Kyawuna Hausa Novels Complete
๐๐๐๐๐๐๐
( ๐ป๐๐๐ ๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐)
๐๐๐โ๐ ๐ฌ๐น๐ฏ ๐โ๐๐๐๐ผโ
๐๐จ
๐ณ๐ฐ๐ฌ๐๐บ๐ฏ๐ฌ๐น๐ป
๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐ ๐๐๐๐๐ ๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐!!
๐๐ ท๐ ธ๐ ผ๐ ต๐ ธ๐ ณ๐ ฐ
____________
A rayuwa kowa ne ษan Adam yana da irin jarabawar sa, Babu wanda ya isa ya canza Abinda Allah ya kaddara masa. Haka rayuwar AISHATU ta taso Allah yayi mata wani irin Kyau, wanda mutane ke kiranta da ๐๐๐๐๐๐๐ . Fara ce sosai irin white milk ษin nan, haskenta me tsananin kyau ne da ษaukar ido, doguwa ce daidai misali sannan tana doguwar fuska me ษauke da dara-daran idanuwa ฦwayar idon ta wata kala like cat eyes, tana da dogon hanci wanda ya dace da fuskarta sannan tana cute lips kalar pink masu kyau da ษaukar hankali. Tana da diri sosai me ฤaukar hankali wanda ake kira da coca cola shape, komai nata me KYAU ne, Allah yayi mata baiwar murya me daฤin gaske idan tana magana kamar ana busa sarewa haka mutum zaiji saboda zaฦinta. Tana da natsuwa da hankali sosai komai tana yinsa ne cikin sanyi da hakuri da kuma tsari. KYAWUNTA ya jawo mata damuwa da tashin hankali, yan uwan mahaifinta sun kyamace ta sosai saboda KYAWUNTA, sun ฦwace dukiyarta wadda ta gada wajen mahaifiyar ta. Sun kore ta bayan sun san bata da kowa sai su, barin ta gida ya kara jefa rayuwarta cikin garari, KYAWUNTA ya kasance wani Haske ga wanda suka ฤauke shi a matsayin hakan . KYAWUNTA ya bar mata wani tabo wanda bazata iya mantawa dashi ba.
Mijin Mu Daya Hausa Novel Complete
Shin ita kaษaice me KYAU a duniya daya zamar mata bala’i da ฦuncin rayuwa ? Babu wanda yake raษar ta saboda Allah sai don KYAWUNTA, Ta yaya ne zata fuskanci rayuwa ta gane masoyanta na gaskiya? Wace duniya dangin mahaifiyar ta suke? Kuma a ina ne zata gano waฤannan dangin mahaifiyar tata….
******
Malam Mannir Muhammad mazaunin garin Katsina ne yana da yara goma sha ฤaya da mata ukku gidan Malam Mannir gidane da duk wanda yake cikin ansan sa saboda tambarin da suke dashi a unguwar. Rayuwar wannan ahali akwai darasi da yawa a cikinta . Gaba ฤaya gidan babu me girmama na gaba dashi, kowa harkar gabansa yake a cikin wannan gida babu me damuwa da damuwar wani, Amma duk da haka suna kaunar junan su basu yadda a taba su ba. Cakwakiya da sharholiyar dake ake zubawa gidan Malam Mannir tana da ban dariya da nishadโi…
******
AHMAD ษa daya tilo ga Alhaji Abdullahi Ibrahim me Dollar , AHMAD ษan gayu ne na bugawa a jarida yana ji da tsanin kyawu da kuษi ya kasance irin mazan da suka amsa sunan su a ko ina, hakan yasa bai ษauki uban kowa da daraja ba. Yana da mugun son wasan kwallo baida lokacin kowa a rayuwarsa daga na mahaifansa sai kwallo, yana da ilmin boko sosai don yayi masters har biyu a kasar London Fannin engineering. Yana da son gayu da kwalisa bai, rayuwarsa ta daban ce ba kamar sauran mutane ba. Ya tsani talaka a rayuwarsa bai ษauki rayuwar takala abakin komai ba, bai shiga harkar kowa haka koma ba kowa yaba damar shiga harkarsa ba .
