Saifuddeen Hausa Novel Complete
*SAIFUDDEEN*
_(Ba mutum ba ne)_
*Wattpad:JamilaUmar315*
*Mallakar:Janafty*
*Amnaf_sudanese _collection*
*Tana saida original laffaya kala daban daban daga Sudan kama daga na Amare da Kuma casual muna da available a Nigeria kuma Muna aikawa daga Sudan Zuwa Nigeria ko’ina a fadin Jahohi talatin da shida har ila yau dai akwai humra da turarrukka sadidan na matan aure daga Sudan,ba fa anan kada’i muka tsaya ba Muna saida kayan lalle akan sari da Rahusa da kuma siyan Daya,akwai mayuka da dilka da kayan gyaran jiki na ainahin ba Mix ba, wadan’da zasu fitar Miki da fatar ki tas ba bleaching fuskarki tayi haske tayi walwal kina kyalkyali and duk abunda kikeso a Sudan Muna kawo Miki shi har gda Nigeria Amnaf Sudanese collaction ba abunda bama saidawa kama daga kayan kamshin jiki na kaya da na fata +249923097401*
*🅿️8*
Conel.Salahudden Inuwa Lere Haifaffan garin Lere ne karamar Hukumar Jahar ta kaduna ya taso yaga kakkaninsu ma duka suna zaune acikin garin lere Sannan ayadda Labari yazo musu asalinsu suna Daga Cikin zuru”ar kabilun Fulanin Sanjaha da suka sauka agarin lere suka samu matsugunni suka zama wasu al”umma acikin garin..
Mahaifinsu Mallam Inuwa Lere Makiyayi ne sannan kuma Manomi ne Hajiya Suwaiba wato Iya kenan itace mai Dakinsa tun ta lalle sannan auran zumunci akayi musu awanchan Lokacin.
Deen House Hausa Novel Complete
Sun haifa ya”ya Goma da ita Guda shidda dukka wabi suke yi da an haifesu kwana daya zuwa Biyu suke komawa,Sai akan Salahudeen sannan ya’ya suka fara tsaya musu,Dagashi Sai Hashimu sai Hayatu,sai karamar su itace Mace Atika daga su kuma Iya ko batan wata bata karayi ba.
Suka Tattara hannu wajen rike ya”yansu da basu tarbiya daidai misali iya karfinsu Iya Tun awanchan Lokaci tafi Mallam Inuwa zafi da Fada shi mai Hakuri ne sannan mai Sanyin Hali ne sabanin ita datake da Zafi da Tsauri kan wasu al”amuran.
Kaf cikin su Salahudeen ne yayi karatun Boko mai zurfi Saboda Hazakarsa,Su kuma su Hashimu iyakarsu Sakandiri suka watsar duk da Lokacin ba”a wani Damu da ingancin Ilimin ba an fi maida hankali a neman na addini akan na zamanin.
Shima Salahudden saboda gidan su babban gida ne agarin na Lere duk wani abun cigaba da su ake farawa Tun kakansu wanda ya Haifi Mallam Inuwa ya rike wata sarauta a fadar Sarkin Lere to bayan rasuwarsa sai Sarautar ta bar gidansu kuma abu ne na Dakuna har Hudu shiyasa sai Mulkin ya barsu dayake suma basu Damu ba sai babu wanda ya ke nuna ma sun Hada jibi da Saurautar garin.
Salahudden kokarinsa da Hazakarsa ta kai sa matakin daya taka kafin ya bar Duniya mutun ne mai Himma da naci kan abunda yasa gaba bawai yana da Saurin Dauke abu bane akansa a”a tsabar nacin ne yake bashi Sa”a kan wasu abubuwan.
