Boddiya Hausa Novel Complete
Boddiya Hausa Novel Complete
*BOƊƊIYA*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION
“`Gidan karamci, rubutu don ci gaban al’umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.“`
*https://www.facebook.com/106494781436168/*
RUBUTAWA
Aisha Sani Abdullahi
*(Xayyeesherthul-humaerath)*
_Hi,Hello,Fans Gani na dawo da wani labari mai ɗauke da nishadantarwa, ilimantarwa ……. ba ma sai na ce komai ba,ku kun sani kuma zaku bada labari, Kafin in ci gaba da Series din Yel na ce bari mu taɓa wanan,kada ku bari a baku labari domin labarin na musamman cikin musamman dinma na daban ne_
*Note: littafina na kudine, 300 kacal*
FREE PAGE-1
Bismillahir-Rahmanir-Rahim
Gabadaya baya cikin hayyacinsa tuƙi yake ba tare da duban hanya ba,duk da kasancewar dare ne kuma ga duhu,motoci sun kauracewa titi sai shi kadai yana watangaririya.
Kamar ance ya kalli gabansa, cikin sauri ya taka burki ganin yadda idanunsa ke nuna masa tamkar mutumne kwance gabansa.
Ƙara motsa idanunsa ya yi da hannu domin tabbatar da abun da zuciyarsa ke aiyana masa.
Jikina Yake So Complete Hausa Novel
Tabbas Mutum ne,ya furta a kasale,jiki ba kwari ya fito, fitowar da zaiyi kuwa gabansa ya yi mummunan faduwa ganin yarinyar da baza ta zarce shekara goma ba kwance cikin jini,ga dukkan alamu ta galabaita ta ko wani bangare,tallafota ya yi,yana kara kallon gaba da bayansa,babu shakka ba kowa a wannan titin a yanzu kam,to amman taya….
Ya gagara karasa furtawa kokarin dagata ya fara yi, ba karfi jikinsa amman haka ya jata a hankali yasa a mota sannan ya ci gaba da tuƙi cikin sauri.
Yana isa gida ya fara Horn Tamkar mala’ikan da aka turo daukan rai da sauri mai gadin ya bude masa ya shiga.
Fitowa ya yi a motar kamar zai faɗi yana fadin.
“Ga,,ga wata nan shigo da ita ciki.”
Bai kara fadin komai ba ya shige kawai.
Kasancewar mai gadin yasan halinsa sarai ba tsaya tambaya ba kawai ya shiga cikin motat tare da ɗaukan yarinyar, shi kan shi sai da ya tsorata ganin yarinya karama cikin wani yanayi ga jini duk jikinta.
“Oh Allah ko meya faru kuma, Allah sa dai ba kasheta ya yi ba.”
Yana fada tare da daukanta ya shiga da ita,a falo ya ajeta kan kujera sannan ya fito.
Shi ko Dr Rowan kwanciya ya yi barcin minti goma kafin ya tashi ya shiga wanka ganin ya dawo hayyacinsa yasa shi karasawa gareta, fara cire mata fingilin zanin ya yi abun da ya kara bashi mamaki shine tabbatar da cewa anyiwa yarinyar fyaɗe ne.
Tsaki ya yi yana fadin, “Oh My God! Wai yaushe za abar hakewa kanun yara hakane? Yanzu shi wanda ya yi wannan aikin me zai ji anan?”
Tsaki ya yi, yana shiga cikin bedroom dinsa, fitowa ya yi da first aid box a hannunsa ya mata dukkanin abun da ya dace harda allurar barci sannan ya dauketa ya je toilet ya wanke mata jiki tas tare da sanya mata wata rigarsa a jiki ya kwantar da ita.
Kayanta kuwa zubarwa ya yi a shara tukun yaje ya kwanta shi ma.
Cikin dare ya ji an farka ana kurma uban ihu,da maimakinsa ya buɗe ido tare da kunna wuta domin shi ya ma manta da batun akwai wata yarinya a gidan.
Ita ko ta dage ban da ihu ba abun da take kurmawa tana fillanci.
“Hey Stop, ki yi shiru ki koma ki kwanta ba kisan yanzu dare bane?”
Maganar da yake tamkar yana kara zugata ihu ta kara yi tana kuka tare da kankame jikinta musamman yanayin dakin da ta lura da shi wanda ko a mafarkinta bata taɓa cin karo da shi ba,bare kuma a zahiri.
Ga shi ,shi kansa ma bata taba ganin mutum mai yanayi irin nasa ba adoron duniya.
Kallon da ta kara masa a karo na biyu ne ya kara tarwatsa mata kwakwalwa ganinsa sanye da fararen kaya.
Ba tantanma ta mutune, nan ba duniya bane, rufe ido ta yi da hannayenta jiki na rawa tana ƙara,motsa jiki take son yi da niyar ta tashi ta gudu ko zata bar wannan lahirar amman ina gaba-daya ta kasa motsawa jikinta ciwo yake ta kowanni bangare.
