Hausa Novels Littafan Hausa Novels

Goje Book 4 Hausa Novel Complete

Goje Book 4 Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Goje Book 4 Hausa Novel Complete

_Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah._

 

 

 

 

*105&106*

To shima nashi ‘bangaran abinda yake faruwa kenan, domin tun bayan ya sauka gida yake kiran wayarta abun ya gagara, da ta fara shiga sai ta katse ya kira ya kai sau goma bai samu biyan bukata ba, sai kawai ya ajiye wayar ranshi gabadaya a ‘bace yaso kafin ya kwanta yaji lafiyarta da ta babynsa dake kwance a cikinta, haka kawai yake tausaya mata, ya san duk wani abu da take daurewa take akan ta nuna masa kaunar ‘yan uwansa, kuma abunda tayi ya siya mata kima da daraja a idonsa, ya sake jin sonta ya k’aru a zuciyarsa.

 

Da tunaninta ya kwana ya kuma tashi dashi, wannan dalilin ne yasa yana dawowa daga massalaci ya dauki wayarsa ya kunna, ya fara laluben number ta, cikin ikon Allah sai ta kira shi, a jiyar zuciya ya sauke mai sanyi kafin ya sanya wayar a kunnansa da sallama a bakinsa.

Mai so na

Ta amsa a sanyaye tana dan gyara kwanciyarta, yace.” My GIMBIYA fatan kin tashi lafiya ya kwanan bakunta.”?

 

Tace.”Lafiya alhamdullihi na kwana da tunaninka da kewarka rashin kwanciya a kirjinka ya janyo min ciwon jiki.”

 

 

Ya lumshe ido yana jin wani feeling na taso masa yace.” Me yasa ki ka takura kanki lallai sai kin kwana umm? saboda na san hakan zai faru ya sa na sauya shawara, yanzu na gamsu da kaunar da kike a kaina da family na.

 

Sanyayyar ajiyar zuciya ta sauke kafin tace.” Nifa ba’a takure nake ba, domin yanayin garin ya burgeni sosai da zamu dawo garin da zama da hakan yayi min dadi.” Tafad’i hakane kawai ba har can cikin zuciyarta ba.

 

Aikuwa yaji dadin maganar yace.” Tunda yanayin garin yayi miki dadi zamu dinga zuwa hutu ko? zan gina miki gida mai kyau.”

 

Tayi ‘yar dariya da fadin.” Naji dadin hakan mijina.”

 

Yace.” Ya babyna ina fatan yana lafiya.”?

 

A shagwabe tace.” Jiya tun bayan da kuka gaisa dashi ya dameni da k’iriniya sai motsi yake min.”

 

Dariya yasa da fadin.” Yana bukatar mu sake gaisawa sosai dan jiya baki sakar min jiki mun gaisa yanda ya dace ba, amma ki bashi hakuri kafin mu had’u.”

 

Itama dariyar take kafin tace.” Aa ni babu ruwana idan kun had’u sai ka bashi hakuri dan da alama yayi fushi tun wayewar gari beyi motsi ba.”

 

 

Gabansa ya fad’i! da sauri yace.” Beyi motsi ba fa ki kace.”?

 

Ta dora hannunta a saman cikin tana shafawa kafin tace.” Eh mana ya tattara a guri daya kamar bashi da lafiya.”

 

 

Gabad’aya yaji hankalinsa ya dawo garin yace.” Ganin tafe insha Allah.”

 

Da sauri tace.” Laa da wasa fa nake maka.”?

 

Ya ‘bata rai da fadin.” ZINAT an ta’ba wasa da lafiya ashe.’?

 

Jin yanda yayi maganar babu wasa yasa ta zama serious tace.” Allah tsokanarka nake yanzu haka ma motsi yake yaji muryarka.”

 

Ajiyar zuciya ya sauke da fadin.” Saboda kin ga na damu shiyasa zaki mayar dani shashasha ko.”?

 

 

Kunshe baki tayi tana danne dariyar dake kokarin subce mata, tace.” Kayi hakuri Darling.”

 

 

“Um-um! naki hakurin.” Cikin shagawaba yayi maganar………Tace.” Dan Allah fa.”

 

Yace.” Nayi amma kada ki sake min wannan wasa hankali na ya tashi wallahi.”

 

Tace.” To ba zan sake ba insha Allah.”

