Littafan Hausa Novels

Kwarton Anti Hausa Novel

Kwarton Anti Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

Kwarton Anti Hausa Novel

*Da sunan Allah zan fara da sunanshi zan gama da ikon Allah,surbajo sabon salo na kudine,wannan da sauran masu zuwa agaba bana kudi bane,Allah yasa sakon dake ciki ya isa inda zaa amfana dashi*

Kwarton anti
*Page 1-2*

“Mummy don Allah kiyi hakuri ki rufamin a siri kar kije club dinnan don Allah ki tausayawa rayuwata da taki”cewar wani matashin yaro da shekarunshi bazasu wuce goma sha biyar ba,

Tsugune yake rike da kafafuwanta yana kuka,kallo daya zaka masa ka fahimci yana cikin tashin hankali me tsanani.

Cikin halin ko in kula matar ta fara magana cikin isa da izza tace. “Sultan kenan,wlh lamarinka ya fara bani tsoro,taya ina kasuwanci dan in rufa maka asiri amman kai kullum kawo min nakasu kake ga kasuwanci na,” Hawaye ya share yace bakinshi na rawa. “Mummy kiyi hakuri don Allah abokaina tsokanata suke suna kirana DAN KARUWA, sunce kin cika yawo mummy ki zauna agida don Allah ki taimakeni”yakarasa maganar cikin matsanancin kuka.

Tantiranci Hausa Novel Complete

Murmushi tayi sannan tace. “In kace ta mutane zakabi zaka mutu da talauci, niko yau wlh ba abinda ze hanani fita,in zakaje ka kwanta kaje ka kwanta,danni se dare”

Bin jikinta yayi da kallo yana kuka,sanye take cikin riga da wando masu matukar bayyana surarta,wanda sam bedace ta fita dasu ba.

Baki na rawa yace. “To mummy kidaura zani akan kayan kan ki fita kinji”

Dariya tayi tace. “Sultan problem,je ka daukomin zanin”

Ba musu ya mike da gudu yaje dakinta ya dauko mata zanin harda hijabi ya mika mata.

Bata musa mishi ba ta daura zanin tasa hijabin sannan ta dauki handbag dinta ta shafa gefen fuskarshi tace. “Ka kulle kofa kayi addua kaji,se na dawo”

Jiki ba kwari yace “Adawo lfy mummy”

Yanaji yana gani ta fice daga gidan,rushewa yayi da kuka ya fada kan kujera yana kuka me tsuma zuciya.

Ita ko tana fita, wani lungu ta samu ta cire zanin da hijabin daya bata tasa ajaka tayi gaba abunta.

Tana tafiya tana juya jiki,har ta isa bakin titi ta hau mashin.

Tana isa gurin club din tundaga bakin kofa matasa ke mata ihu suna kiran. “Lokacinki ne khady baby,” Gaba daya gurin se tafi ake mata itako se juyi take cikin kartin mazan suna tafawa wasu kuma su rungumeta.

Cikin gurin ta karasa shigewa,inda ta nufi mashaya,

Kwalba uku ta siya na cordine bata bata lokaci ba ta shanyesu,mintuna kadan ta mike ta fara hada hanya,

Isa zakara ne ya hangota tana hada hanya da sauri ya nufeta,

DAN KARUWA

Writen by zahra surbajo

Page2

Yana zuwa janyota jikinshi yayi yana dariya,yace. “Khady baby kinyi wuyar gani”

Murmushi tayi tace tana kara shigewa jikinshi. “Zakara,kacika takura ne yasa nake maka wasan buya,kai bakasan kayi abu na marmariba,kai cinye du ne shiyasa bana son alaka dakai wlh,gaka da hannun yan dambe”

Murmushi yayi ya fara shinshinata yana laso wuyanta kamar wani mayunwacin kare,yace. “Khady baby yau zan miki biya me kyau dan akwai kudi ajikina,karkiji komai,wlh kishin ruwanki nake narasa ina zan ganki se yau Allah ya hadamu”

Dariya tayi ta lakace mishi hanci tace. “Shaidan de ya hadamu ba ruwan Allah”

Dariya shima yayi yace. “You are right”

Daga haka jan hannunta yayi suka nufi gurin masu bada daki,biyan kudin yayi ya karbi key suka shige dakin.