Zuwansa makarantar Sojoji ta Jaji ba don ran Iya ba sai dai Mallam Inuwa ya Dafamai shiyasa ya tafi,to kusan irin yanayin karatun awanchan Lokacin Sai mutum yafi shekara bai zo ganin gida ba a irin hakane har sai da Mallam Inuwa ya kwanta ciwo ya Rasu Salahudden bai sani ba sai da ya shafe shekaru biyu sannan yazo ganin gida ya iske mutuwa ta ma kwana Biyu har Iya ta fita Takaba an raba gado sauran yan”uwansa sun Dauki nasu shima aka nuna mai nasa ya gaji Shanaye da awakai sannan da manyan gonaki waannan zafin mutuwar yasa daya koma bai kara Dawowa Lere ba sai da akayi musu passing out Iya da Sauran yan”uwansa sukaje tayasa murna sannan suka Dawo gida Tare,Gadonsa Hashimu ya barmawa ya Hada da nasa yana kular mai da nasu Gonaki kuma yace suyu ta nomawa sai in ya tashi amfani da ita zai karba.
Watansa Biyu agida akayi posting dinsa a Maiduguri chan ya tafi ya fara aiki sai yayi wata shida bai zo gida ba ga Lokacin wayar hannu bata shigo ba sai Telephone ita kuma sai gidan gwamna ko sarki.
Haka Rayuwar ta cigaba da Tafiya Da dadi ba Dadi,yana chan Fafutar aiki aka Turasa gaba kwarewa kan Harkan aiki kana karami acikin Sojojin sannan kana kara gogewa Shekara daya sukayi kafin su gama su Dawo sai a ka kara sauyamai gari akayi Kudu dashi chan Ekiti to yanayin aikin nasu sai ya Dade bai zo gida ba akwai Lokacin da ya haura shekara Biyu har Iya ta fara Tunanin ko an kashesa ne sai gashi abun da ya tarar ya basa mamaki Hashimu har yayi aure bai sani ba to ta ina zai sani..?
Suna chan cikin Daji ba waya bakomai sai godiyar Allah kawai,To da irin wadandan jajircewan nasa yasa manya suka Fara sanin Salahudeen bazai taba mantawa ba da Taimakon wani Major dake jagorantar Team din su yaje yayi karatun Short Service dinsa Wata Ashirin ya fito da Rank din Second letuenet,Bazan ce Lokaci Daya ya samu Rank din Conel ba sai dai nace ya Jure gwagwarmaya ya shafe akallah Shekarun fin ashirin yana Bauta ma gidan Soja sannan anayi ana kara Girma har yakai matakin Conel.
Ya Hadu da Ummi Zaliha yana ma matsayinsa na Captain alokacin,Agarin Bungudu dake Jahar zamfara,lokacin da aka samu Fada da Rigima kan makiyayan mazauna garin da Manoma har rigiman tayi kamari aka fara fada da kashe kashe Dalilin dayasa gwamnatin Nageria ta Turi bataliyan Sojiji da kuma yan Sanda Domin bada Tsaro da Kuma tsawatarwa to awannan Lokacin ne Salahudeen yaga Ummi Suna daga cikin Fulanin da suka fito Daga Bungudun ganin Farko yaji ta shiga Ransa sai dai bai samu Furta mata abunda ke ransa ba,Da Hayaniyar ta Lafa sai suka koma to bayan tafiyarsu ba Dadewa Fadan ya kara barkewa wannan karon abun ba kyau har da kona gidaje da kuma rasa rayuka Dadama Rigimam datasa mazauna garin suka rika barin gidajensu suna yin kaura.
Cikin masu kauran harda Sunusi yayansu Ummi wanda ke shike Rike dasu tun bayan rasuwar iyayansu ita da Zuwaira itace Autansu,Dama Sunusi mai karamin karfi ne sannan kuma yayi sana”o”i kala kala saboda Rufin asirinsa da na kannensa dashi ya Tallafa musu sukayi karatu,yana Dillanci gidaje sannan yana Dillaanci Saida Shanu ammh anfi saninsa a matsayin mai Saida Awakai Farare da Jajaye,da Wannan sana”o”in yake rike da Matarsa sannan da kannensa,Dashi ya Biya Ummi kudin Makarantar koyon aikin Jinya na garin Tsafe sai sun samu Huta take zuwa gida..
Alokacin ya hadu da abokin arzikin Irin Bello da shawaransa da Taimakonsa suka koma garin Gaya da zama suka samu matsugguni.
