Idan ba ke ba Hausa Novel Complete
Idan ba ke ba Hausa Novel Complete
IDAN BA KE
_True Life story_
Nimcyluv sarauta
_*Arewabooks@Nimcyluv*_
1.
Jimeta/Yola
Njoɓoli Rugar Rome
Gudu Saniyar take tana bin ta a baya itama, hannunta riƙe da sanda na korar Nagge, tamkar wanda suke wasan tsere haka Saniyar ke gudu a cikin jejin ita ma bata fasa bin ta ba, sauran Naggen suna gefe guda ko wacce na cin ciyayi wanda bisa kuskure tana can tana bin Saniya ɗaya tilo, sauran Naggen suka faɗa cikin gonar wani manomi, a yunwace suka rufarwa albarkatun gonar. Cikin siririyar muryarta mai nuni da Yarintar ta, da kuma nuna cewa ita ɗin zallar bafullatanar Yola ce ƴar Usul. “Waru! Waru! Waru” shi ne abin da yarinyar ke ta nanatawa cikin hausarta ta Fulani, yayinda Saniyar tuni tai mata nisa cikin gajiya wa da bin Saniyar ta tsaya a wajan wata gaɓar ruwa tana riƙe ƙugunta ta ce “Bone, lalashewa ta samu Nagge Aradu” da sauri kuma ta ɗauki sandar tana ƙara yin kan Saniyar ganin ta tsaya da gudun da take, cikin sa’a ta cimmata tana zuwa ta kama ƙahonta tare da ƙifƙifta idanunta alamar zallar fitsarar dake tattare da ita “d’ume ngid’d’a?” Ma’ana “me kake so?” Kallon ta Saniyar ta yi sai kuma ta kaɗa jela tare da zubewa a wajan ta shiga shura ƙafafuwa kamar zata mutu, cikin tsoro haɗi da razani HALISA ta ce “Jomirawo ka taimakeni” ta faɗa tana kallon Saniyar wacce tai male-male a ƙasa ga wani ruwa mai kama da jini na fitowa ta ƙasanta, kuka Halisa ta sanya domin idan Saniyar ta mutu a nan wajan ta shiga uku, itama watan mutuwarta ya kama. Tsayar da kukan tai kafin ta fara duba cikin jeji babu kowa sai ita, ga wani kwantaccen baƙin hadari dake ƙasa wanda a koda yaushe zai iya tashi.
Juyawa tayi ta nufi wajan wata bishiya inda ta hangi ƙaramar igiya a jiki, tana zuwa jikin bishiyar ta zame hular Fulanin dake kanta, nan da nan sumar kanta ta sauka wacce take jajir babu alamar baƙi ko ɗaya, gashin ba wani cika ne dashi ba, kawai tsayin gashi gareta, domin har fatar tsakiyar kanta ana iya ganowa. cikin sayin jikinta ta fara jan igiyar tana ƙoƙarin kunce igiyar gaba ɗaya daga jikin reshen bishiyar, kamar daga sama taji saukar wani abu mai sanyin gaske zuwa kafaɗunta. Cak ta tsaya tana sauraren yadda abin ke tafiya sululuuuu a jikinta har ya gama sauka, hannunta ta miƙa da nufin kama abin da ya sakko mata domin bata da tsoro ko kaɗan, cikin rashin sa’a hannunta ya sauka saman ƙaton kan maciji wanda yake kwance a jikinta, wani santsi-santsi ta ji a jikin macijin ga wani sanyi sosai dake ratsa fatar jikinta, bata gama yadda da abin da zuciyarta ke ayyana mata ba, a hankali ta juya wani ihu ta kurma wanda ya yi daidai da ɗaukewar numfashinta, baya tayi zata faɗi kafin ta kai zuwa ƙasa macijin ya yi wata girgiza cikin sakanni ya juye zuwa wani saurayi wanda jikinsa ya ke sanye da wasu haɗaɗɗun kayan sarauta na farin saƙi, fari ne tas amma kamar Fatar mace haka fatar hannunsa da sauran jikinsa suke gaba ɗaya gashi ya kwanta luff. Zubewa ya yi a ƙasa ta faɗo jikinsa idanunsa a kan fuskarta, ya jima yana kallonta kafin cikin izza da nutsuwa ya ce “kin tsoratani, kin tsorata kanki Danejo, banyi niyyar zuwar maki ba yanzu” Danejo sunan da ƴan rugar Rome suke faɗawa Halisa ke nan. Sai da ya gama Kallon ta sosai, kallon da ya jima bai mata ba tun tana zanin goyo matsayin Jaririya. Ɗaukanta ya yi ya nufi inda Naggen suke yana zuwa ya tarar da wannan Saniyar dake Shure Shure ta haihu, ashe daman ciwon haihuwa ke damunta. Halisa ya kalla yana sakin Murmushi kafin ya zaro harshesa waje sai ga wani zobe ya bayyana, cikin sauri ya saka mata zoben mai ɗauke da tambarin wata masarauta, kafin ya yi Girgiza sai ga shi ya sauya kama, kamarsa a fuska na nan, amma kayan jikinsa sun sauya sun koma irin kayan Fulani sak komai da komai, goya Danejo ya yi a bayansa, ya ɗauki jaririn Saniyar cikin nutsuwa ya fara kaɗa Naggen zuwa Rugar Rome. Kamar ƙifatawar idanu haka ya ƙaraso Rugar..
