Abinda Zuciyata ta zaba Hausa Novels
Abinda Zuciyata ta zaba Hausa Novels
_*ABIN DA ZUCIYATA*_
_{Ta Zab’a}_
*Littafi Na 1*
*BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
_*cнapтer 1️⃣*_
7:30 am. Unguwar, Angwan tivi, cikin garin lafia, dake jahar Nasawara a Nigeria.
Unguwace ta talakawa.
Wani gidane gini
D’an madedeci, na k’asa an masa kwaskwarima da siminti, wanda wani wajan ma bai samuba.
Yana da soron k’ofa, da d’akuna uku sai band’aki, da kitchen d’an k’arami.
Tin daga soron k’ofar kake jiyo magiyarta, cikin dadd’ar muryata.
Wata matashiyar budurwace, tsogunne k’ofar kitchen d’in wanda tarin kwanikane reras na masu siyan d’an wake da awaran safen da ake agidan.
Gefe d’aya kuma wani k’aton bokitin koko ne,wata matashiyar budurwa ‘yar kimanin 21 years, zaune gabansa, fara siririya, doguwa mai kyawun sura tana da dogon gashi da manyan idanu masu gazar² d’in gashi, idanunta masu lumshewa ne, masu kyawun gaske, tana da dimples tana da cikar k’irji dam suke Masha Allah, duk da siririya ce, amman tana da k’ira mai kyau, ga ta da dogon hanci, bakinta pink d’an k’arami.
Mijin Kwaila Hausa Novel Complete
Idanu ta zubama abokiyar tagwai takar tata, Samha, wacce sam basa kama se dai jini kasancewar Samha ba fara ba ce, kuma ba siririya ba, tayi tagumi, tana mamakin halayen Hussaina, yadda take magiyar abata kud’i bayan ita shegiyar k’iyuwa gareta, banda ci da son yawo ko bacci, ba abinda ta iya.
Kanta ta d’auke tana jiran masayanta, wanda anjima kad’an zasu b’ullo, ta siyar tai shirin tafiya makaranta, dan yau sai 10 suke da lecture.
Gefe guda dattijuwace fara kyakkyawa, wacce kana kallonta ba sai ance Najma jikarta bace tsabar kamar da suke.
Tana zaune ak’ofar d’akin k’arshe casbi ahannunta tana ja ta zubama Samha idanunta, tayi tagumi tana kallon yadda takewa Ayeeyah magiya.
Samha chocolate colour ce, doguwa tana da jiki ba sosai ba, komai nata dai-dai itane, Masha Allah akwai kyan sura da diri, batada idanuwa manya, ‘yan matsagaitane, amman sunada wata irin baiwa acikin su, masu d’aukar hankali duk wani d’a namiji.
Duk wanda ta kalla da golden eyes d’inta sai yaji wani iri ajikinsa. tanada hanci mai tsayi ga gashin ido da na gira gazar² masu kyau, labb’anta tsaka-tsakiya ne, ba k’anuna ba, ba manya ba, jajaye, masu shek’i, da taushi wanda ajikinta idanunta da labb’anta da bom-bom d’inta, ke mugun Jan hankalin manya² maza zuwa gareta.
Tana da k’irji amman ba manya bane, matasane tsayayyau masu laushi, batada gashin kai sosai iya na kitsawane, wanda iya k’eyarta jelar ke tsayawa, ‘yar kimanin shekaru 21 aduniya.
Sanye take da dinki riga da skirt na atamfa shud’iya, ta kame d’an yalulun gashinta iya, k’eyarta, da ribbon.
Hannayenta ta had’e tana sharb’ar hawaye, tana ci gaba da magiyar.
“Ayeeyah nabi Allah nabiki ki tattaro min dukkan jarin hannunki ki bani, tinda yau saura kwana 3 ki kai balas, kafin satin ya cika ki kai balas wlh zan mayar miki kud’inki, don Allah ki fitar dani kunya, yake mahaifiyata ki tuna auren Hannah aminiyata, ace banida anko ba kud’in kitso bare na k’unshi, ba kud’in d’inki. Haba! Abin kunyar ya yi yawa wlh, pls ki temakamin, koda sana’ar za ki daina ni dai aramin jarinki duka wlh zan mayar miki.”
Ta idar da mgnar tana hawaye.
Ayeeyah ta ce“Allah kana gani akullun Hussaina nake fara sakawa acikin addu’a adukkan sallar farilla na guda 5 ko nafilar da duk zanyi, akan ka shirya mana da ita, tashi ki bani waje wlh ko na zuba miki ruwan zafi ashegen kannan naki maras gashi, ko man suyar awaran nan, ke bakida kunya wlh, idan na baki kud’in da uwar me zanyi sana’ar da zakuci kusha?
