Littafan Hausa Novels

Galadima Family Hausa Novel Complete

Galadima Family Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

GALADIMA FAMILY

 

Story& Written

By

*FATEEMA ZAHRA LAWAL*

 

Marubuciyar⤵️

A DALILIN’YAR TSINTUWA.

MIJIN ZAHRA.

DIAMOND LADIES (Daukar fansa) paid book.

RUHIN AMRITA (FATALWA CE)

Now

 

*_GALADIMA FAMILY_*

 

Page 01

 

Tafe take cike da natsuwa kamewa,long Hijjab ne ajikinta sky blue Wanda ake cema jalbab fuskarta sanye da madaidaicin glashi wanda yasake fito da ainahin kalan fatanta sanye take da facemask sky blue tayi matuqar kyau ,kafanta sanye da halfcover golden colour,jakane rataye a kafadarta golden.

Duk dacewa bazata gaza shekaru sha takwas ba sai dai natsuwarta nasa amata kallon tafiye haka.

Bestyn Mijina Hausa Novel Complete

Taqaraso dai² kwanar layinsu,lokaci daya taji wani irin qunci da takaici ya lullubeta badon komai ba sai don masu zaman kashe wandon layin nasu(sunan da tasanya musu kenan),sake tamke kyakkyawar fuskanta tayi duk dakuwa facemask din da ke lullube da fuskarta,a hankali yasake qarfafa saurin tafiyan nata don burinta baiwuce ace kauce inda masu zaman kashe wandon suke ba.

 

“Zuhra sannu da dawowa,fatan kindawo lafiya?kalmar da tatsinkayo daga cikin kunnenta kenan.

Da hanzari tajuyo cike da mutumtawa tadubi inda maganar tafito tare da dan rissinawa tace”barka da gida baba me icce inayini?tayi maganar tare da fadada murmushinta.

 

Amsawa yayi cike da mutumtawa tare da sanya mata albarka,sosai taji dadin albarkan da yake sanya mata.

Walwala kwance akan fuskanta taqariso bakin gate din gidan nasu,madaidaici mai matuqar kyau da tsaruwa,hannu takai da niyyar knocking gate din,ahankali taga anbude taciki.

Koda tadago ido four eye’s sukayi dashi,sosai kirjinta yayi saurin bugawa wanda yasa da hanzari ta sunkuyar da kanta qasa,shiko ta bangarensa kallo daya yamata sannan yadauke kai,rabata yayi yawuce ta gefenta.

Bayanshi driver dinsu ne janye da trolly bag yanufi wata mota dake fake a kofar gidan nasu,kafin zuhra tajuyo taji hayaniyar yaran gidansu nafitowa,maimoon ce tafito da gudu cike da yarinta da rigima tace”pls yah Sauban katafi dani mana inaso naje masarautar su bodejo.

“A’ah ya Sauban kada kaje da ita dani zakaje saboda nayi missing din bodejo kuma bantaba zuwa masarautar ba,Amma maimoon ita taje.

Wani dan murmushi wanda suke kira da ya Sauban din yaqaqalo tare da dafa kan ateek yaron dan shekaru goma cike sanyayyar muryan shi mecike da taushi yace”kada kadamu my aboki insha Allah bazan dadeba zandawo I know lokacin kunsamu hutu a school so insha Allah idan nadawo zan tafi daku,Ok?

Cike da murna yaran suka hau tsallen murna,zuhra kuwa gabadaya tamkar andasata a tsaye ita batayi gababa kuma batayi baya ba,a hankali tasauke wata sihirtaccen ajiyar zuciya tashiga cikin gidan,direct apartment din mommy tanufa,bude kofan tayi tana sallama cikin siririyar muryanta,wanda idan mutum beyi dagaske ba bazaiji abinda tafada ba,mommy kuwa da tataso da alamu fita zatayi hannunta riqe da wani hadadden ledabag tace”My zuhra welcome!

Murmushi zuhra tayi cike da gajiya tace”mommy!tayi maganar tare da langabar dakai tace”nagaji mommy gaskiya nikam nagaji da zuwa jamb class dinnan.

 

Wucewa mommy tayi tare da cewa”kedai kije ki watsa ruwa kici abinci nasan meke damunki duk baiwuce gajiya ba so nasan dakin watsa ruwa zakiji dai² tayi maganar tana fita daga farlon.

