Rayuwar Nafisat Hausa Novel Complete
RAYUWAR NAFISAT
Tsokaci
Wannan labari banyishi domin cin zarafin wani ko wata ba idan labarin yayi dai-dai da nawani ayimin afuwa
Labarin ya k’unshi
Zalinchi
Bantausayi
Soyayya ta gaskiya
Dakuma ruk’on amana
Littafin rayuwar NAFISAT Nasadaukar dashi gareku y’an uwana
Sa adiyya A labaran
Hasana umar Alti
Husaina umar Alti
Khadija umar Alti
Wannan shafin na kune
Mallakin
Zahra amg
Marubuciyar
Ni da Yayana
Kuyi alk’awarin zakuringa yimin comeent bana son na sticker kayimin addu’a, idan littafin yayi dad’i kufad’amin sai incigaba.
Page:1
………Wata Yarinya nagani dake gaban wata garjejiyar mata, baƙace wuluk ga wargajejen baki sai murɗar kunnan Yarinyar take tana ta faman faɗa kamar zata ari baki “wai ke Yar iskar Yarinyar nan Uban wa kika aje da zai girkamiki abincin da za kici? ga wankin Ladi can kuma yana jiranki kin kama hanya kintafin yawon iskancinki, shi Yawalen Uban me yake baki?aka cemin kina wajan Yawale mai kifi shegiya mai hali irinnan uUwarta ni dai Uwarki ta barmin bala’i, wallahi Uwarki ta tafi yawon karuwanci ta barminke wayasani ko kema kina taɓa karuwancin dan Ubanki gaki kamar aljanna” tana fada tana kai mata ranƙwashi ta haɗa mata da dundu abaya kana tamiƙe tayi ball da ita, Yarinyar kuka take kamar zata shiɗw Allah yasa ni ita fa ba dukan Inna Yagana ne ta kema kuka ba a’a zagarmata Uwa da take kullun ƴan Ƙauyen na mata gori wai Uwarta karuwanci ta tafi shiyasa tun tana da shekara ɗaya tatafi tabarta duk faɗin Ƙauyenan ba maison taraɓe shi dan kowa kƙyamarta ya keyi saboda wasu cewa suke kartalala tamasu gida ɗaya ne ke tausayinta gida Malam Sule yana da ƴa ɗaya mai suna Maryam ita kaɗaice ƙawarta, Maryam Yarinyace nitsatstsiya yanzu haka suna zuwa Makarantar islamiyya tare da Nafisa shirye-shiryen haɗa su ake tayi yanzu
Wace ce Nafisat …. Kubiyoni don cigaba
Idan naga yawon comment ɗinku zanfi samin ƙwarin gwuiwar yimaku posting
RAYUWAR NAFISAT
Dinyar Makaho Hausa Novel Complete
ROYAL STAR WRITER’S ASSOCIATION
*_Marubuta masu aiki da fasaha da zallar amana, Fad’akarwa, ilimantarwa da kuma nishad’antarwa_*
_(R.S.W.A) Ruwa kad’ai ke maganin k’ishi_
*Alk’alaminmu ‘yancinmu*
MALLAKAR
ZAHRA AMG
Page:2
…….Asalin Sunanta Nafisa Malam Ahmadu Nafisa Yariyace kyakykyawa ta bugawa Ajarida barace irin farinnan mai Kyau y’ar kimanin shekara sha biyar amman inka ganta Zaka d’auka tafi wannan Shekarun Saboda Allah Yayita da kyawon kiki K’irjinta cike yake aam dashi ga k’ugunta idan Tana tafiya kamar da gayya take, gashinta kuwa har gadon baya Atak’aice dai Nafisat kyakykyawa ce tunda ta tashi batasan Mamarta ba kuma ita har yau bata son inda take ba cewar Inna Yagana dai ta tafi karuwanci Malam Ahmadu ab’angaren Shima bawani sassauci Domin daya dawo Inna Zata fara shirgamai K’arya kennan shikuma Yahau ya zauna yarika Dukanta, Ladi kuwa Yayace gare ta kazama ce sosai sab’anin Nafisa duk da bakaya gareta ba Amman bata zama K’azanta, Ladi bata aje komai ba saidai ci Takwanta tafita yawonta Ko ina take zuwa oho, Wannan kenan.
Mundawo labari
Mikewa tayi tana Kuka Sosai kamar ranta Zaifita Ahaka ta kammala girki Ta jawo kayan wankin Ladi harda aa Inna Yagana wanda kayan In banda wari ba abunda Sukeyi ahaka ta kammala Cikin sauri tayi shirin Islamiyya tayi hanyar FIta kennan taji muryar Yar lelen gidan tana Faman zudda mata Habaici “aikin banza Anb’age da Islamiyya Ana zuwa karuwanci ,aikin banza Uwa nacan nayi ‘Diyama tayi gado mtwwwww” girgiza kai kawai tayi, tayi gaba abin ta gidansu Maryam taje Tana shiga ta hadu da ita Bakin zaurensu harararta Maryam din tayi tace” Ina nan Ina ta jiranki sai yanzu” dariya Nafisa tayi ‘tace sorry Aminiya aiki nayi” tsaki Maryam tayi Tace “aikin kenan kullum Aiki ke dai kinshiga uku Muwuce” kama hanya Sukayi suna Isa suka Iske Har Anfara karatu,v Sallama su kayi aka Amsa Ya Sayyadi yace.
Addu’oinku kawai nake buk’ata
Name: | [Rayuwar Nafisat Hausa Novel Complete] |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML |
Uploaded By: | www.hausanovel.org.ng |
Category: | Hausa Novels Documents |
Tags: | #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | February, 2023 |
[…] Rayuwar Nafisat Hausa Novel Complete […]