Littafan Hausa Novels

Gwatso Wattpad Hausa Novel

Gwatso Wattpad Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

Gwatso Wattpad Hausa Novel

Hannu Yaa Sheikh ya saka yana shafa kan ƴar fillon shi yana mai sauke numfashi da hamdala a ran shi. Idanun Dr A’isha bai hana shi sunkuyawa ya sumbaci goshi da ƙuncin Halisa ba. Bai san mai zai ce da Ubangiji ba sai godiya. Cikin lokacin ƙanƙani ya azurta shi da tarin abubuwan masu yawan gaske!

Ita ɗin alheri ce, kyauta ce daga Ubangiji. Ya lumshe idanunsa yana jin abu na kwanciya cikinsu, sautin kukan babyn na ratsa cikin kunnensa.

Mai Dambu Hausa Novel Complete

“Allhamdulillah!” Cewar Dr A’isha tana zare babyn daga ƙasan Halisa wacce ta galabaita tare da ficewa daga cikin hayyacinta.

Ta riƙe hannu Modibbo da ƙyar naman jikinta duk rawa yake. Yaa Sheikh kasa taɓoka komai ya yi, Dr A’isha ta yanke cibiya tare da goge babyn da zaiton kana ta naɗe cikin showel.

Siffofin Mace Mai Ruwa

“It’s a baby girl”

Gwatso Wattpad Hausa Novel

Ya jinjina kai, fita tayi daga room ɗin, bayan ta kwantar da babyn a baby bed. Jikin Jadda na rawa ta ce “Ya..ya..ya ya ake ciki” Murmushi Dr A’isha tayi ta ce “Ma sha Allah, she give birth to baby girl” Jadda ta rangaɗa buɗa ta ce

“Allahu Akbar, Allahu Akbar kaji yarinya da halin manya Ubangiji ka sanya war haka mu ƙara dawo amsar haihuwa”

“Amin Ya Allah, mene tukuci?” Mother wacce farin cikin saukar Halisa lafiya ya rage mata kaso 50 na daga cikin damuwarta ta ce

“Tukucin faɗar haihuwar matar malam ai na musamman ne, ki kira mijinta ya zo”

Dr A’isha ta wara hannu ta ce “that’s good, kawai zan tura account details”

“Go ahead” suka saki murmushi. Farin ciki ya mamaye zuciyar gabaɗaya Familyn, haihuwar Halisa ya ƙara zama abu mafi muhimmanci a cikin zuri’ar. Zahrah ita kanta tayi farin ciki domin ta shiga damuwa.

Shi da kansa ya tura gadon da take kai zuwa resting room, domin sama mata cikakken hutu. Ya sanarwar da wani Dr ya kawo masa drip da Injection ya sanya mata. Har lokacin bai bawa kowa damar shigowar inda take ba.

Yana riƙe da hannunta gam! Yana kallon yadda take barci a wahale numfashi na fita da ƙyar, ya damƙe hannun cikin laushin murya mai cike da tsananin gajiya da nuna farin cikinsa a fili ya ce “Barakallahu fiik Zawja, meu amor!

So lucky to have you in my life!”

“Ya kamata kaje ka huta, domin kasha ciwo da ya ƙushi, she’s so lazy”

Ya kalli Dr A’isha sai ya miƙe yana zame hannunsa daga cikin na Halisa, kai ka ɗauka shi ne mai haihuwar, duk yadda yaso riƙe kan shi ya gangara.

Yana fitowa Jadda tayi masa ka tana rangaɗa buɗa, ya marairaice domin har tsakiyar kan shi yake ji, baya son takura ko hayaniya zautar da shi suke.

“Congratulations Yaa Lee” Ya jinjina kai ba tare daya kalli Umar-khan ba.

Dr A’isha ta fito hannunta ɗauke da baby dake barci, Abba Hakimi ya fara amsar ta tare da yi mata addu’a, kana Father sai kuma Umma A’isha.