 

Yace.” Uwale ta tashi.”? tace.” Eh tana kicin tana aiki.”

 

Yace.” Idan babu damuwa ki kai mata wayar mu gaisa.”

 

Tace.” To insha Allah bari na kai mata.”

 

Cikin jin dadi yace.” Allah yayi miki albarka.”

 

Ta amsa da “Ameen tana kokarin tashi tsaye.

 

 

****

Hamra’u da kanta ta shirya abincin ta zuba cikin kwanuka masu kyau ta jera kan tire kafin ta nufi bandaki a gurguje ta shiga wanka.

 

A lokacin ne mahaifiyarta Dayyiba ta samu damar aikata mugun nufin ta.

 

Ko kafin ma Hamra’un ta fito daga bandaki har ta sanya k’aramin d’anta ya dauki tiran dake dauke da abincin sun fita a tare.

 

 

D’aya da rabi na rana Uwale na aiki a kicin Dayyiba tayi sallama a gidan.

 

Uwale ta amsa ta fito daga kicin din tana mata barka da zuwa, kai tsaye daki suka nufa.

 

 

Suka fara gaisawa tare da tambayar bayan rabuwa…..Dayyiba tace.” Ai da wuri yau na gama abinci nace bari nazo mu gaisa na kuma ga matar Umaru kin san dama ni ban ta’ba ganinta ba.”

 

Uwale tace.” Allah sarki sannu da kokari Dayyiba har da wahala haka to mun gode sosai.”

 

Tana murmushi tace.” Babu komai Dambu ne na turara mata na san masu ciki da kwad’ayi watakila yayi mata dadi.”

 

 

Tace.” Eh ‘kwarai kuwa, bacci takeyi yanzu amma bari na leka na gani ko ta tashi.”

 

 

Lokacin da ta shiga dakin zaune ta sameta a bakin gado tun bayan shigowar Dayyibar ta tashi duk tana jin maganganunsu.

 

 

Tace.” Ashe kin tashi dama mahaifiyar Hamra’u ce tazo ku gaisa ta kuma kawo miki abinci.”

 

 

Tace.”Allah sarki amma na gode sosai bari na fito mu gaisa.”

 

Ta juya da fadin.” To bari na sheda mata.”

 

Shuru tayi tana nazarin al’amarin, mahaifiyar Hamra’u? ita sunan yarinyar ma bata kauna ballantana wanda ya danganceta.

 

Ajiyar zuciya ta sauke kafin ta tashi da k’yar! yunwa sai sasakar cikinta take, abun goge baki ta dauko cikin kayanta.

 

Koda ta fito bata zauna ba tukkuna sai da ta wanko bakinta ta dauro alwala sannan ta dawo dakin.

 

A nutse ta zauna kusa da Uwale ta kalli Dayyibar dake mata wani munafikin kallo tace.” Ina wuni fatan mun sameku lafiya.”?

 

 

A firgice ta amsa da fadin.” Lafiya lou muke ya mutan gida da can gurin manyan.”

 

Tace.” Duk suna nan lafiya lou.”

Daga haka sai ta kawar da kanta tana nazari akan matar kamar mara gaskiya.

 

Uwale ta bud’e kwanunkan abincin da fadin.” Dambu ne ko kina sha’awa.”

 

Kamshi ya bugi hancinta Dambun ya hadu yaji gyada da zogale ga k’amshin man gyada ziryan yana tashi………..Tunda take sau biyu kacal ta ta’ba cin irin wannan abincin, shima kuma irin na shinkafa bana masara ba , wannan dalilin yasa gabadaya ta rikice yaron dake cikinta ya nuna kwadayinsa akan abincin .

 

Ta kalli Dayyibar da fadin” Na gode sosai.”

 

Tana washe baki ta amsa da babu komai dan nayi miki hidima kamar ‘yar cikina kike.”

 

Murmushi kawai tayi ta kalli Uwale da fadin.” Nayi sha’awarsa.”.

 

Uwale tasa dariya da fadin.” Ai dole ni kaina ya bani sha’awa ballanatana ke da kike da lalura.”

 

 

Dayyiba ta dinga dariyar farin ciki tace.” Ai kin san Hamra’u ta gwane gurin iya abinci gargajiya dama na turawan kowacce mace tana da baiwa, amma tabbas duk macan da ta iya girki zata samu soyayyar mijinta.

