A Sanadin Son Ki Hausa Novel Complete
*A SANADIN SON KI*
*Written by*
Aishat A Muh’d
♻£xclusive Writers Forum
*Dedicated to my Sadeey (saNaz)*
*PAGE 1-2*
Wata mata ce durk’ushe a filin tsakar gidan tana faman risgar kuka, har da shashshak’a kamar zata sume saboda tsabar kukan da take yi, sakamakon fad’an da mijin ta yake mata, gefe d’aya kuma yaran ta ne su biyu namiji da mace suna rungume da junan su, suna taya kan su da mahaifiyar su kukan tausayin kansu.
Tsinkar muryar mahaifin nasu naji cikin tsantsar 6acin rai da rashin mutunci yake cewa
” tun da abin haka ne zan tafi na bar muku garin gaba d’aya, na sha fad’a miki ni bana son haihuwa kwata kwata, ban shirya yin ta yanzu ba saboda bana son ta, ga kuma shegen bak’in talaucin da muke ciki, amman ke kamar kaza kina haihuwa babu dad’e wa ki dad’a samun wani cikin ni na gaji ”
Ya k’arasa fad’i yana wani sauke numfashi, sakamakon hayagagar fad’an da ya gama yi cikin d’aga murya da tsawa, hararar matar tashi yake da ‘ya’yan nashi, zuciyar shi cike da mugun tsanar su, ji yake kamar ya shak’e su, su mutu ko ya huta da ganin su.
Cikin shashshak’ar kuka matar tace
“Kayi hak’uri maigida, ni kaina ba ni na bawa kaina haihuwar ba, Allah ne ya bani su taya zan butulce mishi wajen zubar da cikin da ba shege ba ne, ka tuna haihuwa rahma ce wasu da kud’in su nema suke basu samu ba, amman kai da Allah ya bawa kyauta kana neman butulce mishi”
Ko gama rufe bakin ta bata yi ba ya d’auke ta da wani azababban mari har guda biyu bisa kyakkyawar fuskar ta, sake durk’ushe wa tayi tana rik’e da fuskar ta inda ya mare ta, hawaye ne kawai yake zuba a idanun ta.
Nuna ta yayi da d’an yatsan shi, cikin masifa yace “bana buk’atar jin shawarar ki ko wa’azin ki, idan baki bi maganar da na fad’a miki na ki zubar da wannan cikin ba, to wallahi zan bar garin don ban shirya rainon ‘ya’ya ba, naji ma da uban talaucin da ya dame ni”
Yana gama fad’in haka ya juyo kan yaran, tsawa ya kwantsama musu ba shiri suka shige d’akin uwar ta su da gudu, jikin su na 6ari na tsoron mahaifin nasu.
Tsaki yaja tare da cewa “shegun ‘ya’ya da munafurcin tsiya da sun ga uwar su na kuka, su ma zasu fara kukan ‘yan iska kawai ”
Yana k’arasa fad’in haka ya sake makawa matar tashi harara tare da jan tsaki ya kad’a rigar shi ya fice fuuuu a fusace kamar ya hantsila saboda sauri.
Samu tsofaffin hausa novels wattpad
A hankali yaran suka d’aga labulen d’akin suna lek’en ko mahaifin nasu ya tafi, saboda jin shirun da suka ji, ganin ya fita ne yasa su fito wa da sauri suka nufi inda mahaifiyar su take tsugunne tana kukan nata.
Rungume ta suka yi suna rarrashin ta da tayi hak’uri ta daina kuka, daman sune masu rarrashin nata idan uban nasu ya gama yi mata rashin mutunci.
Dak’yar ta iya mik’e wa tsaye suka shiga cikin d’aki, zama suka yi akan tsohuwar tabarmar su wadda ke shimfid’e a k’asa, kallon yaran nata tayi cikin matuk’ar tsantsar kaunar su tare da mugun tausayin su, ta kamo hannun su ta had’a waje d’aya tare da bud’e bakin ta tace
“Aliyu ga amanar Suhaima nan ko da bayan rai na ina son ka kular min da ita, bana son tayi kukan maraicin na, ina son ku tsaya tsayin daka ku nemi ilimi saboda inganta rayuwar ku ko da bana raye, ina son mahaifin ku yayi alfahari da ku a gaba, ku kasance cikin yi wa mahaifin ku biyayya a duk abin da yace muku, ku cigaba da addu’a watarana sai labari komai zai zo ya wuce kamar ba’a yi ba.”