Wata irin gigitacciyar tsawar da Rowan ya yi mata ne ya bata nutsuwa cikin second guda tare da sake wani mawuyacin fitsari.
Ya lura sam ba jin yaren da yake yi take ba daga turancin har hausa hakan ya sa shi sakin tsaki tare da shiga toilet ya yi alwala ya kama sallar dare.
Ita kuwa tunani ta fada, shin wacce duniya ce wannan ta tsinci kanta a ciki da ko maganar mutanen ciki ba ta ji, ga shi komai nasu ya banbanta da wanda ta saba gani anata duniyar illa abu ɗaya da ya bata mamaki yana sallah kamar yadda ta baro tasu duniyar ana yi kuma har ita ma tana yi,amman bayan nan komai ya banbanta,kanta ne ya fara mata wani jarababben ciwo ta dafe ,kuka kuwa ta kasa yinsa a zahiri domin ji take in ta kara wani motsi mai kara zai iya cinyeta.
Zuba masa idanu kawai tayi yana sallah tana kallo har barci ya kara kwashe ta ba tare da ta ankare ba.
Gari ya waye,motsin Rowan da ta ji ne yasata fara buɗe ido a hankali.
Wanka ya yi yana shirin sa kaya hankalinsa kwance yana taje gashin kansa.
Kashi ta fara ji tana so ta yi magana amman bata san me za ta ce ba,ga shi ya matseta ,a zuciyarta take rayawa, “Daman a wannan duniyar ma mutum na jin kashi kamar yadda muke yi a duniyarmu?”
Kara cikinta ya fara yi yana kurari alamar tabbas kashi ne yake shirin fitowa nan take ta sake wata irin tusa da shegen wari tamkar miyar kukan da tai wata guda a ajiye.
Hada ido sukai nan take tana zaro ido shi ma yaiy tsuru dukaninsu ba su san me zasu cewa juna ba domin ko sun yi magana babu mai fahimtar wani.
Kuka kawai ta kara fashewa da shi,yayin da ka………………
*Mu ci gaba ko mu tsaya?,me kuka fahimta? Shin ya zata kasance tsakanin Dr Rowan da Yarinyar da ba mu san ko sunanta ba? Kar ku manta basa jin yaren juna fa,ga alamu sun nuna duniyar su ba ɗaya ba ce*
*Kofa abude take ga wa inda suke son a tallata masu hajarsu a kowanni feji cikin farashi mai rahusa,kai tsaye zaku iya mun magana ta wannan number.*
08103080717
Urs Xayyeesherthuo
*BOƊƊIYA*
*NOBLE WRITERS ASSOCIATION
°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°°
“`Gidan karamci, rubutu don ci gaban al’umma, mu gudu tare mu tsira tare, alƙalaminmu ƴancinmu.“`
RUBUTAWA
Aisha Sani Abdullahi
*(Xayyeesherthul-humaerath)*
_Hi,Hello,Fans😍Gani na dawo da wani labari mai ɗauke da nishadantarwa, ilimantarwa ……. ba ma sai na ce komai ba,ku kun sani kuma zaku bada labari, Kafin in ci gaba da Series din Yel na ce bari mu taɓa wanan,kada ku bari a baku labari domin labarin na musamman cikin musamman dinma na daban ne_
*Note: littafina na kudine, 300 Normal Group, Special 500.*
FREE PAGE-2
Bismillahir-Rahmanir-Rahim
Kashin ke kokarin kara fitowa da ya lura da yanayinta karasawa ya yi gabanta tare da jan hannunta ya shigar da ita toilet yana nuna mata, “Nan zaki hau.”
Kyankame jikinta tai tare da fadawa wata duniyar tunani bata ma san yana magana ba, gani tayi cikin wata duniyar an kara kawota wata duniya kuma daban ko nan din wacce duniyar ce oho,kuma abun mamaki daga taku kadan har sun bar wancen duniyar?
Mantawa ta yi ma da batun tana jin wani kashi sai da taga an fisgeta an daura kan wani abu tare da janye rigar yana , “Oyaa kiyi.”
Ita dai binsa take da kallo kawai ba tare da ta fahimci me yake fadi ba.
Ya fita tare da jan kofar.
Banda kalle-kalle da sake-sake ba abun da take yi a zuciyarta, Dr Rowan kuwa har ya gama shiryawa ya ga alamar bata dai fito ba,yana leka toilet din kuwa ya ganta zaune kamar yadda ya barta tayi tsuru da ido.
Alama ya mata da hannu ta taso, haka ta taso kuwa ba yadda ta iya domin gudun taki zuwa ya mata tsawar da ta tarwatsa mata kwakwalwa kamar ta jiya.
Binsa take kawai duk inda ya nufa, ya zauna ita ma ta zauna tana kallonsa.
