Gidan Abdallah Hausa Novel Complete
*GIDAN ABDALLAH*
*BY*
*MOMMYN MUSADDIQ*
*ADABI WRITERS ASSOCIATED*
*FREE PAGE*
*PAGE 1*
“Abban Na’emm dan Allah ka
tsaya ka saurare ni.” Ta fad’a tana
k’arasowa gaban sa da sauri.
Tsayawa yayi ya kura mata idanu
yana kallon katon cikin ta da yake
haihuwa yau ko gobe.
“Wai menene matsalar ki Jiddah?
Tun d’azu kin dameni ban san me
kike so ba, dan Allah ki barni na
huta.” Ya fad’a yana sake Jan jikin
sa yana son fita.
“Kasan dai bamu da abin da za mu
ci a cikin gidan nan, abin cin mu
duk ya k’are ga shi yanzu Yara sun
kusan dawowa daga makaranta
suna dawowa zasu nemi abin ci.”
Cak ya tsaya kafin ya juyo ya kalle
ta sannan yace
“Amman Jiddah yaushe aka kawo
kayan abin ci gidan nan? Kina
nufin ba abin cin da zaku ci a
store?”
“Babu komai.” Ta fad’a a sanyaye.
Shiru ya d’anyi kafin yace
“Ni dai Kinga yanzu ina da wajen
zuwa akwai alk’awarin da nayi
zamu had’u, Amman ga wannan
Ya fad’a yana ciro 200
a aljihun sa yana mik’a mata.
Kallon kud’in kawai take ba tare
da ta saka hannu ta karb’a ba, sai
hawaye da suka cika Mata idanu
jikin ta na rawa, dan ita kanta
Jiddah rabon ta da abin ci tun
na daren jiya, yau da safe Basu
da abinda zasu dafa suka tashi
sai guntun abin cin jiya shine ta
dumama ta baiwa Yara suka ci
sannan suka tafi makaranta…katse
mata tunani yayi da cewa
“Idan bazaki karb’a ba ni zan tafi
kina b’ata mun lokaci.”
Hannu tasa ta karb’i kud’in idanun
ta cike da hawaye tace
“Amman Abban Na’eem 200 ba zai
ishemu ba ka sani, yara biyar ga
Gwaggo ga me gadi ga ni kuma, don Allah ka
k’ara mana.”
Tsaki yajaa tare da barin wajen ba
tare da ya tsaya amsa mata ba.
Babban tsakar gidan sa ya fito
Wanda yake d’auke da b’angarori
da dama, wani b’angare ya shiga
bakin sa d’auke da sallama.
Wata dattijuwar Mace ce ta amsa
masa tare da cewa
“Abdallahn Gwaggon sa sai yanzu
ka fito?” Ta fad’a tana karewa d’an
nata kallo cike da tsantsar so.
Zama yayi a gefen ta kafin yace
“Wllh Gwaggona sai yanzu na
samu fitowa, da fatan kin tashi
lafiya?”
“Lafiya k’alau na tashi Abdallah
sai dai tun d’azu yunwa yake
kwakulata tamkar na ci babu, yau
Jiddah batayi girki ba ne?”
Ba tare da ya bata amsar tambayar
da ta mishi ba ya ce
“Ina kayan shayin da na siya Miki
Gwaggo? kika zauna da yunwa har
wannan lokacin?”
YNYN Hausa Novel Complete
Wani kallo ta mishi tace
“Kaji mun wani banzan zance a
wajen yaron nan, Allah na tuba
shayi kuma me zai mun, tun safe
Nasha amman bai rik’e mun komai
ba, kaga tashi kaje ka amso mun
abin kari a wajen Jiddah.”
“Kinga Gwaggo yau fa batayi girki
ba Wai kayan abin ci ya kare,
Amman na bata kud’i ta siya muku
ga ri kafin na dawo.”ya fad’a ya na
k’ok’arin mik’ewa.
Da sauri Gwaggo ta rik’o
tsadadden shaddar sa ta dawo
dashi baya ya zauna tare da cewa
“Abdallah baka da hankali ne?
Ga ri fa kace? Nice zan ci gari Ina
uwar ka Abdallah.” Gwaggo ta
fad’a tana fashewa da kuka.
Rik’o hannayen ta Abdallah yayi
ya ce “Haba Gwaggo na menene na
kuka a nan don Allah? Kiyi hakuri
ki fad’i abin da kikeso yanzu a siya
Miki.”
Kallon sa Gwaggo tayi murmushi
d’auke a fuskan ta kamar ba itace me kuka ba ta ce
“Yauwa d’an albarka gashashen
kaza nakeso me zafi da zan ci na
k’oshi.”
“Yanzu zan baiwa Yahuza ya siyo
Miki.”
“Yauwa Allah yayi maka albarka,
sai Abu na biyu, Wai sai yaushe
wannan figaggiyar Sameeran zata
dawo ne? Ta tafi yau kusan sati
biyu amman shiru ba labarin
dawowar ta.”
“Gobe idan Allah ya yarda zata
dawo Gwaggo.”
