kananun yara akan babbar dadduma aka shimfiɗa kowa zama yayi dan niyyar cikin aɓinci bayan anyi addu’a.

 

 

D’ago kai Kaka yayi yace ” Falmata ki cirewa Haleematul Sa’adiya bakin rabonta tana bacci.”

 

 

“Toh baba ” tace masa,

 

D’ago kai Abba karame yayi yace ” Ansa jeka ɗago min wacce ja’iran ita wacece da za’a ware mata bakin rabonta Baba gatan da kake nunawa *subra* ya fara yawa amma kayi hakuri ”

 

 

“Akam me ay y’arkace kafini iko da ita taso kaji ” Kaka ne ya faɗe haka,

 

Yana kai aya ya mike yabar musu falon.

 

Babban Yayansu Mahaifin Muh’d ne ya juya ya kalle kaninsu kuma autarsu yace ” Umar bai kamata ka faɗi haka a gaba Baba ba tunda yace ayu da kabari Falmata tayi yanda yace kayi hakuri da kome insha Allah nan da wani lkc tayi aure duk wani abunda yake faruwa zai wucce kaga yanzun ya hakura da cin abinci ”

 

“Ohonsa ba shi yasa kar ma yaci mana” Inji Moha kenan,

 

 

Hararsa Mahaifinsa yayi sauran a yan cin abinci kus kus aka fara akan abinda ya faru.

 

Daga can suka jiyo dariyarsu ita da Kaka tana rike da hannunsa har wajen cin abincin sai da ya zauna kafin ta zauna.

 

Yayun Abbanta ta gaidasu sai Abbanta wanda ya amsa ba yabo ba falasa.

Abinci aka shiga ci ko rabi bata ci ba tace ” Alhamdullillah,,,,, ta mike tacigaba da cewa ” Kaka sai na dawo Abba1 Abba 2 Abba 3 har zuwa kan Abbanta tace ” sai na dawo ”

 

“Ki dawo lafiya” sukace mata,

 

Dai dai Moha ya gama cin nasa kenan shima yayi musu sallama da sauri yafita ya rufa mata baya tafe take tana abinda tasaba wato yanga da sauri ya figi hannunta ya dannan key ɗin motarsa ya buɗe ya jefata ciki sannan shima ya fada ciki a guje ya fita daga gidan sai da ɗauki lkc yana tafiya kafin ya fincikota ya murɗa hannunta yace ” waye Ba Namiji ba Karuwa bola shara dattin kasuwa kin zama rijiya kowa saka gugarsa yake a cikinta kin zama shara kowa ya ɗibo dattinsa akanki yake zubawa wawiya munafuka me mutum zai yi dake Jaka Kawaru kawai buɗe motar yayi ya wurgota waje ,

Jan motarsa yayi ya barta a wajen.

*B.W.A.*🖊

 

 

 

 

 

 

 

*💝NI DA YAYA MOHA*💖

 

 

 

 

 

*Devoted*

By

*Aunty Jidda Musa*

 

 

 

 

*Tukwaice ga Ummul Moha,Neenah_Cool,Maman Gausiya*

 

 

 

 

 

*Sadaukawar ga Jameela Musa*

 

 

*RAMLAHT AR MANGA*

👆🏻👇🏻

*Real Me Dambu Ce*

 

 

 

 

 

*2….page*

 

 

Shiru tayi tana kallon shi har ya ɓace da ganinta sa hannun tayi ta buɗe side bag ɗinta ta ciro wayarta Kaka takira ta rushe masa da kuka sosai shiru yayi.

 

Can yayi ajiyar zuciya yace ” ke da Moh’d ne ko”

 

Cikin sheshekar kuka tace ” Eh Kaka ya kawo ni miri ya ajiye ni ya ci mutuncina sannan ya tafi ya barni kuma yau ina da test shine ya min haka”

 

“Toh ki ɗan jira yanzun za’azo ɗaukarki kinjo” Kaka yace mata,

 

Kallon yaransa yayi cike da jin haushi abinda Moha yayi yace ” Isah abinda Me sunana yake min ya fara wucce gona da iri fa akan me zai sa min yarinya agaba toh wallahi ku wucce ku ɗauko min ita tana miri a can ya wurgar da ita”

 

 

haɗa baki sukayi suka ce ” Baba kayi hakuri da abinda ya faru yanzun zamu sa ya ɗaukota”

 

Abba 2 konace Abban saif shi ya ɗauki wayarsa ya kira *Moha* yace” maza ka ɗauko ta tun kafin ranka ya ɓaci ” datse kiran yayi,

 

Dukar kujeransa yayi ya fita daga ofishinsa.

