Littafan Hausa Novels

Abban Sojoji Hausa Novel Complete

Abban Sojoji Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

ABBAN SOJOJI

 

*The Father Of Soldiers*

 

ﻗﺼﺔ ﺣﺐ ﺭﻭﻣﺎﻧﺴﻴﺔ ﺑﻴﻦ ﺳﺤﺮﻳﺶ ﻭﺍﻟﺠﺮﺍﺡ ﺍﻟﻌﺎﻡ ﺭﺍﻓﻴﺖ

 

*Story & Written by*

*Hafsat Bature Muhammad*

 

BOSSLADY

 

_Sabuwar Marubuciya, mai tafe da sabon salo_

 

*Abban Sojoji part 2*

 

*EPISODE 1*

 

Meaning Of Name *AMANI* means *wish* arabic name ne na mata ina faɗin ma’anarsu ne saboda masu tambaya, sunaye ne masu kyau mutun zai iya amfani dashi in yana so wa baby girl ɗinsa

Abban sojoji

Ga masu buƙatar mallakar Littafin Abban Sojoji Book 2 (The Father Of Soldier) zasu tura 300 sannan akwai na V.I.P Su kuma 700 zuwa wannan Account Number 3196407426 (Bature Hafsat Muhammad) First Bank… Sai a tura evidence of payment Via 0810 3884440

A Sanadin Son Ki Hausa Novel Complete

Ruwan sama ake yi sosai garin, yanayin yayi wani irin daɗin gaske, ga wata irin ni’imtacciyar iska wadacciyar da ta gauraye ko’ina, wurin ƙarfe 5 na marece ne amma sai kayi tunanin dare ne sosai saboda Lullumin da garin yayi, a wannan yanayin kowa na ƙumshe a bedroom ɗinsa saman gadonsa, lullu6e da bargo, baka jin hayaniyar komai ko’ina tsit a cikin gidan

 

zaune suke acikin mota suna tattaunawa su biyu, Hafsat ce tare da wata Hamshaƙiyar mata wadda bansanta ba, jikinta na sanye da tsadadden leshi Ash colour, fara ce kana ganinta kasan taji hutu Over ya zauna mata, ita ce a mazaunin driver yayin da hafsat ɗin ke gefen ta suna tattauna wa,

Abban Sojoji Hausa Novel Complete

Hafsat ta natsu tana sauraronta ” Naci sa’a da nasamu address ɗinki kuma na same ki cikin sauƙi, kuma ina fata zaki taimaka mun wurin cimma burina,’ matar ta faɗi tana kallonta,

Hafsat tace “ina sauraronki me kike so inyi miki ne “?

Murmushi matar tasaki kafin tace “Kafin na faɗa miki abunda nakeso, pls ina so ki fara bani acct number ɗinki,”

Bin ta da kallo hafsat tayi cikin mamakin jin abunda matar tace,

Amma batayi musu ba, ta shiga karanto mata numbar acct ɗin, ita kuma tana kwashe wa a wayarta dake hannunta,

Bata jima da gama karanta mata numbar ba sai ga Alert ya shigo a wayarta ƙirrrr!

Cikin sauri hafsat tasa hannu ta ɗauki ƴar purse ɗinta dake asaman Laps ɗinta ajiye, ta zugeta ta ciro wayar jiki na rawa ta duba, gabanta ne taji ya faɗi rass !! Ganin Alert na 6millions abun kamar a mafarki take ganinsa

Cikin tsananin mamaki ta ɗago ta kalli matar tare da cewa “Wannan fa? Na menene?

dariya matar tayi kafin tace ” akwai wasu tagwayen Yara da Marshal Omar ya kawo gidan nan, Sunan su Hosana da Jahad,’

Jin sunan da ta ambata yasa hafsat kallonta cikin mamaki,.

Taci gaba da cewa “Ba wani aiki bane mai wahala, so nake subar gidan nan ! Suyi nesa da Marshal Omar……….’