Iskar dake kaɗawa na alamar tashin hadarin ya sanya matashin ɗaga kansa sama, yana kallon yadda gajimare ke haɗa kansa. A nutse kuma ya fara bin Rugar Rome da kallo ba wata babba bace, amma Ubangiji ya albarkaci rugar da dabbobi musamman Nagge, gasu manyan gwanin sha’awa yawancinsu jajaye ne kafin ka samu farar saniya zaka daɗe. Wasu sun dawo daka kiwo wasu kuma na hanya sbd rashin yawaitar mutane da babu a rugar, daidai wajan wata bukka ya Ƙarasa yana gyara riƙon da ya yi wa Jaririyar Saniyar kafin ya ce “Sannunmu dai” ya faɗa a taushashe jin shiru ya sanya ya ƙara buɗe muryarsa mai sanyi ya ce “Afuwanku dai” daga cikin bukkar wata ƙaramar murya ta amsa da faɗin “Waye nan?” Ta faɗi hakan tana fitowa, lokacin da Idanunta ya sauka acikin ƙwayar matashin gabanta taji ya faɗi saboda yadda taga ƙwayar idanunsa, gane cewa kamar ta tsorata da yanayinsa ya sanya ya lumshe idanunsa kaɗan tare da buɗewa ya ce “Ga ɗan uwanki na kawo shi, arado bashi da lafiya ne can na ganosa yashe a jeji ba rai, har naggenku ya samu zuri’a” yana faɗin hakan ya ajjiye Jaririyar Saniyar a ƙasa wacce take jajir da ita Kuma ƙatuwa. Shatu dai binsa take da Idanunta domin bata taɓa ganin mai kama dashi a rugar ba sai yau, kallon da yaga yai yawa ne yasa ya ce “Shai a mata magani” a hankali ya sauke Halisa Dajeno ya kwantar a ƙasa a nan gaban bukkar kamar zai juya ya tafi sai kuma ya ƙurawa zoben hannunta idanu wanda yake sheƙi sosai ga tambarin masarauta nan ya fito sosai a jikinsa, a ransa yake ji kamar bai dace daya mallaka mata wannan zoben ba, amma bashi da wani zaɓi dole ya bata ta haka ne kawai zai lalubota a duk sanda ta ɓace masa, tun tana ciki yake fama da rainonta lokacin haihuwarta ne kawai bai sani ba.
Ba tare da ya ƙara cewa komai ba ya juya da sauri ya fara tafiya tare da shankwana, yana barin wajan ya ƙara yin girgiza wata iska mai daɗi da guguwa ta mamaye gaba ɗaya cikin Rugar Rome. Nan take ya koma asalin macijinsa kamar yadda ya bayyana a farko, yana iya komawa duk suffar da yaga dama cikin ƙaramin lokaci amma zama maciji yafi masa daɗi sbd yawaitar macije dake cikin jejin daya zagaye Rugar Rome, a haka ya sulale tare da komawa cikin jejin.
