Kalaman Soyayya Masu Dadi 2022
KALAMAN SOYAYYA MASU KARA DANKON SOYAYYA
GA MASOYA Idan kana tare da budurwa masoyiyar ka, ya kasance kanayi mata kalamai masu dadi na jan hankali, wadanda zasu dinga faranta mata rai.
KAMAR HAKA
Na dade ina kallon taurarin samaniya yayinda naga wacce tafi kowacce haske, saina naga bakowa bace nike ganiba sai ke masoyiyata So gamon jinine, haqiqa sonki ya zamo jinin jikina Kinfita daban a cikin mata.
duk lokacin da na kallleki, sai naga kamar babu kyakykyawar wace sai ke Ki kwantar da hankalinki masoyiyata babu wata a zuciyata sai ke kadai Yarda da amincewarki gareni, sune zasu tabbatar da soyayyarki ta gaskiya a gareni.
Farin ciki baya dorewa a rayuwa sai tare da bakin ciki, dan haka kowane hali nike bazan ta6a mantawa dake ba masoyiyata Nakan raba dare ina mai roqon Allah don neman biyan buqata,
Kalaman Soyayya na kwanciyar bacci
kKamar yadda kowacce bishiya kanyi rassa a sama, kuma tayi saiwa a qasa, haka sonki ya mamaye dukkan jikina.
KALAMAN SOYAYYA
Ina ma a ce na kasance da ke a duk bugun numfashina, kaunarki ce take kara tasiri a ruhina, babban burina na ga bayyanar fitar murmushinki a kan wannan kyakykyawar fuskarki, ya kuma zamana ni ne sanadin hakan. Bana son Allah ya kawo lokacin da za ki fushi da ni sosai kaina ba zai dauka ba, hakika Allah ya wadata ki da abin da mata da yawa suke nema sun rasa ke kanki kin san a cikin jinsinku, mata irinku kadan ne da a ce na iya rubuta labari da a kan fuskarki zan rubuta littafi mai suna kyauta daga Allah,
kuma na san zan samu bayanan rubutu kamar guda uku 1,2 da
Sararin samaniya na cike da taurari, teku na cike da ruwa, doran kasa na cike da ciyayi, amma ni zuciyata cike take da soyayyarki ba ta gushewa kamar yadda taurari ba sa gushewa a sararin samaniya, ba ta kafe wa kamar yadda teku ba ta kafe wa, haka zalika ba ta bushe wa kamar yadda ciyayi ba kamar sukan bushe, soyayyarki dauwamammiya ce a farfajiyar madinan zuciyata da akwai wanda zai tsaga jikina da ya ga jininki yana gudana, a kan kaunarki na manta kaina, kikan hau ingarman doki domin ki taho mafarkina, wannan sunan da kika boye a tafin hannunki idan dare ya yi, ki duba sararin samaniya kin ga mai wannan sunan yana haska duniya masoyiyata, hakika na kasance mai bayyana a mafarkinki kin kasance a fatar lebena. Duk wani taku da na yi a doran duniya sai inji takun na iso ni zuwa gare ki. So marurun zuciya ya yi min saka tun asali so ya shige zuciyata yana min suka.
Ganinki burina, idanuwana ko bacci na farka ki amshi soyayyata abadan kada na koka ba ni barinki cikin kunci yaki zo na yi miki tarba. Daga motsin numfashina kika ziyarci rayuwata a matsayin abokiyar rayuwa a duk zantukana sai na ambace ki. Damuwarki kullum tana cikin tinanina ke ce jin dadina kuma ke ce bacin raina ke kadai ce a zuciyata kalamaina, zabina jin dadina, bacin raina, saboda da ke kawai nake rayuwata, kaunarki ce ke kula da ni take kuma kau da duk wata damuwa daga raina koda a ce babu ni ka san tuwata zan zamana a tare da ke har abada. Kamar yanda baki bai isa ya furta ba haka jiki bai isa ya nuna ba, sannan zuciya ta yi kadan ta kwatanta ruhinki ne kadai ya san yadda nake jinki a sakamakon ziyartar da yake yi wa ruhina a kowane dare ina sonki ba zan daina ba har abada saboda ban isa na daina ba.