Mother tabi kyakkyawar fuskar yarinyar da kallo, babu inda ta bar Halisa, hatta ƙaramin bakin iri ɗaya ne. Yanayin gashin kanta ne yake kama dana Yaa Sheikh da yatsun hannunta, wani irin sahihin kyau yarinya ke da shi, gata ƙatuwa tubarkallah kamar ba ƴar fari ba. “Daughter ta haifi mai kama da ita” Umma A’isha ta ce “Anya? Kamar ta Malam nake gani shimfiɗe a fuskarta, bakin ne dai na surutu irin na uwarta”

“Ni fa Ƴar gidan Modibbo babyn ke mini kama”

Dr A’isha ta ce “Sure, They look alike”

Mother ta ce “God made her behave like her father” Sai a lokacin Zahrah ta ce “Kuma Halisa nada kyan hali, open heart gare ta”

Gabaɗaya sun manta tana wajan, sai kunya ta kama su. Mother ta miƙa mata babyn ta ce

“Ga Daughter ɗin taku Zahrah” caraf, Jadda ta ƙwace babyn tana zare idanu ta ce

“Allah ya isa, tsakani na dake sai Allah ni ban zan kulaki ba, kowa yasan jinya nazo, to ba zan zuba idani a bawa kishiya ƴar kishiya ba, salon a shafa mata taitanos mu shiga uku, a cuci yarinya ko gama zafin haihuwar bata gama ba” Zahrah ta sunkuyar da kanta ƙasa, haihuwa na taruwa a cikin Idanunta.

Jadda ta ce “A’a fa bawai magana na faɗa ba, balle a ƙullace ni duniyar ga da babu gasky haka kurum ba za a suɗe mini kurwa ba” “Kiyi haƙuri nifa ba mayya bace” Zahrah ta furta a raunace.

“Kaji mafisa ko? Babu dama kayi magana sai a ƙullaceka, to aniyyar ko wanne ɗan ƙaniyya ta bisa duk yadda kaso da kame baki sai an saka ka faɗar zunubi”

Daidai lokacin Yaa Sheikh ya fito cikin wata Jallabiya Ash colour mai laushi da santsi, ta kwanta sosai saman farar fatar shi, ya naɗe kan shi da hirami.

Yadda fuskarsa ke motsawa tana faɗaɗa zaka fahimci yana cikin farin ciki mara misaltuwa. Ya dubi Zahrah da ta bar wajan tana goge hawaye.

“Hufii, to don Allah haka ba yafi ba? Da cewa nayi ta tashi tabar wajan Alkur’an sai ta tsaneni yanzu dana kame baki nayi magana a nutse ba gashi ta fahimta ba, Alsulhu khair!”

“Eh gwarai ga sulhu nan”

Dr A’isha Said

“Lafiya?” Yaa Sheikh ya furta a taushashe ƙamshin turaren shi na Roja ya cika wajan, wanda ya sanya Dr A’isha sauke numfashi a ɓoye tana riƙe kanta.

“Matarka ta kura, ta hanata ɗaukan baby”

Jadda ta zare idanu tana dafe ƙirji sai kuma tayi shiru ganin yadda Yaa Sheikh ya kafe ta da idanunsa masu tsananin kaifi da sanya mutum shiga cikin nutsuwar shi

“Allah ya raya Baby Ubangiji ya sanya albarka” Umma A’isha ta ce “Allah ya sanya kuma matar malam tayi hankali” Sai a lokacin cikin sakin fuska yana jan jikinsa ganin Ummul na zuwa ya furta.

“Matana da hankali”

Mother ta ce “Ba shakka”

Duk abin nan da ake hankalinta na kan Fattoumah ita da Father daya bar wajan yanzu.

Idanun da sukai yawa a wajan ya hana Yaa Sheikh rungume Ummul kamar yadda ya saba, a hankali yake binta da idanu wanda take ganin tsananin farin cikin dake cikin su.

Suka amsa mata sallamar. Tayi murmushi ta ce “Barrister ya jikin Faɗima? Abu bai yi daɗi ba Ubangiji ya ki yaye ya kuma taƙaita ya bata lafiya” Mother ta ce

“Amin Ya Allah” Dr A’isha ta dinga kallon Ummul ganin yadda take komai a waye cikin nutsuwa da kamala, da shigar nan nata wanda ba a rabata da ita Abaya’s masu kyau da tsada.

“Can Mubasshir ya sameni, ina ga ya manta da na tura resigning letter ” Mother ta ce

“Ikon Allah, amma ba lokacin barin aikin ne ya yi ba?”

“Not at all,There is a reason why I joined the police force, and now I let El-Bashir finish the job”. “To Allah ya taimaka” Ummul tayi kyakkyawan murmushi ta ce “Anyi baby kuma, Allah ya raya ya bawa mahaifiyar lafiyar shayarwa” suka amsa da Amin. Ta juya ta kalli Yaa Sheikh ta ce “Arɗo You left your wife alone, and i think she’s crying”.

