Littafan Hausa Novels

Sabbin Hausa Novels Complete

Sabbin Hausa Novels Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Sabbin Hausa Novels Complete

FIKRA WRITER’S ASSOCIATION

 

AUREN SHEHU

✍🏾 Khadija Sidi

 

 

Kwance ya ke a rigingine kan ciyayi irin wannan ciyayin da ake kira “carpet grass” Hannayen sa biyu tallabe da ƙoƙon kansa, cikin nazari yake duban taurarin da ke jere reras suna sheƙi bisa sararin samaniya. Babban lambu ne mai ɗauke da ɓangare biyu, ɓangaren bishiyoyin ‘ya’yan itatuwa, bishiyar mangoro, gwaiba, yazawa (cashew) da dai sauran su, sai kuma ɓangaren da ke ɗauke da kujerun hutawa. In ka ɗauke kukan tsuntsaya babu sautin da ake ji kasancewar dare ya fara tsalawa, kusan ƙarfe biyu ne.

 

Sanye yake cikin rigar saƙa irin na fulani, kan sa ɗauke da rawanin da ya zaga har kewayen fuskar sa hakan ya sa fiye da rabin fuskar shi ɓuya. Kasancewar shi na daya daga cikin masu gadin daddare na gidan, kusan kullum ya kan kai biyu a nan cikin lambun, yayi kwanciyar sa ya na mai nazari, hakan ba ƙaramin nishaɗi ya ke saka shi ba.

Saduwar Aure Hausa Novels

Gefan sa ƙatuwar sanda ce wacce ake kira da gora, ta korar shanun sa ce duk da kuwa rabon shi da rugar su wacce ake kira “Rugar Shehu” ya kusa shekara.

 

Jin dirar mutum tare da haushin karnukan gidan lokaci ɗaya ya sanya shi yin zumbur ya tashi zauna ya na mai duban in da ya ke kyautata zaton mutum ne ya diro cikin gida. Jin shiru babu wani motsi sai na haushin karnuka ya sanya ya tashi tare da jan sandar gorar shi kai tsaye bakin bishiyar da ke kusa da katangar lambun ya nufa, idan ya ke kyautata zaton koma menene ya diro nan ne hanyar shi.

 

Tun dirowar ta take ƙoƙarin janye niƙabin ta da ya maƙale jikin reshen bishiyar da ya mata tsani. Ƙoƙari ta ke iya ƙarfinta don ta ga ta ciro amma ina, gashi ta san mutukar ba ta samu ta shige ciki ba lalle masu gadi za su kama ta yau, don kuwa haushin karnukan yau ya fi na kullum. Jin ta ku a bayan ta ya sanya ta juyawa da sauri, ganin ya ɗaga sanda ya na shirin runtsuma ma ta aka, ta runtse idanu ta na mai faɗin

 

“Wayyo ni Dady!!!!!”

 

Cak ya tsaya, hannun shi na rawa tsabar firgici na ganin kyawun halittar Allah, tabbas kyau dai babu irin wanda bai gani ba a Rugar su, amma sam bai taɓa ganin wacce ta firgita shi ba kamar wannan halittar da ke gaban sa.

 

Fuskar ta ya bi da kallo, wanda rashin niƙab ya ba shi wannan damar, domin kuwa jikin ta rufe ya ke da hijabi tun daga sama har ƙasa. Kamar yanda ya ke nazartar taurari haka ya tsinci kan sa cikin nishaɗi yayin da ya shiga nazari akan fuskar ta.

 

Baka ce, irin wannan bakin mai shek’i kamar jikin tarwaɗa. Tsayuwar hancin ta da ya zo dab da ƙaramin bakin ta ba ƙaramin ƙarawa doguwar fuskar ta kyau yayi ba……

 

Jin shiru ba ta ji saukar gora kan ta ba ya sanya ya ta buɗe manyan idanun ta, hakan ba ƙaramin sake rikita shi ta yi ba ganin fararen idanun ta bisa kan shi har sai da ya ɗan ja da baya ya na mai tasbihi ga ubangijin sa, domin ya tabbatar wannan halittar da ke gaban shi ba mutum ba ce.