ฦดan mata na haukan son sa sai dai kash basu gaban sa a cewar sa baiga ajin auren sa ba a ฦasar nigeria.
Mace kyakkyawa yake da burin aure, yafi son yadda yake da mugun kyau to matarsa ma ta kasance lamba ฤaya a kyau.Yana son matarsa ta kasance wadda suke da kuฤi na tashin hankali don babu abinda ya tsana a rayuwarsa sama da talaka, bai kaunar yaga talaka ya rabe shi a cewar sa basu da aiki in ba roko ba, bai san ko fita saboda kar ya haฤu da talaka a hanya. Sai dai wata kaddara ta ratso rayuwarsa lokacinda bai shirya ba…..
****
NASEEM ษan gayu me ji da kuษi da kwalisa , ษa daya tilo ga Alhaji Muhammad Mukhtar Naira , Naseem ya taso cikin so da kauna a wajen iyayen sa, basa ฦwabarsa ko kaษan sai daya shekara Ashirin a duniya sannan akayi masa kanwa Najma. Yana da son girma da jin kai, bai yadda a raina shi ba koda da wasa ne yasha shiga gasa ta miliyoyin kuฤin akan abin banza saboda kar a raina sa , sai dai yana da tausayi sosai abu kaษan yake karya zuciyar sa, yayi karatun sa a kasar America, inda ya karanci computer science, ya iya sarrafa computer sosai Allah ya bashi wannan baiwar maye ne sosai babu ta yadda bazai sarrafa computer ba. Yana da ฦดan mata sosai, sannan yana masifar son mace mekyau hakan yasa yake da ฦดan mata sosai don in har kina da kyau to ke tashi ce. Yana da son ace yar wane me kyau budurwar sa ce , yana harkar mata sosai dan babu me cin kuฤinsa inba Mace ba sai dai duk harkar shi baya taba Aikata Haram….
***
ALINA yarinya me tashe ฦyaฦฦyawa ajin farko tana kyau sosai , ฦณa ษaya tilo ga Alhaji Umar Farouk Umar ta taso cikin gata da soyayya, bata da mutunci ko kaษan sannan bata da ragowa balle tausayi, fitsararra ce sosai bata ganin uban kowa da gashin Arziฦi. Tayi karatu a kasar Egypt inda ta karanta medicine cikakkiyar likita ce me zaman kanta.jin kanta da isar ta yana da yawa bata harka da kanan mutane komai kuฤin ka baka wuce wulakanci a wajen ALINA ba . A rayuwar ta bata kaunar ace ga wata tafita, tana da tsananin kishi akan hakan ta fiso ace komai a wajenta aka fara gani ko a wajenta aka samo . Tana harkar social media sosai kuma tayi suna a Fannin babu wanda baisan ALINA ba.
itace me zamani a wannan zamanin sarauniyar kyau me tashe, motarta babu mace me ji dakanta da take hawanta. kawayen ta da ๐บ๐ผ๐ท๐ฌ๐น ๐บ๐ป๐จ๐น suke kiranta saboda ajinta yakai….
KYAWUNA! KYAWUNA!
kai daga jin sunan kasan salon na daban ne. da zafinshi yake tafe kudai ku biyo ni don jin wannan kayataccen labari. basai na koda maku shi ba idan kun biyo zakuji komai.
Ubangiji Allah ka sadamu da Alkhairin dake ciki ya kiyaye mu daga sharrin dake ciki.
๐ฐ๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐ ๐๐๐๐๐๐๐๐. ๐๐๐ ๐๐ ๐ ๐๐๐๐ ๐จ๐๐๐๐!
๐ ๐ฆ๐ โ๐๐๐๐
08060377780
[…] Kyawuna Hausa Novels Complete […]