Bai ce komai ba, bai kuma motsa ba idanunsa akan Jaririyar hannun Ummul, yana jin son yarinyar da komai na wanzuwa a zuciyar shi.

Ya juya zuwa Room ɗin da Halisa ke ciki, har lokacin barcin wahala take yana daga bakin ƙofa ya shiga ƙare mata kallo sai kawai ya girgiza kai fararen haƙoransa a bayyane alamar dariyar ya yi mai kyau a fili ya ce

“Ƴar kwailar matata”

Ya fita zuwa reception Zahrah na ganinsa ta goge hawayen idanunta tana miƙewa tsaye cikin inda inda ta ce

“A…. You” ya bita da kallo tayi murmushi ta ce

“Congratulations sweetheart, ina maka murna da samun babyn” bai ce mata komai ya kama hannunta zuwa ciki ta ce “Zan koma gida”

A hankali ya ce

“Zuwa anjima” ta ce “To zan jira nan” ya dubeta da kyau ta ce “I wanted to be alone kawai fresh air nake so” Cikin ɗaga murya ba wasa ya ce

“Fatymerh Zahrah!”

Sai kawai ta fashe da kuka ta ce “Am sorry, ba zan iya jure abin da Jadda zata faɗa ba, daman Halisa na kawo Thank God ta sauka lafiya zan koma” ya riƙe hannun da kyau ya nufi ciki da ita, sai da suka je corridor ya rungomota jikinsa ya ce “Sorry”

“Na kasa jurewa, na jawa kai na mugun tabo, wanda ya sanya na kasa samun soyayyar ƴan uwanka, na kasa samun taka soyayyar balle nayi zaton samun baby tare da kai, lalai na cancanci haka” Ya yi mata shiru yana dai rungume ta ita.

Gwatso Wattpad Hausa Novel

“Yaa Sheikh” ta ɗago kanta ya kalleta yana lumshe idanunsa ta ce

“Don Allah kada ka barni, nayi al’ƙawarin zama dakai ko ba zan samu farin ciki ba” Ya share mata hawayen ya ce

“Ki riƙe Allah” ya faɗa yana zare ta a jikinsa tayi murmushi ta ce “In sha Allah” Haƙurinta yana ƙara bashi yaƙinin tabbas Ubangiji ba zai barta haka ba. “I love You sweetheart”

“Wife” ya ce kawai… Har Issha El-bashir bai shigo ba. Walking slowly yake tafiya a world ɗin, hannunsa zube jikin aljihun wandon Camouflage-print cargo trousers sai Sleeveless jersey tank top a jikinsa, idanunsa maƙale da Sunglass black. Yanayin yadda yake tafiya sai sanya kasan jinin Mai martaba Ahmad Nuran ne yake gudana a jikinsa.

Fuska a haɗe babu walwala sbd zafin zuciyar da yake ciki.

Ya murɗa handle ya shiga suka haɗa idanu da Fattoumah ya ɗauke ido ganin Mother ya yi tsaye zube da aljihu.

“Sai haƙuri, Allah ya bi mata kadinta” Ya shafa kai ya ce “Oops it’s okay”

Ya fito da waya yana dannawa fita Mother tayi a sanyaye Fattoumah ta ce “Uncle”

“Angela” El ya furta yana zama tare da kama hannunta ta ce “Kada ka barshi Uncle muguwa ne”

Ya runtse idanu yana ayyana azabar da Baba mai gadi ya ganawa Angela ɗin shi.

“Ya zan na bar wanda ya san gonata kafin na sani? He most pay”

Ganin tana ta kallonsa ya ce “Mene Angela?”

“Fitsari zan yi” ya saka hannu ya ɗagota ya ce “Zaki iya takawa?” Ta girgiza kai domin har ɗinki akai mata. Cak ya sunkuceta zuwa toilet, ihu! Ta fasa sbd azabar zafi lokacin da fitsarin zai fita tana kuka sosai jikinta na rawa da ƙyar tayi, sam El bai damu da ganin jikinta ba ya fahimci ita ɗin kawai yake ba wani abu nata ba, ya taimaka mata da wanke wajan tana miƙewa ta shige jikinsa tana sakin wani kuka.

