Littafan Hausa Novels

Azizan Baba Hausa Novel Complete

Azizan Baba Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

AZIZAN BABA

 

Na

R.Hussain (Zinariya)

 

 

*🌟ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION🌟*

{R.S.W.A}

 

 

*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*

_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_

 

*Alk’alaminmu ‘yancinmu*

 

 

 

 

“`MARUBUCIYAR“`

“`ƊAUKAR FANSA“`

“`IFFAH KO HIBBAH“`

“`MASARAUTARMU“`

“`MIJIN DARE“`

“`ƘADDARATA CE“`

Da sauransu.

 

 

*Da sunan ALLAH mai rahma mai jinƙai*

 

 

 

Episode 0️⃣1️⃣

 

________”Dan girman Allah kar ka faɗa na tsaya cin awara kaji wata” wata yarinya ce wacce bata fi, 10 years ba, take ta faman kallon sama tana roƙon Watan da ya haske ƙofar ɗan madaidaicin gidan nasu da ke ƙauyen Mazoji a cikin garin Daura.

Rufaffen Sirri Hausa Novel Complete

“ke AZIZAN BABA me kikeyi anan tsaye iye?” wani tsoho wanda ba zai haura shekara 70 ba ya faɗa yana dogara sandarsa hannunsa riƙe da carbi da alama daga masallaci ya ke, da sauri AZIZA ta nufi gurin tsohon ta ce “yauwa BABANA mai ƙaunata dan Allah ya kamata abinda INNA take min a gidan nan, ba daman in fita da magriba sai ta sa wannan Watan ya biyo ni duk inda nayi sai yayi dan ya faɗa mata inda na tsaya, kuma kasan Allah a wajen Atika mai awara kawai na tsaya” ta fashe da kuka, da rawar jiki Baba ya ƙara riƙeta ya na faɗin “ashsha!ashsha yo meye na wannan kukan babu wanda zai faɗa mata shima Watan ba faɗa zaiyi ba kinji, daina kukan nan kar kisa wani bala’in ya auko mana gida kukan maraya masifa ne, mu je gidan inga uban da ya isa ya bugeki”cuno bakin fitsara tayi tana hura hanci suka shiga gidan, Inna Gaji wacce ita ce uwargida ga Baba tana zaune a kan tabarma wacce take a shimfiɗe a ƙofar ɗakinta,ta idar da sallah kenan, sai Inna Ramatu tana ɗaki. Ganin shigowar BABA da AZIZA ya sa ta ce “aiken da nayi mikin tun la’asar sai yanzu ki ka dawo k….”kinga ya isa Gaji ni banson takura ba dai ta dawo ba ai shikenan” Baba ya katse Inna da faɗar hakan.

 

AZIZA da ta san ta ci kuɗi har naira 150 a cikin kuɗin da aka bata ta kawo ya sa ta ƙara maƙale BABA,, Inna Gaji ta ce “ai shikenan ba ni kuɗin” AZIZA ta kwance bakin ɗankwalinta (kallabi) ta ciro sauran kuɗin 850 ta fara soshe-soshen ƙeya, ta miƙawa Inna.

 

Irgawa tayi ta ce “ina dubu ta baki ya naga jaka huɗu da wazobiya?”

Baba ya amshe “haka aka ba ta ai”Inna Ramatu ta fito tana faɗin “ayyah ta kashe miki ɗari da wazobiya sai haƙuri ai Yaya”

Inna ta ce ” yanzu warar ce har ta 150 kika ci AZIZA?” take AZIZA ta zaro ido tana kallon watan da haske tsakar gidan. Ta ce “ni kuma Inna alkur’an k…. “ungu nan Gaji ga jaka guda ki ɗauki 150 ɗinki ki bata canjin ni banason hayaniya”

AZIZA ta ce “ai babu munafuki kamar Watan nan shine ya faɗa ai, kuma wallahi kar ya ƙara bina ta hau dira ƙafa alamar zata fara bori,gigicewa BABA yayi ya ce ” a’a marainiyar Allah kiyi haƙuri kar kiyi kuka ni nasan yanda zanyi da shi”