 

Ajiyan zuciya zuhra tasake saukewa akaro na biyu tanufi stairs tahaye,shiga dakin mommy tayi tare da cire hijjab dinta,wow Masha Allah tsarki yatabbata ga ubangijin daya halitta wannan halittan,Ashe zuhra kyanta ba’a fuska bane kadai harta da halintan sura Allah yahore mata,ahankali tacire kayan jikinta yarage daga ita sai undies farare tass.

Addu’an shiga toilet tayi sannan tasakai cikin hadadden bathroom din wanda yatsaru kota ko’ina.

Bata bata lokaci ba tafito daga toilet din,agurguje tasanya English wears na riga da wando purple wanda suka sake daukan suran nata,kobi takan lotion batayi ba.Hulan kayan tasaka a gyararren gashin kanta,tazura slippers,zare handbag dinta tayi taciro wayarta qirar iPhone 13 pro max tafito tare da sakkowa daga kan benen,kallo daya tayima dinning din tahango warmers dinda ke Kai anjejjera abinci.

Fita tayi daga farlon tanufi dayan apartment din dake hannun dama,cike da qwarin gwiwa ta Isa farlon sai dai wacce tahango zaune kan one sitter din dake farlon yasa jikinta tsananin yin sanyi,cikin sanyayyar muryanta tayi sallama,ahankali taqarisa shiga tamkar wacce kwai yafashewa a ciki ta isa inda babban mace take zaune wacce aqalla zatayi shekaru hamsin da duriya, fuskarta sanye da medical glass ta’aza kafa daya kan daya.

Gefe guda laptop ne akan cinyarta take sarrafashi,cike da fargaba zuhra ta isa inda take tare da rissinawa tace”Ummi sannu da gida! batare da tadago daga abinda take a ta amsa da “yawwa sannu dawowa.

Cikin sanyin murya zuhra tare da tsantsar mamaki tafurta “yawwa.

Miqewa tayi tanufi stairs,kai tsaye dakinta tanufa,ahankali tazauna akan tsadadden gadonta tare da sauke wata qarfaffan ajiyar zuciya a fili tace”Ummi yau tayi abin mamaki,yau ta amsa gaisuwata batare da kyara ko shakku ba,amma meyasa?kafin tabawa kanta ansa anturo kofan bedroom din nata.

Nihal ce da Laila,murmushi tasaki kamar yanda suma suka saki,nihal tace”kai zuhra yau gaskiya kundade a jamb class dinnan meyafaru ne? Laila tace”tun sanda ya sauban ya dawo damu muke tambayarki akace ai kinshiga jamb class,wai kinanan akan bakanki na zuwa Danfodio din?kizo muyi joining gabadaya a ABU mana.

Zuhra tace”hmmm Laila kenan bazaku gane ba nisam banason harkan takura,kunsan ya Aseef a ABU yake lecturing wallahi takurama rayuwa zaiyi muddin nashiga ABU kunsan halinsa fa tamkar bunsuru yake shiyasa nafison Danfodio akan ABU bawai don wani abuba sannan duk abinda yake aikatawa Ummi bata gani,kunsanta akan ya Aseef zata iya batama kowa rai so shiyasa nahaqura da ABU so Kuma kuyi a hankali dashi.

 

Da mamaki suke dubanta Nihal tace”wai zuhra menene lefin ya Aseef don yace yana sonki dahar kike kiransa da bunsuru?don kawai yace yana sonki?to wallahi kikiyaye bakinki da furta wannan munanan kalmomin akansa don da zarar Ummi taji kema kinsan sauran.

Laila tace”taya Ummi zataji inba wani yafada mataba gaskiya kila yanada wani boyayyen hali wanda zuhra ce kawai tasani.

Dasauri zuhra tadago da daradaran idanuwanta tace”nibansan wani boyayyen hali dayake daba just bana ra’ayinshi ne kawai.

Tabe baki nihal tayi tace”ke dama matsalarki kenan miskilanci.

Murmushin iya labba zuhra tayi batare da tayi magana ba ta miqe tare da nufan bathroom.

*-WASHEGARI-*

Saukowa takeyi daga saman stairs inda tacidda gabadaya ‘yan gidan zaune akan dinning sunan breakfast,a hankali tadubi kujeran da Abbie yake zama amma bashi hakan yasa sam bataji dadi ba,jikinta yaqara sanyi,mommy ce tace”a’ah zuhra qaraso mana da sauri kiyi breakfast don kinsan shagon saloon din hjy asiya akwai layi barinma yau Wednesday amareda dama zasuje gyaran kai.