Yadda take kukan zaka san wahala take sha, ya riƙe da kyau a jikinsa a hankali yake cewa

“Sorry, am sorry Angela” ya ɗauketa zuwa bed ɗin tana kwance a cinyar shi yana waya a hankali ya ce “Oh, ina buƙatar a shige da shi state C.I.D, kafin shiga Court”

A tsawa ce ya ce

“Zanci Ubanki ɗan iska, kai baka san waye ni ba You hve no idea akan abin da zan aikata” cikin ladabi ya ce “My bad”

El-bashir Said “I, El-bashir Ahmad Nuran Sarki ka kula ba wanda zan ɗagawa ƙafa akan matata” ya sauke wayar rai ɓace. “Uncle me ya sa ka ke faɗa?” Ya dubeta yana ƙoƙarin sauke numfashin shi.

“Angela zaki aureni” Sosai Fattoumah ta san kalmar aure, sbd wayonta shekarunta kuma sun kai ta sani tayi murmushi tana ɗauke kai. Ya kamo fuskarta yana zare Glasses ɗin idanunsa ya ce

“Ba zan iya jira ba, fitar da nayi sai dana tabbatar igiyar aurena ta hau kanki Binta, You’re now Mrs El-bashir Ahmad Nuran Sarki, El loves you Angela”….. Halisa ta dinga mamaki wai ita take da yarinya, ita ta haihu, ita ta zama uwa. Sai ta fashe da kuka musamman idan taga babyn na motsi. Da zarar taji ƙamshin turaren Yaa Sheikh take rufe idanu bata mance azabar data sha ba, ita kam gwara first night da wannan azabar ta haihu.

Gwatso Wattpad Hausa Novel

Zuciyar Babban malamin babu daɗi yana ta so ya keɓe da ƴar fillonsa amma taƙi yarda. Umma A’isha ta zauna wajanta. A hankali motar shi tayi parking Umar-khan ya fito da sauri ya buɗewa Yaa Sheikh, lokacin 6:45 na safe sanyi na busawa ya Fito cikin kyakkyawar tufa kamala da Ilhama ya ƙara wanzuwa a jikinsa. Cikin tarin nutsuwa yake sanya ƙafar shi ta daba,kana ya maye gurbinta dana hago har ya isa ƙofar Room ɗin. Bakinsa ɗauke da sallama Umma A’isha ta amsa masa, hannunta riƙe da babyn dake kuka sosai yin duniya kuma Halisa taƙi bata nono, da zarar ta bata taji zafi zata cire kuma nonon ya cika sosai. Muryarsa da ƙamshin turaren shi ya sanya Danejo kame fuska Umma A’isha ta amsa tana faɗin.

“Allahamdulillah, Ya Zahrah” ya jinjina mata kai yana zama saman kujera daman Umar-khan bai shiga ba, ya shige wajan Mother dake kula da Fattoumah.

“Matar Malam riƙe ƴar nan mai azabar kuka, zan duba Faɗimatu” Tayi shiru “Magana nake” nan ma tayiwa.

“Kawo ta” Ya faɗa in clam and golden voice. Umma A’isha ta bashi ita yana amsar ya ɗorata a ƙirjinsa yana jijjigata amma taƙi yin shiru.

Ƙaramin yatsar shi ne ya sanya mata ta shiga tsotsa ya dinga shafata yana mata karatu a kunne har tayi shiru.

“Wannan fushin?” Ya faɗa yana leƙa fuskarta ta tashi zaune ta ce

“Amma Abba ai baka kyauta mini ba” ya ware idanu ya ce

“To fa, dame?” Ta tura baki gaba ta ce “Baka ce mini haka haihuwar yake ba ai” Ya dawo kusa da ita ya ce “Wanne suna ki ke so?” Ta kalli Jaririyar dake ta tsotsar hannun mahaifinta ta ce “Ummul-khairy” ya tsora mata idanu sai ya zaro zam-zam daga jikinsa ya bawa babyn, kana ta tauna dabinon ajwa ya saka mata, ya yi mata kiran sallah kana ya yi mata huɗuba da Ummul-khairy. Ya ce

“Allah ya raya mini Mamana yadda take kama da babarta ka sanya kada tayi rigimarta” Halisa ta ce “A haka dai ka aura daga nan har Rugar Rome”

“Eh tana tallan Kindirmo ba” Ta ƙara cewa “Abba nifa na gama haihuwa ba wasa nake ba” Ya dubeta ya ce “Tare mukai komai fa, Na baki ciki, ki kayi rainon shi, kina laulayi ina kulawa dake, a haka fa akace an tsaneni, naƙudar jiya akai mini dukan tsiya” tana ƙoƙarin magana taji ya ɗage rigarta bakiɗaya tare da kafa….

Add Comment

Click here to post a comment