Cikin kuka Aliyu yace
” Umma ki daina furta cewa zaki mutu ki bar mu, zamu rayu da ke Umma insha Allah, kuma zan rik’e k’anwa ta da kyau zan kula ta da ita Umma duk wani kyautata wa da bata farin ciki zan bawa Suhaima a cikin rayuwar ta.”
Ya k’arasa fad’i hawaye na zuba a idanun shi, cikin zuciyar shi tsanar mahaifin shi taf a ciki, Suhaima da bani wayo ne da ita ba sosai, kallon su kawai take tana kuka.
Nan Umma ta janyo Suhaima jikin ta, rarrashin ta take har ta yi shiru sai sauke ajiyar zuciya da take, kafin kuma ta bud’e baki tace
“Umma ni yunwa na ke ji.”
Umma kallon Aliyu take shima kallon Umman yake, cikin zuciyar su suna tunanin me zasu bawa Suhaima a yanzu taci, don basu da komai a gidan daman wani lokacin Aliyu ne yake fita yin ‘yar sana’a ta k’arfi ya nemo musu abin da zasu ci, idan kuwa ta uban nasu ne kuwa gwara su mutu da yunwa akan ya basu abin da zasu ci.
Gaba d’aya ba wanda yayi k’arfin halin bawa Suhaima amsa, jin haka ya sanya ta fashe da kuka don ko karya wa basu yi ba gashi yanzu azahar tana kok’arin yi, cikin rarrashi Aliyu ya janyo hannun ta yana goge mata hawayen fuskar ta yace
“yi hak’uri ‘yar k’anwa ta yanzu zan fita na samo miki abin da zaki ci, amman kada kiyi wa Umma kuka kin ji ”
Gid’a kanta tayi tana mai had’iye kukan nata, da sauri Aliyu ya fita daga d’akin, yayin da Umman ta bishi da kallon tausayi, yaron da bai fi ace yana k’ark’arshin kulawar iyayen shi ba amman shine yake kula da kanshi, mahaifiyar da k’anwar shi, saboda rashin dace da samun managarcin uba a gare su.
Tun Suhaima na jiran Aliyu har bacci yayi awon gaba da ita a jikin Umma tana mai tsotsan ‘yan yatsun ta a bakin ta, sai da bacci yayi k’arfi sannan Umma tayi mata shimfid’a ta kwantar da ita.
Tashi tayi ta fito zuwa tsakar gidan tsintsinya ta d’auka ta laushi ta fara share filin tsakar gidan, tana yin sharar idanun ta na zubar hawayen tausayin kansu, wani 6angare na cikin zuciyar ta addu’a take yi tare da godewa Allah a halin da ta tsinci kanta a ciki, k’addarar tace ta auren wannan mugun mijin nata mara tausayi, mai butulce wa Allah da baiwar ‘ya’ya biyu da ya bashi ga cikin na uku a jikin ta.
Tun da Aliyu ya fita bai dawo gidan ba sai daf da mangarib, hannun shi rik’e da ‘yar k’aramar leda bak’a, Suhaima na ganin shi ta mik’e da gudu ta k’arasa inda yake tare da kar6ar ledar hannun shi tana duba wa.
Garin kwaki ne a ciki sai k’ullin sugar, kallon shi tayi fuskar ta d’auke da murmishi tace
“Yaya mun gode Allah yasa ka samu sana’a kana samun kud’i kamar yanda Yayan k’awata yake aiki yana samun kud’i yana siyo musu abin dad’i ”
Cikin murmishi ya shafa kanta tare da cewa “Amin ‘yar k’anwa ta ki cigaba da yiwa Yayan ki addu’a da Umman ki .”
“Toh Yaya ina yi kullum idan nayi sallah, amman bazan yiwa baba ba tun da shi mugu ne yana dukan Umman mu, kuma yana zagin mu da dukan mu kullum, nima na tsane shi kamar yanda yace baya son mu ya tsane m…….. ”
Kafin ta k’arasa fad’in maganar taji an zabga mata wani wawan mari wanda yasa ta hantsila k’asa, ledar garin kwakin ta baje a k’asa ta tarwatse cikin dandaryar k’asar tsakar gidan.