Suna shiga dakin suka shige jikin juna,kowa na kokarin nunawa dan uwansa shi gwanine.

Sautin numfashinsu kawai kakeji yayinda suka isa kan gado.

Sosai zakara ya dirji kudinshi dan sun kwana biyu basu hadu ba.

Itako tuni bacci yay gaba da ita me nauyi bata farka ba seda garin Allah ya waye.

Koda ta tashi wanka tayi tai sallah,sannan ta tashi isa zakara dan ya sallameta zata wuce.

Koda ya farka,yaganta sabuwar shaawarta ce ta kamashi,duk yadda taso ya barta yaki seda ya sake kauda bukatarshi.

Mikewa tayi ta maida kayanta,isa dubu talatin ya bata.

Wanda sosai taji dadin su.

Sallama tai masa ta dauki jakarta ta fice ta nufi gida.

Tana isa unguwarsu yara suka fara mata ihun karuwa,itako ko ajikinta,haka ta dunga wuce mutane sanye cikin shigar diban albarka.

Sultan dake cikin gida yana mata wanki,jiyo hayaniyar yaran dayaji ne yabashi tabbacin mahaifiyatshi ce ta dawo.

Jikinshi ne yayi sanyi,sanda ta shigo gidan batare da zani da hijab din daya bata ba.

Wasu hawaye ne masu zafi suka fara biyo fuskarshi.

Dakyar ya iya yima ta sannu da zuwa.

Amsawa tayi cikin walwala,tace. “Sultan ka ganni se yanzu ko wlh wani sabon kamu nayi shine na tsaya tare dashi kayi hkr kai yarona,Allah yayi maka albarka”

Shuru yayi yakasa bata amsa,yana kallo ta shige dakinta baa jimaba yafara jiyo karar ruwa alamun wanka takeyi,

Rasa abunyi yayi dan haka kawai rushewa yayi da kuka,

Muje zuwa.

.surbajo for life.
*DAN KARUWA*
Kwarton Anti Hausa Novel

*Writen by zahra surbajo*

*Page 3*

 

Seda yayi kuka me isarshi sannan ya mike jiki ba kwari ya shiga cikin dakin nata.

Kamar kullum kayan data cire suna zube akan kujera a falon.

Kwaso kayan yayi,yauma har da pant da bra din data cire duk ta ajiye masa ya wanke.

Yana fitowa ya fara wankesu,batare da kyamar komai ba,duk da cewa pant din kallo daya mutum ze masa yasan me aka aykata dashi,hakan be hanashi wankewa ba.

Tsaf ya wankesu ya shanya mata a igiya,sannan ya wuce dakinshi yayi wanka ya kimtsa,ya fito ya nufi dakin mummyn tashi.

Sallama yayi ta amsa sannan ya shiga,.. Tana zaune kan kujera,tana latsa waya,gefe daya kuma tana zukar shisha tana fesar da hayakin.

Dagowa tayi tana kallonshi fuskarta dauke da murmushi tace.

“Yarona dan albarka,Allah ya tsaremin kai yabaka mace ta gari yarona,”

Murmushi yayi na karfin hali yace.

“Amin mummy”

“Se ina kuma zaka danaga kayi kwalliya?”mummy ta tambaya.

Cike da ladabi da biyayya yacs.

“Zanje cikin kasuwane indan samu ayki ko na dako ne insamu insami kudin abinci,sannan inason intara kudin makaranta na kinga na samu admission dole indage”

Murmushi tayi ta shafa kanshi,sannan ta zuge jakarta ta zaro wasu kudade masu yawa,tace tana mika masa.

“Yarona dan albarka kenan,ka kwantar da hankalinka Allah ya baka uwa jaruma,dan haka bakai ba kuka,ga kudin makarantarka nan na tanajesu,gasu ka ajiye agurinka”

Wasu hawayene masu zafi suka zubo masa yasa hannu yashare yace bakinshi na rawa.

