Littafan Hausa Novels

Mai Dambu Hausa Novel Complete

Mai Dambu Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

TAMBARIN SHAHARA… (FREE BOOK)

Mafia Romance story.

*Mai_Dambu*

 

*Barka da warhaka daga Ministan sharholiya 🚶🏽‍♀️🙄😏 a daina zare min idanu firgitani kuke🤫 20 read more a sha karatu lafiya Barka da Jumma’a*

 

Chapter 015

Mikewa tayi tana kallon shi, kafin ta kwashe da dariya, har da rike cikinta tana nuna shi da yatsa. “Ni kake tunanin hanawa shagalin ki? Yo Allah na tuba ko namijin da ya fika isa da iko bai hana ni yadda nake so ba balle kai karan kad’a miya, idan ka isa dakatar da ni” ta saka kai zata fita ya riƙo damtsen hannunta. Wani irin banzan kallo tayi mishi bai san lokacin da ya sake ta ba. “Kwalelen kare da hantar kura idan ma jikina ne ya haukata ka tow ka farka, domin wallahi ko maza sun kare gara na mutu ban yi aure ba, ka ji da kyau ni ba irin sakarkarun yan matan da zaka ce zaka min iko da kaina ba isa ba. Wallahi kayi kaɗan kayi tsararo.” sannan ta saka kai ta fita abin ta, can wurin da babu yawaitar mutane ta zauna, tana kallon yadda ake hidima, idan ranta yayi dubu ya b’aci, wato ita Yazid zai renawa hankali. Tana zaune a wurin ,

Bakar Mace Hausa Novel Complete

A can falon Abba karami kuwa haka suke kiran Baban Yazid, komawa yayi ya zauna rajab kamar babu kashi a jikin shi. Baki daya kome ya tsaya mishi cak, da gaske jikinta ne ya hauka shi ko dai kawai soyayyar ta ne. Baki daya ya rasa ta cewa, dakyar ya mike ya nufi wurin taron, da idanu Kulsum take bin shi, har ya zauna. Yana jin babu dad’i. Wurin sha daya aka tashi. Cikin kwanciyar hankali ta wuce dakin Dadah tayi kwanciyar ta, bayan ta cire kayan jikinta. Itama Dadah shigowa tayi tana faɗin. “Hanjina” “Dadah barci nake ji” ta juya ta kwanta. “Allah ya tashe mu lafiya” “Amin” Washi gari ta kama budar kai. Tun safe sai ga Yazid Dadah tana zaune bayan ta idar da sallah asuba. Dake ita kuma tana up, ya shigo ya zauna, kare mishi kallo Dadah tayi kafin ta ce mishi. “Ba dai Yazidu nake gani ba?” “Eh Dadah ni ne, nazo duba Gimbiya ko ta farka.” Juyawa Dadah tayi ta kalli Hanjinta sannan ta kalle shi, “Yar sarki ce ban sani ba?” “A’a ita ce me mulkar zuciyata” sake kare mishi kallo tayi tana faɗin Yaushe aka bata mulkin zuciyarka ban sani ba?” “Ai wato Dadah al’amarin Ubangiji ya wuce haka, jiya.” Wani irin kallo take mishi me cike da mamaki wato ita Yazidu zai watsawa kasa a idanun sannan ya dibo sawaye kamar na bera ya ce zai dawo. “Ina jin ka aramakallahu” gyara zama yayi sosai yana kallon Hajnah da take barci. “Wato ko Dadah ina son Hajnah har kwanan gobe!” “Kaci durun uwaka” ita kanta Hajnah da take jin su, sama sama sai da ta tashi zaune, domin tsawon shekarunta bata taɓa jin Dadah tayi zagi ba. Tashi zaune tayi ta zauna tana kallon su. “Uwarka na ce, ai dadina da gobe saurin zuwa, wato lokacin da idanunka suka makance ka zata sabida ina niman kai da ita ne? Tow ka ji da kyau wallahi na kuma ganin siraran sawunka anan da suna niman Hanjina sai na ci mutuncin uwarka ba kai ba, tashi ka bani wuri mutumin banza, in sha Allah mijin Hanjina daki bari ne ba irin ka ba, me son kan shi.” “Amma Dadah ai ba cewa nayi bana sonta ba, tunda har yanzu akwai maganar auren mu” “kaci Uwarka da maganar aurenku ke hanjina kina son shi ne? Nace kina son shi ne?” Ta hayayyako mata, “Wallahi bana son shi” ta fada tana sauka a gadon tana me nufar banɗaki. “Kaji ko kaji me tace bata sonka sai kayi gaba a kare kalau Hanjina ta fu karfin ka” wankin babban bargo Dadah tayi mishi tare da kora shi, shima kamar mayye yana barin wurin Mahaifin shi ya wuce,.ai kuwa shima ya ci mutuncin kamar yadda Dadah tayi. Jiki babu kwari ya koma bangaren su na maza, inda ya samu Nurain a daki yana aiki. “Nurain don Allah ka taimaka min ina son a gyara maganata da Hajnah, zan jira ta Dadah da Abba karami sunki bani hadinka” “ai ko hadin gwiwa ba zasu baka ba balle na kai. Kiri kiri kace ba zaka iya aurenta ba da hujja mara dalili, may be shigar jiya ya hargitsa maka lissafi shi ne zaka dawo kana yar murya, Hajnah ba kayanka ba ne. Me shi yana nan yana zuwa gare ta.” Bai tab’a sanin haka zai faru ba, ya zata da yaƙi ta lallaba shi za ayi ya rufa mata asiri sai gashi ko gama bikin shi ba ayi ba, ya dawo sonta gadan-gadan.