Cike da mamaki hafsat ke kallonta , babban abunda ya ɗaure mata kai shine yadda akai tasan cewa Marshal Omar ya kawo yara acikin gidan,.

Daker ta iya cewa “Saboda Me za’ae hakan?

“Saboda basu da amfani,” matar ta bata amsa a taƙaice,

Shiru hafsat tayi tana kallonta acikin zuciyarta tana Was wasi akanta,

“Wacece ke? Taya akai kikasan sunan Tagwayen tare da kuma sunan Omer?

“Ba buƙatar wannan, Kawai kiyi mun abunda nace in aikina yayi kyau nayi maki alƙwarin zan ninka miki abunda na baki har sau uku,

 

Hafsat tace “To shikenan ni zan wuce ciki sai kin jini”

 

Murmushi matar tasaki tare da cewa “sai mun sake haɗuwa,”

fito wa hafsat tayi daga Motar ta rufe mata sannan ta wuce cikin gidan da hanzari saboda ruwan dake sauka ajikinta,

 

Yayin da ita kuma Matar taja motarta ta fuce daga gidan fuskarta ɗauke da murmushin nasara,

 

tana shiga cikin babban falon ba kowa kai tsaye bedroom ɗinta ta wuce, cire kayan jikinta tayi shaf shaf ta canza izuwa riga da wando, ta ɗaure gashin kanta a baya, tana tsaye gaban Mirror tana tunanin maganar Matar nan data kawo mata ziyara sai ga Aunty Babba ta faɗo ɗakin tana faɗin “Hafsat wacece waccan matar da tazo wurinki yanzu”?

Juyowa hafsat tayi tana kallonta tace “Nima bansanta ba address ɗina aka mata shine tazo da buƙatarta,”

“Wace irin buƙata kenan”? Aunty babba ta tambaya tana kallonta,

Hafsat tace “Tayi mun magana akan cewa tana so in raba twins ɗincan da Omar ma’ana subar gidan nan gaba ɗaya, Suyi nesa dashi”

tsoki aunty babba taja tare da cewa “Ita kuma wacece ita isasshiya? halan Omar take so ne shiyasa ta biyo ta wurinki?.

“Bana tunanin hakan, Nafi tunanin Tasan Yaran ne shiyasa take son azubar dasu,”

“To ke kuma kin amince da buƙatarta kenan”?

Murmushi hafsar tasaki tare da cewa “eh mommy na amince da hakan, saboda anan take ta bani miliyan shida kuma tace muddin aikinta yaci ka zata ninkamin abunda tabani ynx,”

tuni aunty babba ta haɗe fuska rai a6ace tace “Amma ke shashashar ina ce? Kawai daga zuwan mata sai ki amince mata da buƙatarta? matar nan fa Omar take so shiyasa takeson a salwantar mata dasu,”

“Koma dai menene Mommy ni bazan bari kuɗin nan su wuce ni ba, saboda ina cikin buƙatarsu, daddy baya sakarmun kuɗi yadda ya dace ke kuma tanadin ki na zuwa wurin bokane kema fa bakya bani ko sisi Burinki akan hayaam da Abrah ne,” .

Matsawa Aunty babba tayi kusa da ita tana cewa “Hafsat Anya kina cikin hayyacin ki kuwa? Ni kike faɗama haka”?

“Na faɗi wani abune daba dai dai ba? ta tambaya tana kallon mommyn nata, Ido cikin Ido

Sassauta Murya Aunty babba tayi a ƙoƙarinta nata fahimtar da hafsat tace “duk wannan tanadin da nake saboda kanmu ne fa ! Ƙaruwar mu ce, in har naci nasara akan burina Hayaam tasamu RAFAYET ita kuma Abra tasamu MARSHAL OMAR mune zamu ji daɗi, don haka am commanding u ki tattara kuɗin da tabaki ki mayar mata dasu yanzun nan !!!! ta faɗi a tsawace

Dariya hafsat ta kwashe da ita hada tafa hannu bayan ta tsagaita tace “Mommy kenan !! nima fa lashe Money ce kamarki, bazan bari garabasar nan ta wuce ni ba!! Akace da arziƙi a gidan wasu ƙwara agidanku, kai agidan nakuma kwara a ɗakinku, a ɗakinku ɗin ma ya faɗo akan ka, don haka ni baxan mayar mata da kuɗinta ba!!!!!!!!!

