Littafan Hausa Novels

Kukan so Hausa novel Complete

Kukan so Hausa novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

Kukan so Hausa novel Complete

NA
MUH’MD ABBA GANA✍🏻
&
BILKISA IBRAHIM {Bily}✍🏻
(Mrs Abdus’salam)

Assalamu alaikum yaku ‘yan uwa, muna farin cikin kasancewa daku a wannan d’an littafi namu, ALLAH yabar k’auna.
Idan kin karanta ko ka karanta wannan littafi namu kaga abinda yay kama da rayuwarka, ba haushi zakujiba bakuma marubutan littafin zaku zagaba, A’a, kamata yayi ku bibiyi littafin domin magance taku matsalar ko gyara taku rayuwar, fatanmu masu kuskure irin wannan su daina, masu sha’awar yi karsu fara, shiyyasa muka kira littafin da suna “KUKAN KURUCIYA, MAI HANKALI NE KAD’AI YAKE GANEWA, to ALLAH yaganar damu ayayinda b’ata ya riskemu.

Kukan so

Page 1⃣&2⃣

Tafiya take tana had’a hanya, kai da kaganta kasan ba,a hankalinta take ba, dan kariyar ALLAH ce kad’ai ke tareda ita a bisa titin, takalmanta rik’e ahannunta, gata dai k’yak’yk’yawar mace dirarriya kuma fuskarta tana nuna alamun hak’uri, wani ihu datayi yasa muka maida kallonmu gareta, tacika hannu dak’asa ta watsa jikinta, tasake kwala ihu saini Ameeda, d’iyar malam dauda da iya Abu, d’iya d’aya tilo agurin iyayenna, nice tafari nice auta, yarinya mai farin jinin tallah.

 

Kallo Daya Hausa Novel 2023 Sabon Littafi

Bansan sanda hawaye suka zubo bisa kumatunaba, takuma kaikaicewa ta rabga ihu, na girgiza kai dan tabani tausayi matuk’a.
Mai adaidaita sahu ta tare, cikin muryar ‘yan maye ta ce, “gidanmu zaka kaini.
Mai adaidaita ya yatsine fuska, toni nasan gidan kunne? kifad’i anguwar dazaki malama.
Tayi shiru🤔 alamar tunani, can tađ’ago tana kallonsa da rinannun idanunta, ta ce, “kaga namanta sunan anguwarmu amma muje zan dinga nuna maka hanya.
Mai adaidaita yaja dogon tsaki yana fad’in saboda nima makakkene irinki ko??, yaja adaidaitarsa yayi gaba.
Ta tuntsure da dariya tana nuna babur d’in tasa, kaga mahaukacin mutum, amfad’a maka dan ina a bige kwakwalwata bata aiki ne?, jiri ya jata kamar zata fad’i, tayi saurin dafe wata mota dake bayanta.
Indai tak’aice muku ta tsaida adaidaita kusan uku amma basu d’auketaba dan jin tamance sunan anguwarsu, da k’yar wani yad’auketa, tako ringa nuna masa hanya dalla dalla har kofan gida, ta zaro d’ari biyu acikin d’ankwalin ta tamik’a masa, yakarb’a yana fad’in toga canjin malama.
Ta juyo tana kallonsa dan harta fara tafiya, ta ce, ” sunana ba malamaba, kuma canji kaje nabar maka duka, tafad’a dad’an k’arfi.
Mai adaidaita ya jinjina kai yana godiya ya ce, “ya ALLAH yashiryeki kinji.
Muda muka biyosu abaya mukace amin ya RABBI.
Cikin gidan tashiga tana tangad’i, iya Abu dake a tsakar gida tana aiki tabita da kallo cikin bacin rai.
Ameeda tazube agabanta tana fad’in iya taimaka mini da abinci wallahi cikina kamar b’arayin duniya sunmin sata.
Iya abu ta balla mata harara ke tsinanniya kada ki bata min rai in abinci kikeso ki koma ki ciwo daga inda kika fito , idan kuma kinje kibar tunawa dani, inkuma bahakaba wlhy yanzu jikinki zaya gaya miki.
ameeda ta tuntsure da dariya harda bugun k’asa ta ce, “iya aii tsinannun nada yawa dankema tsinanniyarce, na tabbata kafin iyayenki su mutu saida suka tsitstsine miki albarka..
Kafin ta k’arasa iya abu tashiga jibgar ta tamkar ALLAH ya aikota, itako sai ihu take da kururuwa harda zagi, makwafta suna jinsu, babu wanda ya leko balle a shigo ceto, dan idan da sabo sun saba, babu wayewan gari dabaza’a daki ameeda ba, saidai idan bata kwana a gidanba, dan wata sa’in bata kwana agida,
duka sosai iya abu tayi mata, saida taga ko yatsun hannunta baya motsi sannan tabarta tana cigaba da kalaman tsinuwa da d’ebe albarka ga d’iyar tata.
Ahaka malam dauda yashigo yasamesu, azatonmu za’a samu rangwame daga garesa, amma saimukaji yana ambatar wannan shegiyar sai yanzu tadawo gida??.
iya abu dake cin rai ta huro hanci ta ce, “yanzu tadawo zatamin iskanci nazane shegiya.
Yayi dai dai,yasa k’afa ya shuri ameeda dake kwance A kasa matsiyaciya tashi kibawa mutane wuri, sai kaurin taba kikeyi asararriyan yarinya.
Na rintse ido nabud’e danjin irin munanan kalami da iyaye ke yima d’iyarsu, lallai dole ameeda ta lalace indai har haka iyayenta suke mata tun tana karama.