Conel.Salahudden har Bungudu ya koma Neman Ummi da tambaya da kwatance aka fadamai sun tashi sun yi kaura Dakyar ya samu wanda yasan inda suka koma har Gaya yaje ya samu Sunusi kan mganar Yaga Ummi yana son auranta alokacin bata nan Tana makaranta Tsafe shi kuma Conel Salahudden Lokacin yana Cikin Zaria acikin barrak din basawa da zama ne ya Dawo kusa da gida Daman ga Iya ta matsa yayi aure Tun da Har Hayatu yayi aure Atika daman Tuni aka aurar da ita.
Gabadaya ya Susuce akan Ummi,wannan Dalilin ne da kuma binciken da Sunusin yayi ya Fahimci Conel nagari ne yasa yace ya bashi kanwarsa Zaliha ammh Tana makaranta sai ta dawo gida,haka ko akayi Ummi na Dawowa Yaya sunusi ya sameta da mganar batayi gaddama ba Tunda ganin yadda yayan ke fadi Tashi akansu ganin Farko da Ummi tayi ma Conel ta Aminta dashi suka fara soyayya cikin Aminci sai dai da yakai mganar Wajen Iya sai taki aminta da mganar tace auran gida zai yi kamar yadda Sauran yan”uwansa sukayi shi kuma yace nan Duniya in ba Ummi ba bazai aure kowa ba Ba Shawaran Iya ya samu Dangin Babansa da mganar su kuma suka mara bayamai batare da sanin Iya ba sukaje Gaya suka Nema mai auran Ummi kuma aka basu sai dai suka Dawo da mganan Tun wannan abun Iya ta Fara kiyayya da Ummi tana ganin Itace Silan da Salahudeen ya fara Gaddama da ita sannan uwa uba ga Hashimu agefe yana faman zugata shi da Atika shi Hayatu ba ruwansa Duk inda ta fadi sha ne a wajensa.
Auran wata Biyu aka sanya akayi aka gama,har aka Daura auran Aka kawo Ummi babban gidansu Conel aka mata Masauki Dakin Iya Domin kwana Hudu zasu yi mijinta ya Dauketa zuwa Zaria Lokacin Saura Wata Biyar ta gama karatunta.
Awannan kwanakin Ummi ta gasgata Iya bata kaunarta hankalinta ya tashi alokacin an samu shigowar Waya hannu ta wayar Conel ta ara ta Kira Yaya Sunusu ta labartamai Halin Datake Ciki shi ya wanko kafa yazo har Gaya ya duka gaban iya yana rokonta sannan ya gayamata Ummi basu da kowa uwa da uba duk basu sannan ba wasu cikakken Dangi shi ne nan uwa da ubansu tayi hakuri ta sanya ma wannan auran albarka,Iya saboda kwarjin ya sunusi da kuma Baiwar iya Sarrafa Harshe yasa ta aminta har ta saka ma auransu albarka Shi kuma wannan karamcin na Iya yake dubawa da har yau duk abunda take yi bata taba bashi Haushi ba.