Tab’e baki Gwaggo tayi tace
“Ni fa ban san amfanin auren ta
da kayi ba Abdallah, yau shekara
da aure Amman yariya shiru ba
ciki bare haihuwa,ni Kam gaskiya
na gaji da ganin ta haka.” Ta fad’a
tana rafka Uban tagumi.
Murmushi Abdallah yayi yace
“Gwaggo na kwantar da hankalin
ki cire wannan tagumin me kikeso
ayi?” Ya fad’a yana gyara zaman sa.
“Ka fi kowa sanin buri na
Abdallah, saboda haka inason kaje
ka sake auro wata matar, ko ‘yar
gidan Uban waye nasan zaka iya
auro ta bazata gagareka ba tunda
Allah ya hure maka arziki.”
Abdallah da fuskan sa ta cika da
murmushi ya ce
“Yanzu haka akwai yariyar da
nake so na aura Gwaggo sai dai
banje musu da maganar aure ba
da yake suna shirye-shirye bikin
yayar ta nan da sati uku idan
akayi na yayar ta ta sai Nima naje
neman na ta auren.” Ya fad’a yana kallon Gwaggo da ta nutsu tana
sauraren sa.
Da sauri Gwaggo tace
“Toh Kai me zaka jira Abdallah?
ai sauri zamuyi kawai a had’a da
na yayar ta ta duk mu huta, yanzu
zan kira Dahiru ayi maza suje
neman auren kawai mu huta.” Ta
fad’a tana sake gyara zama.
Abdallah da farin ciki ya lullub’e
shi lokaci guda ya ce
“Toh Gwaggo Amman kafin ki
fad’awa su kawu Dahirun ki
bari naje muyi magana da ita
Fateemah, idan muka gama
tattauna komai Shikenan sai su
shiga da maganar”
“Toh Shikenan Allah ya taimaka ya
bada sa’a.”
“Amin Gwaggo Bari na wuce sai na
dawo.”
“Toh a dawo lafiya, karka mance
da kazar tawa ina jira.”
“Yanzu za’a kawo in sha Allah.” Ya
fad’a ya na fita daga d’akin.
Wajen adana motoci ya nufa
inda manyan motoci gudu uku
suke a jere, wata farar mota Mai
kyau ya shiga, da sauri Mai gadi ya
nufi k’ofar da sauri yaje ya bud’e
mishi.
Tsayawa yayi a bakin gate d’in tare da lek’o kanshi yace “Yahuza gashi dan Allah ka siyowa
Gwaggo gashashen kaza me kyau a bakin layi.” Ya fad’a ya na mik’a mishi kud’i, da sauri ya karb’a tare
da amsawa.
Figar motar Abdallah yayi da gudu yahau babban titi Wanda tafiyar mintuna goma ta kawo shi k’ofar gidan su Fateemah.
Wayar sa ya d’auka ya kira number ta, ba tare da ya dad’e Ya na ringing ba ta d’auka tare da yin sallama cikin zazzakar muryar ta.
Amsawa yavyi kafin ya sanar da ita yana k’ofar gida, amsa mishi tayi da gata nan zuwa sannan ta katse kiran.
Ba’a d’auki lokaci me tsayi ba ta fito cikin k’ananun kaya da sukayi matukar mata kyau, gashi kuma ya fito da surar jikin ta baki d’aya.
Sallama ta mishi tana wani
kararraya tana juya idanu ga shi ko d’an mayafi bata saka ba,
Abdallah da tun fitowar ta ya
kura mata idanu yana kallon irin halittar da Allah yayi mata, ajiyar
zuci ya sauke kafin yace “Barka da fitowa Sarauniya ta.” Ya fad’a ya na Bud’e mata mota.
Shiga tayi ta zauna kafin tace
“Ka kusan sab’a alk’awari Abdallah
abinda baka tab’a mun ba.” Ta
fad’a tana kallon sa.
Gyara zaman sa Abdallah yayi yana fuskan tar ta da kyau ya ce “Sorry Baby na tsaya wata muhimmiyar magana ne da Gwaggo shiyasa kikaji shiru,Amman Ina neman afuwan ki.”ya yi maganar ya na had’a hannayen sa waje d’aya alamun
neman afuwa.
Murmushi ta sakar masa tare da
juya idanun ta ta ce “Toh baka da matsala yarima na,
Ina fatan kana lafiya.” “Lafiya k’alau Fateemah,da fatan kema kina lafiya gimbiya ta.” “Lafiya K’alau nake, sai gajiyar zirga-zirga da muke ta fama.” “Toh hakan kuwa yayi kyau sosai, Daman magana nazo muyi magana mai muhimmanci
Fateemah, ina son a had’a auren
mu da na Aunty Aysha.”
Da sauri Fateemah ta d’aga Kai ta kalle shi tare da ce wa
“Me kake cewa ne Abdallah? auren
Aunty Aysha fa Nan da 3 weeks ne, ya za’ayi a had’a da na wa?”
