Namiji Baya Kadan Hausa Novel Complete
NAMIJI BAYA KAD’AN* pg 1⃣ Na
Aysha Ali Garkuwa
Pure moment of life writer’s
P.m.l.w
“`Allah mai iko mai tsara abinsa yadda yaso
Wlh kafin Na k’arisa NAYI NADAMA wlh Sam ba lbrin nan bane a zuciyata niyata
Noor ala Noor zan rubata so shi yana buk’atan in koma Na nazarci our,ani da hadisai sosai,
Sai gashi kuma kawai yanzu Na tsinci kaina da typing wannan lbrin
Amman insha Allah next novel Na Noor ala Noor ne, Allah ya bani ikon gama wannan lfy“`
Zaune suke a parlon cikin hiran jin dad’i
dan yau gidan a cikin nishad’i yake,
Mahmud da yanzu ya shigo cikin miskilanci ya zauna gefen
Mamin shi
tare da tab’e fuska yana ta huci,
ya kalli
Khadija dake gefe rik’e da woya tana mgn daga dukkan alamu da mutumin da ya kora yanzu ne take mgn,
Yarima Ashman Hausa Novel Complete
Tana katse kiran ta juyo cikin tsurawa Mahmud d’in ido
da alamun tuhuma ,
Shima idon ya tsura mata tare da katseta cikin had’e fuska yace,
“Wlh ni kunya kike bani ji irin mutanen da suke zuwa suna buga mana layi a k’ofar gida sai kace sun samu gidan mai,
Duk gayyan taru kucen banza”.
Ita kuwa harara ta watsa mai cikin bacin rai ta juya ta kalli Mami da Anty dake wurin tace.
” Wlh Mami kuywa yaron nan fad’a ya fita daga idona fisa bilillahi duk Wanda yazo guna sai yai ta koransu ko ni Sa’ar sace ni wlh ban son raini haka jiya yayiwa Sulaiman rashin mutun ci yau kuma ya kori Alh Bashir tome yakeso dani”?.
Shima fuskar ya had’e yana
“Kai da Allah kiyi ta tara tsoffi bayan ba iya rik’e da gsky zasuyi ba ko sun aureki”.
Mami ce ta kallesu cikin k’osawa da hali irin nasu dan inda sabon sun saba yanzu suita Sa,insa anjima ajisu suna hira da k’us k’us.
Shiyasa ta mik’e tana “toh kai Mahmud meyasa kake kore mata bak’inta kai wanne irin k’anine wannan”.
Anuty ma mi k’ewa tai tana “ke Khadija ya kikeyi har yasan da bak’in naki har ya samu damar koransu”?.
Baki ta tura cikin nunashi da yasa tana
” Wlh Anuty yaron nan ya cika Sa ido ne yaro kamar may”..
Bata kai da rufe bakinta ba ya taso cikin fushi ya tsaya gaban ta yana nunata da yatsa har jikinsa Na bari a fili ake ganin bacin ransa murya Na rawa yace
“Wlh ina gaya miki daina cemin yaro wlh ki kiyayeni waye yaron sai kace wata k’anwar uwata kiyi tace min yaro” a fili b’acin ransa ke bayyana.
“Ehh ancema yaron shekara nawa ne tsaka ninmu ko ka manta Na tunama kana dai sane Nike shiryaku lkcin da kuke zuwa primary ko”?
Had’e fuska yayi tare da matsowa kusa da ita cikin yin k’asa da murya tare da d’an tsura mata ido yana mai lumshesu dayin piki piki dasu yace
” Khadija wlh shi namiji baya kad’an ki dena cemin yaro ko Wai nayi kad’an ni nasan nayi miki yawane ba kad’an ba in kuwa shakku kike Na miki alk’awari gaba zaki gane”.
Dariya ta d’anyi cikin rashin d’aukar kala manshi da komai tace
“Wani ba Amman ba kai bakam Dan kana sane ni Anuty kace Amman Dan ka rainani sai kake cemin wani Khadija kai tsaye wlh sai Na had’aka da Abba tukun zaka gane”.