 

Ta na mai duban shi cike da tsoro musammam ganin mutum mai faɗi da tsayin da tun da ta zo duniya ba ta taɓa ganin irin shi ba, daɗin daɗawa gashi yanayin shigar shiri irin na waɗannan mutanen da suka saka Nijeriya a gaba ko kuma Fulani masu garkuwa da mutane, wannan tunanin tare da jin taku da haushin karnukan da ya ƙaru, wanda hakan ya tabbatar ma ta masu gadin sun kusa shigowa lambun ya sa ta sakin niƙab din ta na mai ɗage hijabin ta yanda za ta sami damar sauri, ta yi amfani da damar gushewar tunanin mutumin da yayi kasake ya na duban ta, ta bi hanyar da zai sada ta da kitchen da sauri, hannu na rawa ta ke ƙoƙarin fidda ɗan mukulli da ta ɓoye cikin dan wando da ke sanye jikin ta.

 

Har tuntuɓe ta ke garin waige domin tabbatarwa ba ya biye da ita.

Allah ya taimake ta ƙofar ya buɗu, kasancewar ta sababbiya a harkar, cikin sanɗa da lalube ta ke tafiya domin wutan lantarkin kitchen din a kashe ya ke, sai dai hasken farin wata da yake ratsowa ta taga. Ba ta tsorata ba sai da ta jiyo muryar masu gadi daga cikin garden, ta na mai roƙon Allah ya sa ba asirin ta ba ne ke shirin tonuwa ba, ta bi ta falo ta shige ɗakin ta cikin rawar jiki. Dan tun da take fitar dare ba ta taɓa shiga tsaka mai wuya kamar na yau ba.

 

Hijabin jikin ta ta cire, ta na mai ajiyar zuciya ta zube bisa gadon ta.

Hasken da ya gauraye ɗakin sanadiyyar wutan lantarkin da aka kunna ya sanya ta yi zumbur ta tashi zaune a tsoro ce. Ganin wacce ke jingine jikin bango ya sanya ta fiddo ido tare da faɗin

 

“Wai ke Halitta ba za ki fita harka ta ba? Wannan masifar har ina haka?”

 

A hankali Halitta ke ƙare ma ta kallo, tun daga dan ƙaramin matsattsan wandan da ke jikin ta (bumshort) zuwa matsatsiyar jar riga wacce ta tsaya ma ta iya cibiya, ga kan nan ya sha kitson attachment da aka yi da gashin doki mai tsada da ake kira (Brazilian hair). Ta na mai girgiza kai ta furta

 

“Yakura…….”

 

“please Halitta, ba yanzu ba, na gaji da yawa!!”

 

Ta katse ta tana ɗaga mata hannu. Ganin an murɗa ƙofar ɗakin ya sanya ta saurin janyo bargo domin ɓoye shigar da ke jikin ta. Mahaifiyar su wacce su ke kira Ammy ce ta shigo, ta na hamma tsabagen baccin da ke idanun ta, ta ke duban su cike da damuwa ta ce

 

” dama na san dole kuma kun tashi, hayaniyar su Audu da haushin karnuku ne ya tada ku ko?”

 

“eh wallahi Ammy…..”

 

Su ka faɗa a tare wanda hakan ya sanya Halitta sakin baki cike da mamaki ta ke kallan yayar ta ta, ita kuwa ko aji kin ta ta ce

 

“na kasa gane menene matsalar su da za su na sakar mana karnuka su na mana hayaniya, ya kamata a hana su shiga garden ma kawai….”

 

“ke da ki ke ɗaki ya aka yi kika san garden su ke?”

 

Halitta ta na sane ta jefa mata wannan tambayar, domin kuwa duk wani rashin ji da ‘yar uwar ta ta ke yi babu wanda ba ta sani ba.

 

Jin haka ta san in da ta dosa dan haka sai ta yi burus tare da faɗin

 

“Ammy dan Allah daga ina hayaniyar nan ke tashi?”

 

“eh toh ni ma na fi tunanin garden din ne, ai Malam shi ma ya fita ya mu su magana….”