 

 

Motarsa ya ɗauka ya koma inda ya barta tana tsaye sai share hawaye take yana zuwa yayi parking ko zata zo tashi amma banza tayi da shi.

 

Horn yayi mata tayi kama ba da ita yake ba sai da yafito ya fincikota ya buɗe bayan motar ya wurgata sannan yashiga yaja toh ta zauna kawai mana sai ta gyara zamanta ta ɗaura kafa ɗaya akan ɗaya sannan ta ɗauko bakin glass ta toshe idanunta ta jefa chewgun abaki tana taunawa shi kam hankalinsa yana kan tuki kaman ance ya kalli madubi kawai sai ya ganta ta haɗar cike da isa da Iko irin ga drive ɗinta..

 

“Kam uba nine drive ɗinki toh fito karuwar banza yar isaka kawai fito min a mota kafin naci mutuncinki” yace mata,

yayinda yake parking.

Ko ajikinta haka tafito daga baya tashiga gaba tace “hmmm ni dai ba karuwa bace gwara ni lafiyaya ce”

 

Cike da bakin ciki ya juya yace ” bari nanuna miki ina da lafiya ko bani da shi fincikota yayi yana shirin haɗa jikinsu sai kuma ya tureta yace” me zanyi da abinda wasu mazan sun gama jagwaigalawa ke kome naki ya zama gwajo dan namiji me kyakyami bazai iya auren fasika irinko ba jakar guy gaki yarinya kamara amma kin ɓata future ɗinki.”

 

Maggaganun mara sa daɗi yake yaɓa mata wanda tuntina sharewa har ta fashe da kuka.

 

Jefa mata magana yake har suka iso gidan da gudu tafita tun bai gama parking ba.

 

Fita yayi yashiga cikin gida dai dai mahaifinsa ya tareta kenan yana tambayarta ita da *Moha* ne gyaɗa masa kai tayi.

Zubawa *Moha* ido yayi cike da ɓacin rai yace ” kai kam baka san me ake nufi da kunya da yakana ba sam baka san halicci ba Allah ya shiryeka jeki abinki Mamana”

 

 

Wuccewa tayi cike da jin daɗi ta shiga part ɗin iyayenta har falo tashiga ta cire shoe ɗin kafarta babu sallama tashiga abinta.

 

Kujera ta nema ta zauna kafin ta gaida mahaifiyarta tace ” Mama Amarya ina kwana ya aiki yau bazaki poly bane ”

 

D’ago kai tayi tsaf ta karewa y’ar autarta kallo sannan tace ” da bankwana ba zaki ganin haka, Ehh banje ba sabida ni ba gantalaliya bace ina zaune ne a inda Mijina ya ajiyeni ko da wani abune *Subraty*”

 

a razane ta ɗago tana kallon Mama Amarya tana mamakin yanda tasan sunan da yan club suke kiranta da shi.

 

Ita kuwa tana faɗa haka tacigaba da duba abinda take a jikin laptop ɗinta tayi banza da autarta.

Tana jin zafin yanda Haleematul ta lalace har itace ke fitan dare da wani ne ya faɗa bazata yarda ba amma da kanta ta ganta tana dawowa daga yawon dare.

 

�?…�?…�?…�?

Da dare bayan kowa ya gama cin abinci *Moha* ne ya gyara zamansa ya kalle Abba 2 yace ” Abba 2 na same wata shine iyayenta suka ce na fito idan nashirya.”

“Masha Allah ” kowa ya faɗa duk wanda yake falon sai da suka taya shi murna Abba2 yace ” masha Allah daga wani gida take kuma yar waye ”

sosa kai yayi yace “yar gidan Alhaji Abdullahi harɗawa ce ”

 

” wacce a kenan *Ya Moha* ba dai wannan yar fashinon ɗin na ba Sunuka kenan me kiran 1 no front no back sigul amama ke yar shilar tin” inji *Subra* wacce ba’a yi da ita ba tasako bakinta,

Tana rufe baki Mama Amarya tana kai mata duka wanda sai da bakin ya fashe domin da bayan hannun ta maketa,

 