Murmushi ya d’anyi tare da cewa
” ai inna ce miki Anuty wlh Na watsa burin raina d’en zan jawowa murad’ina nak’asu”.
Mik’ewa tayi tana d’an takawa a hankali hips d’inta Na juyawa cikin rausayawan tace “wlh kai Mahmud ka feye son girma”.
Shi kuwa ido ya tsurawa bayan ta tare da sauk’e ajiyar zuciya yana mai lasan lips d’inshi da tuni sun fara bushewa cikin wata iriyar murya yace
” dazu naga wata mai kama dake a bakin to titi komai naku iri d’aya ”
Juyowa tayi cikin had’e fuska tace
Mai k’iba ko fara mai hips da yawa ko”?
Ido ya d’an lumshe cikin daga mata gira d’aya yace
“Ya akayi kika san haka take”?
” ai nasan da anga mai irin tsuffata sai ace muna kama ni wlh ban son k’ibar nan”.
Shima mik’ewa yayi ya d’an tako ya matsota cikin rada
yace
” ke wlh mace mai k’iba tayi a rayuwata ni banson mace siririya mai zanyi da ramarta mace kam ka samu ko ina ka tab’a bul bul kamar yadda kiken nan ai yafi ko? Ni Sam ban Sha,awar ramammiyiyar mace
Y’ar duma-duma dai tafi wlh”.
Matsawa tayi cikin ranta ko mmk take yadda k’anin nata Mahmud bai jin kunyar saki mata irin zantu kannan yaron da mgn ma tsada take mai ko yaushe bai da abokin hira sai littata fanshi da karatu k’ur,ani.
Shi kuwa cikin sanyi yace
“Bacci kike jine”?
Kai ta Dan gyada mai alamar a a ,
Ajiyar hrt ya sauk’e tare da cewa
Ki hau online akwai lbrin da zan baki”
Karb’ar phone d’in yayi ya bud’e mata data cikin sanyi yace “bari Na tafi d’akinmu
Baby in baki lbri”
yana fita tana binshi a baya ya tana cewa
“Waye babyn kuma “?
Shi dai tafiya yayi yana shak’ar k’amshinta.
Ita kuwa cewa take
” ji yaro da son girma Wai nice babyn lallai ma kuwa Mahmud ka isa”.
Shi kuwa yana zuwa d’akin toilet ya fad’a wonka yayi ya zira rigar baccinsa sannan ya kwanta .yana mai jawo woyarshi
K’aninshi Sulaiman ne ya kalleshi cikin tsokona yace .
“Sai chart da Anuty Khadija kuma ko wlh Mahmud ka d’ebo da zafi zan ga ta yadda abinga zai kasance, kai kace babbar mace kakeso ita kuma Anuty Khadija kullum cewa take ita matar manya ce saurayi ko sadaka ta yafe bare kuma kai K’anin bayan ta”.
dariya ya danyi cikin sanyi yace rebu da ita, ita bata San cewa namiji bayyin kad’an ko me take so wlh ni Na yadda da kaina Na san zan isar mata nifa ba lusarin na miji bane”.
Shi dai Sulaiman ido kawai ya tsura mai yana mmkin yadda Allah ya jarrabi zuciyar d’an uwan nashi da son Yayarta su.
Shiko cikin jin dad’i ya tsurawa picture d’inta na kan dp d’in ta ido yayi ta piki piki da idon cikin hikima ya fara yi mata mgn.
Slm yace da ita tare da cewa
“da forko dai ki cire pic enki Na kan dp d’in ki in ba so kike muyi fad’aba”.
Itako 😎 wanga ta tura mai tare da cewa
“Nifa Anutyn kace sai ka rink’a abu kamar Kaine babba harda ko mu b’ata to mu bata d’in mana”
dariya yayi tare da cewa “ai ina sonki baby bazan iya b’atawa da keba”
Hmmm tace dashi shi kuwa cikin kuzari da kaifin basira irin nasu Na maza yace.
