Jinsina ne Sanadi Hausa Novel
JINSINA NE SANADI
MALLAKAR,
WASILA OMAR (Mr’s f.h)
MOONLIGHT WRITER’S ASSOCIATION
*”’We are the moonlight writers we shine all over the world.”’*
بِسم الله الرحمن الرحيم
~~~~~~~~~~~~~~
Wannan labari ƙirƙirarren labarine, ban rubutashi dan cin zarafin wani ko wata ba in kinga ko kaga yayi kaman ceceniya da rayuwarka toh arashine kawai,,,,,
GARGAƊI
Wannan labarin mallakina ne ni MR’S F.H, ban yarda wani ko wata ya sauyamin akalar labari ko ya canja masa fasali ba tare da iznina ba…..
~~~~~~~~~~~~~~~~~
page 11&12
Rawa bakinta yake yi gaba ɗaya ta kasa furta kalma ɗaya, ganin hakan da yayi yasa yayi murmushi, ya fara takowa zuwa bakin gadon da take kwance, kujera ya jawo ya zauna bakin gadon da take,
“Hmmmmm! ta sauke ajiyar zuciya kafin da kyar bakinta ya iya tattaro kalamai ta furta,
“Ka ..k.k.kaine”?
tayi maganar tana riƙo hannunsa dan ta tabbatar, murmushi yayi yace,
So Ko Hauka Hausa Novel Page 16 To 20
“Nine Hanana kinyi mamakin ganina ne”? da sauri ta girgiza kai tace,
“A’a amma Na’em yaushe ka dawo”?
“Jiya na shigo garin a hanyata ta zuwa gidanku muka samu wannan hatsarin”,
shiru tayi tace,
“Dama kasan gidanmu”?
ta kuma masa tambaya, dariya yayi yace,
“yaushe kika zama mai tambaya haka, yanzu baki da lafiya ki kwanta ki huta zuwa anjima za’a sallamemu”,
shiru tayi ba dan bata da abin faɗaba sai dan yace tayi, wayarsa yake dannawa yayin da ita kuma take ƙare masa kallo,
Ba yanda Na’em zai canja ta kasa ganewa saboda abokinta ne shi, tun yarinta, sai taga ya girma sosai ya zama cikakken saurayi mai jini a jika, duk da dama can ya girmeta amma girman da yayi a ƴan shekaru huɗun da bata ganshi ba ba ƙaramin girma taga yayi ba,
Dogone sosai Na’em gashi fari amma ba canba, hutu da jin daɗi da kuma yanayin ƙasar da yake yasa ya murje yayi kyau sosai ga wani saje da ya fito ya kwanta a gefen kyakykyawar fuskarsa lufluf, kyakykyawa ne sosai ka kwarjini da cikar kamala,
“Na canja sosai ne”?
firgigit tayi sai kuma taji kunya ashe yana sane da ita dukda ba kallonta yake yiba,
Sai wajen ƙarfe biyar aka sallameta haɗi da bata magunguna, a motarsa ya kaita gida, ga mamakinta sai taga motarta cikin harabar gidansu, da mamaki take kallonsa,
“Ranki ya daɗe kallon fa ko nayi laifi”?
Sunkuyar da kai tayi tana wasa da dogayen yatsun hannunta, wayarta ya zaro daga aljihun rigarsa ya miƙa mata ta karɓa,
“Ki shiga ki huta zan dawo na duba ki”,
gyaɗa kai tayi tana ƙoƙarin buɗe ƙofa,
“Allah ya sawwaƙe”,
da ameen ta amsa ta fita ta rufo ƙofar ta masa sai anjima ta shige,
*******************
A babban falo ta tarar da Hameed yana kallon shigowarta amma bai ɗagoba balle ya fahimci ko akwai wani abu tattare da ita, itama bata kula shiba ta shige dan yace ta dena masa magana,
Ɗaki ta wuce taje ta rage kayanta ta wuce bathroom domin ta ɗan watsa ruwa,
Ta daɗe a toilet ɗin kafin ta fito sanye da rigar wanka sai towel ƙarami data ke goge fuska,
Ko mai bata shafa ba iya turare ta sa ta zira doguwar riga ta rama sallolin da suke kanta,
Ta idar ta zauna gurin tana lazumi tana tunanin rayuwarta, yanzu ta samu accident amma wai ƴan gidan su basu sani ba, yanzu da mutuwa ma tayi sai akai gawarta basu sani ba, hawaye ta goge aranta tace,
“wannan wacce irin rayuwace muke yi a wannan gidan,
Ta jima a zaune kafin taji wayarta na ɗan ƙara alamar shigowar kira, kallonta takai gurin wayar taga bakuwar lamba dan haka kawai ta ci gaba da abinda takeyi,
Ankira yafi sau uku ana huɗun ne ta ɗauka ta kara a kunne tayi shiru,
“Assalamu alaiki”, taji muryar Na’em ta daki dodon kunnenta, shiru tayi ta kasa amsawa sai da ya ƙara wata sallamar sannan ta amsa jiki a sanyaye,
“ranki ya daɗe kodai jikin ne naji ki ba kuzari”, girgiza kai tayi kamar yana ganinta tace,
“a’a jiki kam yayi sauƙi alhamdulillah”,
“Toh masha Allah ki dinga kulawa kinji, kuma ki rage damuwa”, shiru tayi aranta take cewa,
“damuwa ke nan ya gano ina cikin damuwa kar dai yasan mai ya faru” ta ƙarasa maganar tana zare ido waje, kamar yasan me take tunani yace,
“ki kwantar da hankalinki ki nutsu dan kina buƙatar hutu kinji”, da to ta amsa kawai suka yi sallama ta ajiye wayar tana sauke ajiyar zuciya,
Sai dare ta kira Nabiha take faɗa mata abinda ya faru, nan tayi mata jaje tace kuma zata zo duba ta sukayi sallama,
************************
Daga can babban falon gidan kuwa Hameed ya zaune yana duba waya yaji tsayiwar motar mahaifinsu,jiranshi yayi ya shigo,
“sannu da zuwa dady”, Cewar Hameed
“yawwa son kana nan kenan”, dady ya bashi amsa,
“ehh dady jiranka nake yi dama”,
“Akwau magana kenan, to bara na shiga ciki na fito”, cewar dady yana shigewa ciki,
Layin Hanana ya kira bugu biyu ta ɗauka,
” Kizo babban falo”, abinda ya faɗa kenan kuma bai jira cewarta ba ya katse kiran, jikinta duk a sanyaye ga wata iriyar faɗuwar gaba da take ji, kardar yaya Hameed ya yi mata haka bata fata iyayenta susan wannan maganar, Innalillahi wa inna ilaihirraju’un take mai maitawa,
hijabi ta ɗora akan doguwar rigar dake jikinta ta fito tana tafiya kamar kazar da kwai ya fashewa a ciki, tana ƙarasawa momynsu da dady suka fito a tare, gaishe su tayi duka ta zauna a ɗarare,
momy ce ta kalleta tace,
“Hanana baki da lafiya ne”?
girgiza kai tayi alamar a a,
Dady ya maida kallonsa gurin Hameed yace,
“son ina jinka wace magana kake so muyi”,
gyara zama Hameed yayi ya fara yiwa dady bayani,
“dama dady game da Hanana ne”,
a firgice ta ɗago tana kallonsa cikin ƙaɗuwa da razanin abinda zai fito daga bakinsa,
Bai tsaya lura da yanayinta ba ya cigaba……
MR’S F.H
[…] Jinsina ne Sanadi Hausa Novel […]