Soyayyata da ke ba ta mutuwa kuma ba ta tsoran mutuwa koda za a yi mana kwace, ko da za mu mutu ko za mu lalace to soyayyar mu za ta kasance a raye na bayar da zuciyata na karbi ta ki na kamu da sonki. Ki tallafi rayuwata da ta tsunduma a kan tsananin soyayyarki, ki tausayawa zuciyar da ta shagala a kan tsananin soyayyarki ka da rintsi ko zugar mahassada ya sa ki guje ni ko kuma ki rage son da kike min, sonki yana dankare a zuciyata kamar yadda kwakwalwa ke dankare a kan dan’adam da a ce zan samu ikon fito miki da shi da na yi domin ki kara gazgata tsananin kaunar da nake miki.
KALAMAN SOYAYYA MASU SANYA MASOYA MURMUSHI
TA ‘DAYA. Ina son dukkan taurarin da suke bisan sama, amma ba za’a hada son da na ke yi musu da kuma na wadda ta ke a cikin idanuwan ki ba, ina son ki.
TA BIYU. Lokaci yana nan zuwa da zaki mallakawa wani zuciyar ki, ina mai yin kira a gare ki da ki tabbatar da cewa kin mallakawa wanda ba zai raunata zuciyar ki ta hanyar yaudara ko cin amana ba, saboda ita zuciya d’ayace babu wadda zaki dauko ki sauya a lokacin da bakin ciki da damuwa suka mamaye zuciyar ta ki.
TA UKU. Yanzu haka ina cikin farin ciki, shin kin kuwa san mene ne dalili? Hmm saboda na kasance mai sa’a, kin kuwa san tayaya? Saboda Allah ya na so na, kin kuwa san me ya sanya na ce haka? Saboda ya ba ni wata babbar kyauta, kin kuwa san mene ne? Ba komai ba ne ba face KE masoyiyata, ina son ki.
TA HU’DU. A koda yaushe lokaci tashi yake yi tamkar tsuntsu, amma ita soyayyar mu kullum ginuwa ta ke tare da kara samun wajen zama a cikin zuciyoyin mu karda ki manta da ni ki kasance mai yin tinani na kamar yadda nima na kasance a ko da yaushe.
TA BIYAR. Abun da na ke ji a dangane da ke gaskiya ne kema na san kin san da haka cewa ina son ki, a duk lokacin da kika bar ni ba zan iya motsawa ko da nan da can ba, wannan shi ne abun da zai faru da ni a duk lokacin da na rasa ki.
TA SHIDA. SO tamkar wata sarkar zinari ce da ta d’aure zuciyoyin mu a waje guda, a dukkan lokacin da kika tsinka waccan sarka tofa ki tabbatar da cewa tamkar kin kore farin ciki ne daga cikin zuciya ta.
TA BAKWAI. Salim ina son ka, me ya sanya ka ke yin kokwanto a bisa kalmar so da na furta a gare ka? Tabbas kaine mutum na farko da haduwa da shi ya kore min bakin ciki, ya wanzar da farin ciki a zuciya ta ya yalwata murmushi a saman fuska ta hakane dalilin da ya sanya na ke kiran ka da SADAUKI. Salim, ka yi nasara ka yi nasarar jan ra’ayin soyayya ta a kan ka kaine na mallakawa linzamin zuciyata, kaine mutum na farko da na taba furtawa kalmar SO kuma a yanzuma zan kara mai-maitawa a gare ka ina son ka.
Ka amince mu yi tsaftatacciyar soyayya. Sai yanzu na gano cewa a duniya babu abun da ya kai samun masoyi dad’i, a duk lokacin da na rasaka ban san halin da zan shigaba, daga karshe ina mai sanar da kai cewa buri na yanzu bai wuce na ganin ranar da zaka zamo ango ni kuma na zamo mata a gare ka ba, ina alfahari da kai a duk inda na kasance, ka huta lafiya daga mai son ganin farin cikin ka a koda yaushe.