“Kinsan Ku mata kala kala ne kuna nan tamkar lemun zaki”.
cikin dariya da daukar abin as A shi haka yake mai son raha ne tace “toh yaro ya muke”?
Cikin jin zafin Kalmar da take cemai Wai yaro ya d’ago woyar ya kirata
Itako tana gani ta d’aga dan tasan ta cinnashi bai son tace mai yaro.
tana d’agawa
sai jinshi tayi cikin sanyi ya busa mata iska a kunne tare da jan numfashi yace.
” Dan Allah ki dayna cemin yaro ni wlh har ga Allah kina k’ona min rai tunda nasan ni ba yaro bane”
Tab’e fuska tayi tace
“Toh me lbrin da zaka gaya min”?
Jin haka ya sashi k’ara narkewa jikin pillows a ranshi yakeji inama ace a jikinta yake ace gashi gata wlh da sai ya tabbata mata da cewa namiji baya k’aranta fili kuwa cewa yayi
” ko kinsan Ku mata tamkar lemun kuke
Wani lemun zaki ganshi baba a man cikinsa ba komai sai dusa wani kuma ki ganshi k’ara mi Amman cikinsa sai ruwa sai dai kuma sai a samu ruwan ba zak’i wani kuma ki ganshi gashi a cike ga ken fata Amman ba ruwa bare zak’in
Wani kuma zaki ganshi ga kyauwun jiki ga ruwa ga zak’i ga d’an d’ano ga kauda k’ishi da k’ara lfy da Sa kuzari”.
Sai kuma yayi shiru ita kuma tunda ya fara mgnar ta tafi tunanin ehh haka nefa wlh maganar sa gsky ce a ranta take cewa wato su maza mu sannan masu ilimin fikk’iwu komai Na mata sun sanshi.
Mgnarsa ce ta katseta cikin kasala yace.
“Toh ke irin wannan lemunne Na k’arshe da na kwatan ta miki”
cikin jin zafin furucin nashi tace
“In kana hasa shenka ka daina sani a ciki yaro Sam baka da kunya”.
Murya a dak’ile kamar zai kuka yace
” Dan Allah ki dena cemin yaro wlh zakisa duk randa Na iso gareki Na zalum ceki dan kawar da wannan sunan”
Ita dai bata gane me ya fad’iba bare ta gane ma,anar zancen.
Cikin sanyi dan ta fara jin bacci tace
“Mahmud zanyi bacci”
Ajiyar zuciya ya sauk’e jin dad’i yadda ta kirashi cikin sanyi yace
Toh tashi kike kiyi alwala kizo muyi Addu,ar konciya bacci”.
Cikin bacci baccin “tace ai nayi ni tun d’azu ”
Cikin rashin sanin zancen zai fito yace “ai nasan kinyi Amman dai alwalan ya worwore yanzu kam”.
Ita kuwa cikin baccin da k’osawa da surtunshi tace
” Yauwa dama gobe ina so ka kani Geere”
Toh yace tare da cewa ni bari Na sake alwala sai da safe ko”
To tace tare da katsa kiran.
Shi kuma Mahmud kogin tunani ya fad’a yana kitsima yadda zai kasance shine miji kuma shugaba a gun Anuty Khadijan tasu
A fili yake cewa bana jin tsoron komai sai k’iyeyta daga gareta
Idanshi ya lumshe yana tuni surarta shi dai yasan ba matar da zata iya dashi sai itan itanma yana tausaya mata in ta iso gareshi.
A haka bacci yayi awon gaba dashi yana mai murad’in malla karta…
Wannan lbri tukuici ne gareku mata Fasaha Writers online😘
By Garkuwan Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*NAMIJI BAYA KAD’AN* pg 2⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
Pure moment of life writer’s
P.m.l.w
“`Wannan shafi nakune Jannart lamido,
Zahra Muhammad Mahmud, Nana Diso, Rufaida Yusuf Fati Azlad Anty khady Aisha mazoji Sadnaf Halima Auwal sis Ummee Garkuwa“`
Suwaye Khadija da Mahmoud.?