Gaba ɗaya hankalin aunty babba ya tashi don alamu sun nuna cewa Hafsat fa kamar bata cikin hayyacin ta, cikin ruɗi tace “Hafsat anya kina cikin Hayyacinki kuwa”?

Shu’umin murmushi hafsat tasaki sannan tace “Kwarai kuwa! nice dae ƴarki Hafsat ɗiyar general ishaq, jika ga Abban sojoji”

Jinjina kai aunty babba tayi tabbas an samu matsala, domin kuwa tasan Hafsat bazata ta6a fasa abunda tayi niya ba,

Huci kawai take yi tana jinjina kanta a ƙarshe ta fuce daga ɗakin,

Duk wannan suratan da Hafsat su kayi da aunty babba a kunnan Hosana wadda ke la6e a ƙopan ɗakin, jin Takon tafiyar Aunty babba yasa ta gudu izuwa cikin store ɗin da suke,

“Ina kika je hosana bakya jin magana ko? salon sai sun ganki? Mun samu yau sun ƙyale mu basuyi mana komai ba,

Jahad ce ke wannan maganar wadda ke atsaye tana kallon hosana,

Murya na rawa hosana tace “Jahad naji abunda su Hafsat ke cewa ita da Momynta,”

“Me suke cewa ne”? Ta tambaya tare da matsawa kusa da Hosanar don taji dakyau,

Hosana ta kora mata bayani tun daga farko har ƙarshe,

Jahad ta jinjina kai tare da cewa “Ashe buri yayi kama da mutun, shiyasa ta tsane mu kenan saboda tana tunanin cewa Omar zai iya son ɗaya daga cikinmu, ran nan tace mun batason mune saboda mun shiga tsakaninta da abun harin ta, Yanzu nagane inda ta dosa, To amma wacece matar da hafsat ta haɗu da ita yau? Wadda ke son A zubar mata damu!?

“Ni inaji araina jahad so suke su rabamu da ƴa’ƴa Omar kawai,” hosana ce tayi maganar ido cike tab da kwalla don bata son duk wani abu yanzu dazai rabasu da Omar,

“Insha Allah burinsu bazai ta6a cika ba Hosana, baza su iya raba mu ba da yaya omar ɗinmu,” tayi maganar tare da janyo hosana suka rungume junan su

__________________________________________

 

Tuni sun kammala aikin su na dinner, har sun kammala jerawa a dining Kowa ya bama cikinsa an ware, yanzu gidan ya ragu ba laifi kasancewar tun week ɗin daya wuce aka tura mutun Huɗu Aiki, Irfan jabeer, khaleed da Fawan duk basa nan, yanzu wanda suka ragu Acikin gidan Haroon, twins, junaid, Sai Marshal Omar da Sgr duk da basu cika zama cikin gidan ba suma, always working saboda suna bada gudummuwa sosai shiyasa koda yaushe suna headquater ɗinsu don ana buƙatarsu sosai game da insecurity ɗin qasar tamu, kasancewarsu kwararrune a6angaren aikin soja dama sun kasance international Armies, kowace ƙasa aduniya suna bada gudummuwarsu wurin kame tantirai sune maganin ƴan Iska, shiyasa sunansu ya shahara a faɗin duniya duk inda suka je, ansansu girmamasu ake gani kamar kamar me (Tiger da Lion) Kenan ba wasa

Abban Sojoji Hausa Novel Complete

SEHRISH

Shiga bedroom ɗinta tayi Wurin isha prayer, duk ta rame kamar ba Reeshi ba, alwala ta ɗaure a toilet, ta shimfiɗa sallaya, ta gabatar da salla, bayan ta kammala ta naɗe hijab da sallayar ta tura a wardrobe ɗinta, komai nata a slow take yinshi saboda rashin kwarin jikinta da fargabar da take fama dashi na Haroon,