Iskar dake kaɗawa ce tai sanadiyyar farkawar Dajeno daga barcin dolen da macijin ya sanyata a ruɗe ta miƙe tana dafe kanta dake mata ciwo sosai cikin sanyin murya ta ce. “Miyyati Allah” Shatu dake gefen Dajeno tana ɗaure Naggen a garken dake dab da bukkar ta ce “Nassu, ka shigo” Shiru Danejo tai kamar zata tuna wani abu sai kuma tai saurin ware manyan idanunta ta ce “Shai Shatu ina Dadana ya tashi daga barci hoo?” Shatu ta ce “E, yana ta kiranka baka dawo ba, ciwonsa ya tashi yana ta masa zafi” da sauri Danejo ta faɗa cikin bukkar Idanunta ya sauka akan Dada (her mother) tana kwance a rufeta da wani farin zani jikinta sai rawa yake, fara ce matar sosai amma yanayin jikinta kamar ta shekara 60 nan kuma ba tafi shekaru 50 ba idan ma ta cika. “Shannu shannu Dadana” Idanu Dada ta buɗe da ƙyar ta ce “Zakiyi Albarka Halisa ki riƙe gaskiya da amana ki zama mai haƙuri ki daina saurin fushi da rashin kunya” Kallo juna sukai da Shatu da Halisa wacce akafi sani da Dajeno “Dada me yasa kake shaiwa haka?” Dada ta kalli Shatu kana ta juya ta kama Hannun Dajeno ta haɗa dana Shatu ta ce “Meyasa ba zance haka ba? Shatu kece ƙarama Halisa ita ce babba amma zafin zuciya ne da ita, rauninta akai na yake, kuma dole na tafi na barta” da sauri Shatu ta kalli Dada tana faɗin “Ina zaka Dada kuma?bayan Rugar Rome ina muke dashi” Dada ta numfasa ta ce “Babu da inda yafi wannan Rugar, zan tafi zuwa ga Mahaliccin daya samar da Rugar Romen, ciwon nan ba zai barni ba kuɗin amanata ce musamman ke Halisa” Dajeno kasa cewa komai tai sai ƙurawa Dada fararen idanunta da tayi zuciyarta cike da fargaba. “Dadana ba zaki mutu ba, idan kin mutu wa muke dashi a nan rugar wazai dinga kulawa damu?” Dajeno ta ƙare maganar cikin sanyin murya gaba ɗaya jikinta yai sanyi sosai. Shiru kawai Dada tai can kuma ta ce “Hamma Yabi ya dawo?” “A’a birni da nisa Dadana yace gobe zai kai ki can asibitin birnin”. Jinjina kai Dada tai Dajeno ta miƙe bayan ta ce Shatu ta kula da Dada yanzu zata wajan Sarkin ruga ta amso magani.
Cikin sanyin jikin nan nata take tafiya kanta a ƙasa domin bata fiya kallon mutane ba, a yadda jikin Danejo yake da sanyi zaka ɗauka babu ruwan ta, musamman da fuskarta yai kala dana salihai amma zafi da zuciya gareta, ga kuma taurin kai da naci akan abu, idan tace zatai to tabbas zatai, amma idan tace A’a babu wanda ya isa juyata ko Dada sai dai ta zuba mata Idanu. Abin birgewa ga rayuwar Halisa Dajeno tana da saurin yafiya, da kuma tausayi da kuma kawaici. Cikin tafiyar nutsuwa ta Ƙarasa gaban wata bukka wacce tafi ko wacce bukka kyau da girma a cikin Rugar Rome. “Shai shai Mene haka kamar makauniya ina kwaɗa miki shandan nan Aradu” da sauri Danejo ta ɗaga idanunta ta kalli Gwaggo Niyabi wacce ke zaune tana kaɗa audiga, murguɗa baki tai ba tare data ce komai ba, jin tai shiru yasa Gwaggo faɗin “Ko njid’ud’a?” “Magani za’a bawa Dadana” Gwaggo Niyabi ta ce “To baya nan” shiru tai kamar zatai Mgn sai kuma ta juya sai da tayi nisa kaɗan Gwaggo Niyabi ta ce “Yaka Dajeno waru” tsaye Dajeno tai domin ba shiri suke da Gwaggo ba, Murmushi Gwaggo tai sosai kafin ta numfasa ta ce “Idan kinje ki tambayi Dada waye mahaifinki, mene yasa daya rasu bata bar Rugar Rome ba, ta tafi danginta ko dangin mijinta” da mamaki Danejo ta ce “To bayan Baffa ya rasu mene na tambayarsa, ki daina maganar Uwayena” Gwaggo ta miƙe tana kallon Danejo “To ana gab da kurarku a Rugar Rome, domin bama son mara gurbi” harara Danejo ta watsa mata ta ce “Miyidi saro’am” ma’ana ina son iyayena “Kalleki mai ƙaton baki da ƙwalaƙwalan idanu” tana faɗin hakan ta kwasa da gudu zuwa bukkarsu.