Alh Ibrahim da Alh Sani yan uwan junane uwa daya uba daya sai k’anwarsu mace
Zahra, Y’an Asalin Fulanin Adamawa Yola suna cikin Yola sulum,
Ahl Ibrahim shine babba matansa 2 uwar gida mama yayanta 3 Sani sai Usman sai Autarsu Khadija sai Anty Zee mai yara biyu Fadil da Fadila.
Sai Alh Sani shima matansa 2 Uwar gida Mami yaran ta 4 Auwal shine babba sai Rayhana sai Fatima sannan Mahmoud sai autanta Amira sai Anuty Amarya wace take k’anwa ga uwar gidan Alh Ibrahim yaranta 4 Aysha itace baba sai Sulaiman sai Ibrahim takwaran bappanshi kenan sannan Autarta Nabila,
Ita Khadija tun sanda Alh Sani ya auro Anty k’anwar matar yayanshi sai suka dauko Khadija so ita Khadija gidan bappanta take k’anin mahaifinta sannan gaban ummarta k’anwar mahaifi yarta.
Sai Goggo Zahra yaran ta biyu babban danta Ahmad sai k’anwarsa Maryam.
So Khadija da Rayhana da Fatima da Aysha kusan tare sukayi karatu sai dai Dan fifiko da yake tsaka ninsu kad’an,
Shak’uwa ce sosai tsakanin yaran sannan iyayensu kuwa zaman lfy ne mai tarin yawa a tsaka ninsu.
Mahmoud da Khadija sunyi wani shak’uwa na daban wanda ake ganin sabo ne kawai da shak’uwa irin na yan uwan taka duk da Khadija ta girmi Mahmoud dan ko a maka ranta Khadija da Fatima da Aysha suna SS 3 yayin da shi kuwa Mahmoud yake jss 3 Rayhana ko a lkcin ta gama har tayi Aure tana cigaba a gidanta ya Auwal ko ya Dade da had’e digiri d’inshi har ya fara aikinshi sannan yayi Aurenshi.
Mahmoud da Khadija sabone mai tarin yawa a tsaka ninsu wanda ake ganin kawai iskarsu ce tazo d’aya dan Mahmoud shi ba mai yawan mgn bane sannan yana da halin ko in kula zai ganka sou goma Amman bazai sheida kamannin kaba ko yaushe kanshi a kasa, bai da yawan surutu sai in da Khadija ne zakajishi hira harda dry sam baison raini sannan yana da son girma over sam bai lamunci raini ba ita kuwa Khadija ta kasance ta kowace duk taron da suke a family d’in su muddin bata nan basa jin abin yayi armashi
ita kowa nata ne tana da faram-faram da Jama,a ta kasance so popular.
Khadija farace tas mai direrren jiki tana da sura ta ban Sha,awa da tafi ya da hankali duk wani da namiji lafiyye sannan tana da korjini ga cikar haiba komai na jikinta das kullum ka ganta sai kayi zaton yar 18 ce ga tsafta da kula da kai Khadija dai kekkyewa ce ta ajin forko kuma haka Allah yayi ta da farin jini bata fita nan da nan ba tare da wani ya biyota ba.
Shi kuwa Mahmoud Yaro ne mai k’walisa da son girma yana da cikar zati da haiba yana yin shi yasa ko manyan mutanen ke bashi girma dan tako ina ya kasance mai haiba farine tas shima yana da tsawo dan duk yafi yayunshi matan tsawo sannan yana da fad’in girji gashi mutunne shi mai halittar gashi a jikinsa hatta hannu shi da sharaban k’afafunshi suna cike da gashi maitaushi da shek’i yana konce luf a jikinsa gashin giransa ko irin Na Khadija sak wanda har ya kusa had’ewa hancishi zata har baki girjinshi ma rufe yake luf da suma so halittarsa takan sawa yana jin kanshi yes shifa namiji ne
Haka kuwa Allah ya jarabci zuciyarsa da son Khadija shi tun yana yaro ya gane yana sonta so kuma na Aure bawai so Na y’an uwan taka ba
Domain ko lkcin da zai kasance ya gama balaga da mafarkin Khadija balagarsa ta zauna gareshi.