Wallahi bazan baki ko sisi naba, bar had’ani da Allah.”
Surayya da Na’eem and Basira, k’annensu sunata lek’e suna dariya, sun rufe bakunansu sabida gudun kar taji ta jibga musu dukan wulak’anci.
Mik’ewa tai tana diddira k’afa ta nufi wajan yakumbo.
“Yakumbo kinga ta hanani rancen kud’in auren yau sauran kwana 7”
Yakumbo ta ce“Wallahi ba ruwana cikin rashin hankali, haba! Samha ke bakida hankali, wannan sakaran uban naki da zuciyarsa ta mace irin ki, idan ta biye masa duk mun mutu da yunwa.”
Taja tsaki ta shige d’akin tana fad’i“Ku kuma masu gulma wlh babu ruwana, maza kuje ta zuba muku abin karyawa kar lokacin shiga aji yayi.”
Idanuwa suka shiga rarrabawa, ganin Samha tana biye da Yakumbo d’akin, tana fad’in “Wallahi toh zanje na binciki inda zanje nayi koda aikin kwana biyune, ko a akamfanine na samu kud’in anko Allah bazan ji kunya ba, ba dai ni ku ka tsanaba? Ko Hassanata?” Najma ta ce“Don Allah Rabin raina kiyi hkr insha Allahu za ki siya.”
Ayeeyah tanata soye awaranta da jefe d’an wakenta. Yayin da Najma masu siyan kokon suka fara shigowa.
Aguje Samha ta fito daga d’akin ta warci buta, ta shiga band’aki.
Najma dariyarta ta danne dan tasan bai wuce cin muguntar da ta yima, alalar jiya da dare ba.
Kusan 10 minutes ta kwashe sai gata, tana matsalar k’walla tana zaro matsagaitan golden eyes d’inta, tana gwale k’afafunta tana nishi.
Kitchen d’in ta shiga tana turo baki, ta kwashi uwar awara da d’an wake ta kwalhi kokon duk basu tankata ba, ta zauna kusansu Surayya tanaci tana matsalar hawaye tana zabgawa duk yaron da ya shigo siyan abu harara. Yakumbo banda dariya babu abinda take, ab’oye.
Unguwar
*500 Housing Estate*
Wani tanfatsetsan gidane, na sarauta wanda akai masa kwaliya irin ta sarauta, mai masifar kyawu, wanda dukkansa da tambarin sarauta, akai fantin. Tin daga wajen gidan, zaka gane gidan sarauta ne, sabida irin tarin jama’ar da suke k’ofar gidan, tamkar ba safiya ba.
Can cikin gidan kuwa wanda aka k’awata shi da shuke² masu k’ayatarwa, fad’in tsaruwar gidan b’ata lokacine, masu karatu ki kisima tsaruwar gidan sarauta, wacce naira ta kwanta musu, suke tsakiya da jin dad’in mulki.
Akwai b’angarori da dama, acikin gidan. ko ina bayine maza da mata, birjik sunata kai komo sanye da uniform, blue da fari wanda ya haskaka su sosai. Gefen yamma Bangarorin bayi daban², suma tsarin gidajan nasu masha Allah.
Wata hanya mai masifar tsayi wacce zata kai ka, har fad’ar sarki, ta gefenta b’angaransa. sai ta biyunta zata kaiga b’angaran Fulani, da yaranta ta ukunta ‘bangaran Yarima Ashfaq, wanda shine babban d’an a masarautar, b’angaran nasa ya kasance duniyace guda ta jin dad’in duk macan da tai sa’ar mallakarsa.
‘Bangare na 4 shine na Hajjah Kilishi da yaranta.
Wata kyakkywar matace cikin hamshak’in bedroom d’inta, ‘yar kimanin shekaru 50 fara mai matsagaicin jiki.
Zaune take saman wata lallausan dadduma, casbi a hannunta, tin bayan sallar asubah take zaune, har ta gama azkhar, amman bata mik’e ba, addu’a takema d’anta Ashfaq akan Allah ya basa hkr da dangana, ya kuma kawo masa madadin Mufeeda, wacce zai sota fiye da Mufeedan.
Casbin ta ajiye ta d’aga hannayenta sama, tana addu’a, ta jima sosai kafin ta shafa addu’a ta mik’e, ta nad’e sallayan, cike da dattakunta ta fara magana,mai cike da izzar mulki“Ya Rabbi! Yaron nan sai nayi da gaske zai koma Abuja fa! Yau talata, shin anyi rayuwa ahakane? Ya tattaro yazo b’angarena ya tare, yau kam zai koma nasa b’angaran, ya barni da yarana, bazasu iya da wannan harare² ba.”
Ta k’arashe maganar tana bud’e k’ofar ta fice.