Ashe basu ankara da shigowar baban nasu ba gidan, yaji abin da Suhaima ta fad’a shine yayi mata wannan marin da ko babba aka yiwa sai haka, cikin rashin imani ya kama Suhaima ya hau dukan ta kamar Allah ya aiko shi, Umma tana d’aki idar da sallahr mangarib d’in da tayi kenan tana sauri ta fito don ta jawa Suhaima kunne ta daina wad’annan maganganun, don lokacin da dawowar uban su gida yayi, sai kawai taji saukar dukan da yake yiwa Suhaima runtse idon ta tayi da k’arfi hawaye na fita a cikin su tana mai addu’ar Allah yasa kada yayi mata bugun da zai illata ta.
Yana dukan ta cikin fushi yana cewa “shegiya tsinanniya daman ni ai ba son ku nake ba, da zaki ce baza ki min addu’a ba sai uwar ki da Yayan ki, na tsane ku bazan ta6a kaunar ku ‘yan iska matsiyata ”
Cikin kuka Aliyu yace “Don Allah Baba kayi hak’uri ka dai na dukan ta, ka ga Suhaima yarinya ce k’arama ba zata jure dukan nan ba ”
Sakin Suhaima yayi yana haki kamar wanda yake jibgar k’atu, harara ya dalla wa Aliyu tare da cewa
“Don uwar ka ni zaka fad’a wa gaskiya koh ?”
Kafin Aliyu ya ankara tuni Baban ya kawo mishi duka nan ya had’a su ya dunga duka kamar Allah ya aiko shi, sai da yayi musu lilis tukunna ya ce
” yanzu na fara dukan ku ‘yan iska, Allah yasa ku mutu na huta da ganin ku”
Da sauri Umma ta runtse idon ta tana rushe wa da kuka jin mummunan kalaman da uban su yake yiwa ‘ya’yan ta wanda ba yau ta saba jin su a bakin shi ba.
Yana gama fad’in haka ya fice daga gidan yana fad’a kamar wani ta6a66e, Umma tana jin yana fita ta fito waje da sauri zuwa wurin ‘ya’yan nata da suke kwance magashiyan a k’asa suna kukan azabar dukan da aka yi musu.
Nan Umma ta rasa me zata yi musu kawai sai ta had’a ruwa mai d’umi ta fara yiwa Suhaima wanka, daman ta d’ora ruwan tun kafin mangarib, sai da ta gama yi mata wanka ta gasa mata jikin ta, tukunna ta kai ta d’aki ta kwantar da ita, sannan ta dawo wajen Aliyu ta kai shi band’aki tare da ruwan wanka tace
“kayi hak’uri Aliyu na, maza kayi wanka ka gasa jikin ka ”
Gid’a mata kai kawai ya iya yi, sannan ta fito ta tattara garin kwakin da ya zube ta tsince shi tukunna ta jik’a musu.
Dawo wa d’akin tayi ta tashi Suhaima sanya mata kaya tayi sannan ta zuba mata garin a kofi ta mik’a mata, ai kuwa da sauri ta kar6a ta hau shan shi babu k’akk’auta wa.
Ido Umma ta tsura mata tana kallon kumbararriyar fuskar ta ta zuciyar ta fal tausayin su, tana nan zaune Aliyu ya shigo d’akin dakyar ya iya yin sallah sannan ya zauna, mik’a mishi nashi garin Umma tayi girgiza kanshi yayi yana cewa
“Umma ki sha kawai na k’oshi ”
Girgiza kanta ita ma tayi idanun ta fal hawaye tace
“A’a Aliyu ka kar6a kasha idan kana son ganin kwanciyar hankali na ”
Bashi da yanda zai yi ya kar6a ya fara sha a nutse, ita ma Umma ta d’auki ragowar tana sha, bankad’a labulen d’akin aka yi tare da shigowa ba sallama, babu wanda ya d’ago kan shi ya kalli kofar saboda sun san wane mai shigo wa d’akin a haka.
Ko kallon su bai yi ba ya shige k’uryar d’akin ya zauna saman gadon tare da bud’e kunshin tsire da gurasar da ya siyo ya hau cin abin shi hankali kwance, tuni d’akin ya d’umame da k’amshin naman da gurasar suka hau had’iyar yawu dukanin su har da Umma.
Abin ka da mai ciki akwai kwad’ayi gashi ba ci ake ba nan ta shiga had’iyar yawu akai akai haka ma Suhaima, kallon Aliyu yake yi zuciyar shi tana zafi na tsanar halayyan mahaifin nashi, tashi tsaye yayi tare da cewa
“Umma zan kwanta sai da safe ”
Don idan bai fita daga d’akin nan ba zai iya had’iyar zuciya ya mutu saboda tsabar bak’in ciki, kallon shi Umma tayi tare da cewa
“Allah ya tashe mu lafia ”
“Amin ”
Yace tare da fice wa a fusace.
