Littafan Hausa Novels

Dama ace Hausa Novel Tagwaye Biyu

Dama ace Hausa Novel Tagwaye Biyu

 

 

 

 

 

 

 

 

 

DAMA ACE

 

 

*HASKE WRITERS ASSO.

Home of expert and perfect writers.

 

*TAGWAYE BIYU 2023

 

*SLIMZY.*

Wattpad@slimzy33

 

*&*

 

*FEEDHOM.*

Wattpad@Feedohm

 

 

 

*001*

 

 

 

Cikin tsananin tashin hankali ya ke biye da nurses ɗin da su ke gungura keken da ya ke ɗauke da matar shi, yayin da ƙaton cikin da ke gaban ta ke motsi da ƙarfi, kallon ɗaya zaka mani ka fahimci ina cikin tsananin ciwo na nakuɗa, hannayen mu na riƙe da juna, azabar da nake ji bata hana na kalle shi cikin tashin hankali ba, lokaci guda na hango tsananin damuwa a ƙwayar idon sa.

 

Runtse ido na yi da sauri ina jin tsananin kunyar mijina, duk da irin babban laifin da na aikatawa Alhaji Sagir hakan bai hanasa nuna damuwa da kulawa akaina ba, na sake buɗe jajayen idona lokacin da muka je ƙofar labour room ɗin da zaa shiga da ni, hannunsa cikin nawa ya riƙe gam yana kallon fuskata, yayin da gumi ya jiƙa shi.

Burin Abbana Hausa Novel Complete

“Haba bawan Allah ka saki hannun nata mana? Kana ganin fa ɗakin haihuwa za mu shiga da ita amma kana riƙe da ita, tun ɗazu ana magana ka yi shiru, sannan ɗakin haihuwar nan aƙwai wata mai haihuwar a ciki, ka ga da badan hakan ba ai tare zamu shiga da kai ciki in ya so ku cinye juna saboda soyayya.” Muryar wata attender ta daki dodon kunnen ta.

Dama ace Hausa Novel Tagwaye Biyu

Na buɗe idona ina kallon wacce ta yi maganar, a hankali na girgiza kai, rashin sani ya sa ta faɗi haka, amma ni na sani babu wani abu mai kama da soyayya a tattare da shi, kawai tsananin tausayina yake yi, amma abinda na aikata masa ya daɗe da goge soyayyata a cikin zuciyar mijina, muryar sa da na tsinkaya ta sa na yi saurin juyawa gareshi, yana tsugunne gabana yana jifana da wani irin kallo da na kasa banbance ma’anar sa, hannunsa ɗaya dafe da kirjinsa gefen zuciyar sa, i zuwa lokacin jikina ri ga ya mutu, wasu hawaye masu zafi suka zubo min, harshena yayi nauyi, sai na ji ina son yi masa magana, ina son kaɗaicewa da mijina, ina tsananin so in roƙe sa gafara, ina ji a jikina tankar kallon banƙwana na ke masa, kuma ina fatan na mutu yayin haihuwa daga ni har abinda ke ciki na, bana so mu rayu.

 

Cikin dasasshiyar murya ya ce “Ki bar kuka kin ji ko Nadiya, da yardar Allah lafiya lau za ki haihu kin ji? Ki daure ki yi ta addu’a, nima zan taya ki da addu’a kin ji mata ta.?

 

Na tsura mashi ido hawaye na bin kumatuna, ciwon da ke jikina bai kai wanda ke danƙare a zuciyata ba, na girgiza kai a hankali ina faɗin “Bana so na rayu SG, bana so na cigaba da haɗa ido da kai, dan Allah kar ka min addu’ar rayuwa, ka min addu’a Allah ya karɓi rayuwata…!

 

Ya ɗaura hannun shi saman leɓena yana girgiza kai “Ba zaki mutu ki barni ba Nadiya, za ki fito mu cigaba da rayuwar mu, zamu gyara komai Nadiya, komai zai wuce.”

 

Muryar su Umma na ji, don haka na kalli gurin da sauri yayin da na fashe da kuka ina kiran sunan ta “Ummana! Ki tayani addu’a na mutu yayin haihuwa, Umma bana so na rayu.”

 

Kafin su ƙaraso wani ciwo ya taso mun, na soma numfashi da ƙyar tare da rawar ƙafafu, wanda ya sa babu shiri a shiga dani ɗakin haihuwar.