Kwance yake saman wani tamfatsetsan gado, wanda kallo d’aya za kama gadon kasan eh gidan sarauta ne. Rungume yake da wani k’aton pillow, wanda yake d’auke da zanen wata kyakkyawar matashiyar budurwa da bazata wuce 20 years ba, chocolate mai dogon gashi da manyan idanu, da dogon hanci, labb’anta masu kyau, tana murmushi aka zaneta, zanen ya fito sosai tamkar hotonta ne aka lik’a ajikin pillow’n.
Matashi kyakkywa mai cikakkiyar sura dogo ne ingarman namiji, k’akk’arfa mai cikar halitta, Masha Allah, duk inda ake neman namiji, mai cikar zati Mohammed, wanda ake kira da Ashfaq yakai.
Fari irin farin nan mai duhu kad’an. Kyakkyawane sosai mai dogon hanci da dara-daran idanu, farare lumsassu masu wani irin haske, yana da yalwatacciyar sumar kai tamkar balarabe, sajan da yake kewaye afuskarshi yay masa mugun kyau, haka d’an k’aramin gemunsa, sai k’asumbar da ta sha gyara wacce akowane lokaci Muhseen Waziri, yake cikin gyara masa baya yarda ya zauna busu² da ita.
Bakinsa d’an madedecine shi ba babba ba, shi ba d’an k’arami ba, pink colour mai taushi da shek’i.
Yana da gashin ido da na gira masu kyawu, ko ina jikinsa kwance yake luf-luf da gashi. D’an kimanin shekaru 33 aduniya.
Juyi yay ya sake k’ank’ame matashin yana motsa labb’ansa, dai-dai lokacin ne kuma….!
K’arfe 9:30 am, cif Najma ta fito cikin shirin tafiya makaranta.
Asoron k’ofa ta isko Samha tanata kai komo tana dunk’ule hannayenta, ayau so take ta samu mafita. Wani yaro ya shigo da sallama. Najma tana shirin ma Samha mgna ta amsa sallamar.
Yace“Wani mai motane yakema Samha mgna.”
Samha ta damk’o yaron ta kifa masa Mari, ta ce“Dan kutumar ubanka ka tab’a ganina ina zance? Ai wlh…”
Najma ta rufe mata baki ta tunk’ud’a yaron waja, ta ce“Jeka kace tana zuwa. Haba Samha wai ke wace irin mummunar d’abi’a gareki ne? Wace irin rayuwa kika saka kanki? wace irin ak’ida ce dake? Ai sai ki godewa Allah tinda ke akullun sai an samu wanda zaizo yace yana sonki amman ni fa? Kin tab’a ganin wanda yace yana sona? tafi don Allah kije kiji me ya kawosa, karki bari damammakinki su wuce ajiye k’udirinki na bakyajin komai akan maza, ni nasani zakiso wani lokacine bai ba. Je sako mayafi ki fita.” Samha tace “Toh”
Ta shige sbd sosai take respect d’in Najma tamkar ba rana d’aya ba sukazo duniya ba, amman ta amsane kawai.
Ganin ta koma cikin, Najma ta sauke ajiyar zuciya ta fice daga gidan. Bata kalli mai motar da yake tsaye jikin motar yana jiran Samha ba, ta sanya kai ta tafiyarta.
Dattijo ne fari kyakkyawa, kallo d’aya zaka masa kasan shine mahifinsu Samha, sbd akwai kama sosai, duk da Najma tafi kama da shi sbd farinsa ta d’auko, yayin da Samha ta d’auko bak’in Maimunatu mahaifiyarsu, sai tazama chocolate, batayi bak’i ba batai fari ba.
Isiyaku wanda bazai gaza shekaru 50 ba. Zaune cikin rumfarsa ta siyar da shayi, wanda kawai dai sunane sabida ba komai awajen banda shayin da ‘yan cups basu wuce 6 ba, sai biredi bai fi guda 3 ba, sai ledar indomie guda 5 sai k’wai basu wuci gida 10 ba.
Zama Isiyaku ya gyara, lokacin da idanunsa suka sauka akan. Asiya da Radiya ‘ya’yan Garba mai gadi.
Tab’o Bashir yay wanda yake shan shayi ya ce“Oh! Ni Isiyaku, Bashir duba don Allah kaga ‘ya’yan Garba mai gadi, Sam yaran ba tarbiya. Allah ya b’oyi muryata ance Asiyar mad’igo take mata ‘yan uwanta take bi, itako Radiya maza suke d’aukarta amota, bakaga yadda suke samo manyan kud’ad’eba, duk k’wan wajena da indomie su suke siyewa, bari kaga su k’araso duka zasu siye, Allah kyauta.”