 

Ba ita Zinat din ba har Uwale sai da taji babu dadi da maganar Dayyibar dan kamar maganar tayi kama da habaici.

 

Babu dai wanda yayi magana a cikinsu, ta zuba mata a ma daidaicin plate. tayi bisimillah ta fara ci a nutse ba ta tunanin komai a ranta.

 

Sosai dambun yayi mata dad’i, tas ta cinye wanda yake gabanta. a cikinta tana jin k’oshi amma a bakinta ba ta gaji ba, haka dai tayi kawaici tasha ruwa.Uwale ke tambayarta, tace.” A yanzu dai ta koshi sai zuwa an jima tukkuna.”

 

Dayyiba mahaifiyar Hamra’u zuciyarta fes! ta fita gidan, babban burinta cikin ya zube ko kuma Gimbiyar ta galabaita.

 

Aikuwa dai jikinta ne ya mutu kasala ta dame ta, sai kawai taje ta kwanta tana ya mutse fuskarta cikinta ne yake hautsinawa zuciyarta na tashi.

 

Minti ashirin da kwanciyarta ta tashi a gigice! sakamakon jin wani irin mahaukacin amai da yake taso mata.

 

 

Bakin rariya ta gurfana ta dinga sheka aman tana rike kirji!

 

 

Uwale hankalinta ya tashi ganin mawuyacin halin da Gimbiyar ke ciki.

 

Ta rike ta tana mata sannu a lokacin kanta ya dinga juyawa tayi kwance a gurin tana mayar da numfashi.

 

Uwale tace.” Sannu ki daure ki tashi ki koma daki ki kwanta a can kinga nan akwai rana gaki a bakin kwata a kwance.”

 

 

 

Shuru tayi ba ta iya cewa komai ba, gabadaya ma bata cikin hayyacinta, tana jin yanda cikinta yake kartawa! wannan karan ba amai takeji ba zawo! ne mai karfi yake kokarin kwace mata.

 

Kokarin tashi take domin shiga bandaki abun ya gagara domin gabadaya jikinta ya shika babu kwari! duk yanda taso da ta daure ta kasa ba ta ma san lokacin da zawon ya kwace mata ba, kawai sai tsuuuuuu! ta dinga jin fitarsa kamar an kwance famfo.

 

 

Innalillahi wa’ina ilaihi raji’un! shine abinda Uwale take nanatawa.

 

(Cutar a mai da gudawa!) ya kama ‘yar mutane! cutar dake saurin halaka mutum, hankali a tashe ta nufi gidan Tasallah.

 

 

Suka shigo tare lokacin gudawar sai bin rariya take ita kuma tana kwance a gurin sai matagugu take domin wani masifaffan ciwo cikinta yake mata.

 

 

Tasallah tayi salati tana sanar da Ubangiji kafin tayi azamar fita, gidanta ta koma da yake akwai magungunan gargajiya da take aje dasu, ta daga karkashin gadon karfenta ta dauko ledar maganar duk tayi kura da dauda! da yanar gizagizo ajikin ledar ta dauka ta fita.

 

 

Aje ledar tayi a gefe ta taimakawa Uwalen suka fara gyarata, idonta a lumshe yake amma duk tana jin taretaran da suke da ita, ta riga ta mika wuya yanda take jin jiki bata tsammanin zata rayu.

 

Jikinta suka wanke mata lokacin anyi sa’a Gudawar ta tsaigata da zuba.

 

Uwale tayi saurin dauko mata wasu kayan da wando da rigar nono suka sanya mata jikinta mikar da ita sukayi kafafunta suka dinga kyarma! a daddafe suka shiga da ita daki.

 

 

Uwale ce ta shiga gyara gurin, ita kuma Tasallah sai da ta tsaftace hannuwanta, sannan ta kwance ledar maganin data dauko ta fito dasu a daddaure! daka gani sun jima a ajiye, wuta ta hura kafin ta wanke maganin tas ta zuba a tukunya tasa jar kanwa sannan ta d’ora a wuta.

 

Sai da ya tafasa sosai sannan ta sauke domin yasha iska.

 

 

To cikin ikon Allah da hukuncinsa tana shan wannan magani ta samu sassauci ciwon cikin da yake damunta yayi sauki baccin wahala ya d’auketa.