 

Ras! gaban ta ya faɗi

 

“Allah ka rufa min asiri ba dan hali na ba ba dan aiki na ba”

 

Adduar da ta shiga jerowa cikin ran ta kenan. Ita kuwa Halitta dariyar mugunta ta saki, sannan ta furta

 

“Allah ya sa Dady ya gano dalilin wannan hayaniyar ta su ya mana magani, ni dai sai da safen ku”

 

Ta na murmushin mugunta ta dubi yayar ta wacce ke watsa ma ta harara, ta ƙara da

 

“a juri kai zuga gabas wata rana ya zo da ruwa, ko ya ki ka ce Yakura”

 

“uhum”

 

Cewar ta dan tsoro ta kasa magana, gani ta ke burin Halitta ta biye ma ta su yi hayaniya dan ta sami damar tona mata asiri. Halitta na fita Ammy ta bi bayan ta na faɗin

 

“bari na bi bayan ki Halitta, babu mamaki Falmata na nan ɗakin ta tsoro ya hana ta motsawa”

 

Suna fita ta fidda wayar ta da ya dame ta ta da ƙugi, ganin wanda ke kiran ta ta ja tsaki, ɗagawa ta yi tare da karawa bisa kunnan ta, cikin nuna fushi ta ke magana

Sabbin Hausa Novels Complete

“Bobo wai menene? Na faɗa ma ka zuwa na club in dai na dawo hutu gidan nan abu ne mai hatsari, ka bari mu koma school ka ce ah ah, ga shi kai ba za ka iya bari mu dawo da asuba ba sobada jarabar bacci irin na ka, ai gashi yau saura kiris Dady ya kama ni!”

 

Shiru ta yi na wani ɗan lokaci ta na sauraran shi, kafin daga bisani ta kashe wayar ba tare da ta sake tankawa ba. Nan ta kwanta ta na jiran tsammani, jin shiru babu wanda ya dawo ta san asirin ta bai tonu ba tukunna, dan haka ta tashi, kai tsaye toilet ta nufa ta yi wanka tare da ɗauro alwala domin rama salloli uku da ke kan ta, la’asar, magariba da isha’i.

 

***

Allah yayi dare gari ya waye. Babban ɗaki ne irin na ƴaƴan manya, komai na ɗakin an yi masa ado da kala biyu, wato shuɗi da fari. Ba wani tarkace ba ne a ɗakin, face ƙatan gado na alfarma tare da setin madubi da dirowa.

 

Kamar kullum yau ma sai da rana ta take, bayan ladanin masallacin da ke cikin gidan su ya ƙira sallar azahar sannan ta iya motsawa, wayar ta ta jawo, ta shiga Instagram in da ta saka hotan da ta yi daren jiya a club. Nan da nan hotan ya sami karbuwa in da samari da wasu yan mata su ka shiga danna mata “like” tare da “comments” kamar yanda aka saba. Sai da ta gamsu sannan ta aje wayar ta tashi da kyar ta yi wanka tare da ɗauro alwala.

 

Maimakon da ta fito ta yi azama wajen rama sallolin da ake bin ta, wato Asuba da Azahar, sai ma tsayawa ta yi gaban madubi ɗaure da tawul da ya tsaya iya gwiwa, cikin jin daɗi da alfaharin baiwar dirin da Allah ya mata, da ke masha Allah ita kan ta ta san Allah ya mata mata dire. Hakan ya s koda yaushe ta na kan social media cikin saka hotunan ta wanda ta yi da matsattsun kaya, dan kuwa ta na cikin ɗaya daga cikin sannanun matan nan da ake kira “Slay Queen” a Instagram.

 

Sai da ta ɓata lokaci wajen shafe shafe da kwalliya, ta fito fes cikin ɗinkin atamfa riga da siket, sannan ta ɗauko hijabi wanda ya ke kai mata har ƙasa ta sanya. Murmushi ta ke ganin yanda ta fito saliha sak, ita da kan ta ta shiga yiwa kan ta kirari

 

“woo ni Zeee the slay mama, the club mama, kuma salihar Daddyn ta”

 

Nan ta gama juye juye gaban madubi, sannan ta shimfiɗi sallalaya aka shiga jera sallar asuba da azahar.