 

Ummana ta ƙaraso wajen cikin tashin hankali da ita da ƙanwata Surayya, ta yi kan Alhaji Sagir da tuni ya soma baya baya jiri na ɗibar shi, ya silale gurin yayi zaman dirshan, cikin firgici jikinta na rawa take tambayar “Sagir lafiya? Me ke damun ka? Na shiga uku, menene haka? Kar dai ka ce min don Nadiya na naƙuda ka shiga wannan Halin? Haba dan Allah kamar ba namiji ba, dan Allah ka daina haka?”

 

Bai samu amsawa Ummah ba ya yanke jiki ya faɗi, Umma ta dafe kai tana faɗin “Innalillahi wa’inna ilaihir raju’un, na shiga uku ni Hajara, me zan gani haka? Haba Sagir me yasa zaka tashi hankalin ka akan abinda ba kanta farau ba, ba kan ta ƙarau ba, abinda kun shafe lokaci kuna tsumayen wannan ranar?”

 

Surayya ta ruga a guje ta sanar da malan asibitin halin da ake ciki, cikin saa sai ga ma ɗaya daga cikin su ta zata shiga labour room ɗin, don haka aka ɗauki Alhaji Sagir ɗin aka yi emergency dashi, daga Umma har Surayya suka bar ƙofar labour room din suka nufi inda aka kai shi domin babu alamun numfashi a tattare dashi, sai da aka ɗau lokacin tukun ya farfaɗo yayin da hawaye ke bin saitin kunnuwan shi, yana jin zuciyar shi tamkar zata Faso ƙirji ta fito, a hankali ya ke faɗin “Why Nadiya? Why? Me yasa ne? Ina ma ina farin ciki da wannan haihuwar! Ina ma zan iya fidda sirrin da ke zuciya ta na samu sassauci.?

 

Daga Umma har Surayya suna dai ganin bakin shi na motsi amma babu wanda ya san me ya ke faɗa, sai dai ido da suke bin shi dashi sun yi zugum zugum.

 

 

******************

 

 

nurse na rike da hannuna inajin nishin haihuwa amma na gagara sakamakon banida karfi cikin tsananin fduwar gaba nake tunanin halin da mijina yake nakeyi haka kawai nakejin wani mummunan abu na shirin faruwa damu wata nurse ce ta turo kofa rike da allura a hannunta

 

“yanzun baiwar Allahm nan bata haihu ba?gaskiya kiyi sauri ki haihu ko kya ceto mijinki daga halin da yake ciki,lallai na jinjinawa soyayyarku kina nakuda yana ciwo”

 

“ciwo fa kikace nurse hadiza bema kamata ki fadi haka gaban patients ba zakisa jininta ya hau ai”dayar nurse din da ke rike da hannuna tayi maganar kallonsu nakeyi nakasa magana wani nishi ne ya tasomin na rike hannunta gam ina kiran sunan Allah ina fadin “idan na mutu ki rokamun mijina gafara dikda abune mai kamar wuya sagir ya yafemun abinda na aikata masa”

 

hankalinsu na kaina basa ko saurarena kokarin taimakamun babyna ya fito sukeyi cikin saa karfi yazomin nishi daya nayi d’an dake cikina ya fita kuka yakeyi irin na jarirai na sauke numfashi na runtse idona gamm jikina sai rawa yakeyi jin kukan jinjiri ya karade dakin…..

 

nurse hadiza tace “Alhamdulillah nice zanyiwa Alhaji sagir wanan albishir kila sakon haihuwar nan ya warkar dashi daga ciwon da yakeyi,dan nasan akwai goron albishir mai tsoka”bata jira mai dayar zatace ba ta fita jikinta na rawa na bita da kallo ina girgiza kaina zuciyata na tsananin kuna…

 

A hankali na ke faɗin “Kar ki kai masa, dan Allah kar ku kai masa, ku yi mana allurar mutuwa baki ɗayan mu.”