Yau lahadi budar kai za ayi, ankon su Atamfa ce, ita kan tana dakin Dadah tunda tayi wanka ta koma gado, ko falo bata fita ba. Haka tayi ta barcinta sai azhar ta farka ta kuma wanka ta fito cikin doguwar riga, ta nufi part din Mamu. Ganin da mutane a falon yasa ta jin kamar ta koma,.haka tayi kuru ta shiga cikin falon bayan ta gaida mutanen falon. Dakin Mamu ta shiga shima cike yake da mutane. “Mamu ina kwana?” Cikin kulawa ta juya tana kallon ta, kafin ta amsa mata da cewa. “Lafiya sai yanzu kika taso?” “Eh Mamu, jiya da ciwon kai na kwana shi yasa sai yanzu na farka” fada tana nufar wurin kayan abin karyawa. “Kin sha magani?” “Eh Dadahna ta bani” ta dauki kofi ta haɗa black tea. Shukurah Yar kanwar Mamu ce ta shigo tana kallonta. “Kan Uba waye ya ce ki tab’a mana abincin mu?” Bata saurari yarinyar ba, ta dauki plat zata zuba farfesu yarinyar ta saka kafa ta shure. Ita kuwa zuciya ya kwashe ta,.ta watsa mata ruwan zafi a jikin ta. “Kaji shegiya zata kashe min ‘Ya mayya” inji Maman shukurah. Ta taso zata mari Hajnah. “A’a Maman shukurah, me yasa baki mata magana ba da ta zuba mata miya a jiki? Wannan fa babu adalci fisabilillahi idan kuma an ga mutu bai da rashin kunya sai a mai da shi wanda bai san me yake yi ba? Nan gidan Uban Halimah ne, idan har duniya da gaskiya babu wanda ya isa mata gori tunda jinin Imamu yake yawo a jikin Hajnah abin da yayi Aminatu shi yayi Imamu, Shafa’atu kina gani ana cin zarafinta baki yi magana ba, na zata kishin zai wuce ashe har bayan rai akwai kishin. Ki dai ji tsoron Allah kome na duniya me wucewa ne, babu wanda yasan gobe sai Allah, Hakima tashi muje wurina kici abinci.” Inji Sayyadah Karimah, da ta shigo bawa Mamu kayan da Kulsum zata saka. Juyawa Hajnah tayi tana kallon Mamuh tabbas sai yanzu ta fahimci dalilin da yasa Jadwah ta tsane ta. “Mamu dama bake kika haihe ni ba?” Maganar tazowa kowa a bazata. “Mamu me yasa baki tab’a gaya min ba?” Ta fada cikin matsanancin kuka. ” Yanzu na gane kome, na fahimci kome. Na gode koma wacece ta haife ni, bani da na biyun ki Mamu” daga haka ta fita. Wani irin zuciya ne da ita, koda ta fita ma bata wuce bangaren Sayyadah ba, wurin Dadah ta wuce ta kwanta abinta. Bayan fitar ne yan uwan Mamu suka fara kokarin ganin sun zugata. “Don Allah ku rufa min asiri, bana son tashin hankali. Wanda nake ciki ma ya ishe ni, don Allah ku shafa min lafiya, kar ku hada min wanda zai hana ni kwanciyar hankali. Tunda nake batan tab’a ganin fushin ta haka ba, duk abin da za a mata tana hakuri yau daya kunsan mutuncina zai zube.” Shiru suke dama a lokacin da ka bawa mutanen damar maka abu tow kuwa ka sayi tashin hankali, idan kana son kayi maganin abin ka rufe kofar haka ta hanyar da ya da ce. Ko lokacin budar kai bata fita ba tana kwance taci kuka har ta gaji, ita bata san haka ba ne da tuni ta magance kome ta kama kanta, ita babban tashin hankalin ta, Allah yasa ita jinin Abeey ce da haka zata iya samun nutsuwa ba. Anyi budar kai lafiya amma bata halarci taron ba, zaman daki tayi duk da yadda Addah Nanah taso su hadu, amma fir taki fita. Sai da aka fara watsewa ta fita harabar gidan sanye take da riga da skirt ta farar mace, dake Atamfar fari ne sai gashi ya karɓe. Kurawa mata da yan mata ido tayi bayan ta dauki plastic chair ta zauna, kallon wayarta tayi da yake haske. A hankali ta sake murmushi. Whatsp ta bude. “Hi baby!” “Na’am Najlah ya kuke?” “Baby ki mana hoto please we miss