Bashir ya kalleshi ya ce“Tabd’ijam! Isyaku wlh kaji tsoron Allah, ka kiyayi kanka ‘ya’ya fa gareka mata har guda 4 ka guji zagin d’an wani…..”
Sallamar yaran ta sanya Bashir yin shiru.
Amsawa sukayi suka gaishesu cikin girmamawa, Asiya ta ce“Baba Isiyaku abamu k’wai goma imdomi 4.”
Cikin rawan jiki ya had’o musu yana fad’in“Ina baban naku bai iso ba ko?”
Asiya ta ce“Yana gida.”
Ta biyasa kud’insa suka tafi.
Isiyaku ya bud’e baki zaiyi mgna Bashir ya mik’e yace“A’a ni ba daniba baya gareni bazaka janyomin masifa ba, ka zagi d’an uwani azagi nakane.”
Ya sanya kansa ya wuce.
Dariya Isiyaku yay yana k’are waro idanunsa ganin Najma ta tsayar da me napep ta shigo ta iso wajansa, ta sauko ta duk’a ta gaishesa.
Ya had’e rai yace“Wlh Hassana ni tinda na zauna, anan ba wanda ya siyi komai sai Bashir shima bashi ya siya kije kin tambayoni bashi, k’annenki ma nera goma² na basu tinda su ba hkr garesu ba.”
Najma tai murmushi ta ce“Toh Abba Allah ya maka bud’i na alkahiri.”
Ta mik’e ta shiga napep suka tafi.
Isiyaku ya ce“Ina dalili komai ni zan bayar, ga uwarku can sai kud’i take samu sama da dubu 5 ayini, amman sai na Baku kud’in zuwa makaranta, ban bayarwa, dan na haifeku ni wlh aure zan muku ko sadakane gwara na bayar daku, tinda bak’in jini ya muku yawa. Ko ince ya miki ma, tinda Hussaina shegiyar yarinyar nan korasu ne take, k’ila ita aljanune…”
Samha ce tsaye ak’ofar gidan nasu, ta yane kanta da mayafi iya kafad’a. Doguwar rigar atamfar tai mata kyau. ta kalli saurayin wanda yake washe baki ganin mutuniyar.
Fuska ta yamutsa tana takowa cikin tafiyarta mai Jan hankalin duk wani d’a namiji….
Idan kin shirya siya kimin magana ta nan +22796515805
[30/12/2022, 11:14 am] +218 92-3756690: *BISMILLAHIR RAHAMANIR RAHIM*
_*cнapтer 2️⃣*_
Wani irin kallo take binsa da shi, har ya iso kusanta. Bak’i ne mai matsagaicin tsayi, kyakkyawa ba laifi, farar shadda ce ajikinsa, d’inkin ya zauna masa sosai ajikinsa, da ganin shi ba laifi an fara tara naira.
Bakinsa d’auke da sallama, ya iso kusanta yaja ya tsaya.
Kanta ta d’auke tana amsa sallamar.
Usman yace“Ranki shi dad’e pls kimin iso soron k’ofar taku mana, akwai magana abakina.”
Samha ta gyara tsayuwarta ta ce“A’a Malam, nan d’in ma yanisa shin wa yake biyarmu bashi? Da ka bar maganar ka acikin ka, zai fi. Sannan don Allah karka b’ata bakin wajane sbd bazaka samu abinda kazo nema ba, wai shi so, kayi hkr.”
Usman yay murmushi yace“Sbd me Samha?”
Harara ta zabga masa ta ce“Sbd abinda zuciyata ta zab’a sirri na ne, banda ‘yar uwata ba wanda zan fad’awa, abu d’aya na sani, ban tab’a jin zanyi soyayya ba, duk da nasan dole zanyi aure ko dan raya sunnan mazonmu, amman sauran ba sai na fad’a maka ba, don Allah kayi hkr kaje, idan kuma kana son ‘yar uwata so ka gama min komai.”
Fuska ya had’e atake yace“Ni ke zuciyata takeso kuma zanyi ta bibiyarki har na sameki.”
Hannu ya saka cikin aljihunsa ya d’auko ‘yan d’aurin naira d’ari bibiyu ya bek’a mata.
Tsaki taja tace“Bana buk’ata, kaga dai har rance zan shiga nema amman wlh bazan amshi kud’in ka ba, kaje Ngd. ”
Ta shige ciki ta barsa atsaye.
Kai ya girgiza, yace“Ba zanyi fushi ba, har Allah yasa na dace, kuma insha Allah tinda kina nema sai nasan hanyar da nabi kika samu kud’in.”
Motarsa ya shiga ya tafiyarsa.
Samha ta shigo Yakumbo na zaune arumfa, yayin da Ayeeyah take k’irga kud’inta, tana ware na komi daban.
Jikinta ta zube, tana fad’in.