 

*****

 

ummah da surayya na gefen gadonsa surayya ta zura masa ido tausayinsa sosai takeyi tasan irin soyayyar dake tsakanin uncle sagir da Anty nadiya tasan irin yadda yakeji da yar uwar tasa,.

ummah dakyar ta bude baki tace

 

“kai yanzun sagir haka zaka rinkayi kamar wani mace?yau ninaga abinda ya isheni be ishi Allah ba daga matarka na nakuda batada lafiya dik saika fita hayyacinka kaida zakai mata addua tunda ai abun farin ciki ke shirin samun mu”

 

murmushi nurse hadiza tayi tace “nazo ne abani goron albishir”zumbur Alhaji sagir ya mike gabansa na tsananin faduwa yasa hannu ya dafe kirjinsa gefen zuciyarsa dake harbawa kamar zata fito tsananin fargaba,

ummahna ta washe baki cike da farin ciki “tunda naganki cikin farin ciki da dariya nasan baa banza ba ko?nadiya ta sauka kenan”

 

nurse hadiza ta jinjina kai “ta sauka tasamu d’a namiji kato kodasshe kuma lafiyayye yana nan sai kuka yake cewa nayi nice zanzo in fada wanan albishir wajen babansa dan insamu goro mai tsoka”kafin ta karasa maganar tuni Alhaji sagir yayi baya yana shakuwa jikina na rawa ta fada kan gadon,

 

“innahlillahi wainnailaihi rajiun sagir sagir lafiyanka?”turo kofar akai tawagar gidansu alhaji sagir ce “ina yaayah sagir din da nadiyyar “cewar wata dattijuwa fara tas mai hakorin maka kallon suturar jikinta kadai da fatarta kasan akwai naira,

 

 

nurse ce ta Shiga girgizasa shiru ta ruga da gudu “bari na kira doctor”bata jira cewarsa ba,

 

kuka ummah takeyi tana fadin “haba sagir ya zakai mana haka abin farin ciki ya samemu kuma ka rinka yanke jiki kana faduwa daga albishir?”

 

“Anty nadiya ta haihu ne?”cewar wani saurayi dake tsaye mai tsananin kama da alhaji sagir kasa magana ummah tayi ta jinjina masa kai tana kuka likita ya shigo da sauro rike da abun gwada numfashi nan da nan ya Shiga gwaje gwaje dukkansu dake zagaye da gadon ciki. tashin hankali suke daka kalli fuskokinsu doctor ya dauki minti goma gumi ya jikasa sosai ya zare abinda ke kunnensa yana kallonsu daya bayan daya,

 

“likita lafiya?lafiya dai ko?”daidai nan aka gunguro nadiya rungume da jinjirinta aka shigo da ita dakin dukkansu kallonta sukeyi cikin faraa hajja ta daga hannunta sama tace “alhamdulillah yau naga gudan jinin sagir jikan farko a wanan dangi saidai ga ubansa ba lafiya”

 

gabana ya yanke ya fadi ina kallon mijina dake kwance babu alamar motsi likita yayi gyaran murya cike da rauni yace “am sorry to say da abinda zakuji”

 

“likita lafiya?meyasamu sagir din daga albishir?kodai farin ciki ne?”ummahna tayi maganar cikin kosawa tana kallon sagir da gumi ya karyo masa idonsa a rufe,

 

“ya rasu zucuyarsa ce ta buga hakan yayi sanadiyyat muruwarsa”da sauri kanin sagir ya cakumo doctor “karya kakeyi likita tayaya zakace dan uwana ya rasu?be mutu ba bakuma zai mutu a wanan halin da muke ciki na murnar karuwa a dangin mu ba”nan dakin ya rikice kakar Alhaji sagir ta karasa ta Shiga jijjigasa tana kiran sunansa kuka takeyi tana fadin “babu sagir sagir ya mutu innahilaihi wa innahilaihi rajiun wace irin bakar rana ce wanan?”