 

 

***

 

 

Malam Abubakar Birma sananne kuma hamshaƙin Malami ne wanda ya yi suna a Nijeriya, musamman Kano da Maiduguri. Babarbare ne ɗan asalin garin Maiduguri. Matan shi biyu, Hajja Kulu ita ce matar shi ta farko, wacce ta ke ƙabilar Barebari, ta na zaune ne gidan Malam da ke birnin Maiduguri. Yaran ta da shida, maza huɗu da mata biyu. Sai kuma Hajja Aleesha, wacce ta ke ƙabilar Shuwa Arab. Ita ce ke zaune Kano, ƴaƴa uku gare ta, kuma duka mata, sun haɗa da ɗiyar ta ta farko Zainab mai kimanin shekara ishirin da biyu, wacce ake kira Yakura, sai mai bi mata, Halitta mai shekara ishirin, sai auta Falmata, wacce ta ke da shekaru goma sha takwas a duniya.

 

Cikin ƴa’yan Malam, Allah ya jarrabe shi da fitinanniyar ɗiya, wacce babu wanda zai ga ɗabi’un ta ya danganta ta da Malam. Ba kowa ba ce fyace ɗiyar Hajja Aleesha ta farko, wato Zainab. Club ne daga na cikin gida Nigeria kudu da Arewa har zuwa ƙasashen ƙetare babu wanda ba ta zaga ba, sai dai wanda ba ta sami dama ba, haka kuwa buɗe ido babu wanda Zainab ba ta yi ba kasancewar ta na yawan harka da gurɓattun yaran masu kuɗi, yawanci ta haɗu da su ne ta cuɗanyar makarantun boko da su ka yi tare.

 

Social media kuwa ta yi ƙauran suna, mabiyan ta bila adadin haka, haka kuma masoyan ta da masu hure mata kunne domin kuwa abu biyu ne ya haɗar mata, ga kyau ga naira, babu shakka Allah ya bata duniya.

 

Duk wannan hali da Zainab ke ciki Malam bai sani ba, shi a na shi ganin cikin ƴaƴan shi babu mai kamala da nutsuwa da ya kai ta, domin kuwa kullum a haka ta ke zuwa ma sa a nutse. Ga shi shi ba ma’abocin social media bane bare ya san wainar da ta ke toyawa, haka zalika shi ba mazauni ba, yau ya na Maiduguri, gobe ya na Misira, gata ya na saudiya. Sanda ya ke gari kuma ita kuma Zainab ta na makaranta, nan American University of Nigeria da ke yola, dama nan ta fi sheƙa ayar ta, dan idan ka ga irin rayuwar da ta ke yi ba za ka taɓa cewa ɗiyar Malam ba ce, ɗiyar Malam taƙi halin Malam.

 

***

Sabbin Hausa Novels Complete

Jin a ranar Malam zai tafi Maiduguri ya sanya Zainab kafewa a lalle ita za ta kai ma sa kayan shayin da ya nema a kai ma sa falon shi na baki, saboda ta na so ta ga Malam akan buƙatar ta na sake wayar ta ƙirar Samsung da ko wata huɗu ba ta yi da siya ba, a cewar ta cemeran ba ta da kyau sam, ta na buƙutar latest IPhone da gaggawa.

 

Da shigar nan na ta cikin hijab har ƙasa, ta tura ƙofar falon a hankali, zuciyar ta ɗaya da sallamar ta da Shigan ta falon lokaci guda ta yi, cak ta tsaya yayinda idanun ta su sauka kan fuskar nan da ke ɓuye cikin rawani, kamar yanda ta yi arba da shi jiya da daddare. Tuni gaban ta ya fara faɗuwa, babu shiri ta juya da niyar komawa, muryar Malam ne ya dakatar da ita, ya na mai faɗin

 

“Yakura shigo mana, wannan da ki ke gani ɗalibai na ne, da kuma driver da masu gadi, kasancewar kullum kuna killece cikin gida shiyasa ba za ki gane su ba, muna tattaunawa ne akan zargin wasu ɓata garin da su ke yunƙurin hauro mana gida cikin dare…….”