Shugabar Yan mata, kyawawa mai cikkakar haduwa a matsayin mace, kisani inasonki sosai nakumayi missing dinki sosai love U
Sonki tamkar wani fure ne da idanuwana suke Qawatuwa da kallonsa, hanci ya ji daddadan Qamshi, ruhi kuma ya samu nutsuwa. Idan rayuwa ba za ta yiwu ba tare da ruwa da iska ba, haka ni ma ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba.
Kalaman Soyayya
Bata kome nake nufiba kuma allah yasani harcin raina kawaida banaso nafara sankane kamin walakanci kuma akan karna walakantaka na karbeka amma bana so yayya dan banason shiga damuwa kasan dan adan ba a renashi domin yanada muhimmanci da darajah
Dudda haka kagoge wllh banaso agane takwkwala nake him dukda bana gajiya da magana dakai bari inbarka hakanam karna damekah dan allah ka kularmin da kanka banaso wani abu ya sameka allah ya tsaremin kai dan alfarmar wanga wata dan sunayesa guda 99 ameen thumma ameen good night i love you.
Kalaman soyayya A to Z
Kanwata Gaskiya nayi nishadi da wayarmu ta jiya sosai Domin kuwa kin nunamim cikkakar kulawa Love U so much moohm!
Sonki tamkar wani fure ne da idanuwana suke Qawatuwa da kallonsa, hanci ya ji daddadan Qamshi, ruhi kuma ya samu nutsuwa.
Idan rayuwa ba za ta yiwu ba tare da ruwa da iska ba, haka ni ma ba zan iya rayuwa ba tare da ke ba. Jin dadi da walwala ba za su taba samuwa a tattare da ni ba matukar babu soyayyarki a cikin zuciyata. Kin zama tauraruwa da ke haska ilahirin bishiyoyi da furannin da suke a lambun zuciyata.
Kalaman Soyayya
Yayanah ALLAH yamaidaminkai lfy ALLAH kayimin wnnn arzikin na dawowarka lfy ameen kakara yimin addu,a kaji dan kuwa banda lfy i love you
Slm aminchi agareka yayanah mu,awuya him agaskiya idan ba karfin jini ga mutumba idan yana tsaye aka kira wnnn sunam him baridai babynah abin sirrine
Kalaman soyayya masu dadin gaske
Godiya tamusamman my lovely flower ina godiya da kulawarka akaina ngd
My lovely one kana araina dan allah mekamin na yarda dakai lkc guda bayan kuma ni ba haka nakeba yarda da namiji lkc daya, kuma anya kanasona kuwa, nasan kana sona a baki amma bansan xuci ba ma,awuya suna mai dd kuma mai shiga rai help to me
Ammafa idan harkana sonah ya kamata ka nunamin kulawa aha
Hi Yan Mata dafatar kina cikin nutsuwa ana sauraren waazi dakyau, kinsace zuciyata Soyayyarki ta mamayeni tunanin ki yazama aikina kowane lokaci Love U! So Much
Kalaman love
Slm allah sarki babynah dafatan ruwa basu taremin kaiba akace bidar halak da wuya allah baka halalinka kuma ya azzirtaka da halar dinka brk da shan ruwa
Babbar yarinya kin sace Zuciya ta, tunaninki Dakuma Jin muryarki sune muradina dafatar zaki wayi gari lafiya Love U!