Dafa kai ya yi kawai shi ma yana kallonta a zuciyarsa yana tunani, “shin ya zanyi ne da wannan ‘Yar? Ba gane maganarta nake ba,bare in ce zan maidata ga iyayenta, ban ma san yadda zan yi da ita ba kwata-kwata ga yanayinta ba irin na yan Nigeria ba ,ban san mene ne mafita ba sam ga wannan lamarin.”
Nocking din kofar da yaji ana yi ne yasa shi tashi yaje domin karbo ordern abincin da aka saba kawo masa kullum da safe.
Ya karbo yana juyowo kawai ya ganta ƙuru a bayan sa tana binsa.
A jiye abincin ya yi kan kafet ya zauna ita ma ta zauna hatta yanayin yadda ya zauna saida ta kwaikwaya,ita duk a tunaninta haka yake so ta yi duk abun da ya yi kawai.
Mika mata takeaway ɗaya ya yi yana mata alama da ta ci.
Ta karɓa ta rike tare da ci gaba da kallonsa.
Ganin hakan sai ya fara ci.
Yana fara ci ita ma ta fara yadda yake yi.
A hankali.
Mamaki ya isa Dr Rowan, kallon agogon hannunsa ya yi ya lura ya yi letti sosai domin petient na jiransa.
Da sauri ya fara ci,ita ma ta fara kamar ana ingizata.
Dagowan da zai yi ya kalleta bai san lokacin da ya tintsire da dariya ba, ita ma dariyar tasa tana kallonsa
Dukansu biyu ban da sautin dariya ba abun da ke tashi a afalon.
Ya tashi zai tafi ita ma ta tashi, kawai sai ya tuna, shin ya zaiyi da yarinyar nan ba abun ya barta cikin gidan ita kadai ba, ga shi ma tana bukatar a yi mata wanka sanan asata a ruwan zafi har ma abata magani kasancewar raunin da aka ji mata wajen hake mata.
Cikin sauri ya jata toilet ya wanke mata jiki tare da sata cikin ruwan dumi.
Ya bata magani sannan ya dauko wani karamin wandonsa ya sa mata, tare da karamar best.
Ita kam kallonshi kawai take har ya shafa mata mai tukun suka fita tare.
Har mai gadi ya wanke motar ya gyara,gaba ya bude ya sata ciki sannan ya ma mai gadin magana kan in Nanyn da ke kula da gidan yazo y duba kujera ya wanke ya gyara da kyau tukun ya koma motar.
Gani tayi sun fara tafiya cikin mota da sauri ta daura hannunta aka tana sakin ƙara bata son tana ganin titi yadda yake in mutum na cikin mota gani take ana tunkuɗata wani wajen ne.
Tsawa ya kara daka mata kamar na daren jiya kafin ta nutsu tare da kankame kujerar motan tana kara rufe ido.
A haka har suka Isa asibiti
Ita dai har yanzu mamaki yaki daina ziyartar idanunta da ƙwaƙwalwarta domin nan ma wata duniyar ce daman dai da wacce suka baro.
Ganin mutane na shawagi masu yanayi irin na Dr Rowan ne ya kara firgitata yana bude mata kofa ta kankamesa yana tafiya tana binsa a baya,tamkar zata shige jikinsa, takaici kuwa a zuciyarsa ji yake kamar ya jefar da ita gefe.
Gaba-daya Ma’aikatan asibitin kallonta suke cike da mamaki suna gaishesa, “Morning Sir.”
Yana amsawa da “Morning.” Sai su wuce domin sun san Dr Rowan baya da wasan da za su tsaya tambayarsa wannan wace ce naniƙe a jikinsa,ga wani irin shiga da tayi abun dariya da takaici, Sannan ga bayyanar da cewa tsoron mutane take a zahiri.
A haka har suka shiga office dinsa,nuna mata kojera ya yi ta gefe ta zauna,sannan shima ya zauna a tasa wacce yake jin damuwoyin marasa lafiya.
Kusan minti biyar yana duba wasu files sannan ya dau wayar gefensa ya kira kan cewa za a iya fara shigowa.
Wata mata ce ta fara shigowa, suna haɗa ido cikin firgici ta tashi da gudu ta koma bayansa
Ita kanta matar sai da tsorata.
Cikin fushi da tsawa Rowan ya ce, “Ke.”
Ita ma ke din ta maimaita tunda bata san amsar ba shi ba.
*Cakwakiya babbar matsalar shi ne har yanzu bamu san sunan star din ba*
Masu son shiga group maza ga link nan
https://chat.whatsapp.com/KImQQvJwDpD28qyVfH0YD8
mata kuma ku min magana a WhatsApp kai tsaye ta wannan number domin saku a group din Mata zallah
08103080717
*Kofa abude take ga masu so a tallata masu hajarsu cikin farashi mai rahusa, 08103080717*
Urs Xayyeesherthuo
[…] Boddiya Hausa Novel Complete […]
I really love dis book