 

Haye wa tayi saman gadonta tare da janyo pillow ta rungume tunani kala kala a ranta, hawaye ne suka soma gangarowa daga idonta sbd tuna yadda haroon ke ta6a jikinta, hannu tasa tana share su, daga bisa ni tayi lamo tana tunanin duniya,

Tana cikin wannan halin taji an kwankwasa ƙofa, shiru tayi bata Yi magana ba cike da tsoron waye ke mata knocking, ji tayi an sake buga ƙopar muryar na rawa tace “wanene”?

Muryar junaid taji yana cewa “Sehrish ni ne,”

Ajiyar zuciya tasaki jiki na rawa ta sauko tare da karasawa wurin kopar ta buɗe,

Gabanta ne yayi mugun faɗuwa ganin haroon hankali tashe tace “Kaineeee !!!!” a tsorace tayi maganar jikinta na rawa,.

Fashewe da dariya haroon yayi tare da wuce ta yashi ga ciki yana cewa “ƴar shila ni ne, ae nasan bazaki buɗe ba shiyasa nayi maki muryar junaid don na lura kuna good time dashi,’

juyowa tayi tana bin shi da kallo a razane,.

“Me ya kawo ka”!?

“Abunda yasa ba kawo ni, Yau nazo ne ayi ta taƙare, Haƙƙina nake son ki bani,”

Cikin shessheƙar kuka sehrish tace “Me kake nufi wai !!! Wani haƙƙi ka ke dashi akaina? Dan Allah kabarni nayi rayuwata cikin salama !! Ka rabu dani mana !!

ta6e baki haroon yayi tare da cewa “Na amince zan rabu dake, amma bisa sharaɗi ɗaya”? Ya faɗi yana kallonta fuska a ɗaure, a lokacin tadawo tsaye front of side drawer ɗinta tana facing ɗinshi,

Gabanta na faɗuwa tace “Menene shi”? Cikin sanyin murya tayi maganar

Haroon yace “Your Virgin!! shine abunda nake so,and if u do so i wll be out of ur life”

Fashewa da kuka sehrish tayi cikin tsananin jin ƙunci da raɗaɗi aranta, tuni zufa tagama wanko mata kamar wadda aka tsamo daga cikin ruwa, tsanar haroon take ji kamar kamar me, tarasa amsar da zata bashi sai faman kerma take,

A tsawace haroon yace “Ke !!! Ki amsa mun kin amince ko baki amince ba”!?

A Firgice tace “Na’amince” ita kanta batasan ta bashi amsar ba saboda tsoratar da tayi da tsawarsa,

Wani irin shu’umin murmushi haroon yasaki, bin shi da kallo tayi ganin yasa hannu yana zare belt ɗin wandonsa, tuni ta runtse ido ganin gashin jikin shi, bakomai ya faɗo mata arai ba fa ce Sgr shine namijin da take so tafara kasancewa dashi arayuwarta bata buƙatar wani namiji in ba shi ba, shi take so ta mallakawa komai nata muddin ta mallake sa,

Jiki na rawa ta zura hannunta ta baya, taci sa’ar damƙar fititalar Kwan dake gefen gadonta, kafin haroon ya ɗago ta daddage da iya ƙarfin ta na ƙarshe ta ɗago da fitilar dake hannunta ta kwaɗa masa a tsakiyar kai !!!!! Ji kake KWASSS !!! A razane haroon ya ɗago jin saukar fitilar kafin yayi wani yunƙuri tuni Sehrish tabi ta gefensa ta watsa da gudu sai cikin toilet ta datse ƙopa sosai, ta sulale daga jikin ƙopan zuƙunne tana kuka don tasan dole haroon ya ɗauki matakin abunda tayi masa,

Ba ƙaramin buguwa haroon yayi ba, don wurin harya fashe Ae kuwa rai a tsananin 6ace yace “Ke don ubanki ni kika fasa ma kai”?