Yayinda ita kuwa Khadija take mai so irin Na yan uwanta ka takuma daukeshi abokin shawara,.
Masu karatu zakiyi mmk ko wasu Suji takaici innace muku Khadija bazawara ce.
Amman a suna take bazawara a zahiri da bad’iri budur wace,
Domain Aurenta Na fari a deren da aka kaita
Gidan Angonta Sulaiman mahaifiyarshi tace bata yace koda d’akin ya shi gaba kuma tace muddin bai saketaba zata tsine mai dole a Daren ya saketa abinda ya k’ona ran yan kuwa yayinda shiko yake ganin rebonshi ke bibiyarta,
Lkci d’aya kuma Alh bashir ya fito shi kam Mahmoud baiji komai ba sai Aurenta yaji yayi kukan takaici da bak’in ciki ba iyaka a lkcin yawa kanshi kukan takaici da k’unci
Khadija da Alh Bashir sun zauna zaman shekara 3 Amman ba wani Abu da ya tab’a giftawa tsaka ninsu a dalilin matan shi da suka shuka mai tsiya dan kishi duk ran girkinta dashi da mace basu da banbanci,
Shi da kanshi yana tausaya mata yakuwa yi yunk’urin sakinta tun tuni
ita kuwa tace zata iya zama dashi a haka Dan inya sake ta bata San me mutanen zasu ce da itaba
Shi da kanshi yaga dai yana cutar da ita dole ya saketa,
Bayan shi ta kuma Aure da Adam Wanda ko tarewa basuyi ba ya saketa so daga nan tace ita ta hak’ura da Aure.
Kuma duk yan uwa ba wanda yasan cewa Khadija Na tare da budur cinta sai ita sai Mahaliccinta.
Yayinda shiko yake sonta a matsayin bazawarar shi kam Mahmud ya sa aranshi Khadija matarsa ce rebonsa ke juyawa da ita zata dawo kanshi ya kuma yiwa kanshi alk’awari a yan kwana kinsan zai Aureta ya tabbata tarwa kanshi shi zai iya rik’eta…… Wannan kenan!
Kashe gari da safe yana tashi ya shirya tsaf cikin riga da wondo na galila kalar pink ya amshesa ras ya fito cikin k’uriciyarsa da zafin jini sai k’amshi yake zubawa,
11 dai-dai ya Sakai cikin d’akin Anty ita kuwa dai-dai lkcin tana tsaye gaban mirror atampa ce a jikinta riga da siket siket d’in ya zauna ras a jikinta k’ugunta ya fito fes a cikin hips d’inta kamar sunyi mgn ga rigar itama ta wani lafe a jikinta gashinta take ta kiciniyar tubkewa,
Cikin bugawar zuciya da tsinkewar jini ya matsota a ranshi yake cewa
“Wayyo zata karya min Azumi”.
Matsota yayi yasa hannu ya karb’i ribbon d’in cikin kamo gashin yana mai tsurawa k’irjinta ido ta jikin madubin ita kuwa k’ara matsoshi tai da nufin ya tufke matan, cikin rashin Sani hips d’inta ya gogi jikinsa,
Cikin wani irin daukewar numfashi ya……
By Garkuwan Fulani
📝🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
*NAMIJI BAYA KAD’AN* pg 3⃣ Na Aysha Ali Garkuwa
🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇🍇
Pure moment of life writer’s
P.m.l.w
Janye jikinshi yayi da sauri ya juya ya fito parlor ya zauna kan 1 str Nabila dake gefenshi ta kalleshi cikin d’oki tace
Ya Mahmoud nima zanje gidan ya Auwal ko ?”.