 

Duk da mazan da ke zaune falon sun kai su goma, babu wanda ta ke iya gani sai wannan mai rawani, hankalin ta bai ƙara ta shi ba sai da ta ji kalaman da Malam ya furta, ba ta san sanda ta kara kai kallon ta ga mutumin ba, shi ma ɗin kallan ta ya ke ya na mai gasgata abun da zuciyar shi ke raya masa

 

“wannan ita ce ɓingel din da na yi gamo jiya, ashe ba aljanah ba ce, to menene dangantakar ta da Malam? ”

 

Abin da ya yake rayawa cikin ransa kenan, kamar kuwa Malam ya sani, sai ji yayi ya furta

 

“ɗiya ta ce, wannan ita ce Zainab, ɗiyar mai ɗaki na ta biyu, mahaddaciya kuma kamila a cikin ƴaƴana”

 

Jin haka ya daɗa kallon ta, a hankali ya maimaita sunan

 

“Zainab..”

 

To idan dai lafazin Malam haka ne, to babu shakka ba ita ya gani ba. Hukuncin da ya yanke kenan yayinda ya sake ƙura mata ido domin neman bambamcin tsakanin wannan kamilar ɗiyar Malam da kuma waccar da ya gani a daren jiya.

Aje tiren abincin ta yi gaban Malam, kai a sunkuye ta gaishe shi, ya na amsawa ta tashi da sauri ta fice daga falon dan kuwa ita kan ta tana jin idanun wannan bawan Allah a kan ta. Sai da ta kusa isa kitchen sannan ta dan tsaya ta nutsu gudun kar su Ammy da Halitta su gane halin da ta ke ciki.

 

 

Katon kitchen ne wanda mutum goma za su iya aiki ciki ba tare da an takura ba. Ya tsaru sosai dan kuwa cike ya ke bam da duk wani kayan amfanin kitchen. hatta fridge biyu ne cikin kitchen din, na kayan miya da nama daban, sai kuma na ruwa da lemoku da kuma kayan marmari. Ta tarar da Halitta na jera lemo da ruwa cikin fridge, gefe kuma Ammy ce ta ke yiwa Iya mai aikin su bayanin abincin da ta ke so a dafa da rana.

 

“Ammy anya kuwa cikin masu aikin gidan nan ko daliban Dady babu yan Boko Haram ko masu garkuwa da mutane?”

Cewar ta yayinda ta dauki daya daga cikin ruwan da Halitta ke jerawa a fridge.

 

“Auzubillallah!”

 

Ammy da Iya su ka furta tare, ita kuwa Halitta tsayawa ta yi ta na duban yar uwar tata, da ko a jikin ta, kofi ta ja ta zuba ruwa ta jika makoshin ta. Sannan ta kara da

 

“Ya ki ke kallo na haka kamar wata gaula? Wallahi I’m very serious about this one”

 

Tsakanin ta da Allah ta ke bayani yayinda ta mayar da hankalin ta ga Ammy, ta ce

 

“Ammy kin dai san yan boko haram din nan dai malamai su ke hari, ki tuna fa shugaban su Yusuf wanda aka kashe lokacin shugaban kasa yar aduwa an ce ya taba neman ilimi gun shiek Jafa’ar Allah ya ji kan rai, kin ga dole Dady yayi takatsantsan dan wallahi ina kyautata zatan wanda na gani gun Dady dan boko haram ne…..!”

 

“Kul kar na sake ji!”

 

Ammy ta katse ta, cikin tsawatarwa ta juya harshe zuwa yaren ta na shuwa, fadi ta ke

 

“Idan ki ka kuskura Malam ya ji wannan maganar wallahi sai ran ki ya baci, ke fa dadi na da ke danyan kai! Kina maganar Boko haram gaban iya kalan ta fita ta yada cewa Malam na aje yan boko haram gidan sa ko? Oh ni wannan rashin hankalin na ki Yakura ina za ki da shi?”

Sabbin Hausa Novels Complete

“Toh bare ma ni gidan nan kaf ban ga wanda ke kama da Boko haram ba……laaaa ko dai Usman ta ke magana ne?”