Jikin Alhaji Bappa na rawa ya mike ita kuwa sai ihu take ta ga jini a bakinta Umma Babba ce tace” Haba Rumana me ta miki dan ta faɗa ra’ayinta ina yau da yasan yashirya mugunta ay hanata zuwa skull yayi sannan yayi musu test a class idan tayi masa ku ga laifinta baya shima ba tayan baya bane”

 

D’aga hannun *subra* tayi suka fita kallonta Kaka yayi yace ke da mijinki kuna nuna min iko akan Sa’adiya ko shikenan ay ”

 

tunda aka fara maganar Abban *subra* ƴya sunkuyar da kai kasa Abba 2 yace ” Baba kayi hakuri yawwa Baba karame kace sunce katuro ko”

 

Duk jikin *Moha* yayi sanyi sabida abinda *subra* ta faɗa tabbas yar fashion ɗince Raheela amma tafi amfani da Heela gyaɗa kansa yayi Abban Subra yace ” toh Anas, Dalhat, Sahib Samer Hashem Attahir kufa muna jiranku,

 

Murmushi Kaka yayi yace ” Dila sarkin wayyo shine ka nemo daga waje toh ba damuwa duk me niyyar ɗaukowa daga waje zai iya Amma saura wasun an gama nasu

 

Sai kuma yan mata Abida. Iyayen Aliyu sun kawo sadakinki, Khaleesa iyayen Hamza Yake sun kawo Khadija Iyayen Sadiq sun kawo Habiba keman an kawo naki iyayen Abbas.

 

 

 

Sai maza Ansa jibi Haruna Abba 3 (Mahaifin dalhat da Habiba )zasu kai sadakinka kumo.

Dalhat kai anan giɗa ne ko Rafi’a kace toh zan bawa (Abba karame Bello kenan Abban Subra kenan ,)

 

Samer Hashem kune ake jira tsagal Samer yayi yace ” Kaka toh a bani *subra* mana zan cika kudirin Ya saif ne don Allah.”

Kowa zuba masa ido yayi har da mahaifinsa murmushi Kaka yayi yace ” a’a banawa kowa dole bazan fara akanta ba.”�?

[9:38PM, 3/16/2018] �?+234 806 420 6896�?: *B.W.A*🖊

 

 

 

 

 

 

*💝NI DA YAYA MOHA💖*

 

 

 

 

 

 

*RΔMLΔHT ΔR MΔΠGΔ*

“`R̤̈Ë̤Ä̤L̤̈ M̤̈Ë̤ D̤̈Ä̤M̤̈B̤̈Ṳ̈ C̤̈Ë̤“`

 

 

 

 

 

 

 

“`Kubar marubuta su abinda zasu hilis“`

 

 

 

 

*3….page*

 

 

Mtseeew tsakin da *Moha* yaja kenan yace ” idan k’anwace sai kajikata kasha tunda kai baka gaji da ganin takaici ba hmm wata rana saita gumamaka bakin ciki wannar me kama da aljanun ruwan nan ”

 

ɗaga kai Kaka yayi cike da masifa amma sai yayi murmushi yace ” ba damu idan ban jikata ba kai ka jikata sannan babu abinda zata marar kunya ka faɗawa Yahya da Yaqub ga sunan azaune ko tashi kubar min gida nace ”

 

Mikewa kowa yayi suka masa sai da safe.

 

�?…�?…�?…�?

 

Alhaji Muhammad Bappa Gamawa shine cikeken sunansa.

 

D’an karamar hukumar gamawa ne kuma tsohon ma’aikace ne lkc mulkin farar hulla na biyu wato lkc shagari kenan yayi aiki a a garuruwa kafin jahar bauchi ta same jaha state *kenan*.

 

Matarsa Hajiya Halima yar garin gamawa ce auren haɗi aka musu sabida su y’ayan abokai ne dake auren da rabo tana shiga sai tasame cikin Sa,’idu Abba 1 (Baban Moha amma yana da wasu yaran Haleema take bin Moha sai Fahad sai Kubra) sai taya yaye shi sai tasake sami wani ta haifi Haruna 2 kenan (Baban Dalhat da Habiba suke nan Allah ya bashi)

Bayqn ta haifi haruna shima ta yaye shi sai tasame cikin yan biyu Yahya Abba 3 (Baban Saif da Abida da s

Samer da me sunan Alhaji Bappa suna kiransa da Sajid sai autarsu Sajida) toh dake yan biyu ne tare da Yaqub shine (Abba 4 shine Baban ƳHashim da Khadija sai Rukayya sa’ar Subrat. yaransa sunfi na kowa yawa domin har yanzun amaryarsa tana haihuwa sai guda biyu na Amarya dake mahaifiyarsu ta rasu)

Sai Abba karame (Baban subra da Ansa shine Babba sai Surayya sai Khaleesa sai Subra yaran kenan guda uku duk cikin gidan kuwa *Subra* ce bata jin magana gashi kaka ya ɗauki son duniya ya ɗaura akanta.