you” dariya tayi tana duba hotunan su na jiya, ta tura mata. “Wow ya Ilahi, Kamnah 🙀🙀🙀 dis gurl zata kashe ni zo ki ga inda Big B**B” tsaki Hajnah tayi tana faɗin. “Mtsew shegiya mayya, Najlah na jikin ki bai ishe ki ba, sai kin saka min ido” “Yar iska ina zan samu irin naki, nifa duba da acuci nake ciko 😪😭” “Allah ya tsine me karya 😂” inji Kamnah. “Ke bana son iskanci zanyi delete din shi😏” “Allah ya baki hakuri. Baby an fara aiki a asibitin nan, kuma Baba Chindo ya daina zama a bakin Asibitin, Beb ke din haske ce” murmushin farin ciki tayi, sannan ta ce mata. “Alhamdulillahi ” “two weeks ago wannan guy din yazo niman phone number dinki, wai sunan shi JB, Beb na fada mishi” “Najlah Allah ya shirya ki, shi din na hannun damar Mafia King ne, don put your life into danger” “Waw bura Uba. Kice shima Mafia ne, i can’t wait to meet him. Ke kin san duk duniya ba maza da suka iya buga soyayya da mace kamar mazan mafia” dama sun san halin Najlah ko renon Korea sai haka. “Allah ya taro mana ita,🙈 but ai ba shi daya yazo ba beb da wani guy wai Abraham I fell to he” “innalillahi wa’inna illahi raju’un, kuna da hankali 🙆🏾‍♀️🙀🙄 soyayya da yan mafia ai gara ayi sadaka da ku. Kunga bana son maganar haka babu ruwana a cikin shi, kuma kul ku bawa wani number na, don Allah ina cikin nutsuwa bana son Tensions da fitina. And ya karatun ku?” “Beb tunda kika tafi karatun nan baya shiga.” Inji Kamnah, “zai shiga mana baki mai da hankali ba ne.” “Beb nifa aure nake so 😓 dama kece kika samin kwarin gwiwar karatu.” Zaro idanu tayi tana faɗin. “Naj baki da hankali ne? Wani aure ana zaman lafiya, kiyi hakuri mana👏” “Billahi azim ba zamu yi karatu ba, idan baso ake mu fara bin maza a guje ba 🚶🏽‍♀️” “Na shiga uku, Yaran nan duka duka bamu wuce 18 ba, kuke maganar aure? Nifa next August zan cika 18, ke kuma Naj sai June, ke kuma Ajebo sai January ko🤌🏽 dan Ubanku ku daina Iskanci haka” “Haj idan zaki iya rike kanki ba laifi ba ne, amma ki sani ni tunda naga wancan JB wallahi bani da lafiya domin kamar na kai kaina gare shi ” ” Subhanalillahi Allah ya taro ku, kar ku lalata tarbiyyar da Abeey da Mamu suka min ” ita kanta basan dare ya ja ba, sai da taji muryan Abeey yayi mata magana. “Hanjin Dadah ” “Na’am Abeey” kura mata idanu yayi babu abin da tabar Mahaifiyar ta, sanyi hali zafin ta kuma yana da yakinin daga dangi..”Abeeyna ka dawo?” “Eh ga sakon ki da Dadah” ya mika mata laida tun bata bude ba, kamshi ya daki hancinta. “Abeey ina kaje yau baki ɗaya?” “Ban san me yasa na barki kika dauki Medical courses ba, da na bar ki kin dauki law may be zaki iya kare ni a gaban kuliya ” dariya tayi tana tafiya a nutse, bin ta yayi da idanun, kafin ya dauke kan shi daga kallonta sakamakon maganar da Abba karami ya mishi. “Ba kowa yake iya rike amana kamar yadda ka rike ba, idan har amanar zaka rike kayi nazari da kyau. Ɗazun Yazid ya dawo min da batun ya dawo ayi maganar su. Na fatattake shi” murmushi yayi sannan ya ce mishi. “Jini na yake yawo a jikinta, ba amana ba ce jini na ce, Yar Aminatu nawa ne. Babu kuskure akan kome sai dai kuma al’amarin da damuwa ne. Amma wallahi jini na ce” “Na yarda Halima jinin ka ce, domin kamar jini da kuke, amma kuma tow Allah ya kyauta” suka nufi cikin gidan, lokacin da Hajnah ta shiga dakin Dadah ta samu mutane a dakin, fuska tayi ta wuce gaban dan karamin firj ya saka kayan ta rufe ta cire key din firj din ta saka a bra ɗinta, tayi waje.