Itako ameeda tana kwance ko motsi batayiba bare ta amsa kalaman baban nata kota bi umarnin sa, ruwa ya d’ebo ya watsa mata, tabud’e idanunta dak’yar, ya ce, “bacewa nayi kitashi anan ba me kika tsaya kina kallona, ameeda ta mika masa hannu tana fad’in taimaka ka kaini d’aki baba wlhy duk jikina yayi tsami, waccan tsohuwar ta dakeni sosai, kafa yasa ya shureta da karfi yana zagi da tsine mata, ta maida hannunta tana fad’in bakaso natashi kenan, dan nikam bazan iya tashiba, duk cikin yanayin maganar bugaggu take maganar.
Banza sukai mata suka cigaba da harkokinsu, saida taji rana tafara dukanta taja jikinta da k’yar tashiga dakinta a kofar dakin ta kwanta abinta……………..✍🏻

Ku biyomu.

 

Hikayarmu!!!
💖Abba gana💖
&
💞Bily💞

Kukan so Hausa novel Complete
[2/10, 8:06 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 🐾KUKAN KURUCIYA…….🐾

 

NA
MUH’D ABBA GANA✍🏻
&
BILKISA IBRAHIM {Bily}
(Mrs Abdus’salam)

 

Page3⃣&4⃣

 

WACECE AMEEDA???.

Ameeda diyace ga malam Dauda, iya Abu itace mahaifiyarta, ita kad’ai Allah ya mallaka musu, sun dade suna neman haifuwa a kwana a tashi Allah ya albarkacesu da Ameeda, sun nuna mata so da kauna da ya wuce misali wanda hakan ya jawo ta tashi a sangarce, tayi karatu har zuwa secondary kuma tanada kokari, ta samu tarbiyya dai dai gwargwado a wajen iyayen nata.
Ameeda tun tana ‘yar karama take talla, saboda tsantsan son kudi irin na mahaifiyarta tun mahaifinta malam dauda baya jin dadin tallar da ake d’oramata har ya zamana baya iya cewa komai dan iya abu ta mallakeshi sai abinda tace.
AMEEDA k’yak’yk’yawace sosai, ga dogon hanci, tanada hak’uri sosai, dakuma tsoro.
Duk da gatan da iyayenta suke mata wannan baihana mahaifiyarta duka da aibanta d’iyar ta taba, abu kadan ameeda zatayi sai mahaifiyarta ta hauta da duka da zagi, balle taje bata sayar mata da kayan sana’ar taba, aii ranar ta banu.
K’yawun ameeda yasa takasance mai farin jini awajen samari, talakawa damasu kud’i, idan kaga motoci na layi a k’ofar gidansu saika d’auka wani taro akeyi, duk wanda yazo kuma dole taje balle idan yanada mota, inko tak’i zuwa mahaifiyarta tafara tsinemata kenan dayi mata gori, wai babanta talaka itama taje ta auri talaka, saisu dawwama a talauci.
Wannan maganganu suna k’ona zuciyar ameeda, amma babu yanda zatayi tunda mahaifiyarta ce.