“Ayeeyah don Allah ki aramin kud’in siyan kayan bikin nan dubu ashirin duk sun isa fa!”
Duka ta kai mata had’i da fad’in.
“Wallahi bansan bakida hankali ba sai yau, kar kije wajan bikin, sakara kawai, kink’i karatun boko kink’i na addinin, sai iskanci agida, sai ci sai bacci da yawon tsiya, tashi ki ban waje.”
Samha ta mik’e ta nufi wajan Yakumbo ta rungumeta, tana fad’in.
“Kinji ana min gori?”
“Goro aka miki ni ba ruwana da ashattarki, wlh idan kika biya mahaifinki bone y’a gama cinki agarin lfy.”
Mik’ewa tai ta ce“Na tafi wajan Abba ya dafamin indomie.”
Ba wanda ya tankata ta fice.
*500 Housing Estate*
Mirginawar da yay, bakinsa na motsi ya k’ank’ame k’aton pillow’n, ya yi dai-daiz da shigowar Fulani.
Kai ta girgiza tana fad’in.
“Tau mafarkin Mufeeda ake ko?”
Zama tai saman makeken royal bed d’in, ta sanya hannunta ta shafi lallausan sumar kansa, ta fara k’ok’arin janye pillow’n da ya rungume.
Sake k’ank’ame pillow yay.
Da d’an k’arfi ta kirashi.
“Ashfaq! Tashi don Allah ka shirya ka wuce Abuja, yanzu zan saka ashiryama tafiya.”
Lumsassun fararan manyan idanunsa, ya fara bud’ewa ahankali yana yamutsa fuska, har ya bud’esu tar. Tsarki ya tabbata ga ubangiji mak’erin wannan halitta, duk inda ake neman hadd’and’an namiji mai kyau d’à cikar zati ta ko ina toh Ashfaq ya kai, komai nasa daban ne.
Kyawawan labb’ansa ya fara motsawa, alamar addu’a yake yi.
Kallon mahaifiyarsa yay, ya shagwab’e fuska can k’asa² yace“Please Momy sai sati mai zuwa…”
No! Yau nakeso ka tafi, tashi maza ka kaima mai martaba gaisuwa kuyi sallama.”
Ba yadda ya iya dole ya mik’e ya shiga bathroom.
Fulani ta mik’e domin zuwa ta kira ta bada umarnin ashiryama Yarima Ashfaq da Muhseen Waziri tafiya Abuja yanzu.
Cikin 40 minutes Ashfaq ya gama shirinsa, ya nufi sashensa.
Duk yadda zan fad’in had’uwar sashan Yarima Ashfaq abin ya wuce nan, masu karatu ki kisima da kanku.
Bayan an gama shirya masa duk abinda zai buk’ata na tafiya, ya na zaune atamfatsetsan falonsa yana shan tea dan bai cin komai da safe, sai irin wajan k’arfe 1 na rana.
Muhseen kallonsa kawai yake.
Yana d’ago kansa suka had’a idanu.
Fuska ya had’e yana ajiye cup d’in saman center table.
“Haba Ashfaq don girman Allah ka ajiye wannan damuwar taka gefe ka fuskanci rayuwar gabanka, Mufeeda ta mutu bazata tab’a dawowa ba, kasan da hakan, kuma idan kayi hkr Allah zai baka wata ka sota fiye da Mufeeda…”
Cikin izzarsa ta jinin mulki da yake yawo ajikinsa, jikinsa har tsuma yake ya katseshi ta wajan d’aga masa hannu yana fad’in.
“No! Wannan k’arya ne wlh, ba ahaifi macan ba, na kulle daga kan my life Queen.”
Yaja bakinsa ya tsuke.
Muhseen kai ya girgiza sbd yasan tabbas sai an sami kalar matar da Ashfaq zai so fiye da Mufeeda.
K’aran doorbell d’in k’ofar ne ya hana Muhseen Waziri magana, ya mik’e. Ljcin da ya bud’e,
Jakadiya ya gani tsaye.
Gaisheta yay, tace“A min izinin ganin Yarima mai jiran gado insha Allah.”
Muhseen ba tare da ya nemin izinin hakan wajan Ashfaq yace“An baki bismillah.”
“Godiya nake”
Jakadiya ta fad’a tana shigewa.
Ashfaq, na zaune yana kallon wani gefe wayace ahannunsa k’irar IPhone 13 pro, yana tura wani sak’o ta gmail tamkar bai jisu ba.
Jakadiya ta zube nesa da shi saman tamfatsetsan carpet d’in mai laushin gaske da yake malale ak’aton falon, wanda aka d’ora kilishi b’angaran wajan da Ashfaq yake zaune, hakan ba k’aramin kyau ya k’arama falon ba.