Da ƙyar suka samu zazzaɓi Dada ya sauka tasha paracetamol sai 12 na dare ta samu barci. Shatu ma barci take kusa da Dada a hankali Danejo ta miƙe daga kwancan da take har yanzu fararen kayan Fulani ne sanye a jikinta, hula ta ɗauka ta rufe kanta a nutse ta fita daga cikin bukkar kai tsaye garken shanun dake dab da bukkar ta nufa, wanda aka kunna musu wuta tana ci kaɗan kaɗan. Gobe da sassafe take son tafiya tallan kindirmon. ƙwarya ta ɗauka ta tsuguna tare da kama nonon jikin wata Nagge ta fara tatsa gaba ɗaya hankalinta baya jikinta sai a lokacin maganar Gwaggo Niyabi ta faɗo mata, a haka ta gama tatsar nonon acikin ƙwayar ta ajjiye can gefe guda a bukkar tasu. Gari na waye ba tare da yin wanka ba ta shasshafa ruwa ƙafa duk lam’a ta dungura sallah. Dada na gefe tana kallon yadda take sallah tana son tuna wani abu amma ta kasa har zuciyarta take jin kamar yadda Danejo ke sallah ba haka ake yi ba, amma ta kasa ganewa da kuma tuna yadda ake?. “Ina Hamma Yabi?” Danejo ta kalli Dada tace “Mi naddi mo (na kira shi)”. Jinjina kai Dada tai, Danejo sai kallon Dada take kamar zatai shiru sai kuma tace “Dada waye Baffa?” Da sauri Dada ta juya gabanta na faɗuwa sosai na rashin amsar tambayar Danejo tace “Kamarya Halisa? Baffa mahaifinku ne kuma ya rasu mene?” “Na sani Dada, ina dangin Baffana suke me yasa muke zaune a Rugar Rome?” A hargitse Dada ta ɗaga hannunta tare da ɗauke Danejo da mari sai kuma ta fashe da kuka ta ce “Wacce masifa ce wannan kika koya Dajeno? Bance miki nice Dangin uwa dana uba a gareku ba? Ban gaya miki ba Halisa?” Hawaye na sauka a fuskar Halisa ta ce “Kiyi haƙuri Dadana ba zan sake ba, ban san mene yasa nai miki wannan tambayar ba” kasa magana Dada tai saboda hakin daya fara cin ƙarfin ta, zuciyarta na bugawa da ƙarfi Danejo na ƙwala ihu ta shiga kiran sunan Hamma Yabi wanda ke garken shanu, tattara Dada Hamma Yabi yai zuwa wani ƙaramin asibiti dake gefen Rugar, suna zuwa kusan sune na farko amma abin mmki sai kwasar wasu ake ana barinsu sbd cin hancin da suke bawa Nurse’s ɗin, har lokacin tashi yai ba’a samu damar duba Dada ba a haka suka dawo gida.
Alamomin Mace Mai Dadi Mace mai Ni’ima
Yola South
Abti America
Babbar makaranta ce Wacce ta kasance Private school tun daga primary school har zuwa University makarantar dake da ita, Abti America mallakin mataimakin shugaban ƙasa kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na yanzu Atiku Abubakar ce. Makarantar na cikin Yola South ko ace Yola town duk ɗaya. Makaranta ce wacce sai ɗan wane da wane suke zuwanta duk wanda ka gani a ciki to ka tabbatar ubansa ya mallaki arziƙi ba dukiya ba.
Adamawa/jimeta.
Yola shi ne babban birnin jihar Adamawa. Yola South ana kiranshi da Yola town acan fadar lamiɗon Adamawa yake ma’ana gidan sarauta (LAMIƊO’S PALACE).
Yola North, jimeta kenan. Acan fadar gwamnati yake, jimeta yafi kyau haɗuwa da tsari fiye da Yola South. Manyan abubuwa gaba ɗaya acan Yola North wato jimeta suke. Babu wani nisa tsakanin Yola South da Yola North/jimeta hasali ma roundabout ne ya raba tsakaninsu, akwai wani roundabout mai ƙwayoyin ƙwaryar nono da ludayi a kai muna ana kiransa da Yola roundabout, akan hanyar express yake daga shi sai wata ƙofa, to wannan ƙofar shine da zarar ka shigeta ka shiga yola kenan, sunan ƙofar “JIPPAJAM” da kuma “JAƁƁAMA” Ma’anar Jippajam shi ne Ka sauka lafiya. Wannan idan kazo fita kenan ta cikin yola zaka ganshi, idan shiga garin zakayi kuma za ka ga an rubuta Jaɓɓama ma’ana Sannu da zuwa.
Njoɓoli wani ƙauye ne sosai dake cikin ƙauyukan dake zagaye da Yola south wato yola town,ƙauyen yawancinsu fulani ne makiyaya,amma akwai manoma ma, babu nisa da cikin gari, sannan suna da tashar mota mai tafiya ƙauyen a cikin yola. Wannan kenan.
Tana tafe hannunta riƙe da sanda tana kaɗawa, a hankali bakinta ke motsawa tana karanta 1,2,3-10 cikin fillatancin karatunta bai nisa ba, babu arabi ba boko kuma ba za’a kirata da jahila ba,ita dai gata nan ne dai, ba wanka sosai ma’ana ba tsafta.