Akwana a tashi wani saurayi mai suna Naseer yashigo rayuwar ameeda, Naseer d’an mai kud’ine sosai, gashi shima an sangartashi, dan shikadaine awajen iyayensa, kwata-kwata bashida tarbiyya ko kad’an, ya kware a fagen shaye-shaye da neman mata, tunda ya k’yalla ido akan Ameeda yaji yana buk’atar yayi tarayya da ita, amma saidai ameeda tak’i bashi had’in kai, yaja ra’ayinta da kud’i, amma ta bijirewa buk’atarsa.
wani abokinsa Badaru shiyya bashi shawarar yakama k’afa da mahaifiyarta mana, yasan dole tasa ta kulashi , yakoji dad’in wannan shawarar tasa, dan haka sukayi shiga ta mutunci sukaje har gidansu ameeda, yanemi izinin zuwa wajenta zance, dafarko mahaifiyarta tak’i amincewa, dan ta ce, “baza’a kashewa d’iyarta kasuwaba tana tashenta, amma da Naseer ya ajiye mata d’aurin kud’i saita amince da sauri, harda alk’awarin mallaka masa ameeda.
Tun daga nan Naseer yasamu damar zuwa wajen Ameeda, saidai tak’i bashi hadin kai, ganin wannan yasa yafara zuba mata benelyn acikin lemo, tun bata sha harta fara saboda tana ganin nan gaba shi zai kasance mijinta,
Ahankali lemon dayake kawomata yafara tasiri a rayuwarta, har takanji idan bata shaba bata jin dad’i.
Da Naseer ya kula tazo hannu, saiya koma kawo mata zallar benelyn, da sauran kayan saka maye, akwana atashi harta fishi kwarewa wajen iya shaye-shaye, ya kuma koya mata zuwa club, takanje ta kwana acan, ba tare da wani fargaba ba, Ameeda tayi suna a club saboda iya rawa, da d’ibar kayan maye, idan tana rawa dolene abata fili a club.
Saidai abin sha’awa ga rayuwar ameeda, duk iskancin nata bata tab’a aikata zina ba, babu lallab’ar da Naseer bai mataba amma tak’i, bayanshi wasu dayawa su kan sha kawo mata hari amma tak’i, duk buguwar datayi baka isa kaja ra’ayin taba, bare kace zaka nuna mata k’arfi.
Wasu samarin kuma suna tsoron Naseer ne saboda zarransa, yanzu Ameeda tazama cikakkiyar ‘yar maye.
Gashi iyayen nata sun tsaneta, suna kuma tofin ala tsine da k’addarar rayuwar data da baibaye d’iyar tasu.

Yauma kamar yanda ta saba ta tashi tayi wankanta, tad’au kwalliya cikin wando da riga na fakistan, tayi matukar kyau, tafito tana goge takalmi, iya abu tafito daga kicin hannunta rikeda kwarya da gari, Ameeda ta ce, “iya yau babu abincine??.
Iya abu ta watsa mata harara, tana fad’in tunda kin bani kud’in yi abinci basai ki danne ni ki kwataba.
Ameeda tayi murmushi tareda jawo jakkarta, tazaro ‘yan dubu dubu guda biyar ta mik”a mata, ga wannan kuyi cefane kafin nadawo.
Jikin iya abu na rawa takarb’a tana washe baki, yauwa ‘yar albarka, idan kina bada irin wannan mai zai sa muringa fada, kedai ALLAH yabaki miji nagari mai kud’i da mota.
Ameeda tayi murmushi domin jin furucin mahaifiyar nata, tana mamakin kwadayi irin na mahaifiyarta, itadai indai kanada kud’i to komai mugun halinka zata zauna dakai, ahankali ta furta ya ALLAH ka shirye iyayena, kakawo mini canjin rayuwa mai albarka…….

Ku biyomu.

 

©2017

Kukan so Hausa novel Complete

Hikayarmu!!!.
💖Abba gana💖
&
💞Bily💞
[2/10, 8:09 PM] 💖Äbbå-Gãñâ💖: 🐾KUKAN KURUCIYA……….🐾

 

 

NA
MUH’MD ABBA GANA✍🏻
&
BILKISA IBRAHIM {Bily}✍🏻
(Mrs Abdus’salam)

 

Page5⃣&6⃣

 

AMEEDA tamik’e tana fad’in iya bari naje saina dawo, iya tajuyo tana kallonta ta ce, “to Yau kuma sai ina??.
AMEEDA tad’an gyara tsayuwarta ta ce, “iya zanje wajen falmata ne, amma zuwa yamma zan dawo, zanbawa hashimu sako yakawo muku yanzu idan nafita.
Iya ta washe baki tana fad’in to madallah, Ameedan baba, amma dan ALLAH yau kar a dawo a buge d’innan.
Ameeda ta fice tana fad’in to inna, a zaure ta tsaya tana share hawaye, da alamun tana cikin damuwa, tad’an dad’e tana zubar da hawaye, daga baya tagyara fuskarta sannan ta fice.
Gidan wata k’awarta taje falmata, itama dai falmata irinta ce, dan a club suka had’u, saidai falmata tana zaman kantane, wannan halinne ya banbantata da Ameeda, a hankali suka shaku har suka zama k’awaye mafi kusanci.