 

ta juya ta kalli jaririn dake hannun surayys kanwata ta karbesa cikin tashin hankali hawaye na diga a idonta yana sauka a fuskar kinjirin……

 

 

wata irin kara na kwalla ina yunkurin mikewa jikina sai rawa yakeyi na manta da ciwon dake jikina na haihuwa na nufi gadon da mijina ke kwance sambal na rukosa na cukumo rigarsa “katashi mijina Dan Allah ka tashi idan ka mutu bakin cikin zai zamemun biyu ka tashi mu warwere kullin dake tsakaninmu ka tashi mijina karka tafi ka barni cikin wanan hali da nake ciki….nasan kana jina baka mutu ba sagir idan wasa kakeyi ka tashi kaji bazan jure wanan wasan ba ka tashi”jinjigasa nakeyi ina kuka gashin kaina ya yamutsa na juya na kalli ummah na da tayi zaman yan bori tana kuka na kalli surayya dake rungume da jinjirina wanda fuskarsa dana kalla tayimun bakij kirin wata irin tsanar kaina da jaririn ta darsu a cikin zuciyata jiri ne ya soma daukata nan nafara ganin duhu ina cigaba da kiran sunan sagir take na fadi kasa sumammiya…….

 

 

*SLIMZY*

*FEEDHOM*

#DAMA ACE…..

[ *DAMA ACE….!*

 

 

*HASKE WRITERS ASSO.*

Home of expert and perfect writers.

 

*TAGWAYE BIYU 2023🔥🔥*

 

*SLIMZY.*

Wattpad@slimzy33

 

*&*

 

*FEEDHOM.*

Wattpad@Feedhom

 

 

*mai bukatar a tallata masa hajarsa ya tuntubemu 08036953516 ko 07042277401

 

*002*

 

matashin saurayine da bazai wuce shekaru talatin ba a duniya kyakkyawan gaske ajin farko yana zaune akan tabarma ya rafka tagumi mahaifiyarsa dake rike da kwanon abinci ta shigo da sallamarta ta zura masa ido sam beji sallamarta ba dan bai amsaba,

 

“kai sulaiman yanzun tun dazun kana nan zaune kayi tagumi?kai baka fita ka zagaya da napep dinba kai bakaci abinci ba kaganan ne dai tuntuni nake tambayarka matsalarka da damuwarka”

 

hawayene suka zubo masa ya girgiza kai inama zai iya fadawa innah damuwarsa inama zai iya fada mata tashin hankalin dake tunkararsa?tsura mata ido yayi hawaye na gudu a fuskarsa,

 

“subhanallahi sulaiman ya kake kuka?ninarasa gane kanka a wanan watanni. kwata kwata meye matsalarka kaki fada mun ko kanada wadda ta fini ne?”sulaiman ya girgiza kai cikin kuka besan lokacin da yace “Ina cikin masifa Inna. ”

 

“Masifa kuma?”innahrsa tace tana kokarin ajiye kwanon dake hannunta jikinta a sanyaye sai lokacin ya fuskanci zancen zuci ne ya fito fili yayi saurin share hawayensa yana sosa keya “am innah nace bari na zagaya da napep din nan ko zaasamu wani abu ko?”

 

“ina zaka baka fadamun wace irin masifa kake ciki?ka faɗa mun wanda ya jefa ka a masifa”bata rufe baki ba sukaji sallama daga inda suke zaune innah ta amsa,

 

cikin alhini wata matashiyar mata ta shigo “innah sai kikaji rasuwar Alhaji sagir ko?yanzun nan aka sanar wallahi dik jikina a mace yake Alhaji sagir mai dala”

 

“innahlillahi wainnailaihi rajiun…..Alhaji sagir dai dake taimakon talakawa?”innah tacw jiki a mace,

 

wani fitsari ne ke neman zubowa daga wandon sulaiman cikin sassarfa ya soma gumi jikinsa sai rawa yakeyi wani takaici da kunci ke azalzalar shi maganar matar ce ta katsesa “kuma ance matarsa ta haihu yau din nan dan kamar sakamakon labarin haihuwar matar ne zuciyarsa ta buga tsananin farin ciki”

 

 

. cikin zuciyar sagir yace ko kuma tsananin bakin ciki ba?yasa takalminsa ya fita ko ganin gabansa bayayi haka yake jefa kafarsa tafiya yakeyi tamkar mara hankali yana surutai batare da sanin inda zashi ba…..

 

“****

sanye nake da hijab hawaye ya gama wankemun fuska tin ina kukan fili nakomayin nazuci ina zaune babban parlor inda gida cike yake dankam da mata da yan uwa da dangi ina d’aga kaina nayi tozali da mukarar da aka sako mijina sagir a ciki na mike tsaye cikin tashin hankali aka diresa tsakiyar parlor nan cikin gida ya kaure da kuka,

 

“shikenan tafaru takare sagir katafi kabarni a wanan duniyar mai cike da kunci da takaici da duhun rayuwa na tabbatar alhakinka da hakkinka bazasu taba barina in zauna lafiya ba yanzun ne lokacin da zan girbi abinda na shuka”tsittt cikin parlorn kowa na kuka saidai hankalin kowa nakan maganganun da nakeyi tamkar zararriya…..