Go’a 1 D’id’i 2 Tati 3 Nay 4 juy 5 Je go’o 6 haka ta dinga maimaitawa har ta ƙarasa can nesa da gate ɗin makarantar Abti America. Ajjiye ƙwayar kanta tai tare da neman waje ta zauna tana jira a tashi duk da cewa ba’a talla amma sbd ƙarancin masu sai da kindirmo yasa ake siyan nono a wajanta sosai. Tana zaune wata mota baƙa ta taho da gudu gadan-gadan zata take Danejo cikin tsoro da firgita har tana ture ƙwayar nonon Danejo ta miƙe tsaye tare da fasa ihu tana ƙanƙame jikinta idanunta rufe sbd gaba ɗaya motar kanta tayo da alama giyar motarce ta ƙwace. Motar na gab da taka Dajeno ba zato taji an saka hannu tare da yin sama da ita…
let’s see yadda zaku amshi labarin HALISA DAJENO wanda ya faru a gaske bawai fiction story bane.
IDAN BA KE
Nimcyluv sarauta
*_Arewabooks@Nimcyluv_*
2.
Ihu Danejo ta fasa lokacin da taji an saka hannu tare da yin sama da ita cikin muryarta ta Fulani ta ce “Mi boni Dada’am mi nasti tati hande mi mayi” gaba ɗaya ta tsorata ta ɗauka motar za tabi ta kanta. Jin an direta gefe guda ya sanya ta buɗe idanunta a hankali a tsaye ta gansa nesa da ita kaɗan hannunsa harɗe a ƙirji yana ƙare mata kallo tare da nazartar yanayinta. Kasa daina kallonsa Danejo tai sbd yanayin shigar jikinsa wani farin yadi ne a jikin nasa amma yai baƙiƙƙirin sbd dauɗar daya haɗa gaba ɗaya yadin ya yayyage har ana iya ganin farar fatar jikinsa, sumar kansa rabi furfura rabi baƙa. Ajjiyar zuciya ta sauke da sauri kuma ta juya sbd ƙarar motar da taji sai a lokacin lura da shegewar motar cikin Abti America.
Ƙugu ta riƙe tana fari da manyan idanunta cike da tsiwa ta ce “Shai mutum ya tsaya yaga yadda ake tijara aradu ina iya fasa gilahin moto ɗin” daga bayanta taji murya mai sanyi ta daki kunnenta ance “Zaki biya?” Juyawa tai ta kallesa mutumin ɗazo ne dai wanda ya taimaketa kafin motar ta bigeta, harara ta banka masa ta ce “Kai Almajiri Sukajo meye ruwanka dani? Ina ruwanka idan moto ya takani, da kayanka duk a yage” ta faɗa tana murguɗa masa baki. A hankali ya nanata kalmar “Sukajo” a ransa idan ya fahimta Sukajo na nufin “Saurayi” Girgiza kai kawai yai ba tare da yace mata komai ba ya juya zai bar wajan. Da sauri ta sha gabansa tana faɗin “hani inbano ina ka kai mini kindirmon shaniyata? Waye ya tittila a tumbinsa?” Juyawa yai tare da kallon ƙwayar nonon babu komai a ciki sbd tuni ta zubar da nonon dalilin tsoran da taji, amma ta kasa fahimtar ita ta zubar ɗin. Yana dai tsaye bai ce komai ba can kuma ya kalli cikin idanunta da sauri ta ɗauke nata idanun tana murguɗa masa baki cikin ƙasa da murya ya ce “Siya akai ai” baki ta buɗe ita ai ba taga wanda yazo ya siya ɗin ba kuma gaba ɗaya nonon aka siya kenan? “Ina kuɗin to ɗan Almajiri mai yagaggun kaya?” Da hannu ya nuna mata ƙasan ƙwayar yana rufe idanu da buɗewa ya ce “Gasu can” ta durƙusa ta ɗaga ƙwayar sai ga kuɗi da gudar dubu ɗaya da ɗari biyar guda biyu sai ƴan ɗari guda goma. Zaro idanu tai waje jikinta na rawa ta ce “Kai ɗan Almajiri mai ƙarya wannan kuɗin duk na kindirmona ne? Ai aradu kuɗin yai yawa” hannunsa dake harɗe a ƙirji ya wara tare da ɗaga kafaɗa ya ce “haka suka bayar ai” “su waye?” Shiru yai mata yana ƙoƙarin juyawa ta ce “Mene wannan a ƙafarka?” Zaro idanu waje yai tare da yin baya ganin tana ƙoƙarin zuwa inda yake yasa yai saurin faɗin “ke fillo bayanki” juyawa tai da sauri amma babu kowa a