Littafan Hausa Novels

Wake Daya Hausa Novel Complete

Wake Daya Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Wake Daya Hausa Novel Complete

*WAKE ƊAYA

MomIslam

 

Page1

 

Ɗanɗano

 

A gigice ta durƙusa a gaban, Inna Meramu. tana cewa “dan Allah Inna kiyi haƙuri ki taimakamin karki jefani cikin wannan ruwan wlhi zan iya mutuwa”

Hawaye nabin kumatunta kamar an buɗe famfo.

 

Cikin rashin tausayi da sanin darajar ran ɗan adam, Inna Meramu ta dagata sama ta waiga taga babu mai kallonta ta wurga Hanan cikin tafkeken kogi.

Tayi min kankanta Hausa Novel Complete

Inna meramu ta juya a guje tana darara ihun neman agaji, tana isowa ƙofar gida ta zube a gaban malam Junaidu tace “rabona da ganin Hanan tun safe nayi yawo har nagaji, yanzu nan daka ganni daga Kadage nake”

Malam Junaidu ya miƙe tsaye tare da rafka salati yace “nima zama bai ganni ba dole ina shiga gari nemanta”

Sai kuma ya tsaya ya kalli Inna meramu yace “ammafa sai naji kamar Halliru mai shago yace “yaganta da tiran tallar shinkafa?”

 

Inna meramu ta fara ƙirƙiro kalaman kare kanta kafin tace “uhm malam me kake nufi?”

Bai tsaya jin abinda zatace ba ya bazama gari neman Hanan.

 

Kowa yagani a hanya sai ya tambayesa yaga Hanan, suce basu ganta ba.

 

Yayi tafiyar datakai ta d’ari biyar amma bai ko ga d’ankwalin Hanan ɗin ba, zama yayi gindin wata bishiya ya yakice zufar data karyo masa kafin yace “ina yarinyar nan ta shiga?, a iya sanina bata saba yin nisa da gida ba, Allah ka nunamin ta inda zan ganta”

 

Ya miƙe yaci gaba da tafiya a gajiye.

Yamma liss ya dawo gida ya samu Inna meramu tana alwalar magriba, shima butar ya ɗauka tare da nufar bayi, yana shiga aka kwashe shi aka watsar gefe kamar kayan wanki, ya rafka salati yana cewa “nashiga uku meramu kinajin halin da nake ciki?”

Tana daga bakin murhu tayo kansa da gudu har tana kujewa a jikin bango tace “malam koda ka taka musu ƴaƴan ne?”

Ta fita waje da gudu tana ihun neman agaji,

Cikin sa’a Halliru mai shago ya jiyo kururuwarta ya taho da gudu yana cewa “Inna meramu meke faruwa?”

Tasa hannu akai ta rusa ihu tace “malam ne ya faɗi a banɗaki ka taimaka ka fito dashi”

Halliru ya shiga gidan da sallama ya shiga banɗaki yaga malam a yashe sai wani irin numfarfashi yake,

Cikin azama ya fito dashi, Inna meramu ta shimfiɗa tabarma ta fara yi masa fifita,

“Akira malam mai karatu?”

Halliru ya faɗa yana kallon Inna meramu,

“A’a barshi muga abinda Allah zeyi dan wlhi sisi bana magani bare ince ka kira shi”

Halliru yace “inhar befi ƙarfina ba zan taimaka”

Inna meramu tace “to tunda ka kafe kamar ƙanin ubanka”

Halliru baice mata komai ba ya fice yana jajanta rashin mutunci na matarnan,

Cikin natsuwa ya isa gurin malam mai karatu yace “malam Junaidu ne ya faɗi a banɗaki shine nazo dan Allah ka taimaka masa”

Jinjina kai malam mai karatu yayi kafin yace “bana son shiga gidan nan saboda niƙanmu baya laushi da Meramu”

Halliru ya haɗe hannayensa biyu kamar zeyi kuka yace “dan Allah kai taimaka masa malam ka duba halin da yake ciki”

Malam mai karatu yace ” to Allah yasa mu dace, muje yanzu na dawo daga sallahar magriba zan shiga gida”

Suna shigowa suka samu tanata adu’a tana tofa masa, malam mai karatu yace “kull karki sake ta6ashi bare tofa masa gubar bakinki”

Cikin rashin fahimta da dama ba shiri take yi dashi ɗin ba tace “ban gane ba?, ko dole sai kaine idan kayi masa magani zai warke babu wanda Allah yaba sa ni?”

Malam ya girgiza kai tare da fara karantowa malam Junaidu karatun Alkur’ani mai girma, yana yi yana tofa masa, tashi ɗaya ya fara ɗaga hannu amma babu bakin magana,zatayi magana malam mai karatu ya dakatar da ita cikin fushi yace “idan na kaiki Shari’a wlhi bazamu dawo tare ba acan zan barki?”