sallama tayi ta shige ciki, Suka rungume juna cikin farin ciki, falmata tace kai Ameeda wlhy yau kinyi k’yau, ga idanunki yau dai-dai suke.
Ameeda tayi dariya ta ajiye jakar ta a saman kujere, ta warware gyalen data nad’e akanta shima ta ajiye, ta kwanta.
Falmata ta ce, “badai barciba Ameeda??, Ameeda tad’an yatsine fuska, ta ce, “barci tsiya nakeji, ga yunwa ya takurani yakamata abani abinci.
Falmata ta ce, “to mizakici? Asiyo miki, kinsandai ni ba girki nakeyiba.
Ameeda ta harari falmata tana fad’in ai ba abin kirki kikayiba.
Falmata tayi dariya kawai, dan kullum Ameeda tana bata shawara akan tadage ta iya girki, saboda wataran dole subar shashancin nan suyi aure.
Babu dad’ewa aka kawo musu abinci, suka zauna sukaci suka k’oshi, Ameeda ta kalli falmata ta ce, “wai babu komai yau agidan ne??.
Falmata ta harareta, dan tasan kayan maye take nufi, ta ce, “plz Ameeda karki sha komai, ke wai bakya zama sai abuge, yakamata yau d ki dan huta, gashima zanyi bak’i daga abuja, shi yasama na ce, “kizo da wuri, danki tayani gyaran gida.
Ameeda ta ce, kice dai kawai kin maidani ‘yar aiki, amma wane irin bak’ine maza ko mata, idan mazane kema kinsan bazan zau…….
Falmata tayi saurin katseta sannu ustaziya, nibansan randa zaki wayeba Ameeda, kishigo harka sosai dan ki wuce wajen, kifita daga tarkon talauci, ki fidda iyayenki.
Ameeda ta had’e fuska tareda d’agawa falmata hannu, “kinsan nasha gargadinki akan wannan maganar, wallahi dana tara dukiya da kudin banza gwara na mutu acikin talauci, tamik’e a fusace taja gyalenta da jakka.
Da sauri falmata ta tareta tana bata hak’uri, akan bazata sakeba, dak’yar tashawo kan Ameeda ta hak’ura ta zauna.
Ameeda taje ma’ajiyar kayan mayensu takwaso kwalabe uku tadawo tazauna, dan sune kad’ai zasu gusar mata da b’acin ran da falmata tasakata, ta tsani kace mata tayi tarayya dana miji, haka tadinga korawa harsuka kare, tamik’e zata k’aro wasu, falmata tayi saurin tareta tana fad’in ya isa haka.
Ameeda ta ce, “d’aya kawai zan k’ara, falmata ta ce, “A’a, bazaki k’araba wlhy uku fa kika sha, nan dai falmata tayita lallab’ar ta, harta hak’ura tashige bedroom ta kwanta.
Falmata tabita da kallo tana girgiza kai, tana mamakin yanda Ameeda take caja kanta da kayan maye, amma bata yadda ta aikata wani fasikanci ba, zata iya cewa bata tab’a had’uwa da mutum irin Ameeda ba, dan sunsha yin fad’a akan hakan, koda yake tasan tunda Naseer ya gagara tursasa Ameeda dole kowama ya kasa.
Dan idan har Naseer yasaka ido a kan mace tofa dolene tashiga tarkonsa, amma Ameeda ta gagareshi, yayi dai nasarar koya mata shaye-shaye, da zuwa club, amma sauran bad’ala ya gagara.

WACECE FALMATA???

Falmata ‘yar asalin barno ce, ita cikakkiyar babarbariya ce.
Falmata yarinyar kirkice mai ilimi da addini, mahaifiyarta ta rasu wajen haihuwarta, daganan kakarta ta reneta tsawon shekara bakwai daga baya Allah ya karbi abunsa.
Bayan rasuwar kakarta sai aka dawo da ita gidan mahaifinta, daga nan falmata tashiga tsananin rayuwa, dan matar babanta tana gallaza mata, bata sonta ko kad’an, amma agaban mahaifinta ta kan nuna mata tsantsar so da tausayawa.
Wannan yasa mahaifinta yakasa fahimtar halin da falmata take ciki, gallazawar tayi yawa, dan har takai abinci yana gagarar ta agidan, wannan yayi matuk’ar tasiri wajen lalace warta, daga baya ta gudu zuwa garin kano, anan tahad’u da badaru abokin Naseer.
Shiya siya mata gida, yake mata komai data buk’ata kamar matarsa.

takaitaccen labarinta ..

Add Comment

Click here to post a comment