wajan tsaki taja tana kakkaɓe zanin jikinta ta ce “Mai ƙarya dai ɗan wuta” ta ƙare zancan tana ɗago kanta babu Almajirin kamar yadda ta raɗa masa suna babu ko inuwarsa sai wani farin Zomo data gani kyakkyawa dashi ya ƙura mata idanu, itama kafesa tai da idanu kamar zata kamasa sai kuma ta ɗauki ƙwayarta ta nufi bakin hanya inda zata samu motar da zata kaita Njoɓoli. Da idanu Zomon ya bita har tayi nisa sosai yana kallon sanda ta samu abin hawa, girgiza yai yana kaɗa kunnuwansa sai gashi ya koma mutumin ɗazo wanda take ce masa Almajiri mai yagaggun kaya. Murmushi yai mai kyau a kuma fili ya furta “Danejona”
Da gudu motar mai ƙirar Toyota Rav 4 ta Ƙarasa shiga cikin compound na Abti American University Yola (AUN). A hankali akai parking motar a tsakanin jerin motocin da suke cikin harabar. Buɗe murfin motar tai cikin faɗa faɗa ta ce “No! I mean I lost my eye sight for a while, my Mom slapped me and i was very shouked da marin, Sbd kawai wancan banzan ya kai ƙarata gida i hate him wallah ai babu dole cikin aure ko? I’m 29 years mene ya sa za ana damuna akan wani aure?” Yanayin yadda take maganar kaɗai zai sanya kasan ranta ya ɓaci har buga kan motar take sbd zafin zuciya tsaki tai ta ce “No am okay nazo ganin Zahrah ne, i will catch you later” kashe wayar tai baki ɗaya tana fitowa daga cikin motar tunawa da yadda Yarinyar ɗazo da yadda ta firgita ya sanya tai Murmushi tana nufar hanyar wani office. Office ɗin ba kowa sai some of things da suke saman table zama tai tana danna number Zahrah.
Zahrah na tsaye cikin hall ɗin da take lecturing wayarta tai ringing ta san babu wanda zai kirata at this time sai Surayyerh da sauri ta kalli students ɗin dake hall tana faɗin “Ok guys Conservation biology has two central goals 1. to evaluate human impacts on biological diversity and 2. to develop practical approaches to prevent the extinction of species (Soulé 1986, Wilson 1992)” tana faɗin hakan tace “You get it?” Gaba ɗaya suka ce “Yes Maaa” jinjina kai tai tana taɓe baki idanunta akan wani matashi da sauri kuma ta juya hannunta riƙe da Ink pen ta nufi wajan bord da sauri ta shiga rubuta.
“What is Bachelor of Science in Conservation Biology?” Dake tana ɗaukar su course ɗin Conservation Biology Under Faculty of Sciences ne. Shiru duk sukai suka kasa bata amsa hakan yasa Zahrah sakin tsaki a file ta ce “Is an assignment, ba zan wasting time ɗina wajan yi muku explanation ba, i have so much work to do bye” wani daga cikin students ɗin ne ya miƙe yana dariya tare da ƙwaiƙwayar yadda Zahrah ke tafiya ya tsaya gaban ɗaliban ya ce “I have so much work to do bye… Big Maaaa The arrogant one I hate this woman. But i like her style” gaba ɗaya Students ɗin suka saka dry ba kuma kowa ke ƙaunar Zahrah ba, wulaƙanci da disga mutane ya mata yawa, kuma idan ta shiga hall babu wanda ya isa ya shiga ga bada Assignment da shegen text da Attendance. Zahrah na fita ta nufi Office a nutse take tafiya cikin takun isa da gadara tana sanye cikin wata atamfa Amarya collection mai tsada ɗinkin riga da skert ya kama jikinta sosai, idanunta sanye cikin farin cat eyes wanda ya ɗan haska ɓakar fatar jikinta she’s classes and educated ƴar wanka ce ga tsafta da tarin ilimi. Ƙafarta dake sanye cikin Derby shoes ta tura cikin office ɗin tana ya tsona fuska ta ajjiye handbag ɗin L.v akan kujera idanunta