“Kuka kuma na nawa mummy,ay kullum cikin sani kuka kike,mummy inason ki ayadda kike,ina alfahari da zamanki mahaifiyata, mummy bana danasani gameda haka,amman bazan yafewa kaina ba in na amshi kudin da mahaifiyata ta fita yawo ta zubarmin da mutunci da nata da sunan kasuwanci ba,mummy ki daure ki rufamin asiri,kidena gurbatamin rayuwata data zuriaar da zan samar agaba,nifa danki ne mummy me alfahari dake amatsayin uwa,kiyi hakuri ki fadamin nawa kike samu aduk fita idan kinyi,namiki alkawarin ayki tukuru in kawomiki kudin”

Tasss ta daukeshi da mari,ta fara mgn tana hawaye.

“Sultan ni kake cewa ina yawo,inma yawon nake anfada maka jin dadi nakeyi nima in inayi,kasan balain da nakeji idan banyiba,koma me nakeyi Ay dan kai nakeyi,akan me kullum zakasani agaba kanamin fada kaine ka haifeni konice na haifeka,kasan wahal danasha dan ganin kazama mutum kasani nace?”ta karasa maganar cikin matsanancin kuka,

Kan kujera ta fada ta rushe da kuka me tsuma zuciya,da ganin kukan kasan an fama mata tsohon ciwone.

Sultan gigicewa yayi yama rasa abinda zeyi,kifa kanshi yayi kan cinyarta yana kuka yana fadin.

“Mummy kiyi hkr don Allah kar fushin Allah ya kamani,kukanki masiface agareni,kigafartamin mummy kiyi hakuri nadena bata miki rai kiyi shuru”

Rungumoshi jikinta tayi gaba daya rana cigaba da kukan,yana share mata hawaye.

Cikin kukan take fadin.

“Sultan kaine kawai gatana se Allah,bani da kowa da komai sekai,wannan sanaa da nakeyi sultan har cikin raina banaso,narasa taya zan dena wlh ba dadin yi nakeba kawai masiface don Allah kar hakan yasa watarana kaima kace zaka gujeni,in ka gujeni munin abinda zan aykata seyafi wannan da nakeyi”

Rufe mata baki yayi yace.

“Mummy bazan gujeki ba,har abada inasonki,mummy zan miki addua Allah zesa kidena mummy na kidena kuka”

Haka yay ta rarrashinta,dakyar tai shuru,suka fara hira dan ya sake kwantar mata da hankali.

Duk yadda taso ya amshi kudin yaki amsa dole ta hakura ta kyaleshi.

Kitchen yashiga ya dafa mata abinci me dadi dan tuni ya jima da kwarewa gurin girki.

Yana gamawa ya zubo mata yazo yazauna ya dunga bata abaki tanaci tana sa masa albarka har ta koshi ya kwashe kwanukan yakai kitchen.

Yazo yay mata sallama ze fita,dakatar dashi tayi,tasowa tayi ta karaso kusa dashi tace tana murmushi.

“Sultan ko abincina bakaci duk abinda na siya da kudina bakaci,base kamin bayani ba nasan kana gudun cin haramunne,”

Murmushi yayi ya dukar dakai kasa.

Dubu biyar ta mika masa tace.

“Ka amshi wainnan kudin,wlh tlh blh ba ta haramtacciyar hanya nasamesu ba,na halak ne,kai amfani dasu koda gurin jari ne kafara seda wani abun kaji dan albarkan dana”

Murmushi yayi yasa hannu biyu ya amsa dan yasan mahaifiyarshi karuwace de amman tana sawun gaba gurin mutane masu gaskiya.

Godiya yay mata yasa kai ya fice ta bishi da adduar samun nasara.

Kasuwa ya wuce,inda yasai abinci yaci sannan,ya shiga bangaren yan saida turare,ya saro su kala kala,

Muje zuwa

 

Add Comment

Click here to post a comment