 

Cewar Hallita, yanda ta ambato sunan Usman ɗin cike da farin ciki, in da idanun ta har wani sheki su ke ya sanya Ammy da Zainab kura mata idanu. Ita ma din sai a sannan. Ta ankare ta yi saurin faɗin

 

“Daya daga cikin almajiran Dady ne fa, ina ranar da mu ka je taron makarantar su Falmat? Ranar mu ka tarar da shi bakin gate ya na jiran Dady ,a gaban mu ya gabatar da kan shi wajan Dady, ya ce sunan shi Usman, ya na so ya zama daya daga cikin almajiran Dady in da hali, Amma sai dai be da kudin sadaka sai da a bashi aikin yi, Ammy I’m sure Dady ya fada mi ki sai dai kin manta tunda daliban na sa da yawa, ku tambayi Falmat ma ku ji zancen fa ba na yau ba ne an kwana biyu”

 

“Ahaaa kin ji ai Ammy, kawai out of blue mutum ya zo Dady ya karbe shi! Gashi nan dai magana za ta fito, Dan Boko haram……”

 

Ammy na mai kallan Zainab ta ce da Iya

 

“Iya dan je ki zan neme ki zuwa anjima kadan, bari dai na gama da yaran nan”

“Toh Hajiya”

 

Iya ta fita ba a san ran ta ba, dan kuwa ta na dan tsintar zancen da ake duk da Ammy ta sauya harshe.

 

Iya na fita Ammy ta mayar da hankalin ta ga yan matan na ta biyu, ta na mai nuna Zainab da dan yatsa ta ce

 

“Kin ga Yakura? Idan kalmar Boko haram din nan ba ta fita bakin ki ba Allah sai na sabar mi ki! Malam ne zai aje dan boko Haram gidan sa?”

 

“Bare ma ba dan Boko Haram ba ne, mutum ne kamili mai ilimi da zurfin tunani…..”

 

Cewar Hallita ta na mai hango Usman cikin ranta.

 

“Halitta?????”

 

Ammy da Zainab su ka kira sunan ta a tare. Nan ta yi wuki wuki da idanu, gudun kar mahaifiyar ta da yar uwar ta su gano tuni ta kamu da san almajiri kuma daya daga cikin masu gadin gidan ne ya sanya ta tashi da sauri ta na mai aje ruwan da ya rage cikin fridge. Sai da ta rufe fridge din sannan ta juyo ga Ammy da Zainab wanda su ka tsura mata idanu su na jiran jin ba’asi.

 

“Ammy na gama bari na je na gyara daki na”

 

Ta fada in da ta yi hanyar fita. Kan ta kai koma Ammy ta katse ta, in da ta ce

 

” Halitta ya aka yi ki ka san mutumin da Yakura ke magana akai kamili ne? Mai ilimi da zurfin tunani….?”

 

Gaban ta na faduwa ta juyo su ka hada idanu, ta yi saurin mayar da kallan ta ga Zainab wacce ta daga mata gira cikin alamar tambaya.

 

“Dady na ji ya na fada Ammy, Kuma duk wanda Dady ya amince ya rabe shi ko shakka babu mutumin kirki ne”

 

Ta na gama fadin haka ta fice. Zainab kuwa dan tsalle ta yi tana dariyar mugunta har da tafa hannu ta ce

 

“Ammyyyy you see your child abi? Allah ya sa ba siriki za ki yi da Mai gadi ba”

Duka Ammy ta kai mata ta na fadin

 

“Bakin ki baya fadan alkhairi Yakura! Allah ya rufa mana asiri da wannan mugun fata, bakin ki ya sari danyan kashi”

 

“Toh ni kam sai dai na taimaka da amen, kin dai san halin diyar ki sarai ba hankali gare ta ba, bari na dena kiran sa Boko haram kar dai brother in-law ne, Ni kam na yi gaba”

 

Ta fice ta na jiyo Ammy na fad’in

“Yar butan uwa, za ki dawo ki same ni ne, oh ni Aleesha Allah ka raba ni da mugun ji da mugun gani!”

 

Ta na maganar ne tana girgiza kai.

 

***

 

Halitta dakin ta ta shige, har lokacin gaban ta bai dena faduwa ba, in da ta haye bisa kan gadon ta tana mai rufe idanu. Tun da ta ke babu mahalukin da ya taba shiga ran ta tamkar wannan bawan Allah da yar uwarta ke ikirarin dan Boka haram ne. Ba za ta taba mance ran da ta fara tuzali da shi ba.