Kai ya gyad’a mata dan in yace zai mgna muryarshi rawa zatakeyi ita kuwa tana gamawa ta fito sai k’amshi take
Cikin harara tace
“Yau kuma su Mahmoud d’inne a kusa ba mgn sai tsune ido da kauda kai”.
Shi dai bayyi mgn ba sai mik’ewa yayi ya fita ita ko hannun Nabila taja suka fito d’akin Mami suka shiga bayan sun gaisa tace “Mami bari muje gidan ya Auwal dan jiya ya kirani yace inje akwai mgnar da zamuyi dashi”. Cikin kula tace “toh ki gaishesu Amman ki dawo da wuri”
Toh ta amsa tare da fita ta yafa gyelenta a kafad’a sannan ta kama hannun Nabila
Suka fita a cikin matar ta sameshi zaune ya kife kanshi kan siteri ga gate an bud’e mai
Cikin tsokana ta ajiye Nabila a baya sannan ta bud’e gaba ta shiga cikin
tab’e baki tace
“Yanzu k’arfe 11:20 Am shine har azumi ya fara juya ma kai gsky Mahmoud akwai ka da ragwanta”
Cikin sanyi ya d’ago kanshi yayi motar key sannan ya harba cikin sanyi ga sanyi AC ga k’amshi turarukan jikinsu
Har saida suka hau babban titin da zai sadasu da jimeta sannan ta kuma kllonshi tace.
” nifa ba dole in zuwanne baka so”
Juyowa yayi ya tsura mata ido dai-dai lkcin da ya karya kona ya hau kan titin hayin gada
Mmk sosai tayi ganin fararen inda nunshi sunyi jazir sun kuma k’ank’ance cikin kula tace
“Broz ko dai baka da lfy ne”?
Kai ya jinjina da k’er ya bud’e baki yace
” ahhahh lfy ta lau kawai haka Na tsinci kaina”
ido ta tsura mai cikin mmkin jin yadda voice nashi ke fita gashi yak’i ya kuma mgn sai.
Ita shirun tayi har suka gaggara k’asan gadan sannan,
yace
“Khady me zakiyi a gidan ya Auwal naga satincan ma kinje”?
” nima ban saniba ya dai ce naje”.
Hmm yace sannan yaci gaba da tfy,
12 dai-dai suka isa cikin Geere suna isa aka bud’e musu gate suka shiga yana tsayuwa Nabila ta bud’e mota ta fita a guje tayi cikin gida.
Itama Khadija hannu tasa zata bud’e sai kuma taji ya rufe motar,
Cikin tabb’aya ta juyo sai kuma tayi sauri kauda kanta ganin shima gaba d’aya ya juyo ya sata a gaba ya tsura mata ido,
Bata kulashi ba dan tasan fitina yake ji yanzu zai tsareta da wa,azi
Cikin sanyi kamar mai rad’a taji yace
“Khady”
Sai kuma ya d’anyi shiru sai ido da ya kafeta dasu cikin dan dak’ilewar voice yaci gaba da cewa
” Na rasa yadda zan fahimtar dake illar irin wannan shiga da kike yi ke baki san irin fitina da kike had’a sawa ba nace miki ki dena Sa gele amman bakya jin mgn ta”
ya k’arisa mgn cikin sigar fad’a da isa,
Ita kuwa dan sunkuyowa tayi ta dannan pin din da ya rufe k’ofar aiko ta kifa k’irjinta kan cinyarsa,
shi kam gaba d’aya jikinsa ya rink’a sakewa yana macewa jikin sit ya koma ya jingina ya lumshe idanshi cikin fizgar numfashi.
Ita kuma tana bud’ewa ta fita kai tsaye tayi cikin gida shiko hips d’inta yabi da ido harda baki yana mai jin tsoron abinda zai mishi katank’a da ita gaba d’aya yaji jikinshi ya mace bazai iya tuk’in ba.