 

Sabida ranar da Hajiya Haleema ta rasu ranar aka haifeta dake hajiya haleema tayi fama da jinya kafin ta rasu.

 

Kafin a haife *subra* Moha da Anas sune yan gaban goshin kaka bayan an haifeta ya ɗauki son duniy ya ɗaura mata.

 

Umma Babba itace mahaifiya Moha sunanta Asiya yar jama’ar ce acan Abba 1 ya aurota.

Hajiya falmata Matar Abba 2 ce Maman Dalhat da Habiba.

 

Sai Mama binta matar Abba 3 Maman Saif da Sameer da sauran.

 

Sai Mama hajja ta rasu matar Abba 4 mamansu Hashim da Khadija Amaryata me suna Rabi’a Aunty Amarya suke ce mata.

 

Sai Hajiya Rumana itace mahaifiyarsu Subra da Anas Surayya da Khaleesa.

 

 

 

Akwai fahimtar juna da haɗin kai a cikin family ɗin sosai.

 

Dake yan gidan duk yan boko ne ga ilimin addini da ya ratsasu sosai.

 

Moha shine Babba sai Saif sai Anasa sai Dalhat sai Samer amma sai ya rasu shekara ɗaya da rabi ya wucce duk cikin giɗan da shine kawai suke shiri da Subra sabida yana masifar sonta sosai lkc da za’ayi auren Moha da Surayya yaso a haɗa shi da subra sam Kaka yaki dake ba rabon aure a tsakaninsu yayi hatsari rasu mutuwar ta shiga jikin subra sosai.

 

 

Subra bata ji sabida goyan bayan Kaka da take samu shi yasa take abinda ranta yake son.

 

Tana ajin farko a jami’a suka haɗu da Elman asalin sunansa Lukman ne amma dake shaiɗani ne Babansa senato abunda yake so shi yakeyi toh subiyu kawai iyayen suka haifa shi yasa yake yanda yaso.

 

Lkc da subra tashiga bata kula kowa sabida kashedin da aka mata kuma a cikin makarantar take a hostel ana suka haɗu da Husna ita lkc tana tare da abokin Elman ɗakin Husna ɗaya da Subra dan haka ita ta faea koya ma subra wasu irin ɗabi’u.

Toh lkc tana mugun jin tsoran Moha dake a A.t.b yake koyarwa kin yarda tayi inda take faɗa mata tace ” Husna Dr Moha yaya nane bazan iya wannan abin ba ”

Shiru husna tayita rabu da ita.

 

Sannun a hankali tariga cusa mata wasu halaye kaman fita party zuwa club da saka kananun kaya.

 

A lkc da Moha ya fara jin kishin kishin tattarata yayi ya dawo da ita gidansa dake bayan gidan iyayensu wajen Surayya sabida lkc tana da ciki daga nan take zuwa makaranta gashi sun faɗa soyayya da Elman shi niyyarsa ya lalata ita kuma tana masifar sonshi amma bata taɓa yarɗa ya rike hannunta ba.

 

Duk da tana gidan Moha bai hanata tana fitan dare daga Surayya sai Moha shima wai yaji dan be taɓa ganinta ba.

 

 

�?…�?…�?…�?…�?

Watan guda da zuwa gidan ita take kome kafun ta tafi skull zamansu ba laifi dake Subra bata da son jiki duk wani aiki na giɗan ita takeyi.

 

Gashi surayya tana jun dadinta sosai a duk lkc da suke hirar Surayya takance mata ” kina kuskure subra yawon dare ba na mace bane kiyi hakuri ki daina tun kafin lkc ya kure min ”

“Toh Adda zan daina”.

 

 

Kullum hirarsu kenan.

 

 

 

 

Add Comment

Click here to post a comment