***

Mafia City

A kwance yake a bakin Beach House, yana me rufe idanun shi, motsi ya ji na ruwa alamar wani ya shigo gidan. Yana jin motsin ruwan, ko yana kwance a wurin a hankali ta gama wanka ta taso wurin shi. Har ta haura kansa, a hankali ta balle bra ɗinta. Har lokacin bai bude idanun shi ba, asalima kamar baya wurin hannu ta kai zata ta ba mishi wando ya rike hannun ta. “Sauka karya” ya fada yana bude idanun shi. Bakinta ta kawo zata sumbaci bakin shi, ya ture “you’re very stupid,” ya fada yana mikewa, tashi tayi tana faɗin. “AJ!” Bai saurare ta ba, ya wuce cikin gidan wai a haka ya bar asalin gidan shi da wurin zaman shi ne ya dawo beach house da zama amma yarinyar kamar mayya har bin guard din shi take tana rokon su gaya mata inda yake,da gudu ta biyo shi tana me shan gaban shi. “Akan wannan halittar kake wulakanta ni? Me take da shi AJ? Na daina bin maza saboda kai amma kai sai wulakantani kake, AJ i swear I love you, zan sauya idan kace na daina yawo na daina kome zan yi AJ ina sonka” “bana son ki, ki cire idanun ki akan ko Kawarta ne idan ba haka ba, gawarki ma sai an nima an rasa” daga haka ya bar wurin, kuka take kamar ranta zai fita. Kusan wata uku kenan yana niman yadda zai huce haushin sa, JB ma tafiya yayi ya bar shi tun da AB yaso suka tafi. Sai dai su hadu ta video call. Yanzu bai cika zama a nuwanda ba, idan har zai tafi asibitin tow abu me muhimmanci zai kai shi, idan an ajiye a appointment na ganin mara lafiya, baki daya asibitin ya fice mishi a kai, sai yanzu ya fahimci rayuwa babu abokin fada bai da dad’i. Yarinyar ko a kwayar idanunta yana son ganin fusatar ta, yadda zai ji dadin mata rashin mutunci. Amma babu al’amar ta, shima wancan dan iskan ya daina zaman kasar da alamu shege yana can suna soyayya, shi kuma sun bar shi a gantale. Wayar shi ce tayi kara guard din shine da yake kula da wasu al’amarin social media ya kira shi. Dauka yayi yana me gyaran murya. “Sir mun samu hoton yarinyar a IG, amma ba ita ta daura ba, shi ne James ya bani Shawaran muyi hacking account din ita yarinyar. Mun yi Nasarar hacking din ta, mun samu wani number na Nigeria.” “Ok ka turo min”