“Allah shi temaki Yarima Ashfaq mai jiran gado, Allah ya k’ara maka lafiya da hkr da rashin abar k’aunarka da kayi, Mai martaba yake son ganinka yanzu², kafin ya shiga fada, afito lafiya jikan Mohammed Abdallah Sanda.”
Bai tanka taba har ta idar ta mik’e tana shirin ficewa ya ce“Jakadiya ina kwana? Ina tafe insha Allah, agaishesa.”
Murmushi tai d’abi’ar Ashfaq na burgeta, koda bazai cemata komai ba, zai gaisheta.
“Godiya nake Afito lafiya.”
Ta k’arashe maganar tana bin mek’akk’iyar hanyar zuwa fita falon.
Ashfaq ya mik’e ya nufi bedroom d’insa.
Tafiya yake mai cike da wata irin k’asaita, Masha Allah idan ka kalleshi sai ka sake kallonsa.
Bai jima ba ya fito cikin wata arniyar shiga ya d’ora alkyabba saman kayan nasa, sai wani fitinannan uban k’amshi yake zubawa. wani shegen takalmi wanda kallo d’aya zaka masa kace tabbas eh lallai takalman sarakaine.
Muhseen yay murmushi yana rik’e da wayoyin Ashfaq ya bud’e masa k’ofa suka fito.
Masutsaron b’angaransa suka fara zubewa suna sake bek’a gaisuwarsu. Hannu yake d’aga musu kawai.
Kai tsaye b’angaran Mai Martaban wanda yake mallakinsa suka nufa.
Kafin isowarsu Jakadiya ta sanar da Mai martaba Yarima Ashfaq na tafe yanzu.
Tin daga k’ofar farko ta sashan na sarki ko ina masu tsaron wajan ne, suma zubewa sukayi suna gaishe da Ashfaq, ana bud’e musu k’ofofin har suka iso k’ofar k’arshe, wacce nan suka tsaya neman izini kafin a basu.
Wani hamshak’in falone suka shigo wanda kyawunsa ya kere na Ashfaq.
Wasu narka-narkan kujerune na sarauta baje acikin falon wanda ya Sha ado irin na zamani aka sakaya da ta gargajiya, abin ba k’aramin kyau yay ba.
Wani kyakkyawan dattijo ne bak’i D’an kimanin shekaru 64 kallo d’aya zaka masa kasan shi d’in sarkine ko cikin sarakuna ma sai antona samun irinsa.
Da sallama suka shigo bayan sarki ya amsa musu suka zube dab shi inda yake zaune k’asa saman wani tattausna kilishi.
Atare suka gaishesa ya amsa fuska asake.
Muhseen ya mik’e yace“Afito lafiya.
Mai martaba yace“A’a Muhseen koma zauna, ka zama kaine shida.
Babana sau nawa nace ka sake fito da wata matar? Mufeeda Allah yayi ba matarka bace ta amsa kiran mahaliccinta, ran d’aura aurenku, yau tsawon shekara d’aya da wata 5, shi kenan sai kace bazaka sake aure ba? Ayau idan Allah ya d’auki raina kaine shugaban garin nan kai zaka gajeni, ko ba hakaba shekarunka 33 ba aure kanaso azageni agarin nan”
Ashfaq cikin kwantarwa da mahaifinsa hankali, yace“Allah shi temakeka yaja da tsawon ranka ayi hkr insha Allah zanyi yadda kakeso kwanan nan zan fito da mata ayi hkr.”
Mai martaba yace“Ok naji na baka sati biyu, na gaji da bani lokaci, wannan karo nq 3 kenan, wlh shine na k’arshe. Ashfaq wallahi idan sati 2 ya cika baka kawoba, zan zab’o ma cikin ‘ya’yan sarakai na aura maka”
Ashfaq wata irin fad’uwa gabansa yay yaji hankalinsa ya yi mummunan tashi, shine za’a ma auren dole?
Cikin tattaro jarumtarsa yace“Allah ya k’aramaka lafiya insha Allah ma hakan baza faru ba, za’a kawo kafin lokacin.”
Mai Martaba yace“Muhseen ka zama shida.”
Muhseen kansa ya rikice sati 2 kawai ace Ashfaq ya kawo Mata? Ahima jarumta ya aro yace“Eh Allah ya k’arama tsawon rai da lafiya zamu kawo insha Allah. ”
Mai Martaba yace“Toh kun temaki kanku Allah ya muku albarka.”
Su ka amsa da “Ameen”
Ashfaq ya masa bayani zai wuce Abuja, yanzu.
Sarki yay masa addu’ar sauka lafiya yace“Muhseen kaci gaba da kulawa da d’an uwanka wanda aka damk’ama amanar komai nasa, Allah ya kareku aduk inda kuke.”
Su ka sake amsawa da “Ameen.”