Ummi ta fara zama abarikin Sojoji na Zaria a basawa,cikin Aminci ita da Mijinta mai sonta,sati Uku sukayi ya shiryata ya maidata makaranta,in ya samu Lokaci yana zuwa ya ganta suna Jarabawar gamawa,ta samu Cikinta na Fari Dakyar da Sodin goshi ta karisa Jarabawan,Daga Tsafe Gaya ta koma gidan Yaya Sunusi domin bata Fadama Conel ramar zasu gama Jarabawa tana ko zuwa gaya kamar Ciwo na Jira ta fara amai Da Zazzabi Har da su kwanciya asibiti,Achan ne aka Tabbatar tana da shigar Ciki Wata Uku murna wajen Conel baki yaki Rufuwa Saboda farimciki yasa da Ummi tace zata zauna agida bai Hanata ba sai da yaje Lere ya sanar da su Iya Atika ta zugata tace Ummi ta Dawo gaban Iya ta kula da ita aiko Ya na Dawowa Iya ta Murje ido tace ga yadda za”ayi bai da yarda zai yi Daya Fadama yaya sunusi bai nuna wata Damuwa ba sai ma Ummin ce ta Damu ganin haka yasa Matar Ya sunusu da suke kira Umma tace Su tafi Zuwaira Wacce tayi Candy tana Gida,Sai ya sunusi ya amince ammh bayan Conel ya tabbatar mai da ba matsala,Ko da Ummi ta koma gaban Iya da Renon Cikinta Iya batayi murna ba ganin harda Zuwaira tun awannan Lokacin Iya da Zuwaira basa Shiri Saboda Zuwaira tafi Ummi baki sannan tun tana budurwanta bata Cika Daukan Reni ba in Iya ta Fadi Daya ita zata maida mata ashirin ne sannan ko Atika in tazo gidan suna Gogawa da Iya ta gaji ne tace Conel ya Tattarasu ta gaji Cikin Ummi na Wata Biyar ta koma gidanta dake Zaria ita da Zuwaira tana tayata wasu ayyukan.
Haihuwar SAIFUDDEEN yazo da wani Budi da Tarin Alherai,ya kuma ga Soyayya da Kauna wajen iyayansa Sannan Hatta da Iya haihuwan Saifuddeen ya Saussauta kiyayyarta ga Ummi Gida gaya ta koma Umma ta mata wankan Jego duk da ba Haka Iya taso ba sai dai wannan karon har Lelenta bai goyi bayan Ummi tazo Lere tayi jego ba wato Hashimu.
Shiyasa tayi shuru da bakinta sai dai kafin sugama wanka Iya bata san adadim zuwanta gaya ba Saboda Saifuddeen da Conel ke matukar so Shiyasa ya sakamai irin sunansa Wato Saifudeen Salahudden kenan..
Ummi dai agaban mutane ta na ma Saif alkunya bata iya Daukansa sai in ba kowa saboda kunya sannan Tun Watarana da sukaje Lere yana kuka ta Rikesa tana jijjgasa tana kiran sunansa Iya ta mata tas tace bata da kunya tana ma yaron fari wasa har tana Kiran sunansa,Wannan shine mafarin da Ummi bata kiran sunan Saifuddeen sai dai YARO.
Mafarin zaman Zuwaira a Hannun su kenan Conel ya riketa ya sakata makaranta ita kuma Ummi jarabawarta ta fito kuma tayi kyau Conel yayi mata alkawarin nema mata aiki acikin asibitin barikinsu duk da ita ba Soja bace ammh ai matar Soja ce.
Saifuddeen na da wata goma sha Daya yana Tafiyarsa ko”ina Conel ya samu karin girma da Sauyin wajen aiki an maidasa barrak din Jaji chan suka koma ita kuma Zuwaira tana Kano chan tayi aure har ta fara karatunta a Sa”adatu Rimi collage kano.
Sun koma Jaji ba Dadewa Conel ya shiga ya fita Ummi ta fara aiki da asibitin Barrak din a matsayin ta na matar soja sannan kuma da albashinta mai tsoka duk Dalilin Jajircewan mijinta da har gobe bata Daina kukan mutuwarsa ba.
Wani karin baiwa ta Ubangiji Saifudden nada shekara uku a Duniya ta samu cikin Sadiya,Cikin bai bata Wahalan kamar na Yaro ba har cikinta na wata tara tana zuwa aikinta Ranar ma data haihu a wajen aikinta ne ta haihu achan sai dai aka Kira Conel aka fadamai Matarsa ta Haihu
A barkin Jaji aka sha sunan Halimatu Sadiya wannan karon sannan Iyami dake matsayin kakarsu ya sunusi ya Daukota Daga chan bungudu tana zaune dasu ita tazo ta zauna da Ummi har ta gama wankanta sannan ta koma Gaya alokacin Zuwaira sun samu Hutu tazo,Sai wahalan bata yi ma Ummi yawa ba,Saifudden nursing School din cikin Barikin ya Fara karatunsa,Sadiya ma data tasa sai aka sakata suna zuwa Tare alokacin har Ummi kuma na cigaba da kula da ya”yanta da mijinta da aikinta Tana kuma samun kwarewa alokacin ne Conel ya barta ta koma Makaranta ta Dora Hnd dinta akan Midwife,sai dai tun kafin ta fara Iya dataji Labari tace bata amince ba Taya ya zata tafi gantalin karatun ta bar ma yaranta da wa..?Ya sunusi shima Dayaji shima bai goyi baya ba Shiyasa sai Ummi ta Hakura ta Cigaba da aikinta kawai ba yadda Conel zai yi shima sai ya Hakura.