Murmushi Abdallah yayi yace “Haba Fateemah ya kina magana kamar ba wayayyar yariya ba,
menene Dan nan da 3 weeks
ne? Naga dai idan da kud’i babu abinda bazaiyu ba, toh inaso Nima ayi namu a wannan lokacin ko nawa zan iya kashewa Dan na
mallakeki Fateemah.” Ya fad’a Ya
na sake kallon ta ganin tayi shiru
tana sauraran sa.
Numfashi ta sauke kafin ta ce
“Ok idan dai har zaka iya Abdallah ba wata matsala, Amman ka sani zaka kashe kud’i da yawa dan kaga shirin gaggawa ne zai buk’aci
kud’i.”
Murmushi Abdallah yayi ya ce
“baki da matsala indai ta wannan
b’angaren ne Fateemah, nidai buri na naga na mallakeki a matsayin matar aure na, inaso yanxu idan kin shiga gida ki sanar da su Mama zan turo da magaba ta na.”
“In sha Allah zan sanar dasu.”
Sun dad’e sosai suna hira kafin
sukayi sallama Abdallah ya tafi bayan ya bata kud’ad’e masu yawa.
A hankali Jiddah take d’aga kafafun ta dan wani irin nauyi taji sunyi mata, a hankali take takawa har ta K’arasa part d’in Gwaggo, da sallama ta shiga cikin falon na ta,
Gwaggo da take cin kaza tana jin muryan Jiddah tayi saurin turawa k’asa kujera tare da cewa “Wanene da uban ranar nan
haka?” Ta fad’a tana goge hannun ta a jikin zanin ta.
D’aga labulen Jiddah tayi tace “Nice Gwaggo.” Shigowa tayi ta
samu kasan kafet ta zauna kafin ta
gaishe ta.
Amsawa Gwaggo tayi tana Kare
mata kallo ta ce
“Sannu Hauwa’u da alama
cikin nan yana wahalar da ke.”
Murmushin k’arfin hali Jiddah tayi
tace
“Gwaggo daman ga ri ne da Ya
Abdallah ya bada kud’i ya ce aa siya na kawo miki Kar yunwa ya dameki.” Ta fad’a tana ajiye filas d’in, Tab’e baki Gwaggo tayi tace “Aa Jiddah d’auki ki tafi da abar nan ni ba iya ci zanyi ba, zan daure har zuwa lokacin da za’a
dafa abin cin sai na ci.”
Kallon Gwaggo Jiddah tayi tace “Haba Gwaggo ya zaki zauna da yunwa da kinyi hakuri ko ya ya ne kin ci kafin Ya Abdallah ya dawo.”
“Ke karki takura mun bazan ci ba, ke da naga yunwa a idanun ki ki
d’auka ki ci na bar miki Amman
Nikam ko kallon sa bazanyi ba, maza d’auki ki fitar da shi aiki
zanyi.”
Mikewa Jiddah tayi sannan ta d’auke filas d’in ta fito daga d’akin
Gwaggo ta nufi nata d’akin.
Zama tayi akan kujera tana sauke numfashi, tabbas zaman gidan
Abdallah baya mata dad’i ko kad’an toh Amman ya ta iya tunda
Allah yasa shine mijin ta uban ‘ya’yan ta, idan bata zauna don soyayyar da take mishi ba zata zauna kodan ‘ya’yan ta.
Ta dad’e zaune a haka kafin ta
bud’e filas d’in ga rin ta soma ci.
Sai da ta gama tas sannan ta mik’e ta nufi kicin ta had’a na yaran taWanda yanzu daf suke da dawowa daga makaranta.
***********
“Ni fa gaskiya Ummah Ya Abdallah nake so, shi nakeso na aura wllh bayan shi bazan auri ko wanne namiji ba.” Cewar Meenah wacce suke zaune da mahaifiyar ta a d’aki.
Kallon ta Ummah tayi tace “Wai Meenah me Kika gani a jikin
Abdallah ne da Kika na ce masa,
kinsan fa shi ko kallon kirki baya
miki.”
“Tabbas Ummah naga abubuwa da yawa a jikin Abdallah, ga kud’i ga kyau ga wadataccen muhalli, na ci me kyau nasha Mai kyau na saka suturar da naga dama, Ummah nifa wllh Abdallah yayi mun
100%.”
Murmushi Ummah tayi ta ce “Toh ke yanzu Meenah ya zakiyi ki same shi? Kinsan fa shegen girman kan Abdallah mutumin da idan ya shigo gidan nan gaishe da mahaifin ki ko kallon ki baya yi.”
Ta fad’a tana kallon Meenah da ta
kura mata idanu.
“Haba Ummah na dan Allah Ina da
ke a duniyar nan zan nemi wani
abu na rasa ne? Na sani Ummah ke
d’in uwa ta ce idan nace Miki ina
son abu nasan ko ta halin k’ak’a sai
kin nema mun abin.”
Dariya Ummah tayi tace “Haka ne Meenah, ni Kai na ina son ki shiga “GIDAN ABDALLAH*
ko dan ki cika mun buri na.”
Kallon Ummah Meenah tayi ta ce “kema kina da wani buri game da
Abdallah ne Ummah?.”