Sorry babynah kasan wllh inasonka banasone ka cutamin amma kayi hkr kaji my blood and heart
Da girman kujerarka dafatan ansha ruwa lfy brk da dawowaKalaman Soyayya
“MATARKA
1. Idan tayi fushi jawota jikinka
2. Idan kaga tayi shiru tambayeta meye matsalarta
3. Idan tayi kwalliya ka yabawa kwalliyarta
4. Idan tayi girki kaci kana santi, Koda bai yi yadda kake so ba
5. Idan tace zata matsa daga kusa da kai riqeta kace baka yarda ba
6. Idan kaga tana kuka sa bakinka ka tsotse hawayenta
7. Idan kaga tana kishinka kyaleta kar ka kyareta
8. Duk sanda zaka fita ka sumbace ta agoshinta
9. Kana kasuwa ko office kirata ta waya kace kana kewarta
10. Kada kalmar (ina sonki ta dinga yiwa harshenka nisa)
Shawarace nidai nabita nanhkKalaman Soyayya
20. Masoyiya ta Halimatut Sadiya, Shin wani ya taba sanar da ke cewa murmushin ki abin so ne?
Sannan kuma a duk lokacin da kike yin murmushi ya kan mayar da fuskar ki tamkar wata fitila mai haske?
Ke kyakkyawa ce, hakan ya sanya kwakwalwata ta zana mini kyakkyawar fuskar ki a cikin zuciyata wacce ta zamo abar nazarta a gare ni a duk lokacin da nake zaune ni ɗaya cikin kaɗ’aici a dare ko safiya.
Ke ce abar so na.
21. A duk lokacin da na zauna ina yin nazari a dangane da soyayyar mu, sai nai hasashen cewa dama a ce fika-fikai za su bayyana a jikina da na nausa da ke izuwa kayatacciyar fadar dake can babban birnin masoya na sabuwar duniyar mu domin sada ki da kujerar alfarma ta mukamin sarauniyar ‘yan matan duniya da na dade da baki.
Shin Halima kin kuwa lura da cewa ina neman na zama zautacce a cikin soyayyar ki?
Na nitse a cikin son ki ta yadda ba zan iya fita ba.
Soyayyar mu ta dabance a cikin wannan duniya ta mu da muke ciki.
Soyayyar mu ta zamto tamkar wani rubutaccen labari ne wanda masoya za su shekara suna nazari a kanta.
Fatana dai mafarkina ya zamo gaskiya a dangane da ke.Kalaman Soyayya
KI YARDA DA NI.
15. A dukkan lokacin da dare ya yi, ki ɗaga kanki sama ki kalli sararin samaniya, za ki ga wani tauraro yana saukowa izuwa gare ki.
Karda ki yi mamakin me ya sa haka ya faru? Ki yarda da ni, hakan zai iya faruwa a zahiri domin kuwa ni ma na yi hakan har ta kai ga na same ki. Hmm!
Ki Huta Lafiya.
INA SON KASANCEWA A TARE DA KE HAR ABADA.
16. A lokacin da na samu soyayyarki sai na ji tamkar ni ne na fi kowa sa’a a duniya.
A dukkan sanda na rintse idanuwa na sai na hango ni tare da ke muna tafiya a bisa gajimare.
Idan na kwanta bacci sai na yi mafarkin mun zama mata da miji.
Ina sonki, tare da son kasancewa a tare da ke har abada. Ki Huta Lafiya.
A CIKIN IDANUWANKI AKWAI WANI SIRRI.
17. Sama cike take da taurari masu hasken da ke haske duniya a cikin kowanne dare.
Amma haske mafi haskaka fuska da yaye duhun zuciya, na gan shi ne a cikin idanuwan ki.
Ki Kula Min Da Kanki. Ina Son ki.
HARSHEN ZUCIYA.
18. Furanni na furta kalmomin yabo a kanki a dukkan lokacin da na shiga lambu mai d’auke da ‘korama gami da korayen ciyayi da bishiyu masu d’auke da tsintsaye.
Sukan rera baitukan yabo a gare ki, cikin harshen da zuciya ce kawai ke iya fahimtarsa. Ina Son Ki.
BA ZAN IYA RAYUWA IDAN BA TARE DA KE BA.
19. A mafarki da kuma a cikin soyayya babu abun da ba zai iya faruwa ba.
Ina son ki sosai hakan ya sa nake ji tamkar ba zan iya rayuwa idan ba tare da ke ba.
Ba na fatan rasa ki a rayuwa ta, domin kuwa a dukkan lokacin da na rasa ki, na tabbatar da rayuwa ta za ta shiga garari.