 

Uwale ta kalli Tasallah da fadin.” Sai yanzu hankalina ya kwanta Tasallah al’amarin nan ya tsorata ni mutuka.”

 

Tace.” Dole ne, ni kaina ganin yarinyar a galabaice sai da na firgita kasancewar na san cewa wannan cutar na saurin halaka mutum! Allah yasa akwai ajiyayyun magunguna kinga cikin ikon Allah sunyi amfani ”

 

 

Ta sauke ajiyar zuciya da fadin.” Tasallah nifa ina zargin Dayyiba.”

 

Shuru tayi tana kallonta da mamakin maganarta.

 

Tace.” Tun bayan da yarinyar nan taci Dambun da Dayyibar ta kawo mata shikkenan ta rikice shiyasa nake zargin ko da abunda tayi.

 

 

Tace.” Uwale zato zunubi aka ce koda ya kasance gaskiya ne, ni kuma nafi tunanin ko sauyin cima ne da ruwan sha, kin san hakan na iya janyo faruwar mummunar matsala.

 

 

Tace.” Idan hakane me yasa jiya da taci abincina ta kwana lafiya? ruwa kuma ba irin wannan muke sha yarinyar take sha ba, kafin mijinta ya tafi sai da ya siya mata ruwan roba gashi can a daki kwali guda. gaskiya ina zargin Dayyiba.

 

 

Tasallah tayi murmushi da fadin.” Hakan na iya faruwa amma kada kiyi gaggawar yanke hukunci tukkuna.

 

Shigowar Hamra’u ne ya katse maganar, babu wanda ya nuna mata wani abu a fuska, ta zauna suka gaisa, kafin ta kalli Uwale da fadin.” Ummana ta kawo miki Dambu ko.”?

 

Tace.” Eh ta kawowa dai Gimbiya.”

 

Ta dan ‘bata rai da fadin.” Ai naki ne kasancewar na san kina son Dambun masara yasa na tashi da wuri nayi miki, ko kafin na fito daga wanka na samu Ummana bata gidan wai ashe anan tazo.”

 

Tace.” To Na gode sosai Allah yayi miki albarka.”

 

Tasallah na ‘yar dariya tace.” Hamra’u kenan to menene dan kishiyarki taci ai abun burgewa ne ”

 

Zumbura bakinta tayi tana ya mutse fuska…….Dukkaninsu babu wanda yaji dadin abinda tayi, kiri-kiri take nuna kishinta a fili.

 

 

 

 

*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, ‘yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne……0542382124….Binta umar gtbabk….Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE*

[3/26, 9:55 PM] Matar Malam😊: _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah._

 

 

 

*109&110*

Gidan ya rage saura ita kadai, sai ta shiga tunanin abubuwan da suke faruwa, jiya da daddare kafin su kwanta Uwale tayi mata cikakken bayanin abunda yake tsakanin mijinta da yarinyar da tuntuni ta d’ora zargi a kanta, tabbas koda Uwale ba tayi mata bayanin komai ba dama tuntuni ta fahimci wani abu, duk da dai shi bai fad’a mata cewa akwai al’kawarin aure a tsakaninsa da yarinyar ba, to ita yarinyar ta nuna mata alamu tun farkon fara had’uwarsu…Ba zata ha nashi aure ba, domin a yanda Uwalen ke sheda mata yanda yarinyar tayi wahala a kansa hakan ya sanya taji tausayinta, bayan haka kuma ta san duk daran dadewa bai zama lallai ta zauna ita kadai ba, wannan ne dalilin da yasa ta tausayawa yarinar. wai akace son maso wani koshin wagala! amma babu shakka ba zata lamunci munafurci da kumbiya-kumbiya ba. domin tafiso duk abinda za’ayi a fada mata kada a munafurce ta, abu na karshe kuwa dole ya jawa yarinyar kunne ta kiyayi shiga gonarta ko kuma yi mata rashin kunya anan ne za’a samu matsala! domin mutukar yarinyar tace zata raina mata hankali to abu ne mai sauki a gurinta ta cire blet ta zane mata jiki dashi, sai dai duk abunda zai faru ya faru.

 

 

To can gidan biki kuwa ya kacame! da hayaniya mata sun fi ashirin akan Uwale dake rabon turaman atamfofi da mayafai da sabulai na wanka da wanki.