 

kukan jinjiri ne ya karade cikin parlorn surayya ce rungume dashi ta nufoni idonta a kumbure alamu sun nuna tasha kuka “Anty nadiyya ki karbesa ki bashi nono sai kuka yakeyi tun dazun hajja tace na kawo mikishi”

 

wani kallo nayi mata ina nunata da yatsa jikina na rawa “karkizo nan karki tako inda nake bana son ganinsa bana kaunarsa bana kaunat hada fuskata da wanan yaron wanda shine yayi silar rabuwa ta da mijina rabuwa ta harabada”

 

“nadiyya kina haukane wasu irin kalamai ne wadanan kike jifan dan da kika haifa dashi ?ko zafin mutuwa ne ke neman haukataki?baki ganin niimah Allah yayi miki?ya baki kuma ya karba ubansa daga gareki?”girgiza kai nakeyi ina kallon ummahta dake wadanan furucin ummah bazata taba gane masifar da nake ciki nasa kaina a ciki ba……

 

waigawa nayi ina kallon wadanda suka zagaye munkarar mijina sunayi masa addua na durkushe a kasa hannuna na rawa na yaye zanin da aka rufe farinsa dashi ina kallonsa hawaye na d’iga daga idanuwana zuwa jikinsa ina girgiza kai ban taba shiga tashin hankali da masifa irinta yau ba yau sagir ne a kwance a kasa ya zama gawa na durkusa na kwantar da kaina a jikinsa ina tsananin rusa kuka “sagir nasan kana jina ni inaji a jikina tamkar baka mutu ba bazaka mutu ba yanzun kada kabari a birneka a rabaka dani sagir nasan kana jina meyasa ka zabi boye sirrina?meyasa ka zabi rufamun asiri?gashi mutuwarka zata bankade asirin da ka rufamun tafiyarka rasa wani jigo ne na rayuwata sagir ina tsananin sonka idan katafi ka barni tabbas nima bazan dadeba Zan biyoka Dan da kaina zan mika kaina zan hukunta kaina”

 

mari naji an saukemun a d’agani daga jikin gawar nayi taga taga zan fadi na bude idanuwana ina kallonta “ke nadiya kin haukacene?koko kin zare ne kike wadanan kalaman a dukunkune?idan kinsan akwai wani kulli a tsakaninki da sagir ki kwancesa tun wuri kafin asirinki ta tonu kamar yadda kike ikirari”ta karasa maganat tana zabgamun wata uwar harara momy ce kanwar abbah na ta fuzgoni ina kallo aka d’aga gawar sagir sama aka fice da ita ina daga masa hannu wasu hawaye nakeyi madu tsananin kuna ke sauka a kumatuna

 

wasu dake zaune gefe suma hade kansu waje daya suna kus kus “Anya maganganun yarinyar nan babu lauje cikin nad’i ki duba irin furucin da takeyi kardai itace silar mutuwar mijinta”

 

jinjina kai wadda suke maganar tayi tace “da walakin goro a cikin miya”muryar surayya kanwata sukaji tana fadin “andaini kunya anyi mutuwa baa kauda gawa ba ma amma kuna gulma kunji haushi wallahi munafukan banza munafukan wofi”ta karasa maganar tana jefa musu harara tana jijjiga jaririn dake hannunta dake faman tsala kuka,

 

 

mikewa nayi tsam daga cikin mutane na kalli surayya “ina wayata?”ta cirota daga aljihun rigarta suka bini da kallo can dakin mijina na Shiga na rufo kofar dakin na zauna gefen gado ina kallon hotona da nasa dake manne a jikin bango muna dariya cikin farin ciki na girgiza kai “shikenan wanan farin cikin ya gushe daga gareni katafi kabarni”

 

jikina har rawa yakeyi wajen daddana numbobinsa a wayata na kara a kunne na gabana na tsananin faduwa zucuyata na harbawa don jin abinda zai fada idan ya dauka,

 