 

Watanni bakwai da su ka wuce, sun dawo daga taron makarantar su Falmat su ka tadda shi bakin gate. Ka na ganin shi ka ga buzu ko bafulatani saboda yanda yayi nadin rawani da kuma yar riga yar shawara da ke jikin sa. Kasancewar shi bafulatani sam be yi karamin jiki irin na zubin fulani ba, dogo ne mai alamun karfi da faffadar kafada.

 

Kafin Mai gadi ya bude gate Malam da ke zaune a gidan gaba tare da direba ya sa aka sauke masa gilashin motar in da yayi masa Sallama. Ganin Malam ya taso da sauri, har kasa ya durkusa zai gaishe shi, Amma ya ce ah ah ya tashi su gaisa, Malam ya bashi hannu su ka gaisa.

 

Nan ya gabatar da kan sa a matsayin Usman, bafulatani dan cirani, ya zo ne gidan Malam domin neman ilimi kasancewar Malam na daya daga cikin Malaman da ya ke sauraran tafsirin su gidan rediyo, be da arzikin biyan Malam sadaka, Amma zai yi masa aiki har lokacin da zai gama samin ilimin a sallame shi.

 

Daga gidan baya Halitta da Falmat ke hango shi, ita kan ta Falmat ta yaba da kamalan sa, bare Halitta da ta saki baki da hanci ta na kallan sa.

 

Bayan Malam ya gama nazari kan sa na wasu mintina ya ce da shi ya bari ya dawo gobe da safe. Da haka su ka yi sallama ya tafi, inda su kuma su ka shige ciki. Bayan sun sauka daga motar ne Hallita ta dubi Malam ta ce

 

“Dady dan Allah ka duba lamarin bawan Allan can, kamar dai ya na da kamala, idan da yiyuwar taimaka masa a taimaka masa”

 

Malam na murmushin jin dadin yanda diyar ta shi ke da tausayi ya ce

 

“Toh in Sha Allah diyar albarka, dadi na da ke tausayi da jin kai, na mi ki alkawarin matukar na yi bincike na ga be da aibu zan dauke shi matsayin dalibi na, kin san rayuwar ce yanzu ba kamar da ba, mutane sun zama abin tsoro”

 

“Wallahi da gaskiyar ka Dady, muna zaman zaman mu kilu ta ja bau, ka yi binciken dai, rabi da wannan sarkin tausayin”

 

Falmat ta fada yayinda ta ja hannun yayar ta su ka yi hanyar ciki.

 

“Dady a duba dan Allah”

 

Cewar Hallita ta na mai sake waigowa. Kai Malam ya jinjina mata alamar ya ji ta.

Haka Halitta ta yi ta bibiyan lamarin har Allah ya taimaka bayan Malam yayi bincike, a iya binciken da aka yi ya gano Usman bafulatanin wata riga da ake kira rugar Shehu ne, Baban shi ne shugaban rugar, haka kuma Usman shi ne babban dan sa. Kasancewar bai ga wata bayyananniyar matsala daga gare shi ba ya sanya Malam karbar shi a matsayin daya daga cikin almajiran sa da ke daukar karatu a gida. Malam ya ce zai iya bashi ilimi ba tare da ya biya sadaka ba, Amma shi ya dage lalle a bashi aiki cikin gidan, idan har ya sami ilimi a arha ba lalle ya ga darajar sa yanda ya kamata ba. A wannan dalilin ne Malam ya bar shi ya na taya Mai gadin gidan gadi cikin dare.

 

Ajiyar zuciya ta saki ta na mai juyi bisa gado, ita kan ta tasan lamarin da zuciyar ta ke bijiro mata akan Mai gadin nan lamari ne mai girma a gaban iyayen ta. Ba ta ji shigowar ta ba, sai jin zaman ta tayi bisa gado. A hankali ta furta

 

“Halitta shin ba za ki dena sa kan ki cikin tunani ba? Sai kin sakawa kan ki cuta akan abin da ba zai taba yiyuwa ba!”