akan Surayyerh ta ce “Lafiya dai?” Surayyerh taja tsaki ta ce “ina lafiya? Can you imagine yau Mom ce ta mareni sbd wancan banzan?” Buɗe idanu Zahrah tai kamar ba zatai Mgn ba sai kuma tace “mene abin damuwa?” “Zahrah mari fa? Wallahi ba zan ƙara ɗauka ba idan aka sake marina, Look at me am 29 going to 30 ace Mom bata bar marina ba?” Girgiza kai kawai Zahrah tai ba tare da ta ce komai ba. “Ina magana Kinyi shiru, wannan miskilancin naki na tsana fa” “uban me kike son nace maki Surayyerh? Your mother has been slapped you sbd kinyi kuskure sai nace bata kyauta ba? Babu abin da zaki iya sbd Uwa ce dole ki hqr” Zahrah ta faɗa cikin ɓacin rai. “i can’t bazan iya jurewa ba” cewar Surayyerh “ok zaki rama kenan? Are you going to beat your mother?” Surayyerh ta girgiza kai cikin damuwa ta ce “A’a kawai zan faɗa mata kada ta kuskura ta sake marina, Nasan Uwa tace kuma sai tai ta dokana akan wanne dalili, ɓacin rana nake gudu” Kallon Surayyerh kawai Zahrah keyi kafin taja numfashi ta ce “Ina cikin damuwa Surayyerh na fara tsorata fa” Surayyerh ta ce “Damuwa akan me?” Hannu Zahrah ta ɗora akan cikinta ta ce “Am pregnant Surayyerh ina da ciki wata uku, kuma na gaji da zubar da ciki wallahi” zare idanu Surayyerh tai tana faɗin “Pregnant? ciki na huɗu kenan fa Zahrah? Kina da hankali kuwa? Wannan karan dole ki yafe cikin kin manta mai Dr yace miki ko?” Ajjiyar zuciya Zahrah ta sauke kafin ta kalli Surayyerh da kyau ta ce “I’m not ready for this, kin san ba aure gareni ba, idan na bar cikin na haihu me zance a gida? Me zan faɗawa Mimi? daman Kullum cikin faɗan naƙi aure take wai na girma da yawa, karatun boko ya buɗe min idanu yanzu kusan shekaruna 31 ne Surayyerh” Surayyerh ta numfasa ta ce “Me kike jira? Ki kira Deen mana kuyi magana ya turo iyaye kuyi aure, Mimi nada gaskiya Kinyi primary, secondary, N.c.e, degree, kinyi masters to what are you waiting for wanda ya shige kiyi aure, haba ai ta boko ai ta boko nifa idan yanzu ne wlh ba zan wata boko ba, shekara 31 ana abu ɗaya sai zallar iskanci kawai da kike kina zubar da ciki a banza, sai kin gama zubar da ƙwayayen da Ubangiji ya baki matsayin zuri’a a banza wlh” Tsaki Zahrah tai “wani lokacin wlh ke Mahaukaciya ce, ni kike tunanin zan iya auren Deen yanzu? Inda a yanzu nasan rayuwa nai boko naje ƙasashe kala-kala da ace ko secondary schl ban rufa ba shi ne zan iya auren Deen amma yanzu kam i can’t, zanje hospital a cire cikin, da kike maganar haihuwa waye ya faɗa miki daman ina son raya da haihuwa da yawa ne? Abeg ta shi muje Madam am not in the mood” Surayyerh ita dai mamakin Zahrah take bata, ta rasa ita da Zahrah waye yafi laifi, ita tana ganin mahaifiyarta na takura mata domin har kusan zaginta take a zuciya, ta hanata jin daɗin rayuwa komai sai ta ce wai taji tsoran Allah, ita kuma Zahrah iyayenta sun sake mata duk abin da zatai babu me cewa dan me gidansu gidan boko ne a waye suke gaba ɗaya, hakan yasa Zahrah keta aikata alfasha hankali kwance. “Kinzo da mota ne?” Surayyerh na miƙewa tsaye ta ce “E, kefa?” Zahrah ta ce “A’a, ba zan iya driving ba wannan cikin duk ya sauyani muje kiyi dropping nawa gida” “ok let’s go” Fita sukai Zahrah da Surayyerh aminai ne duk faɗan da za suyi har abada babu mai ji, su gama fushi su shirya. Mota suka shiga Surayyerh na driving Zahrah na gefe a haka suka bar cikin Abti America.