Yana ɗauka kafin na yi magana ya tari numfashi na “Allah ya isa tsakanina dake Nadiya? me kika kirani ki fadamun?kin kasance mace mara godiyar Allah wadda take dauke da fushin Allah wallahi nayi danasanin saninki a rayuwa nayi danasanin haduwa dake kin dasamun bakin cikin da harabada bazai taba gogewa ba a zuciyata kin jefani cikin matsalar da ban taba shigaba shedaniya kawai mai dauke da tsinuwar mala’iku data ubangiji”

 

naja wani numfashi na sauke yayi shiru sai kawai ji nayi ya saki kuka cikin wayar cikin kuka na soma magana,

 

“Ba kak keda kuka ba nikeda kuka nice dauke da mummunan tabon da bazai taba goguwa ba a danginmu ko bayan ba raina ko bayan na mutu…..nakiraka ne in sanar dakai yaro namiji yana nan lafiyayye na haifa maka “turo kofar akai yasa na jefar da wayata kasa ina kallon wadda ta shigo dauke da jaririna,

 

“nadiyya me kikeyi cikin dakin nan?nan kikazo kina kuka nadiyya?abinda zaki sakawa sagir dashi kenan bayan babu ransa?”na girgiza kaina cikin zucuyata nayi hamdala da bataji mai nake fada ba,

 

ta zauna gefen gadon ina kallon hajja tausayinta ya kamani tsohuwa kakar alhaji sagir tana matukar kaunarsa daga ganinta kasan taci kuka sosai “karbi yaronki ki bashi nono kinji?”

 

na girgiza kai tayi saurin taryar numfashina “nasan ciwon da kikeji nadiyya nasan bakin cikin mutuwar mahaifinsa yasa ko ganinsa baki sonyi ko?”na jinjina mata kai ina hawaye nasa kai na karbesa na kura nasa ido tamkar maison gano wani abu,

 

muryar tace ta katseni “bashi nono nadiyya kada ki dauki alhakinsa”banason yiwa hajja musu yadda take tsananin kaunata da jikanta hakan yasa jikina na rawa na ciro nono nasa masa a baki caraf ya cafke yana sha tamkar ba jaririn da aka haifa yau ba,

 

yanashan nonon nawa inajin wani zafi da radadi cikin zuciyata hajja ganin nasa masa nono a Baki yasa ta mike ta fice hade da rufo mun kofa,

 

na kafesa da ido cikin tsananin takaici inajin tsanarsa na darsuwa cikin zuciyata…..

*****

juyi kawai nakeyi nakasa bacci cikin dare kowa yayi bacci na mike na zauna tunanin yadda zan saci jaririn nan in kaiwa uban shi nakeyi yadda ya haddasa mun bakin ciki nima saina haddasa masa sainasakasa a tashin hankalin da bai taba shiga ba zan tabbatar masa da nidin shedaniya ce mai tafiya da tsinuwar mala’iku kamar yadda ya fada,

 

sad’af sad’af na dauko jinjirin na fito dashi saidai na kawo bakin gate din gidan naga inuwar mutane biyu maza a bayana nayi saurin juyawa da sauri na rungumesa kam na kwalla kara ganin dayan ya zaro wuka ya nufoni dashi…..

 

 

 

 

 

*SLIMZY*

*FEEDHOM*

#DAMA ACE….



Muna dauke da Littafan marubutan Hausa…

 

 

 

Name: [Dama ace Hausa Novel Tagwaye Biyu]
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: www.hausanovel.org.ng
Category: Hausa Novels Documents
Tags: #Hausa Novels Documents #Hausa Novels Books Complete Hausa Novels #Hausa Novels #Hausa Novel #Romantic Hausa Novels #Sabbin littafan hausa
Novel Price: Free
Last Modified: February, 2023

 

 

Idan Kuna Bukatar Hausa Novels Audio Ku Shiga anan Kana ku danna Subscribe a tashar My Novels TV

Zaku iya sauke Manhajar Android ta Abokin Hira anan Domin samun littafan Hausa Novels maras adadi


Zaku iya shiga WhatsApp Group namu na Hausa Novels anan domin samun Littafan Hausa Novels Maras adadi


Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Hausa Novels Telegram


Powered by: www.hausanovel.org.ng

Add Comment

Click here to post a comment