Suka fice.
Agaggauce Ashfaq yay sallama da Fulani da hajiya kilishi suka shiga narkekiyar motar Ashfaq wanda Muhseen ne yake driving suka nufi Abujan wanda ba wani nisa garetaba.
Samha tafe take ko ina jikinta motsawa yake, wanda kai kace da gan-gan take hakan, azahirin gaskiya kuma ba haka bane yanayin halittarta ne.
Su ukune zaune cikin rumfar shayin nasa, Shu’aibu Houdu sai Isiyakun.
Habiba d’iyar Tukur mai wanki, ita da Radiya d’iyar Garba mai gadi suka nufo wajan hannunsu sak’ale da juna suna magana suna murmushi.
Isiyaku yace“Shu’aibu Allah dai ya shiryemu kalli kayan da yake jikin Radiya har gwara na d’azu akan na yanzu, amman ance matan nan ‘yan mad’igo basuda wata kunya…”
Shu’aibu yace“Haba! Isiyaku wlh ka daina wannan halin, k’ilama muma haka kake zagin ‘ya’yanmu, shin wama yacema d’iyar Garba mai gadi tana wannan aikin banzan?”
Isiyaku yace“Kalli fa yadda ta mak’ale hannun d’iyar Tukur, amman fa kar Allah ya tasheni ranan shaida, ranan naji wasu sunzo cin indomie su na fad’in hakan.”
Houdu yace“Hamm kaci gaba Isiyaku duniyace ka zagi d’an wani azagi naka, ai kaima Hussaina zaginta ake acikin unguwa kun barta tana yawa da matsatsun kaya.”
Da sallama suka iso wajan, abinda ya sanya Shu’aibu k:arasa bayaninsa, yana amsa musu sallama.
Isiyaku ya waro idanu ya ce“Lah! Kace ana son sakamin yarinya abakin duniya?”
Radiya tace“Yauwa Baba Isiyaku dan Allah ka dafama Habiba indomie da k’wai anjima kad’an zan kawoma kud’in, yanzu wajan k’itso zanje.”
Isiyaku ya yace“Lah! Haba d’iyata ai karki damu daman saura d’aya kafin ajima na kawo bari adafa Mata.”
Radiya tai masa godiya suka zauna jiran ya dafa musu.
Samha Ce ta iso wajan bakinta d’auke da sallama.
Shu’aibu ya kallo Houdu suka sunne kai k’asa.
Samha tace“Uhmm Radiya kwana biyu shegiyar wai meye labarin kinyi wani fresh, sai kyalli kike?”
Ta k’arashe maganar tana zama kusansu ta kalli mahaifin Nata tana turo baki gaba tace“Abba ni adafamin indomie da k’wai, sai black tea, kaji.”
Isiyaku ya shiga rarraba idanu ganin kayan jikinta sun kamata sosai.
“Ke! Hussaina kinci ubanki tashi maza wuce gida idan na dafa zan aika miki shegiya uwa cin tsiya, yarinya kamar mai macijin ciki, yanzu kin rantse da Allah bakici komai d’azu da safe ba?”
K’afa ta fara bubbugawa tana k’wab’e fuska tace“Ni bancinba abinda gidan an tsaneni.”
Radiya tai dariya tace“Kai Samha bakya girma wallahi, sai shagwab’a.”
Isiyaku yace“Ki tashi ko na watsa miki ruwan zafi wlh shegiyar yarinya mai taurin kan tsiya.”
Samha tace“Allah ban zuwa ko ina sai an dafamin indomie.”
Houdu dariya taci k’arfinsa ya mik’e yabar wajan.
Shu’aibu yace“Yauwa d’iyar albarka gaskiya adafa miki indomie kam, Isiyaku bari naje na dawo.”
Isiyaku yace“Kaga d’iyar taku sai Iya shege ko?”
Kai ya jinjina yace“A’a banga komai ba ma ai.”
Yasa kai ya fice.
Radiya tace“Toh Baba tinda indomien d’ayace kuma Samha naso kawai dafa mata sai Habiba ta sha shayi da biredi.”
“Taci gidansu wlh baza taci ba.”
Samha tace“Ni nama fasa ban nera d’ari biyu toh. Radiya inason magana dake zo kiji.”
Ta Kama hannun Radiya.
Isiyaku yace“Hissaina kije gida nace tin banci mutuncin ki ba, bar wajan nan, bari zanzo gidan Maimuna zata raina kanta iskancin na daga wajanta kika gadoshi, bazanyi shiru na zuba idoba wlh.”
Samha tace“Radiya wlh yau sauran kwana 7 auren Hannah k’awata ban siyi anko ko d’ayaba cikin ukun da za’ayi inata neman rance na rasa.”