Sehrish dake acikin toilet murya cike da kuka tace “Ba dai ubana ba sai don Uban Mai zagi !! Fasiƙi ɗan iska insha Allah bazaka ta6a cin nasara akaina ba, sai Allah ya nuna maka iyakarka, wulaƙantacce kawai ƙazami mai warin baki,”

Tuni idon haroon sunyi jawur kamar garwashin wuta, ransa yayi mugun 6aci bai ta6a tunanin yarinyar zata iya mayar masa da martani ba, amma sai gashi yau ta zage shi tass,

“Bazan ƙyaleki ba, sai na wulaƙanta rayuwarki ba dai kina acikin gidan nan ba kuma zaki fito ba, zamu haɗu ne wlh,” Ya faɗi tare da tunkarar hanyar fita yana mayar da belt ɗin wandonsa daya fara cirewa,.(ba’aci nasara)

Sehrish batayi shiru da bakin ta ba taci gaba da cewa ” Ta Allah bata ka ba wlh !! Mugu azzalumi mummuna kawai, da wasu idanuwan ka kamar na Mujiya ni ina kokwanton Cewa anya kai Jinin Abban sojoji ne !! Sbd duk ƴa’ƴansa ba Fasiƙi irinka,”

Jinjina kai haroon yayi kawai yana huci, ya tura ƙopar ɗakin ya fuce,

 

Wani sabon kukan ta sake fashewa dashi, tana faɗin “wayyo Allah na nasan haroon baxai ƙyale ni ba, nashiga uku……..’

Jiki na rawa ta miƙe ta nufi wurin bathroom cabinet ɗinta, akwai wasu Chemicals dake ajiye cikin toilet ɗin masu illah ga jikin mutun tamkar poison suke, ta riga ta yankewa kanta shawarar kwara ta kashe kanta ta huta da fitinar haroon,

Hannunta har kerma yake yi, wata ƙaramar roba ta ɗauko mai ɗauke da chemical ɗin, buɗe murfin tayi yayin da idonta ke zubar da hayawe, bakowa ya faɗo mata arai ba face Hosana Jahad, junaid, Aunty azmee uwa uba Burin ranta, yanzu shikenan duk zata rasa su? Zata mutu tabarsu?

Runtse idonta tayi aranta tana faɗin “bani da wata manufa face wannan, kuyi haƙuri ku yafe mun bazan Iya cigaba da rayuwa a wannan duniyar ba mai cike da tashin hankali, ban ta6a cutar da kowa ba, amma gashi wani nason cutar da rayuwata …………………”

Cikin sauri ta shiga zazzaga hodar abakinta

 

A dai dai lokacin Motocin Sgr da marshal Omar suka shigo cikin gidan atare jiniyarsu ta karaɗe ko’ina har cikin kunnan Sehrish

Zuciyarta ce taji tayi wani irin bugu, nan take kuma zuciyarta tace “Yanzu kin amince ki mutu baki cika burinki ba!? ke fa musulma ce ! Kin kuma son hukuncin wanda ya kashe kansa da gangan!!

Runtse idonta tayi hawaye na zuba, fuskar sgr kawai take tunawa da fuskar su hosana da jahad,

“Ina son sake sashi a idona,” ta furta da wani irin sound, nan take tayi wurgi da robar chemical ɗin dake hannunta, cikin hanzari ta shiga amayar da wanda ke bakinta agaban basin, fanfo ta kunna tashiga kuskure bakinta da hanzari ta kora aman, sannan ta wanke face ɗinta ta fito,

tana tafiya zuciyarta na ƙara bata ƙwarin guiwa da cewa “Saboda wani shashasha zaki halaka kan ki, share hawayenki sehrish kina da damar rayuwa, wani banza bai isa ya tarwatsa miki burinki ba,”

Gyara jikinta ta shiga yi saboda tana son zuwa kai mishi dinner ɗinshi shi da Omar don ta son da yunwa suka dawo, duk da tana tsoran kada suci karo da haroon a fitarta,

dama riga da wando ne ajikinta, gashin bakinta kawai ta manna, ta gyara hular kanta da mayafin da take naɗe hular dashi, bayan ta kammala ta buɗe kopan cikin fargabar ta fuce,.