Inna meramu ta miƙe tsaye tana nuna malam da hannu tace “ƙarya kakeyi wallahi ko an gaya maka niɗin lafiya ce?”

Cikin rashin fahimta Halliru yace “malam wai meke faruwa ne?”

Malam yace “kambun baka ne da ita, sarai tasani inada yaƙinin wlhi akwai kalmar data furta masa muguwa”

Inna meramu ta miƙe rai a 6ace tana share hawayen da suka fara sintiri a fuskarta tace “wlhi yau sai na kaika gidan mai gari”

Malam mai karatu yace “ki kaini gaba da nan ma”

Ta fice.

Wasu irin yaruka malam Junaidu yakeyi wanda babu wanda yasan abinda yake faɗa dagashi sai Allah.

 

A gajiye suke tafiya ɗaya na goye da jaka a bayansa ɗayan kuma yana riƙe da waya, samari ne kyawawa daka gansu zaka tabbatar da hutu ya zauna a jikinsu ba wasu farare bane sai dai akirasu da chocolate color sbda kalar fatarsu,

Mai goye da jaka a baya yace “Hamud kana ganin gobe zamu sami mashin ɗin da zeyi sammako a ƙauyennan kuwa?”

Hamud yace “kaifa Lirwan ɗan iska ne, cemaka akayi basu da mashina ko yaya?”

Wanda Hamud ɗin ya kira da Lirwan yace “kanaji ɗazu da mukayi tambaya cewa akayi sai dai idan sun kawo goyo daga nan cikin garin Saminaka”

Suna cikin magana suka iso bakin kogi, Hamud ya ware idanuwansa sakamakon ganin mutum da yayi yana tasowa yana komawa,

Yaja da baya yana cewa “Lirwan tayani gani kamar mutum?”

Lirwan yace “yarinyar ce wlhi zatayi shekara sha uku”

Hamud yace “bashi na tambayeka ba”

Yana rufe baki Hamud ɗin ya faɗa cikin ruwan, sosai yake kaiwa da komowa a ciki dan ganin ya dawo da Hanan bakin kogi, amma abin yana neman gagararsa dan sai yayi kamar ya dawo da ita sai a kuma yin gaba da ita, lokaci ɗaya Hamud ya sauya yanayi, gashi da naci yaƙi fitowa, Lirwan yace “dalla malam ka fito tamutu sai kaje ka kashe kanka a banza akan wata ƴar ƙauye”

Hamud ɗin yana jinsa amma babu halin ya bashi amsa.

Cikin sa’a ya turota gaban kogin tare da fitowa shima, kana ganinsa zakasan ya mugun walaha gashi itama ɗin daya ciro ko numfashi batayi,

Hamud ɗin na fitar da wani irin numfashi yace “Lirwab Please taimakon gaggawa”

“Ban gane ba, kana nufin bayan na daddana mata ciki in sanya bakina a nata impossible, kama godewa Allah dana dinga haska maka”

A zuciye Hamud yayi kanta ya fara yi mata taimako yana danna ruwan cikinta yana karanto adu’i duk wace tazo bakinsa.

Da sauri yasa bakinsa a nata yana hurawa a hankali, ƙirjinta ya fara bugawa yace “problem ɗin basu da hospital anan kusa gashi mukuma bamu zoda mota ba”

Lirwan yace “malam kaje gurin me gari ayi cigiyar iyayenta Dan wannan aikin ba naka bane”

Hamud yace “meyasa zuciyarka babu tausayi a cikinta?”

Zai sake magana sukaga ta buɗe ido tana kallonsu, duk da hakan bawai ta gama warwarewa bane, Hamud yaje gurinta da sauri ya kamo hannunta cikin siririyar murya yace “zaki iya tafiya?”

“A’a” tace masa tana daɗa ƙare musu kallo,

Hamud ya ratayata a kafaɗarsa ya shiga gari da ita, duk wanda ya gani ya tambayesa shin yasan wannan yarinyar?,

Yawancin yara sunƙi cewa eh saboda tsoron Inna meramu da masifarta, cikin sa’a sai gashi a ƙofar gidansu, malam mai karatu ya fito zai koma gida sukayi ido biyu, Hamud ya ɗan sadda kansa ƙasa yace “malam wannan yarinyar a kogi muka cirota dan Allah ko zaka taimaka mana da cigiyarta inason ganin iyayenta?”

Malam mai karatu yace “inda nake a tsayen nan ne gidansu zomuje mahaifinta ma babu lafiya”

Lokacin Lirwan ya ƙaraso suka shiga gidan.