Murmushi kawai Ummah tayi ta
ce “tabbas Ina da buri ka da dama
amman bazan fad’a Miki yanzu ba har sai bayan auren ku, zan cika
Miki burin ki na shiga GIDAN
ABDALLAH ko da kuwa zanyi yawo tsirara ne Meenah.”
Wani mugun ihu Meenah ta saka tare da rungumo Ummah ta ce “Nagode sosai Ummah na, shiyasa
nake son ki sosai.” Ta fad’a tana
kissing nata a goshi.
Dariya Ummah ma tayi ta ce “Ke kadai ce’ya ta kaf duniyar Nan saboda haka dole nayi Miki duk
abin da kike so.”
Wani mugun ihu Meenah ta saka tare da rungumo Ummah ta ce “Nagode sosai Ummah na, shiyasa
nake son ki sosai.” Ta fad’a tana
kissing nata a goshi.
Dariya Ummah ma tayi ta ce “Ke kadai ce ‘ya ta kaf duniyar Nan saboda haka dole nayi Miki duk abin da kike so.”
**********
“Amman kina ganin babu wata matsala Mama, kin gadai auren
Aunty Aysha sati uku ne kawai ya rage.
Murmushi Mama tayi tace
“Babu wata matsala Teemah ke dai
kawai ki fara shirye-shirye kamar yanda yayar ki take yi, in sha Allah
auren ku tare za’a d’aura, tun dai
har ya ce zai iya ai Shikenan.” Ta fad’a tana mik’ewa Jin sallaman
Mai gidan ta.
Amsa mishi tayi sannan ya k’araso cikin falon, Zama yayi daga d’aya cikin manya-manyan kujerun falon, Mama ma zama tayi kafin ta
mishi sannu da zuwa.
Amsawa ya yi yana kallon
Fateemah da itama sannu da
zuwan take mishi, bai amsa ba sai
cewa ya yi “Wai ke Fateemah ban hanaki saka
wad’an Nan banzan kayan ba?
Meyasa bakya jin magana ta ne?
Kusan kullum sai na fad’a miki
Amman duk ta bayan kunnen ki yake wucewa ko?” Ya fad’a a d’an
tsawace.
Turo baki Fateemah tayi tare da mik’ewa tabar falon tana bubbuga k’afafu.
Kallon Mama yayi ya ce “duk ke
Kika sangarta yariyar nan Naja sam bakya mata fad’a akan duk
wani abu da take aikatawa.”
Murmushi Mama kawai tayi tace “Alhaji da zakayi shiru ka saurareni yafi wannan surutun da kake yi, yanzu fa Fateemah ta girma ba k’aramar yariya ba ce, tana da yan cin yin duk wani abu da take so, sannan ni yanzu ba wannan ba, Abdallah da yake neman auren Fateemah ne ya ce
zai turo a had’a auren su da na
Aysha.”
Kallon Mama Alhaji Idris ya yi da
sauri tare da furta “Alhamduiilan
Allah na gode maka, Naji dadin labarin nan sosai Naja, domin wllh kullum abin da yake damuna kenan wannan yariyar, kullum
Addu’ar da nake shine Allah ya fito mata da miji na gari Wanda zai iya
da halin ta.”
Tab’e baki Mama tayi ta ce “Ko ma dai menene yanzu sai ka fara shiri har da Fateemah, ka tura itama ayi Mata order kayan gado tunda an riga da anyi na
Aysha,Kuma Alhaji kasan gida da kishiyoyi har biyu inason kayiwa
Fateemah abinda ba kayiwa Aysha ba saboda kishiyoyin ta Kar su
samu abin goranta mata su rai na
ta.”
Murmushi irin na manya Alhaji yayi ya ce “Naja kenan! Bazan matsantawa
Kai na a banza akan wani banzan
tunanin ku irin na mata ba, abin da yake arzik’ina shi zanyi mata bayan haka bazan kara da komai ba.” Yana gama fad’an haka ya mik’e yabar falon.
*********
Daddare da misalin k’arfe tara
Abdallah ya dawo gida, direct wajen Gwaggo ya wuce sai da suka tattauna sosai dangane da maganar auren sa, dan har sai da Gwaggo ta Kira Kawu
Dahiru ta sanar dashi akan gobe zasuje nemawa Abdallah aure, sai kusan goma da rabi ya shiga d’akin Jiddah bayan sun gama tattaunawa da Gwaggo.
Yaran gabaki d’ayan su sunyi barci suna d’akin su, ita kad’ai ce zaune
a falo tana kallo, sai dai a zahiri ne
zakaga kamar kallon take, Amman
a bad’ini tunani take sosai Wanda
tayi zurfi a cikin sa.
Sam bataji sallaman Abdallah ba
sai Jin hannun sa tayi a kafad’ar ta
ya na ce wa
“Jiddah lafiyan ki kuwa?”
Ajiyar zuci ta sauke kafin ta d’aga
Kai ta kallesa ta ce
“Sannu da zuwa Abban Na’eem.”
Zama yayi tare da cewa “Yauwa ya kike?”