Da idanu Dada take bin kuɗin da Danejo take bata, a sanyaye ta ce “Duk wannan?” “E, Dadana ɗan Almajirin mai yagaggun kaya ne yace mini aradu duk kindirmo ake siya dasu, kuɗin da yawa” Dada ta jinjina kai ba tare da tace komai domin magana bai dameta ba, tun bayan rasuwar Baffansu Danejo ta zama shiru-shiru sanadin hakan ciwonta ya sake yin tsamari. “Dadana nawa ce wannan?” Danejo ta tambaya tana nunawa Dada gudar dubu ɗaya, girgiza kai Dada tai bayan ta tsurawa dubu ɗayar idanu ta ce “Ban san sunanta ba, ki bari Hamma Yabi ya zo sai ki tambayeshi ko?” Miƙewa Danejo tai ta ce “Bari naje wajan Shatu na tayata irga Naggenmu” fita tai a hanya taci karo da Hamma Yabi, da sauri Hamma Yabi ya kama hannun Danejo ya shiga duba Funa, Fobbina, Wayla, Hirna. Ma’ana Gabas, Kudu, Arewa, da Yamma, ganin ba kowa yasa Hamma Yabi faɗin “Mun shigesu Danejo, gobe ake bikin gasar wasa da maciji, wanda Sarkin ruga yake sawa, kuma yau za’a zaɓi wanda za’ai wasan dashi” fararen idanunta ta juya sosai cikin rashin damuwa ta ce “Hamma mene abin damuwa, ni Dadana kawai nakeso ta samu lafiya ina ta mafarki wani kala” girgiza kai Hamma Yabi yai kaifn ya kama Danejo sosai ya ce “Baka iya wasa da Mashiji ba Danejo, kuma Sarkin ruga zai iya zaɓarki matsayin wacce zatai wasan, idan baki iya ba Mashijin zai iya saranki ki mutu murus, ko baki mutu ba idan baki iya ba Sarkin ruga zai iya korar mutum daga cikin Rugar Rome” cike da tsoro Danejo ta zaro idanu waje ta ce “Mi boni Hamma Yabi yaya zanyi?” “Yanzu shai mu jira muga wa za’a zaɓa, kije ki ɗauki kindirmo mai man shanu ki bawa Dada gobe zamu koma ashibiti” kai ta ɗaga alamar to Hamma Yabi ya nufi cikin jejin nemo wani sassaƙen magani ita kuma ta nufi wajan garke a nan ta samu Shatu ta kama bakinta a nonon Nagge tana ta sha hankali ƙwance. Zama tai kan wani Leggal (Icce amma kututture) samun kanta tayi da tunani wanne kalar Mashiji za’ai wasan dashi? Meyasa idan taje Birni take ganin wasu mutanan ba irinsu ba komai nasu daban ne, meyesa birni ta banbanta da Rugar Rome?. Ajjiyar zuciya ta sauke tana murza yatsun hannunta da sauri takai dubanta zuwa ga ƙadamin yatsarta idanunta ya sauka akan zoben dake maƙale da yatsar da tsananin mamaki take kallon hannu yaushe wannan abun ya zo hannunta? Mene sunansa ita bata taɓa ganin abu mai kama da zobe ba sai yanzu, ga wani zane a tsakiyar zoben kamar tambarin abu amma bata san ko mene ba, ƙoƙarin zare zoben take amma ta kasa hakan yasa dole ta hqr. Suna zaune a garken suka ji ana shelar Sarkin ruga yana neman jama’ar Rugar Rome baki ɗaya. Da Shatu da Halisa suka kalli juna zuciyarsu cike da zullumi amma Danejo tai ta maza ta kama hannun Shatu suka nufi wajan. A tsaye suka samu mutane wasu na sanye da fararen kaya na Fulani wasu kuma Kuraye yawancin su gaba ɗaya farare ne, amma sam babu cikakken addini ga rashin tsafta. Sarkin ruga ya gyara tsaiwa yana faɗin “Kamar yadda kowa ya sani, a gobe ne zamu gabatar da gasar wasan Mashiji, za’a zaɓi mutum ɗaya ya buga wasa da ƙaton Mashiji kamar yadda muka saba, idan mutum ya kashe Mashiji akwai kyautar Nagge da kuma ƙwayar nono guda hamsin, idan Mashiji ya kashe mutum Shi kenan wasa ya zo ƙarhe, idan mutum bai mutu kuma za’a kuresa daga Rugar Rome baki ɗaya, don haka yanzu zamu fito da alƙalin wasa ya zo ya zamu wanda za’ai wasan da shi” Shatu ta ƙankame hannun Danejo ita ko kalmar Mashijin bata so taji an faɗa balle ta gansa a gabanta. Dajeno kam shiru tai kanta a ƙasa tunani fal ranta domin gaba ɗaya ma hankalinta baya wajan. Alƙalin wasa ya fara zagaye mutane har ya shige kan Danejo gama dubawa yai sannan ya gyara murya ya ce “Mun zaɓi Halisa Dajeno Rome a matsayin wacce zata fafata da ƙaton Mashijin mu a gobe….
#Sarautar marubuta
#True life story
[…] Idan ba ke ba Hausa Novel Complete […]