Ko’ina haske fauuu gidan cikin sanɗa ta wuce kitchen taji sanyi aranta ganin babu kowa,

Cikin hanzari ta shirya ma Omar nasa a tray, a palor ɗinsa takai masa babu kowa aciki alamar yana cikin bedroom ɗinsa, ajiye masa kawai tayi ta fuce, izuwa kitchen ta sake shirya wani a tray sannan ta wuce upstairs part ɗin BABBAN YAYA

 

Haryanzu jikinta kerma yake, kuma bata fasa maganar shan poison ɗin nan ba, burinta ta sanya Sgr a idonta 4 the last time before tabar duniyar, Baiwar Allah

Babu kowa a palor ɗinsa tsit kake ji sai ƙamshin dake tashi, shiga ciki tayi ta ajiye masa a saman table ɗinsa,

Tsayawa tayi tana faman sauke ajiyar zuciya yayin da idonta ke cike taf da hawaye, kamar daga sama taji muryarsa ta cikin bedroom ɗinsa yana faɗin “who’s There”?

Runtse idonta tayi saboda jin sanyayyiyar muryarsa, daker ta dai daita natsuwarta tace “Tukur ne mai aiki,”

Voice ɗinsa tasake ji yace “Come In! i wanna see YOU Right now,” zaro ido sehrish tayi jin abunda yace wato ta shigo ciki yana som ganinta.

 

Dake ta dai dai ta natsuwarta, ta tafi izuwa cikin bedroom ɗinsa kamar yarda ya umarta ta shiga da sallama”Assalamu alaikum”

“Wa’alaikum salam” ya amsa mata,

tsaye yake agaban mirror jikinsa sanye da sleeping dress riga da wando Milk colour masu ɗigon² baƙi ajikinsu ba ƙaramin kyau su kayi mishi ba, turarurruka yake ta fesa ma jikinsa,

Sam tagaza janye idonta akan shi daker ta iya cewa “barka da dare” ya amsa mata da “Yawwa” sannan ta ƙara da cewa “Gani”

Hannu yakai ya ɗauki kalbar turaren SHUMUKH ya feshe shi sannan ya mayar ya ɗauki wani turaren na Jar yana fesawa, mutun ne mai tsananin son ƙamshi shiyasa baya gajiya da bin jikinsa da turare,

Shiru sehrish tayi zuciyarta na ɗar ɗar, kusan 15 minsa sannan Boss Man ɗin yace “Ni zan zo ne”? Ya tambaya yana jiran amsa,

Cikin sauri sehrish ta ƙarasa hankali atashe ta tsaya daga bayansa jikinta na rawa,

Cikin natsuwa yaso ma magana” Wacece ke”?

Waro ido waje sehrish tayi jin abunda yace murya na rawa tace “Ni…..mai…..aiki…ne ….” a wani irin slow sgr ya juyo kai tsaye ya tunkare ta gadan gadan, a tsorace sehrish ke ja da baya tana kallonsa tuni zufa ta gama wanko mata sharkaf a jikinta,

Abban Sojoji Hausa Novel Complete

Sam idonsa basa a kanta ƙasa suke, har sai da suka ƙurewa bangon gaba ɗaya, yarfa hannu sehrish ta shiga yi a tsananin tsorace take karanto addu’o’in da duk suka zo mata abakinta, kuma abayyane take yi saboda tsaban ruɗi tuni ƴan hanjin cikinta sun motsa, gaba ɗaya jikinta rawa yake yi kamar wadda sanyi yakama,

Hannunsa yasa ya daki wall ɗin data ke manne ajikinsa ya aza hannun anan jikin bangon ya dafe sannan yace “ƙarya ke bana so arayuwata, am gonna ask u some questions idan aka min ƙarya za’a fuskanci matsala,”

Ya faɗi yayin da idonsa ke a lumshe tamkar a datse suke ba don komai ba sai don gudun kada mai aikin ya Sume a ƙaro na biyu saboda launin ƙwayar idonsa dake razanar da shi, .