Suka sami malam Junaidu a kwance, Lirwan ya haska fitilar wayarsa yace “sannu baba”

Malam Junaidu yace “yauwa a ruwa kuka ciro min Rashidan?”

Hamud yace “eh baba, ya jikin naka?”

Malam Junaidu yace “Alhmdulilah”

Inna meramu dake shigowa yanzu ta hango Hanan kwance tana ta rarraba idanu, da sauri ta ƙaraso kana tace “mezan gani kamar Hanan?”

Malam mai karatu yace “itace uwar ƴan tsibbu”

Ta nuna shi da yatsanta tace “gobe mai gari yana nemanka a fada dole ayimin iyaka da rashin mutuncin da kakeyimin wlhi”

Malam mai karatu yayi murmishi.

Sai kuma yace “wayasani ko kece kika Kaita can ɗin?”

Cikin masifa tace “innalilahi wa inna liaihir raji’un sharrin harda na hallaka yarinyata, malam kana jinmu fa?”

Malam Junaidu daya samo kansa yace “bazan iya ba”

“A yau da zan sami mai auran Hanan wlhi da babu abinda zai hana ban badata ba”

Hamud yace “inhar zaka bani ita baba wlhi Allah ina sonta kaje kaga dangina dan Allah”

Malam mai karatu yace “ba ɓoyayyu bane fa na ganesu gidan hakimi sukazo yau kwanansu huɗu”

Karaf Inna meramu tace “an yi baikonta dan haka sai abarta tasha ruwa”

Malam Junaidu yace “nidai a iya sanina banyiwa ƴata miji ba, saboda ban taɓa ganin wani yazo da niyar zance ba”

Inna meramu tace “malam kadai tuna dan wlhi munci dubu arba’in na Usaini mai gidan duhu”

Malam Junaidu ya zato ido ya kalli Inna meramu cike da mamaki kafin yace “toki tattara ki maida masa da kayansa dan bana fatan musiba a rayuwata”

Malam mai karatu yace “wannan wane irin dabbanci ne? ke zaki aurar da ita kenan ba mahaifinta ba, kowa dai a garinnan yasan irin ginin Gidan duhu, matan gidan basa fita ko zaure kullum gidan a kulle yake da kwaɗo kinsan bayan haka ko fitowa basayi gaisuwar marar lafiya sai cikin dare kamar munafukai”

Inna meramu tace “kai kaga haka, kuɗinsa kawai ya isa yasa a aureshi ni nan daka ganni badan na rigada na auri malam ba yace yana sona wlhi auransa zanyi”

Malam mai karatu yace “Ashsha budurwar zuciya Allah wadaran naka ya lalace wannan wane irin san zuciya ne?”

Malam Junaidu yace “oho nidai babu zancen aure a wannan lokacin Ni da kaina zan nema mata miji”

Inna meramu tace “kuma sai kayi wlhi inhar kaga Hanan bata auri Usaini mai gidan duhu ba, to bani da numfashi ne”

Malam mai karatu ya fice ransa a ɓace.

Hamud da Lirwan da suke durƙushe sun gama gano matsalolin da yarinyar take fuskanta daga ɓangaren uwar goyonta, Hamud ya mike kafin yace “baba gobe zamu tafi, yakamata kuyi shawara a tsakaninku domin duba dacewar irin mijin daya kamata Ku aurawa y’arku”

Baba yace “to”

Har suka fita baice musu komai ba, ya kasa furta koda kalma ɗaya ne tsabar baƙincikin dake ci masa rai,

Inna meramu ta shiga ɗakinta, ɗakin daya kasance duk abubuwan tsibbace tsibbace, dalilin da yasa suke yawan faɗa da malam mai karatu kenan,

Ta kalli gaban ta ɗibi wani baƙin abu ta watsa tana cewa “Juuunaiiiiiduuu,”

Sai data kira sunan sau uku sannan ta kunce ɗaurin wani lanƙwasashen ice tana dariya marar sauti,

Malam Junaidu na zaune a tsakar gida har akayi sallar isha’i, Hanan ɗin tana gefensa bacci ya ɗauke ta dan batasan wainar da ake toyawa ba,

So yakeyi ya mike sam ya kasa ƙafafunsa babu ƙwari sai ƙyarma suke, a hankali ya kama bango yana cewa “meramu zoki ɗaga Hanan taje ɗaki”

Inna meramu tace “meyasa kai baka ɗagata ba tunda ka nunamin rashin mutunci ƙarara a idon jama’a to ka rubuta ka ajiye wannan aure anyishi an gama, kuma zai kawo sadaki dubu ɗari uku kaga ya isheka siyan iri da takin noma”

Malam Junaidu nadaga tsaye ya zube a gurin yana salati yace….

 

08141799224

Add Comment

Click here to post a comment