Ina Son Ki kuma ba zan taɓa canjawa a kan hakan ba.
Kalaman Soyayya
Duk wani hoto wanda kaga ni a jikin wannan Video Idan Ka/Ki san me hotan, ba muyi amfani da hotan Ka/Ki domin wata manufa ba , sai dai kawai domin isar da saƙon cikin Nishaɗi.
Dafatan Kai/Ke zaku yi mana Kyakykyawar Fahimta.
Mungode!
KIN ZARCE SAURAN MATA.
10. Ina neman wata kalma wadda babu wanda ya santa. Ina neman wata kalma da zan furta miki cewa…..ke ta daban ce, ke kyakkyawa ce, kin zarce sauran mata.
Zuciya ta da taki ba za su ta6a rabuwa ba har abada. Ina son ki.
SINADARIN RAYUWA TA.
11. SO shi ne abun da ya dun’kule zuciyoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba za ki bari wani d’an ‘karamin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? Ina son ki.
Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Ki Huta Lafiya.
ZAN SO KI JI.
12. Da akwai wasu tarin tsintsaye da suke wuni suna tattauna batutuwa a kan irin matsayin da na baki a cikin zuciya ta.
Zan so ki ji irin abun da suke cewa, domin kuwa a lokacin ne za ki tabbatar da irin son da nake yi miki. Ina Son Ki!
KE CE MURMUSHI NA.
13 Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniya.
Da a ce zan tsunko kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba.
Ke ce murmushi na, kuma ke ce farin-ciki na. Ina Son Ki.
SONKI NA MOTSAWA A ZUCIYA TA.
14. Ni M. Kabir Muhammad Da akwai wasu lokuta da nake zubar da hawaye saboda ke, na san za ki ce saboda me?…..
Da akwai wani lokaci da yake zuwa na ji tamkar na yi fika-fikai na tashi sama…..Kin kuwa san duk saboda mene ne?
Saboda motsawar sonki a cikin zuciya ta da tsintar kaina a cikin matsanancin shauƙi a dukkan lokacin da na ji muryarki ko na tina da ke….
Ina fatan za ki amince mu rayu a tare har abada. Ina Son Ki!Kalaman Soyayya
NA SHIDA.
SO tamkar kurbar ruwan shayi yake mai tsananin zafi, a karon farko zaka kasance cikin shaukin begen shi wanda daga bisani kuma zai ƙona maka harshe na tsawan lokacin da zaka shafe kana yin jinyar shi.
NA BAKWAI.
Soyayyar da na ke yi miki tamkar tafiyace mai nisa da na fara yinta wadda bata da lokacin yankewa har abada.
Na san burina zai cika matukar ina tare da ke domin kuwa dukkanin burina yanzu bai wuce na samun ki a matsayin matata uwar ‘ya’yana ba.
Ina son ki fiye da gwal ko kuɗi.
NA TAKWAS.
Karda ki fadawa kowa kalaman sirrin bude soyayya da kawancen dake tsakanin mu, domin kuwa a dukkan lokacin da kika furta wadannan kalaman sirri ga wani wato “INA SON KA”
Hakan na nuni da cewa zai yi amfani da shi wajen bude mana akwatin soyayyar mu ta sirri wanda hakan zai bashi damar yi mana gagarumar sata har ya yi sanadiyar raba ni da ke har abada. Ina son ki.
NA TARA.
Na yi shiri tare da niyar turo miki da dikkanin soyayyata amma sai dai wanda zan turo da sakon nawa gare ki ta hannun shi ya bayyana hakan a matsayin wani babban abu da zai gagari bil’adama d’auka, amma karda ki damu zan zo nan bada daɗewa ba domin ki tabbatar da abun da na ke faɗa gaskiya ne, dama an ce zuwa da kai ya fi saƙo.
Ki huta lafiya farin cikin zuciyata.
Ina son ki.
Kalaman Soyayya 4
Soyayya Ruwan Zuma
Idan ba zaku manta ba a kwankin baya mun kawo muku Sakonnin Soyayya Guda 32 cikin Audio Insha Allah a yau kuma ga rubutattun sakonnin soyayya 32 domin kara dankon soyayya.