“Lafiya k’alau.” Ta fad’a tana kallon
sa kafin tace
“Na kawo maka abin ci?” Ta
tambaye sa dan tasan dakyar
Abdallah ya ci abin cin da suka girka.
“Aa ki barshi a koshe nake.”
Shiru Jiddah tayi domin daman tasan amsar da zai bata kenan, shiru ne ya biyo baya babu me magana a cikin su, sun d’auki
kusan mintuna 30 kafin Abdallah
ya d’auki hular sa ya Soma k’ok’arin mik’ewa, kallon sa Jiddah tayi tace “Abban Na’eem ina son magana da
Kai.”
Juyowa yayi ya kalleta tare da
cewa
“Wai ke Jiddah wacce irin mace ce? Tun d’azu ina zaune bakiyi
maganar ba sai da kikaga zan tashi sannan zakizo mun da wata
maganar banza.”
Cikin sanyin murya Jiddah tace “Kayi hakuri bana son na takura maka kana hutawa ne shiyasa banyi maka magana ba.”
Tsaki yajaa kafin ya ce “Fad’i inajin ki menene?”
Shiru ta d’anyi tana shakkan fad’a mishi abin da ke ran ta, dan bata
San yanda zai d’auki maganar ba, daure wa tayi ta ce
“Daman Abban Na’eem inason
Kaltum tazo ta zauna mun a gidan nan kafin Allah ya sauke ni lafiya, abubuwa sun mun yawa gashi nima kuma bana jin dad’in jiki na, ga kuma kula da yara da ai yukan cikin gida, shine nace Bari na fad’a
maka tazo tana taimaka mun.” Ta
fad’a tana kallon shi gaban ta ya na bugawa ganin irin kallon da yake
mata!.
*GIDAN ABDALLAH DAGA JIN SUNAN BA SAI NA FAD’A MUKU BA AKWAI RIKICI, CHAKWAKIYA, KISHI, KISSA, TARE DA DARUSA DA DAMA NA ZAMANTAKEWA TSAKANIN KISHIYOYI TARE DA UWAR MIJI IRIN GWAGGO, DAMA MIJI IRIN ABDALLAH, DA MACE ME HAKURI IRIN JIDDAH, DA MAKIRAR MACE IRIN MEENAH,DA MUGUWAR KISHIYA IRIN SAMEENAH KAI KUDE KU BIYA 500 KACAL TA WANNAN ACC DIN 3144651347 KHADIJA IBRAHIM SUNUSI FIRST BANK, SAI KI TURO MUN SHEDAN BIYA TA LAYIN NAN 08146196391 DOMIN JIN IRIN RIKICIN DA BADAK’ALAR DA KE CIKIN GIDAN ABDALLAH.*
*MOMMYN MUSADDIQ*
[ *GIDAN ABDALLAH*
*BY*
*MOMMYN MUSADDIQ*✍️
*ADABI WRITERS ASSOCIATED*
*MASU BUK’ATAR A TALLATA MUSU HAJARSU SU K’OFA A BUD’E TAKE KUMUN MGN TA WANNAN NUMBER 08446196391*
*FREE PAGE*
*PAGE 2*
“Amman da alama baki da hankali
Jiddah! haka kawai ki kawo mun wata cikin gida ta zauna saboda wata maganar ki da bata da hujja, toh Bari kiji bazan iya ba wllh, yanzu ba da bane kayan abin ci sunyi tsada bazan kawo wata k’atuwa ta karamun nauyi akan Wanda nake fama ba, idan dai dan aiyukan gida ne gobe Sameenah zata dawo
Kinga ai zaki huta, maganar yara kuwa yaran nawa ne? Ba Yara biyar ba, idan har bazaki iya kula
da su ba toh ki zauna Amman ban
amince da wata k’atuwa tazo ta
zauna mun a gida ba.” Yana gama fad’an haka ya shige d’aki yabar
Jiddah zaune tana hawaye.
Zama tayi a falon tasha kuka sosai kafin ta mik’e a hankali ta shiga d’aki, a kan gado ta samu Abdallah kwance yana waya da Fateemah, ganin Jiddah bai sashi yanke wayar ba sai ma dariya da yayi ya
ce
“Haba amarya ta karki damu da koma nawa ne ni Abdallah nayi
miki alk’awari kashe miki ko nawa
ne a shagalin bikin nan, sannan maganar anko kuwa gobe idan
Allah ya kaimu zan zo na d’auke ki muje shago ki zabi duk Wanda kikeso ki d’aukawa k’awayen ki, sannan ki Soma zab’an kayan lefen ki.” Shiru yayi alamun yana sauraren maganar ta, dariya yayi
ya ce “Karki damu Baby gobe zanzo mu k’arasa maganar, sai da safe.”
Ya fad’a yana katse wayar, kallon
Jiddah yayi wacce take tsaye a gefe
yace
“Wai ke Jiddah anya ba aljanu
bane da ke?
Shikenan ni a rayuwa na bazan huta ba, idan dai ina gida toh gabaki d’aya hankalin ki yana Kai na kina takura mun, nifa bazanbyarda da wannan iskancin ba.” Ya fad’a yana huce kamar zai d’auke ta da mari.