Radiya tace“Ai kece kin zab’arwa zuciyarki abinda ba zai tab’a yubawa bane, dole zakina zama cikin talauci, amman yanzu ki bari naje wajan kitso na dawo ban number wayarki sai na kiraki kizo gida zan samo miki hanyar da zaki samo dubu 20 ayau na tabbata idan kinyi duk abinda ya dace wlh kin huta.”
Samha ta rumgume Radiya tana fad’in “Wayyo dad’i amman wane irin aikine wannan ayau dubu 20? ai inajin Ayeeyah sai ta yankani?”
Radiya tace“Bari na dawo daga wajan kitso zamuyi maganar kinga Habiba ma can zan kaita.”
Samha tace“A’a ban aikin komai agida muje kawai, sai kimin bayani kafin agama kitson idan naji zan iya toh idan aikin yafi k’arfin shekaruna sai na hkr naci gaba da neman rance.”
Radiya tace“Ok ba damuwa muje d’in, amman kinsan bazan miki bayani cikin jama’a ba.”
Samha tace”Toh yanzu bari na zagaya mu had’u ak’ofar gidanku, sbd Abba kar ya kama zage² nan yace yawo zani.”
Samha ta dawo wajan mahaifin nata ta kafa rigima sai da ya had’a mata shayin yana tambayarta hira me sukayi da Radiya tace hira bikin Hannah k’awarta suke Shayin da biredi ya bata ya korata gida, ta amsa ta tafi gida, su Radiya ma suka amshi indomie d’in suka tafi.
Samha agaggauce ta shanye shayin da biredin, tana idarwa ta shirya cikin Abaya doguwa brown, irin mai bin jikin nan, mai sauk’in kud’ice amman tanada kyau, ga ta da adon duwatsu sosai, ta fesa turare tai sad’ab ta fice agidan.
Kai tsaye gidansu Radiya ta nufa dake ba nisa 5 minutes yakaita gidan.
Tana zuwa ba b’ata lokaci suka nufi gidan kitson.
Acikin keke napep d’in Samha ta addabi Radiya ta fad’a mata wane irin aikine wannan?
Radiya ta kamo tattausan hannu Samha tana murzawa ahankali tana wani lumshe idanunta, ahankali tace“Pls ki bari agama min kitso mana ai ni nace za ki samu, amman fa zan d’an baki wata shawara kafin muje ga wancan batun, idan bata miki ba, bass sai na miki wancan bayanin.”
Samha ta zare hannunta jin yadda take Mata tafiyar tsutsa aciki, ta ce“Nifa kinsan idan naso jin abu kamar d’a yaso fitowa daga cikin uwar nake, ni dai muje Ana miki kitso kina min bayani.”
“No! Samha ta ya zan miki irn wannan bayanin acikin jama’a? Kawai ki jira agama min.”
“Samha bata sake magana ba, har su ka iso k’ofar gidan Ablah mai kitso.
Radiya ta biya me napepe d’in su ka sanyo Kansu cikin gidan.
Tin daga nesa ake jiyo hayaniyar taron matan da suke bin layin kitso.
Daga nesa Ablah ta tsinkayo Samha, wacce take tafiya cike da nutsuwa, sassan jikinta na girgiza, tayi shewa tace“Shegiyar kasuwa cikar ki sai da marece. wani kayan sai amale jakai kutumar ubansa, kaga mace har mace shegiyar amman maza basa gabanta bare mata. Wai yau kitson akazo ba kira bare nasan da zuwan manya?”
Samha ta yamutsa fuska tana kallonta akaikaice tana sakin d’an guntun murmushi wanda siririyar wushiryata ta bayyana dimples d’inta suka lob’a, tana dab da isowa taron matan da suka zuba mata idanu kamar zasu cinyeta, duk da kuwa akwai gogagu awajan wanda suka fita wayewa.
Cikin zazzak’ar muryata tana karkad’a ‘yan matasan tsayayyun k’irjinta, wanda ko bra bata sakaba, hakan yasa suke juyawa sosai, kuma sam ba wai da niya tai ba, tana kallon Ablah ta fara magana da niyar tsokana, ganin saura k’iris ta gamama matar da akewa kitson, tace“Uhmm! Ai kuwa kowa ta matsa sai an gamamin kafin ayima kowa…” Samihat wacce itace akeyima kitson ta ce“Ai dole wallahi ko ni zan janye amiki sai ak’arasa min daga baya, sbd kin had’u ba k’arya dan Allah zakiyi k’awa dani……!?” kwab, taji an gwabji bakinta, an rufe mata bakin ruff Ana fad’in…..!
Idan kin shirya siya kimin magana ta nan +22796515805
[…] Abinda Zuciyata ta zaba Hausa Novels […]
[…] Abinda Zuciyata ta zaba Hausa Novels […]