“wallahi ba zan yarda ba, wayyo uwata wayyo Ubana ba’a ƙaunata a gidan nan an tsane ni, BABA idan an bata kuɗin nan ba zan kwan a gidan nan ba alkur’an kabarin Uwata zan je na shiga” ihu take tana burgima a ƙasa Inna Gaji da Baba Tabawa sun yi shiru suna kallon rikicin AZIZA, BABA ya zauna dafa’an a ƙasa yana ta ƙoƙarin cicciɓo AZIZA ya na faɗin, “ungo nan AZIZAN BABA ba zan bata kuɗin ba riƙe jakar gaba ɗaya kinji ta so daina kukan inga ɗan kusun uwar da zai ƙara maganar kuɗin, a gidan nan” duk ta ɓata masa malum-malum da jar ƙasar da ke gidan, Inna Gaji ta ce “ai shikenan”ta shige ɗakinta ta na nadama da aiken AZIZA da tayi, Hakama Baba Habiba ta koma ɗaki, dan idan suka tsaya to kuwa akansu BABA zai wuce.

 

 

AZIZA kuwa jin abinda BABA ya faɗa ya sa ta daina ihu da gunjin da take, kanta yayi fututu da ƙasa,ga kitson ta sabo tas,sai da Inna ta biya har 50 sannan AZIZA ta amince ta zauna Innar tayi mata shi zane huɗu,kasan cewarsu Fulanin Daura ya sa jelar ta sauko har gadon bayanta duk da an tufke mata amma burgima ta warware tufkar.

 

 

Ta shi tayi ta na cuno baki, BABA da jikinsa ya fara ciwo saboda ƙoƙarin ɗaga AZIZA ya ɗauko sandarsa ya miƙe da ƙyar,kwankwasonsa na ciwo. AZIZA ta kalli wata ta ce “kuma na rantse da Allah ka ƙara faɗa sai na faɗo da kai ƙasa” BABA ya hau ƙwala kira “Gaji,Gaji ” Na’am” Inna ta fito tana amsawa,

Ina ajiyar da na ce ki ajiye min?”

Juyawa tayi ta ɗauko leda baƙa ta ce “ga ta Malam”ta durƙusa ta ba shi, ya karɓa ya ce “zo mu je ki ci Kifinki”

 

AZIZA ta bi shi ta na washe baki, Inna Gaji ta ce “mu kuma fa Malam?” BABA ya juyo yana watsa mata kallon tara saura kwata ya juya AZIZA ta bi shi ɗakin.

 

 

 

Baba Tabawa ta ce “Allah ya kyauta, Fatima kin tafi kin barmu da aiki,Allah yaji ƙan Abdul-azeezu kai dai ba haka kake ba”

Ta nufi kitchen dan ɗauko wa BABA tuwon dare.

AZIZA da BABA suna ɗaki tana ta auna Kifinta ga ɗari biyunta a hannu suna hira BABA ya ɗauko man zafi ya na shafawa, yajin man ya sa AZIZA zunduma ihu ta na faɗin “yaji yaji, wayyo idona yaji” a ɗari BABA ya rufe man ya hau goge wanda ya shafa yana faɗin “ayya bansan yajin zai shigar miki idanu ba” Baba Tabawa ce ta shigo da sauri ta ajiye tiren abincin,ta kamo AZIZA wacce take ta murza idanu ta na ihu” mu je na wanke miki idanun”

Kamota Baba Tabawa tayi su ka nufi bakin rariya jiki na rawa ta haɗa ruwan zafi ta hau cire mata kaya dan daman wanka take so tayi mata, tun jiya ake fama a kan wanka taƙi, jiua sai ruwan aka zubar ba’ayi wankan ba, wanke mata fuska ta farayi, yajin taji babu, daman tun da ta bar ɗakin yajin ya tafi,tsananin masifa ya sa ba ta sani ba.

 

 

Inna Gaji da BABA duk sunyi cirko-cirko BABA kamar zai yi kuka sai sannu yake faman yi wa AZIZA, ana gama wankan ta koma gefe ta raɓe tsindir da ita ta hau cuno baki.

 

Inna Gaji ce ta ce “ki zo a sa miki kayan ko haka zaki zauna?”