Share idanun ta Jiddah tayi tace
“Amman Abban Na’eem abinda
kayi ka kyauta kenan? A d’aki na a gado na kana kwance kana waya da wata, zan iya juran komai a wajen ka amman Banda cin fuska, haba dan Allah yanzu Kai idan akayi maka haka zakaji Dad’i?”
Abdallah da ya kura mata idanu yana kallon ta ya ce “Ke Jiddah ni kike fad’awa haka?
Nan gida na ne babu Uban Wanda ya bani ko sisi a lokacin da nake gina shi, har kina da iko mun magana dan Kinga Ina waya da wata, ok dan na kwanta a wannan banzan katak’on wanda ya gama mutuwa shine zaki nemi yimun rashin kunya ko?
To Bari kiji daga yau ni Abdallah
bazan sake kwana a wannan
banzan d’akin ba!” Yana gama fad’an haka ya d’auki kayan shi ya fita daga d’akin.
Zubewa a bakin gado Jiddah tayi ta fashe da kuka me tsuma zuciya, bata San me yake damun Abdallah ba amman abubuwan da yake mata sun soma yawa, da farko ta d’auka wani laifi ta mishi haka zataje ta durkusa ta nemi yafiyar sa akan su dawo daidai tamkar yanda suke da, Amman yanzu ta gama fahimtar Abdallah ya gaji da ita ne kawai, ya gaji da ganin ta a cikin gidan shi shiyasa yake azabtar da ita ta ko wanne b’angare.
Washe gari
Kawu Dahiru ne ya fito daga d’akin sa cikin manyan kaya shadda me matsakaicin kud’i, hular hannun sa ya saka a kanshi
tare da kwallawa matar sa kira
“Habiba!”
Da sauri Ummah ta fito daga
d’akin tana me amsa kiran da
mijin nata yayi mata.
Kallon sa tayi tace “Aa Malam fita zakayi ne?” Ta tambaye sa ganin yayi shirin fita
tsaf.
Gyara babban rigar sa yayi kafin
ya amsa mata da
“Eh wllh Habiba zamuje nemawa
Abdallah aure ne tare da su Malam
Ladan yanzu haka suna k’ofar gida suna jira na.”
Ummah da zuciyar ta ya buga da sauri ta dafe kirjinta tare da cewa “Ina shiga uku ni Habiba, Malam
bakasan cewa Ameenah tana son
Abdallah bane zakaje nema masa
auren wata?”
“Kamar ya bangane Ameenah tana
Son sa ba?
Dan ita tana son sa shi yace yana
son ta ne? Ni maganar da mukayi da su wata ‘ya daban yake so Kuma yanzu haka neman auren zamu
tafi karku kawo mun wani shiriri
ta a naku.” Yana fad’an haka ya fice yabar gidan.
Meenah da take lab’e a jikin labule
tana sauraron su ta fito da sauri
tare da cewa
“Na shiga uku Ummah Ya
Abdallah aure zai kara? Wlh
Ummah shi nakeso ki fad’awa
Abba ya dawo karsu je neman auren nan, idan har suka aura
mishi wata wllh kashe Kaina
zanyi.” Ta fad’a tana fashewa da
kuka.
Rungumota Ummah tayi tace “Haba Ameenah menene na tayar
da hankali?
idan ma yanzu sukaje aka d’aurawa Abdallah auren mata
uku ne fa, toh ni Kuma Ina Miki
albishir din kece ta hud’u kuma
Nan da wasu kwanaki kema
za’a d’aura Miki aure dashi,
ke dai kawai ki zuba idanu ki
ganni,amman bazan tab’a barin ki zubar da hawaye akan Abdallah
ba.”
“Toh Ummah dan Allah ki taimaka
mun, inason sa nasan Abba bazai tab’a goya mun baya ba har sai dai Ya Abdallah ne yazo da Kan sa
neman aure na.”
Murmushi Ummah tayi tace
“Ai kuwa Abdallah da kanshi zaizo
neman auren ki Meenah ta.”
Sosai Meenah ta shiga murna jin alk’awarin da Umman ta tayi mata Wanda tasan idan dai
ummah ce to tabbas sai ta cika
wannan alk’awarin indai har tana
numfashi a doron k’asa!.
Su Kawu Dahiru direct gidan
Abdallah suka nufa b’angaren
Gwaggo, gaisawa sukayi kafin
Gwaggo tayi musu bayani sosai game da yanda sukeson auren ya
kasance. sannan ta Kira Abdallah ta waya tace ya kawo sadaki a
had’a duka a Kai musu.
Da yake Abdallah baya rabuwa
da kud’i a d’akin sa dubu dari
biyar ya d’auko ya baiwa su Kawu
Dahiru Sannan ya Basu kudin da zasu siye goro da minti, duk su
Kawu Dahiru kuwa mamaki ne
ya kamasu ganin irin kud’in da
Abdallah ya basu na neman auren da zasuje masa.