 

Da yawa wasu basu samu zanin ba, saboda yawansu, wasu kuma mayafai suka samu da sabulai, duk wanda ta mik’awa sai tayi masa bayani cewa daga matar Umaru ne.

 

A cikin wa’inda suka samu kayan har da mutanan Dayyiba……sai suka silale suka nufi gidanta domin kai mata rahoto.

 

Wasu kuwa gidan Uwalen suka nufa domin mika godiyarsu da kuma jin dadin alkairin da akayi musu.

 

Hayaniyar shigowarsu gidan ya katse tunanin da take.

 

Ta fito tsakar gidan ta gan su da yawa a tsaye….ikon Allah har da masu durkusa mata, ta jingina jikin bango (garu) tana amsa gaisuwarsu da fadin.” Ku daina godiya haka babu komai an zama daya.

 

 

D’aya daga cikinsu tace.” Dole muyi godiya yarinyar kirki! domin bamu tsammaci haka daga gurinki ba, dalili mun samu labari a bakin wasu daga cikin ‘yan uwanmu cewa baki da kirki mutuniyar banza ce ke da dai sauransu, sai gashi kinyi mana bazata mun gode sosai.”

 

Murmushi kawai tayi kafin tace.” Ba komai kun san mutum tara yake bai cika cif ba, kowa yana kuskure a rayuwa, wa’inda na ‘batawa rai a cikinku su yafe min tunda har Allah yasa na shiga cikinku ai mun zama daya dama rashin sabo da juna ne.”

 

Matar tace.” Kwarai kuwa Gimbiya to mu dai muna bayanki insha Allah domin dai Dayyiba bata da alkibula mai kyau! mu mutanan *KAFUR* muna sonki da kaunarki dan haka ki cire kokwanto a ranki.”

 

 

Tace.” To na gode sosai Allah ya saka da alkairi.”

 

Gabadaya suka amsa da ameen. kafin suyi mata sallama su fita….Itama cike da farin ciki da jin dadi ta koma dakin ta kwanta, cikin zuciyarta take adduar Allah ya bata hakurin zama dasu, tunda tana son mijinta babu abinda ba za tayi ba.

 

 

Dayyiba da labari ya iske ta kamar ta kurma ihu saboda bakin ciki, idonta ya ciko da ruwan hawayen bakin ciki ta kalli Taburni da fadin.” Amma dai kinji kunya wallahi Ashe amincin da yake tsakaninmu na ‘karya ne.”?

 

 

Taburni tace.” Kamar yaya ban gane ba.”?

 

Ta zabga mata harara da fadin.” Meye amfanin zuwa ki kar’bi turmin atamafa kamar baki ta’ba daura zani ba.”

 

 

Ta daga mata hannu da fadin.” Kinga Dayyiba saurara! kawai saboda gudun bacin ranki ina kallon alkairi sai na bar shi, kema kin san ba zai yuwu ba, zani da sabulai na samu ke ko dake ko babu ke dole ina da rabo saboda matar Kawunsa ce to meye abin damuwa.”

 

Dayyiba ta sanya gefan zani ta share guntun hawayen daya fara fitowa tace.” Taburni ban san ya zanyi ba akan wannan al’amari, wallahi idan Hamra’u ta samu shiga gidan Umaru buri na bai wuce ace ta zama mowa ba, amma na san hakan ba zai yuwu ba sai na taka muhimiyyar rawa. gashi bani da kudi a hannuna ballanatana naje a taimaka min.”

 

 

Tace.” Yanzu dai abu na farko da za fara shine janyo hankalinsa kan ‘yarki, ma’ana ya daina ganin kowa a gabansa sai ita, kafin ace ta shiga gidansa, sai kuma ayi musu farraku da Uwargidansa.

 

Tace.” Taburni bani da kudi wallahi, kuma kin san wannan harkar sai an ajiye kudi dole a zubar da jini.”

 

 

Taja tsaki da fadin.” Ashe wasa ki ka dauki al’amarin, ai idan zakiyi yawo tsirara ba abun damuwa bane mutu’kar bukatarki zata biya, ki sayar da gado da katifarki ai ba’a kanki aka fara ba.

 

Tayi shuru tana nazarin maganar, tabbas hakan shine mafita domin idan ta tsaya kallon ruwa to kwado ne zai yi mata ‘kafa gwara ta tashi a tsaye.