Shiru tayi tana ta uban ajiyar zuciya kamar wacce aka yi wa dukan mutuwa, Baba Tabawa ta shiga ɗaki ta ɗauko mata pant da kaya har da mai ta ce “zo in sa miki kinji ƴar albarka”

BABA ya ce ” ina turaren nan da AUDUL-ZEEZ ya aiko min da shi, na bata maza ɗauko a sanya mata a jikin kayan yayi ƙamshi” Inna ta ce “ya na ɗakina bari in kawo” sai da aka ɗauko aka dinga lalaɓata taƙi zuwa, Ƴar tsanarta BABA ya ce ” ɗauko min ƴar tsanarta guda in kaiwa Amina tunda ba za ta zo ba” jin haka ya sa AZIZA ta tawo da sauri, gaba ɗayansu suka sa dariya ganin ta zo, mai aka shafa mata aka sanya mata kayan sannan ta ce ” idan ba sai na mata dukan tsiya a makaranta ba hum zata sani wallahi ba dai ƴan babe na take so ba” jin haka ya sa Inna Gaji ta ce “a’a ba ita ta ce tana so ba,kar ki daketa kinji kinga Aliyu ya ce idan ya koma Makka zai ƙara siyo miki wasu har da mai magana ma”

Take ta hau murna ta zauna ta shiga ba su labarin yanda zata dinga yiwa babenta.

 

 

Ɗaki BABA ya koma ya zauna ya ci tuwonsa ya na jin radio fitowa yayi ya wanke hannu da baki, ganin su Inna na hira AZIZA tayi bacci a cinyar Inna Gaji, BABA ya ce “don Allah ku kula da amana yarinyar nan marainiya ce ba Uwa ba Uba saboda kar a cutar da ita ya sa na hana kowa ɗaukarta” idan da sabo sun saba da jin wannan karatun na BABA, Inna Gaji ta ce “oh ni Halima da ba ni na haifi Abdul-azeez ba da sai Allah, yanzu Malam ko bare ka kawo zamu riƙe amana ba re jikarmu”

BABA ya ce “ni dai na ƙara jaddada muku duk wanda bai kula da ita ba wuta bal-bal alkur’an………

 

 

 

 

 

 

GARIN KANO

 

Unguwar Tudun yolah.

 

 

Wani dangareren gida ne a bakin titin unguwar kai da gani ba sai an faɗa maka irin dukiyar da aka narka a gidan ba, wani gandsome ne ke ƙoƙarin fitowa da mota daga cikin gidan,ma sha Allah, kyakkyawa ne da ganinsa anga cikakken bafulatani, jajir yake tamkar a taɓa shi jini ya fito, sanye yake cikin dakakkiyar shaddarsa fara tas, ya ƙarya hularsa right side, wacce take mai ratsin fari da ash, agogon da ke ɗaure a hannunsa na azurfa ya duba, ya na faɗin ” Allah ya sa ba su ƙaraso ba”

Gudu ya ke sosai dan zuwa ɗauko Hajiya Hadiza daga airport wacce ta je ganin doctor ne a India, tare da Alhaji Aminu Muhmud Dollars.

 

 

 

Alhaji Aminu Dollars shi ne Babba a wajen Malam Muhmud (BABA) ya na da ƙanne har huɗu su Baba Aliya da Baba Zainab sai kuma Abdul’azeez (Mahaifin AZIZA) shi ne auta a gidan.

 

Alhaji Aminu mutum ne mai son jama’a, sai dai matarsa ta na daƙile shi, tafi son daga ita sai ƴaƴanta da ƴan uwanta kawai ne za su mori Alhaji Aminu dallars ƴan’uwansa duk suna ƙauye, sai dai yana ƙoƙari wajen ganin ya kula da iyayensa Matarsa Hajiya Hadiza (Mami) ita ce wacce ta ke daƙile shi ganin yanda yake yawan maganar ƙauyensu, ita kuma ta fi son ganin su kaɗai zai wahaltawa.

 

 

 

Cikin lokaci kaɗan ya isa tashar jirginsama na Malam Aminu Kano, dai-dai da ana announcement na jirgi zai yi landing.

Jingine ya ke jikin motarsa ya tsirawa wajen da jirgin ya sauka ido,ganin fitowar parent ɗinsa kawai ya ke jira, Alhaji Aminu ya fara hangowa, fuskar AZEEZ ce ta cika da walwala, ganin hamdila hamshaƙiya Mami (Hajiya Hadiza) ta sha Abaya yellow tare da shade yellow rolling tayi ta dawo tamkar ƴar shekara 30,tsantsar gayu da jindaɗi shi ya ɓoye manyan takanta.

 

Duk bayan wata uku tana zuwa ganin likitanta saboda hawan jinin da take da shi tun haihuwar AZEEZ, shekara 23 kenan. Kasa jira su ƙaraso AZEEZ yayi ya nufe su da sauri rungume Daddy ya yi, sannan ya koma ya rungume Mami ya na faɗin welcome to the 9ja sweet momcy……..

 

 

 

*Znariya ce

Add Comment

Click here to post a comment