A can kasa kuwa wani irin kuka Duah take, tana mugun son AJ amma baki daya baya ta ita, duk abin da zata yi ta ja hankalin shi tayi amma fir ya ki kulata, ita kuma ba zata iya cutar da wata mace dan shi ba, musamman yadda take hango kwayar idanun shi akwai abin da yake nufi da yarinyar? Da gudu ta fita daga gidan shi. A compound na gidan ta gyara kayan ta, cikin wani irin gudun ganganci ta bar gidan baki daya ta hautsina lissafin mutane a cikin City din, kafin ta isa Dragon castle inda gidan su yake, tana shiga ko parking bata yi me kyau ba, ta shiga cikin gidan. Tana me wurgi da kome na hannunta, “Papa gaya min me na rasa a duniyar nan? Meye na rage da shi da AJ ya ce baya sona, meye na rasa? Meye ya rage min? Idan ban samu AJ ba zan iya kashe kaina.” Ta dauki wani wukar da aka ajiye a gefen fruit basket, ta yanke jijjiyar hannunta, “na shirya kome idan har na rasa shi, don haka ka san yadda zaka yi da ni AJ nake so.”

***

Bayan biki da sati suka juya abin su, zuwa Lagos, kamar ba ita ba sai dai tayi mugun fita harkokin yan gidansu. Musamman ta fahimci cewa ita ce bakuwa a cikin su. Wato irin mutanen nan ne da suka iya dafa mutum da hali, domin tsakaninta da Mamu ina kwana, Barka da gida, sai da safe. Jadwah kuwa zuba mata idanu tayi, domin kuwa ko kallo bata ishe ta, haka yasa take mugun shakkar Hajnah, irin mugun shakkar nan, domin yanzu zaka ga fuskarta kamar bata taɓa dariya ba, yadda take a gida haka take a school, haka ba karamin ja mata girma yayi ba, gashi Allah ya mata baiwar iya jan aji. Satin su biyu da dawowa Hameem da Nanah da Yazid da Kulsum suka tawo musu sallama, domin ta lagos zasu wuce, tunda ta fahimci Kulsum din tana mata wani irin gani-gani, ta kuma kame kanta, yadda matukar ba kasan tana magana ba, sai ka zata kurma ce. Tsakaninsu da Nanah kamar su cinye juna, suna kuryan daki sai shewa suke, da hiran su, domin wani irin kaunar juna suke. Suna zaune suna hira Yazid ya shigo dakin ya tsaya a bakin kofar. “Fadima kice Queen ta bani number ta please” kallonta Nanah tayi tana fama cin grape, “Baby girl wai ba zaki bashi number ki ba” cikin wani banzan hali ta dauke kai kamar ba ita ba, haka suka gaji suka barta har ya fita. “Baby girl me yasa?” Murmushin takaici tayi ta ce mata”me kika gani?” “But yana bin ki, sai jan shi kike a kasa” tab’e baki tayi tana cewa “and so what? Ba namiji ba ne, domin me aka yi su? Idan mace ta isa kanta bata bin namiji, shi yake bin ta like mad dog, don Allah ni a jini na yake jan aji, domin ni mace ce ba namiji ba ce, nasan darajar kaina. Don Allah yayi ta wahala da kan shi ba ni da lokacinsa…

#Mai_Dambu

Add Comment

Click here to post a comment