NA ‘DAYA.
Ke kamar hasken wata ki ke mai hasken da ke haske idaniya,
haka kuma kalamanki tamkar siga suke ma’abocin za’ki, tabbas kin yi kama da kanki hakan ya sanya na ji ina son ki.
NA BIYU.
A lokacin da kika ji kina son wani, to yi maza ki adana sunan shi a cikin ɗaya daga cikin kogunan da ke a cikin zuciyarki,
Domin kuwa ita zuciya takan iya raunata a kowanne lokaci amma shi kogon zuciya ya kan kasance tare da ajiyar da aka yi a cikin shi har abada.
Ina fatan zan kasance ni ne wanda za ki adana a ma6oya mafi sirrinta soyayya da masoyi? Ina son ki.
NA UKU.
Sauda yawan lokaci idanuwana sukan yi kishi da zuciyata!!! Kin kuwa san mene ne dalili? Saboda a koda yaushe kece abu mafi kusanci da zuciyar tawa su kuma idanuwa kin kasance mai yin nesa da su.
Ina son ki saboda zuciya ɗaya.
NA HU’DU.
Na kasance ma’abocin soyayya zuciyatama ta gaskata hakan, lokaci na shuɗewa soyayyar ki na ƙaruwa a cikin zuciyata,
A lokacin da ki ke cikin farin ciki kyakkyawar fuskar ki na bayyanar da murmushi mai taushi da tausasa zuciyar ma’abocin kallonta,
Kece wadda na ke so a cikin zuciyata babu wata da zata iya canja matsayin ki a wajena. Ina ƙaunar ki.
NA BIYAR.
SO tamkar rayuwane, ba ko yaushe yake zamowa abu mai sauki ba haka kuma ba a koda yaushe yake wanzar da farin ciki ba, to amma mene ne zai sa matukar muna raye da rai da lafiya za mu yanke alakar soyayya a tsakanin mu?
Har zuwa yau babu kamar ki a cikin zuciyata domin kuwa jin muryar ki a kullum na rubanya adadin soyayyar da na ke yi miki a cikin ko wane dare ko safiya.
Karda ki rabu da ni dan Allah, domin hakan zai iya sanyawa na zamo mutum mai rauni a rayuwata.
Kalaman Soyayya
Kalaman soyayya
zafafan kalaman soyayya da ke jefa mata a tarkon kauna
zafafan kalaman soyayya da ke jefa mata a tarkon kauna Hakika ke kyakkyawa ce, tamkar zinariya ga iya takun kasaita tamkar jimina, kwalliyarki na rikita mai kallonki
zafafan kalaman soyayya da ke jefa mata a tarkon kauna
zafafan kalaman soyayya da ke jefa mata a tarkon kauna
Hakika ke kyakkyawa ce, tamkar zinariya ga iya takun kasaita tamkar jimina, kwalliyarki na rikita mai kallonki
kalaman sanyaya zuciya, yabon masoyi, kogin soyayya, yadda zaka sace zuciyar budurwa, ko da kauna, masoya, rayuwar masoya,
zafafan kalaman soyayya da ke jefa mata a tarkon kauna
Hakika ke kyakkyawa ce, tamkar zinariya ga iya takun kasaita tamkar jimina, kwalliyarki na rikita mai kallonki, surar jikinki na sanya maza tuntube har su fadi basu sani ba.
Hakika ke yar gidan manya ce yar gida mai asali da kuma tarbiyya, hakika ke yar babban gida ce kin fito daga gidan mutunci sannan kuma karamci da kawaici da tausayi da kuma kyautatawa dukkan su halaye na da suka fito daga gidanku.
Tabbas duk wanda ya sameki a matsayin matar aure ya gama samun komai a duniya, sai dai kawai ya jira lahirarsa ta yi kyau.