Ita kuwa tana shiga
Anty Salma ta fito suka zauna a parlon sai hira suke dan Salma mace mai son Jama,a.
bayan sun gaisa ta kalleta cikin fara,a tace “ke Khadija ina Mahmoud d’in bazai shigo bane”?
Cikin mmk tace “kai Anty ya akayi kika san shi ya kamo mu”?
Dariya tayi tace
” ai nasan Mahmoud din ke kawoki”
dariya tayi sannan sukayi ta hiransu.
Suna cikin hiran ya Auwal ya fito parlon shi cikin fara,a ya amsa gaisuwar ta sannan yace
“dama akwai wani abokina Nasir shine ya ganki kuma ya nace yana son Ku had’u so tun last week kullum sai yazo yau dai nave bari in had’aku, ki isa yana parlor na”
Rau rau tayi da ido lkci d’aya kuma sai hawaye cikin sanyi tace
“ya Auwal Aure kuma?
Ya Auwal me Na samu a auren bare nayi sha,awar sakewa wlh ni tsoron maza nakeji samida kowa da bak’in niyanshi a ranshi”.
tana mgnar ne da iya gskyarta lkci d’aya fuska ta ta sauya,
Shi kuwa Mahmoud sai yanzu ya d’an dai-dai ta nitsuwarshi sannan ya samu ya fito ya shiga cikin gidan cikin SLM ya shiga,
Cikin mmki ya rink’a binsu da ido a ranshi kuwa cewa yake daga zuwa sai kuma a sata kuka, a fili kuwa gefenta yaje ya zauna cikin sanyi yace,
” Khady me ya faru? me aka miki?
Me ya same ki?”
Haka ya jera mata tabb’ayoyin tun kafin ya gaisa da mutan gidan.
dariya Anty Salma tayi cikin wasa tace “ka tabb’aya kam Mahmoud ase Aure Na zama abin tsoro ga dan Adam ji
yadda take zubda k’ollah Dan ance ana sonta”.
Wani dum durum yaji a ransa a take ya had’e fuska cikin had’e rai yace
” shike nan bazan kubar yarinya ta hutaba aurena tunda anyi d’aya ba Sa,a an kuma Na biyu ba canji an kuma Na uku kazalika sai k’unci
ase bai isa a barta ba sannan wayema mai cewa yana sonta dan naci da mayta ai naga sai a barta ta huta ko”?
Ido kawai ya Auwal da Salma suka zuba mai abin har tsoro ya bawa Ya Auwal din dan ganin kishi k’arara a fuskar k’anin nashi.
Ita kuwa cikin jin dad’i zancen tace ni kamma ba Aure zanyi ba .
ganin zasu raina mai wayyo yasa cikin had’e fuska ya ce
“Ke tashi kike yana parlor na jiranki,
ji yarinya da shirme ke a zatonki barinki zamuyi ki zauna ba Aure ”
Mik’e tayi cikin sanyi ta nufi parlon nashi,
Shi kuwa Mahmoud tuk’uru ya rink’a fad’a kamar shine baba kan Auwal d’in,
Abin ya basu mmk ganin haka yasa yace
“Kai Mahmud ko dai sonta kake ne”?
Cikin wata iriyar murya yace
” ehh sonta nake ya Auwal kuma sonta da Aure nake ni zan Aureta wlh itace burin raina”.
Cikin mmk Auwal ya bishi da ido itako Salma ba mmk a fuskar ta dan ta dad’e da gane Mahmoud son Khadija yake.
Cikin had’e fuska ya kalleshi yace lallai baka da hankali Mahmoud na yarda yarinta ke cika inaba hakaba ina kai ina Aure Wai shin yaushema ka gama rik’a”?