 

Uwale ta kawo mata gurasa *(band’asho)😃* Kanawa mune gurasa Allah yasa akwai wa’inda suka san meye ma’anar *(Band’asho)* Taji k’uli da man gyada mai kamshi gefe da kabeji da sauran kayan had’i, sosai taji dadi gurasar taci ta k’oshi kafin tayi wanka ta shirya jikinta cikin wani milk din les mai taushi da stones a jikinsa, sai ta dora alkyabba mai tafe da hula a jikinta, ta sanya takalmi rufaffan takalmi irin nasarauta, sosai tayi kyau, kamshi turaranta duk ya cika gidan.

 

 

Waje ta fito da wayar ta a hannunta…….ido yayi caaa! a kanta, itama kallonsu takeyi sunyi rukuni-rukuni a gindin bishiya suna ta cin abinci babu kimtsi balle kamun kai.

 

Can gefe kuma amaryar ce da k’awayenta da ango da abokansa sun sanya katuwar redio a tsakiyarsu kalangu sai tashi yake amarya da ango suna rawa ana lika musu ‘yan biyar-biyar.

 

Abin ya burgeta ya bata dariya kai tsaye gurun ta nufa cikin yanayin tafiyarta.

 

 

Hamra’u tare da Zabbah dake can nesa suka hangeta tawagar ‘yan matan garin sun rufeta a lokacin da take tsakiyar amarya da ango tana manna musu ‘yan dari biyar-biyar…….Ihu!!! da kaya-kaya ya cika gurun!

 

 

Takaici ya hana Hamr’au karasawa gurin, ta juya a sukwane ta koma gida…..Ita kuwa Zabbah! sai da ta k’arasa gurin, ta kutsa ta samu rabonta dan sai da ta tsira da dubu biyu.

 

 

Da wayarta ta dinga yi musu vedio sai hauka suke suna he da he kowa so yake tayi hoto dashi, amarya da ango kuwa kamar su zuba ruwa a kasa su sha a tarihi ba a ta’ba biki irin nasu ba.

 

 

Hamra’u ta ‘karaso gurin tana wani dauke kai! ita gata wacce ta fita zakkah a cikinsu, da ba a san asalin balbela ba sai ace daga masar tazo …….Ta zuge jakar hannunta ta fito da kudi ‘yan dari -dari ta fara watsawa a gurin………Wani abokin ango yayi saurin sanya wakar *Komai na Babah yafi na yaro!* Zinat kuwa ganin haukan da yarinyar take ya sanya tayi gaggawar fita daga gurin.

 

Ita kuwa Hamra’u sai wani jin kai take tana wani ya mutse fuska! Zabbah taja ta gefe da fadin.” Wannan wa’kar fa da Salmanu yasa dake yake, kinzo kina lika dari-dari ita kishiyar taki dari biyar biyar ta dinga watsawa kuma ta watsa yafi dubu ashirin kinga nima na samu dubu biyu. amma ke kina lika ‘yan dari -dari sai wani jin kai kike.”

 

Jikinta yayi sanyi ta kalleta da fadin.” Kina nufin dama saboda naji haushi Salmanu yasa wannan wa’kar!

 

Ta fashe da dariya da fadin.” E mana ma’ana kiji haushi kema ki watsa musu kudi.”

 

 

Ta girgiza kai da fadin.’ Lallai Salmanu bashi da mutunci.”

 

Tace.” Hamra’u ni dai shawarar da zan baki shine kiyi hakuri ki kwantar da kanki ku zauna lafiya, dan na fahimci matar nan kamar tana da saukin kai kuma ba zaki samu matsala da ita ba, sannan kuma a zahiri ta fiki ta ko’ina kada kice zakiyi gasa da ita.”

 

Tace.” Idan na fahimce ki kina so kice na zauna nayi mata bauta ko.”?

 

Ta girgiza kai da fadin ” Aa ba haka nake nufi ba, ina nufin ki dai daina kishi a kanta dan naga kin zafafa da yawa, baki da gashin wance dole ki zauna a matsayinki.”

 

 

Ta girgiza kai da fadin.” Ba zai yuwu ba Zabbah shekara sama da goma ina dauki ba dadi akan biyan bu’kata na amma lokaci guda wata ta shiga rayuwata, wallahi ba zan iya daina kishi a kanta ba, domin bana kaunarta na tsaneta! kuma zan iya komai akan ganin bayanta.”