Na yi alkawarin maishe da ke tamkar sarauniya a cikin gida na mudfdin ki ka aureni, sannan kuma na yi alkawarin tanadar miki da dukkan farincki a cikin gidana ta yadda za ki manta da wata kalma da ake kira damuwa.
Kedai kawai ki bani dama ta hanyar mallaka nimi zuciyarki, ma’ana ki bani soyayyarki ni kuma zan baki kulawar da duk duniya ba namijin da zai iya baki kamar ta.Kalaman Soyayya
INA SONKA MASOYI NA!
Tsuntsaye na bu’katar fukafukai domin tashi, kifi na bu’katar ruwa domin ya yi rayuwa, ni kuma ina bu’katarka domin na yi rayuwar farin-ciki. Ina son ka masoyi na!
MU KASANCE A TARE.
Ina son jinka a kusa da ni, ta yadda numfashi na da naka zasu gauraya, ta yadda zan ke juyo sautin bugun zuciyoyinmu na fita a tare. Mu kasance a tare har abada. Ina Son Ka!
INA FATAN MAFARKI NA YA ZAMA GASKIYA.
A kullum na kwanta bacci, na kan yi mafarkin ka zama uban ‘ya’ya na, ni kuma na zama mata a gare ka.
Sai dai na san iya mafarki ba zai wadatar da ni ba a bisa kulawar da nake tinanin samu daga wajenka. A saboda haka nake fatan mafarki na ya zama gaskiya watarana. Ina Son Ka!
MASOYI NA.
Ina Son Ka, zan kuma ci-gaba da sonka tun daga futowar rana har izuwa fad’uwarta a cikin kowace rana har abada. Ka Huta Lafiya.
KA ZAMA RUHI NA.
Ina fatan ka fahimci manufa ta? ina fatan ka gane nufi na a kanka? Zan rayu ne cikin sonka har zuwa ranar ‘karshe, saboda kai ba saurayi ne kawai a waje na ba, ka zama ruhi na, sonka na yawo ne a cikin jinin da ke gudana a jiki na. Ina Son Ka!Kalaman Soyayya
KIN ZARCE SAURAN MATA
Ina neman wata kalma wadda babu wanda ya santa. Ina neman wata kalma da zan furta miki cewa…..ke ta daban ce, ke kyakkyawa ce, kin zarce sauran mata. Zuciya ta da taki ba za su taɓa rabuwa ba har abada. Ina son ki.
SINADARIN RAYUWA TA.
SO shi ne abun da ya dun’kule zuciyoyinmu waje guda har muka tsinci kanmu a cikin soyayya, ina fatan ba za ki bari wani d’an ‘karamin abu ya zo ya raba tsakaninmu ba? Ina son ki. Ke tamkar gishiri ce a cikin rayuwa ta, idan na rasa ki zan yi rayuwa ne da babu armashi a cikinta. Ki Huta Lafiya.
ZAN SO KI JI.
Da akwai wasu tarin tsintsaye da suke wuni suna tattauna batutuwa a kan irin matsayin da na baki a cikin zuciya ta. Zan so ki ji irin abun da suke cewa, domin kuwa a lokacin ne za ki tabbatar da irin son da nake yi miki. Ina Son Ki!
KE CE MURMUSHI NA.
Da akwai miliyoyin furanni a cikin lambun masoya a wannan duniya. Da a ce zan tsunko kowanne fure na baki shi a hannunki, hakan bai isa ya bayyanar da adadin yadda nake son ki ba. Ke ce murmushi na, kuma ke ce farin-ciki na. Ina Son Ki.
SONKI NA MOTSAWA A ZUCIYA TA.
Da akwai wasu lokuta da nake zubar da hawaye saboda ke, na san za ki ce saboda me?…..Da akwai wani lokaci da yake zuwa na ji tamkar na yi fikafikai na tashi sama…..Kin kuwa san duk saboda mene ne? Saboda motsawar sonki a cikin zuciya ta da tsintar kaina a cikin matsanancin shau’ki a dukkan lokacin da na ji muryarki ko na tina da ke…..Ina fatan za ki amince mu rayu a tare har abada. Ina Son Ki!.
Add Comment