Kallon shi kawai take yi zuciyarta na bugawa da ƙarfi, daker take haɗiye yawu ga wani fitsari daya matse ta tunda taji ya ambace ta da mace tasan cewa ya gano ta kenan,

“maca ce ko Namiji”? ya tambaya yana jiran amsa,

Shiru tayi tana tunanin amsar da zata bashi, muddin tamasa ƙarya wannan ba ƙaramin shaqa zata sha ba,

Wannan shirun da tayi masa shiya fusata shi, buɗe Blue eyes ɗinsa yayi duka akanta , ta firgita sosai amma sam ta sanƙare ta gaza motsi da alama suman tsaye tayi

Hannunsa yasa ya damƙi hular kan sehrish yayi wurgi da ita tare da mayafin duka, nan take sumar kanta tasoma warwarowa tana saukowa saman kafaɗarta, kyakkyawan sumar kanta mai matuƙan kyan gaske ga laushi,

mayar da hannunsa yayi saman gashin bakin da take sawa ya cire shi shima, nan take ainihin kyakkwar fuskar reesh ta bayyana a matsayim mace

sam fa bata motsi idonta sun kakkafe sun ƙame, kamar wata saƙago haka tayi,

jinjina kai sgr yayi maganar Adams ta tabbata, yayi mamakin ganin yarinya ƙarama kamar wannan da ƙarfin halin Yin shigar Maza tazo gidan sojoji aiki, ko nawa aka biyata don tayi hakan? Ya tambaya aransa, sam shi baya tunanin ta haura 12years saboda ƙarantarta dayake gani agabansa Ko shouder ɗinsa tsayin sehrish bai kai ba, daga tsaye inda yake yana kallon tsakiyar kanta saboda ba ƙaramin tsayine dashi ba, kowa yazo gabansa kallon ƙarami yake masa,

Janye hannunsa yayi daga jikin wall ɗin da sehrish take sannan yayi tattaki izuwa inda fridge ɗinsa yake, buɗewa yayi ya ɗauko bottle water mai sanyi sannan ya dawo inda take tsaye,

ya buɗe murfin ya yayyafa mata, a wani irin firgice sehrish ta girgiza ta dawo in sense ɗinsa, sai faman zazzare kyawawan idanunta take, bin chest ɗinsa tayi da kallo izuwa face ɗinsa cikin tsoro, hannu tasa ta shafa sumar kanta gabanta ne ya faɗi jin wayam babu yar hularta, hankali tashe ta wurga idonta inda sgr yayi watsi dasu………nan fa tashiga faɗin “innalallahi wa’inna ilaihirraji’un dan Allah kayi haƙuri…..nashiga ukuna……..’ tana kuka tana magana , gaba ɗaya yayi mata rumfa tamkar Zaki haka take ganin sa agabanta

Abban Sojoji Hausa Novel Complete

Idonsa na kumshe yana sauraronta left hands ɗinsa na riƙe da bottle water ɗin, yayin da ɗayan hannun kuma ya mayar dashi jikin bangon ya dafa, sehrish kuma na agabansa suna fuskantar juna,

“haɗiye wannan kukan bana so” cikin hanzari sehrish ta dakatar da kukan tashiga taitayinta, bakomai take kallo ba fa ce damtsen hannunsa, tunani kawai take yarda zai kai mata naushi tabbas tasan sai dai Uwarta ta haifi wata (Hafsat bature ana magana)

 

 

 

Name: Abban Sojoji Hausa Novel Complete
File Type: Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML
Uploaded By: Hausa Novels Team
Category: Hausa Novels Documents
Novel Author: Null
Novel Price: Free
Last Modified: October, 2022

 




Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe


Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…


https://play.google.com/store/apps/details?id=mynovels.com.ng.gidanuncle

Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram



Powered by: www.hausanovel.org.ng

Add Comment

Click here to post a comment