Mik’ewa yayi cikin murtuk’e fuska Wai shi sai aitacemai yarinta yarinta
Fuska a had’e yace
“Wlh ni dai nasan ni ba yaro bane kuma nasan zan iya rik’e ko mata 4 zan kuma iya wodatar musu sannan da kuke cewa yarinta
Ina dai
Amira k’anwar tace?
Shekara nawa nake bata?
Kuma ina yanzu saura 9 days Aurenta wato ita ba yirinya bace saini”?
A harzuk’e yace,
“can matsa daga nan ita mace kai namiji”.
Mik’ewa yayi yana
” sai kuma akace namiji bai da rai ko ba zuciya ne daniba”?
Ganin fad’an zai nisa yasa ya matsoshi cikin dariya yace
“Haba Mahmoud ka bari ko digiri d’inka ka had’a mana tukun
yanzu kai kama san yadda zaka iya kula da mace ne”?
dariya yayi ta irin kumma rainani
Cikin ko in kula yace.
” tsaf zan iya kula da ita har nai mata ciki ta Haihu ”
Toh mgnar fa ta girmama ganin haka Auwal ya bishi da ido shiko
Phone d’inshi ya zaro ya kirata
tana d’agawa yace
Khady ki fito mu tafi ina da abin yi”.
fita yayi batare daya sallah mesu ba,
Ita kuwa tana samun haka ta dan juyo ta kalleshi cikin sanyi tace
“Kai hak’ura zamu tafi Mahmoud na jirana kuma Azumi yakeyi”.
ajiyar zuciya ya sauk’e tare da jin dad’i voice nata yace.
“Ba matsala
gimbiya sai kuma nazo gida ko”
Hmm kawai tace ta mik’e ta fita shima binta yayi suka fito tare shi sai ya tsaya tare da Auwal ita kuma hannun Nabila takama suka yi musu sallah ma suka fita.
Suna shiga mota ya figi motar a guje
suna fita ya juyo cikin had’e fuska yace.
“Kina sonshi ne”?
Tab’e fuska tayi cikin gyatsine tace
” me zanyi dashi ina zan kaishi ai ni ko aurenma zanyi ba irin shi zan Auraba dan yamin k’ank’anta yamin kad’an nifa nafisin namiji mai haiba”?
Shiru yayi bai sake mgn ba Dan ji yake kamar da ganggan take gaya mai kuma dashi take.
Ita kuwa ta dage sai cewa take yara k’anana dason tara mata yanafa da mata yake son k’ara Aure ina zai kaimu “.
Ba tare daya kalleta ba yace
” Wlh ki dena raina namiji ni Na tabbata duk k’ank’antar namiji zai dai cika miki mararki”
Cikin tsoro da kunyar mgnarsa ita har ga Allah ba haka take nufiba shi kuma
Daga nan bai kuma mgn ba dan ya mata daya tamkar da 1000 suna isa gida d’akinshi ya shige yana ta nemawa kanshi mafita tun kafin aimai shigar sauri.
Ita ma Azumin take
5 dai-dai ta shiga kitchen ta had’a musu abin bud’a baki kamar kullum,
Bai shigo ba sai da akayi sallah sannan ya shigo a parlon Anty suka zauna,
Fruit salad ta samai a Cup ta mik’a mai tana
“Gashi kaci Sa,a na regema wlh da shanyewa zanyi,
shi kuwa
Ido ya d’an tsura mata tare da cewa
” ai duk d’aya ne inma kin shanye ni kikewa tanadi gaba,
Cikin rashin gane mgnar da ya nad’e mata tace
“ai yayi dad’i ne shiyasa bazan hanaka ba”
Wani irin kallo ya bita dashi
A ranshi yace Na tabbata kinfi haka dad’i
A zahiri kuwa cewa yayi
“Ngd baby”
Jin haka yasa ta had’e fuska ta bud’e baki da nufin cewa yaro
Shiko gane Abinda take son fad’a yasa cikin sauri ya had’e bakinta da…….
[…] Namiji Baya Kadan Hausa Novel Complete […]