Saifuddeen nada shekara Shidda Sadiya kuma uku da wani abu Conel ya samu karin girma da mikaminsa na Conel alokacin Cikin Barrak din I Division na Kaduna suka koma da zama Sun bar Jaji,Lokacin Rayuwa tayi kyau sosai kudi da jin Dadi sun zauna Conel kusan duka shine Hidiman yan”uwansa har da na yan”uwan Ummi.Saboda da suka bar Jaji sai ta hakura da aikin ta zauna tana kula da ya”yanta da basu Tarbiya Mutuwa ita ta yanke wannan zaman jin dadin Conel ya Rasu Saifuddeen yana da shekara goma aduniya Sadiya kuma Bakwai,Sakamakon Hadarin Mota,Daga kaduna zuwa zaria sai gawansa aka kawo Ummi tayi kuka kamar ranta zai fita a Lere aka yi Jana”izarsa Sojoji suka rakasa makabarta Dakyar aka bari Iya ta gansa ita da Ummi sukamai addu”a Saif yasan babansa ya rasu alokacin Sadiya ce sai dai bim mutane da kallo Zuwaira tazo da D’anta Mujaheed wanda Tsakaninsa da Saifudden Shekara ne da wattani.
Tun bayan bakwai Ummi tasan tayi Rashi Domin zama na musamman iya ta shirya akan Ummi zata basu su Saifudden in Conel yayi Arba”in da Rasuwa da wannan bakincikin ta koma Gaya da zama tana Takabarta Ya sunusi da Umma na faman bata baki ganin yadda ta damu yasa yaje Lere da kansa ya roki Iya ta barma Ummi Sadiya sai su Dauki Saif ganin girmansa yasa ta amince haka kuwa akayi Tana fita Takaba Iya ta karbe Saifudden Sannan an raba gadon Conel,Hukunar Soja ta kasa ta kawo kudade masu yawa ga iyalan Mamacin sannan ga Gonakin conel da Shanayensa Daya gada su aka bar ma Sadiya da Saifudden kudi kuma aka Raba da Iya da Ummi sauran kuma nasu Sadiya ne da Saif.
Saifuddeem a garin Lere ya Rayu yayi kukan rabasa da Ummi da Adda Sadiyarsa kanwarsa abokiyarsa sai dai ba yadda zai yi Dole ya saki Jiki ko mutuwa zai yi, iya bazata barsa ya koma Gaya ba sai ya maida hankali a karatunsa inda ya tafi makarantar kwana dake kafachan Federal Science Tecnical Collage(FCTE) KAFANCHAN Ya cigaba da makarantarsa Dayake yana aji Biyar ne Conel ya rasu.
Saifudden tun fara karatunsa mai kwazo ne kuma gifted ne gasan duniya in makaranta zata saka shi zai ce sun sha zuwa Quiz da makarantu Saifudeen Salahudden lere ke daga musu martabansu tun a wadannan shekarun nasa malamai da Dalibai suka Shaida kokari da Hazakarsa uwa uba ga Uban naci irim na babansa Daya yi gado in ya Dukufa kan Littafi kamar Computer in ji Iya alfahari take dashi matuka tana kallonsa kamar Mahaifinsa sau dadama a wajen Iya Saifudeeen ya samu Labarin kuruciyar mahaifinsa da gwagwarmayansa Duk in da akayi hutu yana zuwa Gaya,wajen Ummi wacce ta koma tana Dora Hnd dinta a Tsafe inda tayi Diploma dinta,Sai ta samu Hutu take zuwa gida Sadiya kuma tana Tare da ya”yan Sunusu an saka ta makaranta Umma na kula da ita bata da wata damuwa.