 

Zabbah ta dinga yi mata kallon mara hankali da tunani! itafa gabadaya rayuwar yanzu ta zama wayo da dubara da kuma siyasa mutukar ka iya wannan zaka zauna lafiya, amma shikkenan tunda tayi iya bakin kokari gurin ganin ta nusar da ita ta kasa fahimta zata kyaleta kawai taje duk abinda za tayi rayuwarta ce.

 

 

Shida shaura ya sauka a garin…….Tun kafin ya fito a mota gurin ya hautsine! hayaniya da ifece-iface! tare da haushin karnuka!

 

Saboda ba ta san ganin bacin rai yasa tayi gaggawar shiga gida, ta san mybe sai ya tsaya yayi abinda ya saba.

 

 

Sai dai kuma bata jima da shiga gidan ba ya shigo cikin inform da alama daga gurin aiki yake.

 

 

Koda ya shiga gidan hankalinsa gabadaya yana kanta….ya rungumeta yana ta sumbutar fuskarta. A lokacin su Uwale suka shigo gidan.

 

Uwale Hamra’u da Zabbah dake bayansu……Gabadaya jikin su ne yayi sanyi ganin irin soyayyar da ake zabgawa a gurin, kamar zai cinyeta ya rike fuskarta sai so yake ya kama bakinta tana kaucewa.

 

Gilmawar Uwale a gurin ita ta hankaltar dashi, ya sakar mata fuska yana sauke wani irin numfashi…..Juyawar da zai yi yayi ido hudu da Hamra’u dake tsaye kamar wacce aka dasa, gwiwarta tayi bala’in sanyi!

 

Ya d’an ji kunyarta amma da yake namijin duniya ne sai ya basar yace.” Kanwata ina fata dai kin shirya kin kuma yi sallama don yau zamu tafi.”

 

 

Murya na rawa tace.” Ni ba zan koma ba.”

 

Ya kalleta da mamakin furucinta a tare dashi yace.” Saboda me.”?

 

 

Ba tace komai ba, kawai ta juya ta fita kawarta ta rufa mata baya.

 

 

Ajiyar zuciya ya sauke yana mamakin al’amarin.

 

Ya dan juya in da take, wayam babu ita a gurin……bai kawo komai a ransa ba, ya cire takalman dake kafarsa ya shiga dakin da sallama a bakinsa.

 

 

Gabadaya suna uwar dakin ita da Uwalen.

 

Kusa da ita ya zauna yana d’an satar kallonta a idonsa ya hango rama a tare da ita kwana uku kacal ta sauya masa tayi haske sannan duk ta rame.

 

Uwale dake had’a kaya tace.” Naji kuna magana da Hamra’u ko.”

 

Yace.” Eh wai me yake faruwa ne?

 

Murmushi takaici tayi kafin tace.” Alkairi ne, amma tunda tace ba zata koma ba, sai ka kyaleta a ranar da aka daura muku aure ai dole ta zauna a dakinta.”

 

Gabansa ya fadi da jin maganar da Uwalen tayi zata tona masa asiri! be shirya sanar mata da maganar yanzu ba, ya saci kallon fuskarta yaga babu abunda ya sauya a yanayin ta wayarta ma take dubawa.

 

Ajiyar zuciya ya sauke cikin zuciyarsa yake addua Allah yasa ba taji maganar ba, duk da ya san da kamar wuya hakan dan kyau Uwale ta fadi maganar.

 

 

Ya kalli agogon dake d’aure a hannunsa shida da rabi har an fara kiran sallar magriba, yace.” Zan je nayi sallah mu gaisa da wanda ya dace kafin na dawo sai ku shirya.”

 

Tace.” Ai mu a shirye muke Umaru sallah kawai za muyi.

 

Yace.” Uwale anya ba wani abu ne ya faru ba kuwa.”?

 

Tace.” Me ka gani kake wannan maganar.”?

 

 

Yace.” Naga kamar kina Allah-Allah mu bar garin bayan kinyi alkawari cewa sai kinyi sati uku ko hudu.”

 

 

Shuru kawai tayi ba tace masa komai ba. Ya girgiza kai tare da mikewa tsaye. bahaushe yace shuru ma magana ce, lallai akwai abinda ya faru bayan barin sa garin.