Abdallah da kanshi ya d’auki su
Kawu a mota ya kaisu suka siye su goro sannan ya wuce dasu gidan
Alhaji Idris me kaji.
Kasancewar ansan da zuwan su
tarba na musamman akayi musu sannan suka gabatar da abinda sukazo nema, ba tare da b’ata
lokaci ba Alhaji Idris ya Amince
tare da karban sadakin su.
Koda su Kawu suka fito bayan sun kammala abinda sukazo yi babu
Abdallah Babu motar sa Kiran
sa sukayi a waya Amman sai ya tabbatar musu ai ya dawo gida tun
d’azu.
Napep su kawu suka hau suka koma gida suka sanar da Gwaggo duk yanda sukayi, sosai Gwaggo tayi murna jin Uban yariyar ma me kud’i ne, hakan ba k’aramin dad’i yayi mata ba, domin ita sam a rayuwar ta batason Abdallah ya shiga gidan matsiya ta, ko auren
Jiddah da yayi kawai dan ya nace
ne Amman ita Sam bataso haka
ba, sai Sameenah wacce itama ‘yar wani hamshakin me kud’i a garin
kaduna.
Misalin k’arfe sha biyu na rana
Sameenah ta shigo gidan ta, me gadi yana biye da ita da tulin kayan ta da tazo dashi.
Ak’ofar ta ya ajiye tare da sake juyawa domin d’auko wasu kayan da suke bakin gate.
Sanye take cikin doguwar rigar abaya wacce ta haska farar fatar ta duk da kana ganin ta kasan cewa ba farin Allah bane, kyakkyawa ce ba laifi tana da dogon hanci da idanu, a hankali take tauna cingam tana karewa gidan nata kallo, tsit gidan yake da alama Yara
duk suna makaranta, Jiddah Kuma
tana d’aki ko barci take ohoo.
Mukulli ta saka ta bud’e k’ofar
falon ta tare da d’aukan akwatin
ta ta shiga dashi, falon yayi kura sosai ko Ina busu-busu yake da kura, tsaki tajaa tana ajiye akwatin ta a gefe guda.
Fitowa tayi ganin Yahuza ya shigo
Mata da sauran kayan nata, kallon sa tayi tace “Yauwa Malam Yahuza nagode.”
Ta fad’a tana Jan kayan zuwa cikin falon.
Tsimma ta d’auko ta goge kujera
sannan ta fad’a a kai tana cewa
“Washh Allah bayana.” Ta fad’a tana kwanciya akan kujeran.
Ta dad’e a kwance kafin ta mik’e
ta d’auki tsintsiya ta Soma share falon sama-sama, sai da ta gama sannan ta gefa tsintsiya bayan k’ofa tare da d’aukan kayan ta ta
saka cikin bedroom d’in ta.
Cikin ma yayi kura Amman bataji zata iya sharewa a yanzu ba, hakan yasa ta ajiye kayan ta
sannan ta shigoa toilet domin yin
wanka.
Bayan ta fito shiryawa tayi cikin dogon rigar ta atamfa sannan ta d’auki k’aramin mayafi ta rufa kafin ta fito daga d’akin ta.
Part d’in Gwaggo ta nufa bakin ta d’auke da sallama, amsawa Mata
Gwaggo tayi tana me mik’ewa ta
zauna tare da cewa
“Aa ke kuma saukan yaushe?”
Zama tayi akan kujera kafin tace “Wllh Gwaggo na d’an dad’e da zuwa na tsaya hutawa ne shiyasa ban shigo ba, da fatan nasame ku lafiya?” “Lafya k’alau ya iyayen naki kuma, shiru-shiru kin tafi ba ko labarin ki Sameenah, kinbar gidan mijin ki kusan sati biyu me kike ci
a kadunan haka?”
Kallon Gwaggo Sameenah tayi ta tab’e baki tace
“Gwaggo wajen iyaye na fa naje, tunda akayi auren mu ban tafi ba
sai wannan karon toh menene Dan
nayi sati biyu.”
“Toh Dan kinje wajen iyayen ki sunfi mijin ki ne? Kaji mun maganar banza a wajen yariyar nan, Kuma ai da ace kin haihu babu me hanaki kije wajen nasu ki zauna har arba’in babu me hanaki,
Amman da yake ke gaki nan sai ci ba ciki har yanzu shiru Allah dai ya sakawa Abdallah albarka a cikin kasuwancin sa ya ci gaba da ciyar da ku, Amman kam gaskiya yana wahaluwa.” Ta fad’a
tana kallon Sameenah wacce ta
kumbura da bacin rai.
Mik’ewa tayi tsaye kafin tace “Naji Gwaggo daga dawowa na
ba abinda Zaki mun sai ci mun
mutunci, naji Kuma na amsa sai
dai Kuma abinda zan fad’a Miki
shine haihuwa na Allah ne, shine
baiga Daman bani ba, sannan Naga
ko kema ai Abdallah kad’ai kika
Haifa bayan shi ko kin haifi wani ne?” Tana fad’an haka ta fice daga falon.