Rayuwar ta gangara Ummi ta zo ta gama karatunta ta zama Cikakkiyar Midwife alokacin aiki baya wahala sai ta samu aiki a aaibitin dake garin Gaya Allah ya taimaketa ba”ayi nisa da ita ba ta fara aikinta cikin kwanciyar Hankali alokacin ne Manema suka mata cha ita kuma tace bazata kara aure ba Har Abada Tun Ya sunusi baya mgana har ya fara mata mganar aure domin yace tana da kuruciyarta bai dace ta zauna haka ba.
Ummi dai ta dinga Zillewa sai da Conel ya shekara bakwai a kasa sannan tayi aure shima saboda ya sunusi ne kada yace taki jin mganarsa wani Lauya ta aura dake aiki a Supreme Court na garin Abuja Shi Haifaffan Sulaja ne Banufe ne sai dai yana da Tarin Nagarta yazo gaida matar wani makocinsu da a ka kaahe mijinta to Matar yar gaya ce bincike ya kawosa yaga Ummi asibitin datake aiki yako makalemata ya taba aure matar ta rasu wajen Haihuwa ita da abunda ke Cikinta.
Lokacin da Labarin Auran Ummi yaje lere Iya kuka ta saka tana Fadin Ummi taci Amanar Salahudeen duka duka yaushe ya rasu har tayi aure.? Iri wadanan mganganun na Iya sun sakama Saifudeen jin Haushin Ummi Tunda Lokacin suna shiryen shiryen Zana jarabawar gama secondary School ne,har Ummi ta tare agidan mijinta Dake Abuja Saifuddeen bai je ba sai da ga baya da Mama zuwaira taje har lere ta samu Saif din sukayi mgana ya gayamata abunda Iya ta dinga Fadi ita ta lallashesa sannan ta Daukesa bada Izimin Iya ba sai Abuja yaje yaga Ummi da Addansa da Barrister yace ta Daukota zai riketa Cikin Amana sai Hankalin Saif ya kwanta nan Mama zuwaira ta barsu shi da Mujaheed ta koma kano zasu yi ma Ummi Hutu taji Dadi shi kanshi Barrister yaji Dadin haka zai kwashesu su fita parks park ya siya musu wannan ya siya musu wannan nan da nan suka saki Jiki dashi har gobe Saif na jinjina karamcin wannan bawan Allah.
Tare suka fara karatu da Mujaheed a Jami”ar Bayero Dake kano,ammh ba Course dinsu daya ba shi mujaheed shi Computer ya karanta yayinda Saifudeeen yake karantar B.A English Saboda Ra”ayinsa ne wannan tun fara karatunsu ana ma bai yi Laushi ba kaf Department dinsu ba wanda ya kama kafarsa a kokari da naci kan abunda ya sama gaba mujaheed ma na da kokari sai dai bai kai Saifuddeen ba,Lokacin da suka gama Degree dinsu na Farko Saifudden yaje yayi Jarabawar Scolarship,da Jahar kaduna ke tallafama matansa masu kokari irinsa kuma yaci yana gama Service dinsa aka turasa Standford University inda ya Hada Master dinsa akan B.A English again,kafin Tafiyarsa ne Ummi ta Haifa Zainab suna kiranta Laala sannan yana chan bai Dawo ba ta kara haihuwan zeeha Samina,Domin Daga Mastes dinsa gwannati ta basa Damar Hado Phd dinsa Akan Literature,Tsatsan Turanci kenan Allah sarki Yana chan yaji Rasuwar Baba Barisster ba ciwo ba komai Daga Dare zuwa Safe daman Ya samar ma Ummi aiki a asibitin gwannati dake Unity Hopital and maternity Dake garin na Abuja.Iyayansa masu karamci ne basu kwace su Laala ba,sai suka bar mata ganin ta fara aiki sannan tana da Rufin asiri sannan wajen rabon gado su Laala sun ci gidan data ke ciki yasa ya Sunusi yace tayi zamanta anan ta cigaba da aikinta.