 

A hankali ta bude idanun ta tana mai duban kanwar tata Falmat. Falmat ta na da jiki sosai da kuwa gidan kaf babu wanda ya kai ta kiba. Kiban ta be sa ta yi muni ba dan kuwa irin matan nan ne Duma duma masu kyau na kayatarwa. Kamar Zainab ita ma Falmat baka ce, ta na da hanci har baka da manyan idanu. Duniyar nan kaf babu wanda ya san cikin ta kamar wannan kanwar ta ta, ita kan ta takan yi mamakin yanda ta ke bude mata cikin ta. Falmat sanye cikin kamfala mai ratsin shudi da ja, dinkin goguwar riga har kasa, kannan ya sha tauri da kallabi kai ka ce gidan biki za ta je.

 

“Falmat ya zan yi da jarabawar ubangiji? Kin san dazu na yi barin baki gaban Ammy da Yakura kuwa?”

 

Halitta ta fada cike da damuwa. Falmat na mai dafe kirji ta ce

 

“Kai Halitta! Wasa ki ke yi wayan ki ya fi gaban haka!”

 

Kai ta girgiza sannan ta ce

“Idan dai a kan abin da rai ke so, I’m full of disappointment Falmat, wallahilazim! Amma dai na gyara maganar, Allah ya sa dai kar su gane halin da na ke ciki”

 

Shiru ne ya biyu baya, kamin daga bisani Falmat ta ce

 

“Halitta?”

 

Halitta ta amsa mata da

 

“Uhm”

 

“Ina mai baki shawara da ki sassauta wannan lamarin, kin san ba abu ba ne mai yiyuwa ko da kowa wannan mutum ya kai matsayin haka, bare kuma bakauye, dadin dadawa Mai gadi a gidan mu…..”

 

“Bakauye Mai gadi ba mutum ba ne? Ba Allah ne ya halicce shi kamayar yanda ya Halicce mu ni da ke da su Dady ba??”

Halitta ta katse, ba ta gushe ba ta kara da

 

” Saboda Allah ya dan san mana kankani daga ni’iman shi sai mu zamo ma su butulci ta hanyar kaskantar da bayin shi? Bari na fada mi ki magana daya Falmat! Ina san shi! Ina san Usman tsakani da Allah!”

 

Jikin Falmat sanyaye ta ce

“Allah ya ba ki hakuri, Allah ya kawo sauki cikin lamarin ki, dama na zo fada mi ki Dady ya tafi, kin ce ya na tafiya na fada mi ki”

 

Zumbur Halitta ta yi ta mi ke, da sauri ta nufi bandaki, ta na fadin

 

“Toh ina zuwa na wanke fuska ta, Allah ya taimake yau dai na kara ganin Usman Falmat”

 

Shiru Falmat ta mata ta na kallan ikon Allah. Bayan ta fito daga bandaki ga mamakin Falmat sai ga Halitta an tsaya gaban madubi ana goge fuska tare da shafa hoda. Dake Halitta irin matan nan ne jajur sam ba ta damu da shafa powder ba tsabagen farin ta, ita da Zainab kamar su daya, kalar fata ne ya bambamta su, in da Zainab ke baka, Halitta Fara ce sol, dan fari har wani jaja ta kan yi musammam idan ta sha wuya ko ta shiga rana.

 

“Wannan shafa powder na menene? Ina za ki wai?”

 

Ta na shafa man lebe ta ke duban Falmat ta cikin madubi, ta ce

 

“Ina dai za mu je, ai har da ke za mu fita yanda Ammy ba za ta zargi komai ba”

“Ina za mu toh”

 

Falmat ta tambaya cikin rashin fahimtar in da Halitta ta dosa. Sai da ta shirya tsaf cikin bakar doguwar riga, tare da nada bakin mayafi, kallo daya za ka mata ka san ko shakka babu Halitta jinin larabawa ce, dan kuwa ta fito a shuwar ta sak. Zuwa ta yi ta na mai ruko hannun Falmat ta ce

 

“I want to see him, please, na san dai ba zai yiyu cikin gidan nan ba, Amma duk yanda za mu yi na gan shi ko sau daya ne Falmat, ba sai mun yi magana ba, kawai na gan shi ya ganni Falmat…..”

 

‘wannan bawan Allah ko dai asiri ya yiwa Halitta’

 

Cewar Falmat cikin zuciyar ta, dan kuwa lamarin na Halitta ya fara bata tsoro, lalle lokacin da za ta shaidawa Ammy halin da take ciki yayi!

 

Add Comment

Click here to post a comment