 

 

Uwale na idar da sallah ta kalleta da fadin.” Kafin Umaru ya shigo zan dan shiga muyi sallama mutane.”

 

Tace.”To shikkean ba komai idan ya shigo zan sheda masa.

 

Fitar ta keda wuya ya shigo gidan, yana haska dakin da wayar hannnsa, kan dadduma ya sameta, ta idar da sallah amma bata tashi ba.

 

 

Ya zauna saman gadon karfen dake dakin yana kallonta.

 

 

Babu yabo babu fallasa ta juyo suka had’a ido taga yana mata wani irin kallo kafin yace.” Zo nan ki fada min abinda ya faru bayan tafiya ta.”

 

 

Ta iske in da yake ya rike hannunta tare da zaunar da ita kusa dashi, gabadaya hankalinsa yana kanta, yana jiran abinda za tace.

 

 

Tace.” Kai me kake tunanin zai faru.”? Shuru yayi be san me zai ce ba kawai yana ji a jikinsa ne.”

 

 

Tace.” Kamar yanda Uwale ta fada maka alheri ne hakane, Allah ya sanya alkairi a tsakaninku.”

Hunayda Love and Romantic Love Story

 

Ya rasa gane abinda take nufi……Ganin yana kallonta yasa tace.” Ya aiki ina mutuminka Asp ina fatan kuna lafiya.”?

 

 

Hannunta ya rike da fadin.” Asp yana nan lafiya har ya bani sakon gaisuwarki amma da ba kiyi maganarsa ba na manta, sai kuma ni da nake cikin matsala.”

 

 

Tace.” Matsala kuma.”?

 

Kai ya daga mata kamar karamin yaro.

 

Ta zuba masa ido tana kallonsa.

 

Hannunta dake cikin nasa ya fara kokarin cusawa k’asan mararshi…….Tsigar jikinta ta tashi da sauri ta fizge hannun tana harararsa.

 

 

Ido jawur! yake kallonta, kafin yace.” Kin gane matsalar ko.”?

 

Tace.” Kai kam baka da matsala sai wannan.”?

 

Yace.” Ina dasu amma wannan itace a kan gaba.”

 

Ta’be bakinta kawai tayi ta d’auke kanta.

 

Duk ya rasa yanda zai yi baya so tana sha masa k’amshi! tabbas ya san da akwai wani abu a kasa.

 

Ganin abinda take yasa ya kama kansa, yayi kokarin danne kwad’ayinsa, saisaita muryarsa yayi kafin yace.” Ina Uwale take ne.”?

 

Ba tare da ta kalleshi ba tace.” Ta fita domin yin sallama da mutane.”

 

Ya mike ba tare da yace mata komai ba ya kama hanyar fita, kallo ta bishi dashi tana girgiza kanta.

 

 

Bata yarda ta zauna kusa dashi ba, a kusa da Uwale tayi zamanta suna hira, shi kuwa kamar maraya suka mayar dashi direba haushin hakan ya sanya bai sa musu baki a maganarsu ba, sai dai sa’i da lokaci yana amsa waya jefi-jefi! a haka suka isa gidan kowa da abunda ya dameshi.

 

A maimakon ya nufi side dinshi kawai sai ya bita nata, ta riga ta san bin diddigin da yake mata, haka kawai ta tsinci kanta da jin haushinsa.

 

 

A nan yayi wanka ya kimtsa ya fita ya siyo musu abinci, sai da ya kaiwa Uwale nata sannan yayi mata bankwana, koda ya fito kai tsaye sashen Gimbiyar ya nufa babu wani kuzarin kirki a tare dashi.

 

 

 

 

*Kada ki karanta min littafi ba tare da kin biya ba, kada ki saya ki fitar dashi, ‘yar uwa kada kiyi sharing, idan kina bukatar biyan kudin littafin #500 ne……0542382124….Binta umar gtbabk….Idan kati zaki turo sai kiyi min mgn ta WhatsApp da wannan number*

*07084653262*

*BINTA UMAR ABBALE*

[3/26, 9:55 PM] Matar Malam😊: _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number…… 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k’iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da ‘yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!…ga masu bukatar sari ko sayan d’aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi…….*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya ‘kare da ikon Allah._

 

 

 

Add Comment

Click here to post a comment