Mama zuwaira ma babansu mujaheed ya rasu bayan ta kara haihuwan Saudat Sai ta barta chan hannun Wan babanta ita kuma ta dawo gidan ya Sunusi daya kara aure matansa biyu sannan yasamu rufin asiri sosai fiye da baya.
Mujaheed daman Saifudeen na Tafiya kasar Turai yayi joining din Airforce,Saifudden kuma sai da ya shafe wajen shekaru Takwas sannan ya Dawo alokacin yana da shekaru ashirin da tara aduniya ya iske Sadiya ta kusa gama karatunta a nile Universty a Abuja sannan mganar Soyayyar su da Mujaheed kowa ya sani Sannan su Laala duk sun girma har sun kusa gama primary dinsu.
Bayan dawowarsa bai zauna ba ya koma Hardvard University ya kara yin Kwas na wata goma akan Literature,Daya dawo ne yafara Koyarwa a Abu zaria a Deparment din B.A Englishi kamar yadda yafi kwarewa akan haka shi kuma Mujaheed har ya gama karatunsa anyi posting dinsa anan kaduna ana ma shirin auran su ne shi da Sadiya.
Gadonsa shi da Sadiya Su Baffa Hashimu suka damka musu Saifudeen yayi shawara da Ummi akan gudurinsa ita da kawu ko su Iya basu sani ba ya saida duka kaddaransa,ummi ta hadamai da kudadenta alokacin sannan ta saida gidan da suke ciki ya siya mata wani babba wanda yafi girma anguwan Apo dake Abuja,Na sadiya kuma Gonakinta suna chan lere tana bada Haya Shanayenta kuma sun zama garke.
Saifudeen ya Dade yana Tsari da Tunani kafin ya fara gudurinsa,ba karamin Wahala yasha ba,Sai dai duka kudinsa ya kare Allah ya taimakesa albashinsa na aiki Sannan kuma da al”amarin ya cushemai sai ya nemi Tallafin Sadiya take matsayin matar Mujaheed alokacin ta Saida gonakinta guda Biyu ta basa kudin ya hada dasu,bayan Ummi da kawu sai mujaheed ba wanda yasan gudarinsa bai kamallah aikin nasa ba sauyin Gwannati Gwamna Abdulhadi shitu ya zama sunansa amatsayin kwashinan ilimi wannan itace silar Daukakansa bai Rufe shekara ba ya gama Hada gudurinsa sai Lokacin su iya suka sani Domin sun hallaci walimar Bude wajen sannan bai samu matsala da Hukumar ilimi ba Tunda ai sune Hukumar alokacin.
Ganin wannan Daukakar ne yasa Iya ta hada sa aure da Amirar da ita ta rike ta adakinta,Aikuwa a washegarin Ranar da aka Daura aure ya Dankara mata Saki akayi ta rigima domin Har alokacin Iya bata Daina jin Haushin Ummi ba barin ma ga auran data kara sannan ga kuma mganar auran Sadiya da taso tayi hadin zumunci da yaron wajen Baffa Hayatu Sadiya tace Mujaheed take so sai ya kara Wutar kiyayyan ballatana da Saifudeen ya Girma yasan matsayin uwarsa.
Iya ta dinga zagin Ummi ita da goggo Atika kan ita ta zuga Saifuden yayi musu ewannan aikin ita kuma sai kuka Mama zuwaira ne ma ke kare mata Dayake ita ai sun santa Tuni.
Dakyar Ya Sunusi ya kashe mganar Sannan shima Saifuddeen din yama zuwa sai kaji mgana ta kwanta Har Amira ta sake aure shine kuma su iya suka sake shirya na Majeeda basu dandara ba.