Gwaggo kuwa fashewa tayi da
kuka tamkar wacce aka aikowa
da mutuwa sai surutu take Wai
Sameenah ta zageta.
Da misalin k’arfe biyar na yammah Jiddah ta fito daga d’akin ta dakyar saboda kumburi da k’afafu ta sukayi, a hankali ta k’arasa k’ofar Sameenah tayi sallama.
Sameenah da take kwance saman
kujera mik’ewa tayi ta fito ta tsaya
a k’ofar d’akin.
“Sameenah Ashe kin dawo ban
sani ba ai sai da naga fitowar ki d’azu, yasu Mama da fatan suna lafiya?” “Lafiyan su k’alau suna gaishe ku,
na d’auka idan na dawo kin haihu
ashe har yanzu shiru.”
“Wllh kam Sameenah gashi nan dai har yanzu Allah bai kawo lokaci ba, daman Abban Na’eem ne ya ce na sanar miki yau kece zakiyi girki Wai ya kira wayar ki baya shiga.”
Wani kallo Sameenah tayiwa
Jiddah tare da cewa “Kan Uban nan! Daga dawowan nawa ne zan muku girki? Gaskiya bazan iya ba kiyi idan yaso gobe
sai na karb’a.”
Kallon ta Jiddah tayi fuskan ta d’auke da damuwa tace
“Kiyi hakuri ki girka Sameenah wllh banajin dad’in jiki na, ki duba kiga yanda k’afafu na suka kumbura, tsayuwar Nan da nayi
ma ji nake tamkar zan fad’i.”
Tab’e baki Sameenah tayi tace
“To kuwa za’a zauna ba’aci abin ci
a gidan Nan ba, Dan Nikam bazan iya shiga kitchen yanzu ba.” Tana gama maganar ta juya ta shige d’akin ta.
Da kallo Jiddah tabi Sameenah tana mamakin irin halin ta, ita yanzu ko tausayin ta bata ji ba.
Juyawa tayi da niyar komawa, sallaman yaran ta da taji yasa ta juyawa tana sakar musu murmushi, duk zuwa sukayi gaban ta suka zagaye ta, d’aya bayan d’aya take shafa Kan su tare da
cewa
“Da fatan Yara na sun dawo cikin
koshin lafiya?”
Yaseem wacce take itace Babba
a cikin su wacce yanzu zata Kai shekaru 11 tace
“Lafiya k’alau Ammy ya jikin ki?”
Murmushi tayi mata tace
“Da sauki na warke ma.” Sauran yaran ma duk cewa sukayi “Ammy ya jikin ki?” Suka fad’a a tare, murmushi tayi musu tace “muje ku cire uniform d’in ku.” Ta fad’abtana jan hannun Afrah wacce take itace k’arama.
Sosai Jiddah takejin jikin ta babu dad’i hakan yasa batayi gigin d’aura girki ba.
Bayan magriba Abdallah ya dawo daga kasuwa kana ganin sa kasan yayi mugun gajiya, dakyar yake daga kafafun sa har ya k’araso cikin gida bayan ya gama parking
motar sa.
Direct D’akin sa ya nufa, a falo ya zub’e duk da kuwa falon ya d’anyi kura, ya dad’e zaune a falon
Amman babu Wanda ya shigo, lokaci lokaci yake kallon k’ofar d’akin ko zaiga Sameenah ta shigo
Amman shiru ba ita ba labarin ta.
Mik’ewa yayi ya fito dan wani mugun yunwa yake ji, d’akin
Sameenah ya nufa sai dai samun
d’akin yayi a banke an rufe ta ciki.
Kwankwasawa yayi Amman shiru, ya dad’e yana buga k’ofar kafin
Sameenah ta bud’e tana kallon
Abdallah da ya had’e fuska.
“Me kikeyi haka Ina ta buga k’ofa
baki bud’e ba?.”
Dankwalin hannun ta ta d’aura a
kanta kafin tace
“Sorry banji bane Ina ciki Ina aiki.”
Kallon ta yayi yace “Ok bakiji dawowa na ba kenan?” “Naji man lokacin ma aiki nake.”
Cike da Jin haushin yanda take mishi magana Abdallah yace
“Ok ki kawo mun abinci na falo
na.”
Tab’e baki tayi tace “Ni ban girka komai ba, a gajiye nake sai dai zuwa gobe.” “Kamar ya? baki girka komai ba
Sameenah? Jiddah bata fad’a miki
ba ne?”
“Ta fad’a mun Amman a lokacin
na sanar da ita bazan iya ba.” Tana gama fad’an haka ta juya ta shige falon ta.
Abdallah da ran sa yayi mugun
baci a har gitse ya juya ya nufi d’akin Jiddah.
*Kar fa ku bari a baku labarin GIDAN ABDALLAH ku biya 500 kacal ta wannan acc din domin samu ku karanta cikin salama da kwanciyar hankali 3144651347 Khadija Ibrahim sunusi first bank ko Kuma katin mtn ko Airtel ta layin nan 08146196391*
*MOMMYN MUSADDIQ*
[…] Gidan Abdallah Hausa Novel Complete […]