Qarasawa zuhra tayi tare dajan ajiyan zuciya,kujerar da take zama taja ta zauna a hankali cikin muryanta wanda batafiye son magana ba tace”Barka gida Ummie Ina kwana?batare da Ummie tadubeta ba tace”barka dai a takaice.

Duban mommy da ya taufeeq daya Aseef tayi tace”gud morning mommy gud morning yaya’s.

Murmushi ya taufeeq yayi yace”morning sweet sister,shima Aseef murmushin yayi yace”morning sis, idanunta nakan ya taufeeq tana murmushi har tabude mouth daniyar sake magana Ummie tayi gyaran murya, duban inda take zuhra tayi a rashin sa’a kuwa sukayi four eye’s da zuhra,wani rikitaccen kallo ta aika mata dashi wanda yasata saurin dukar da kanta,a hankali ta dauki spoon da plate ta aje agabanta tare da bude warmer din wanda chips ke ciki,kadan tadiba tazuba a ciki.

 

Laila tace”shikenan abinda zakici?batare da tayi magana ba tadaga ma Laila kai alamun eh.

Nihal kuwa kyabe baki tayi don Allah yasani tana tsananin takaicin wannan miskilancin na zuhra.

A hankali tacigaba da cin abincinta aqasan zuciyarta kuwa tarasa dalilin da yasa Ummie tatsaneta tun tasowarta,inda sabo yaci ace tasaba sai dai sam hakan taqi yuwuwa,ita da zasubi ta nata dasun maidata maidugri wajen bodejo don tafi samun natsuwa da kulawa,maganar mommy ce takatse mata tunani.

“Zuhra kiyi kigama ci mana yanzu fa kusan 11:28 yakamata ace kinje har kindawo.

Cikin sanyin muryanta tace”tohm mommy ai yanzu zan gama,cikin natsuwa tagama cin abincin tare da daukan tisue tagoge bakinta, miqewa tayi tare da rataya jakanta tace”Ummie,mommy natafi,sister’s sai nadawo.

Laila tace”Bari nazo narakaki sis,murmushi zuhra tayi najin dadi tace”yawwa aiko naji dadi, duban ya taufeeq Laila tayi tace”Yaya pls ko zaka saukemu al shagon ne?kafin yayi mgn mommy tace”a’ah kuda kukeda shiririta?taufeeq sauri yake zashi company don yakusa ma late sai dai Aseef yakaiku.

Wani irin dadi Aseef yaji a ransa,sai dai kafin wani yayi magana taufeeq yace”No no no no mommy bari na’ajesu sharp ² saina wuce.

Fuska kwance da fari’a mommy tace”toh shikenan taufeeq ka ajesu,duban nihal yayi yace”keba zakiyi rakiyar ba nihal?

Murmushi tayi tace”a’ah Yaya bazani ba,dariya Laila tasaki cike da sharri tace”ae Yaya nihal tana takaicin zuwa saloon taga yanda ake wankema masu gashi kai Amma ita kai kamar na jariri dan wata hudu😃

Gabadaya farlon dariya akasa harda Ummie idan kacire Nihal da tataso aguje tabiyo Laila tana zazzage mata kwandon masifa,da gudu Laila tafita tana dariya, Nihal dinma baya tarufa mata,mommy tace”Kai Laila Laila akwai sharri.

Fita ya taufeeq yayi yana dariya, Ummie ma miqewa tayi tanufi main farlo.

Daqyar ya taufeeq yadawo da Nihal ciki sannan suka tafi,a mota kuwa banda dariya babu abinda zuhra keyi,sosai hankalin ya taufeeq dana Laila yakoma kan zuhra don rabonda tayi irin wannan nishadin tun ana saura sati daya Abbie yatafi Indonesia,sai gashi yau tayi,hakan baqaramin dadi ya taufeeq yajiba dagashi har Laila,a haka suka karisa shagon saloon din,saukesu yayi sannan yajuya yatafi,sukuma suka shiga cikin shagon.

 

WAI WACECE ZUHRA?MENENE MATSAYINTA A CIKIN GIDAN?AKWAI TURKA-TURKA DA HAUTSIMA ANAN GABA KUDAI KUBINI MUJE

 

Xahratty Ce

Lallai Alqalami yafi takobi

Add Comment

Click here to post a comment