Ummi azuwa lokacin Dadewarta aiki yasa ta kai matsayin Metron,Sannan tana jin dadin zamanta anan Abuja Inda su Laala ke makarantar Intetnationl Community School Abuja,Ita kuma Saudat tana chan kano Hutu ke kawota gaya ko Abuja Hamma Saifudeen kuma awata sau Daya yakan zo Abuja ya gansu ya koma kaduna inda yake aiki.
Akwai kyakyawan alaqa da abota mai karfi Tsaninsa da Sadiya kanwarsa yana sakin jiki yayi hira da ita bayan Ummi wacce indai su kadai ne zata saki jiki dashi in kuma taga idon mutane kunya take ji Saifudden tun yana jin haushin rashin kiran sunansa da Ummi batayi har gaji ya Daina ya cigaba da amsa sunan Yaro da riga ya saba dashi.
Lere ma yana zuwa ya Dubasu Lokaci bayan Lokaci sannan Alheri kan kamar mahaifinsa hatta da mutanen garin Lere sun shaida haka Chan Gaya ne dai bai cika zuwa ba sai dai suna waya da kawun sannan suna taba juna da Datti Babban yaron Kawu Sunusi.
Saifudden mutum ne Nagari mai kirki da sanin Darajan manya,Sannan yana da naci kan abunda ya sama gaba,Bai da hayaniya ammh kuma bai cika Miskili ba,Saifudden shi yafi kaunar karatu fiye da komai yana son karatu koma na wane bangare ne Dalilin haka ya jone da Unites States University(USU)San_Diegoi California Dayake suna karatunsu ta online yana son samun kwarewa kan harkan Na”ura sannan takardan Degrree garesa kan harkan siyasan cikin gida Saboda ai yana cikinta tsumdum Dole yan kwarewa akan hakan yafi maida Hankalinsa akan aikinsa baya neman mata baya shaye shaye,sai dai ba”a ce baya kallon matan ba yana kallonsu tunda Hulda na Hadasu ammh bai taba jin ya kalli mace yaji wani sauyi atare dashi ba tun yana ganin wasa ne har dai ya amince bashi da Lafiya har Bff yasha daukowa ya kallah ko zai ji wani abu bai taba jiba indai akan mace ne,Sannan mace ya tabbata ko Tsirara zatayi agabansa bazai ji komai ba ammh kuma abun mamaki yasha yin mafarkin yana Saduwa da mace har in ya tashi ya gansa cikin yanayin yin wanka,Saboda wannam matsalan har India yaje yaga Likitan Daya shafi wannan bangaran Dr Mathew,an yi mai gwaje gwaje an kuma Tabbatar mai da cewa komai lafiya ba inda yayi Rauni ajikinsa amatsayinsa na da namiji Jin haka yasa sai ya gasgata sai ya saka aransa in ya aurin mace dayake so komai zai Daidaita shiyasa bai yarda ya zauna da Amira ko Majeeda ba domin yana ganin zai cutar dasu Saifudeen yana da rauni ta bangaran addini matuka domin zaman a lere ba wanda ya kula da wannan bangaran karatun bokon ma shi ya jajirce. Sai dai shi mutum ne
Mai Tsantsane wajen sabama Allah,in dai yasan wannan abun in ya aikata Allah zai kamasa da Laifi to gwara ya sabama koma waye da ya sabama Allah,shiyasa batare da sanin kowa ba yake sakin su gwara ran su Iya ya baci da Allah ya kama sa da Laifin Danne musu hakki yasan dai baya sonsu kuma in ya zauna dasu zai kwaresu,Kuma aransa yake jin bazai iya zama da su ba in yace zai iya kuma sai yaci aransa kamar ana zare mai wani abu acikin jikinsa.
*Littafin Saifuddeen na kudi ne pay N500 via 0552179550 Jamila umar Gt bank,sai a turo evidence of payment ta wannan Lambar 09069067488 ko kuma katin waya na Mtn sai adauki Hoton katin a tura ta wannan Layin kai Tsaye 09069067488 mutanen mu na Niger kuma zasu tuntubi Kausar aglan Nissa ta wannan lambar domin karin bayani +22796562223 Ina maraba da masoya na a duk inda suke*
*Janafty*
Add Comment