“shege mai zuciyar tsiya da bak’in hali ”
Babu wanda ya tanka mishi har Suhaima bacci ya d’auke ta tana had’iyar yawu na son cin naman, kwantar da ita tayi tare da lullu6e ta da zani saboda lokacin hunturu ne.
Tashi tayi tare da nufar gefen gadon k’arfen nata ta kwanta a can k’arshe tana mai tunanin makomar rayuwar su a gaba, ga cikin ta da yake k’ugin yunwa da haka bacci ya fara d’aukan ta, can cikin baccin nata taji mijin nata na lalubar ta alamar akwai abin da yake nema a wajen ta, wasu hawaye ne masu zafi suka dunga fita a idanun ta, duk dare ta saba da wannan halin mijin nata gashi ba abinci kirki yake basu ba, shi yasa kullum take tashi jiki ba kwari a gala6aice, tana kuka shi kuma yana sha’anin gaban shi har zuwa lokacin da ya rabu da ita ya juya mata baya, ba dad’e wa ta fara jin saukar minsharin shi, dakyar ta iya mik’e wa ta fito zuwa band’aki tayi wanka don bata iya bacci a haka, tana fito wa ta ga Aliyu zaune a tsakiyar gidan ga tsananin sanyin da ake zabga wa cikin mamaki tace
“Aliyu lafiya? ”
D’ago kanshi yayi tare da cewa “Umma na kasa bacci ne, zuciya ta rad’ad’i take min ”
Ya k’arasa fad’a hawaye na fita a idon shi, cikin tausayin shi tace
“kayi hak’uri Aliyu komai tsanani yana tare da sauk’i, bana son kana sa damuwa a ran ka wani ciwon ya kama min kai, kasan kai ne mai taimakon mu, yanzu tashi kayi alwala kayi sallah tare da addu’a, ka mik’a wa Allah buk’atun ka ”
Tana nan tsaye yayi alwala sannan ya shige d’akin shi, tukunna ta juya ta shige d’akin ta kwanta, jikin ta babu k’arfi da ita ma nafilar zata yi ta fad’a wa Allah matsalar ta, amman duk da haka sai da ta janyo carbi ta fara istigifari tare da salatin Annabi (SAW), da haka bacci mai k’arfi ya d’auke ta………..
*** **** ***
*ASALIN LABARIN SU*
Aishat A Muh’d ✍🏻
[2/4, 11:28 AM] Aıʂɧąɬ A Mųɧ’ɖ ✍🏻: 💝 *A SANADIN SON KI*💝
*written by*
Aishat A Muh’d
♻ £xclusive Writers Forum
*Dedicated to My Sadeey (SaNaz)*
*PAGE 3-4*
Umaru direba miji ne a wurin Fatima, auren so da kauna suka yi don sai da suka d’an jima suna soyayya kafin su yi aure.
Bayan sun yi aure ne suna zaman su lafia cike da so da kulawar junan su, don ma bai fiye zama a gida ba tun da direba ne shi suna tafiye tafiye zuwa garuruwa daban daban, amman hakan bai hana shi kula da ita ba sosai kwatsam ana haka sai Fatima ta samu ciki tun daga lokacin ta rasa gane kan Umaru don gaba d’aya ya canja mata, duk wata kulawa da yake bata ya bari.
Saboda sam shi baya son yara gaba d’aya wahala ne rainon su kawai, yayi rarrashin da ban bakin don kawai Fatima ta yarda a zubar, amman sam tak’i yarda saboda tana matuk’ar kaunar yara sosai, ganin tak’i yarda da buk’atar shi na zubar da cikin yasa shi fara gallaza mata tare da yi mata wulak’anci da rashin mutunci kala kala.
Amman duk Fatima ta shanye wannan wahalar da yake bata har zuwa lokacin da Allah ya sauke ta lafiya ta samu d’a namiji inda ya ci sunan shi Aliyu, saboda rashin babu ko suna ba’a yi ba balle yiwa yaro yanka kamar yanda ake yi a al’adance, saboda iyayen Fatima basu da k’arfi su ma kuma waje ba d’aya ba don suna da d’an nisa a tsakanin su, tun kafin ta haihu da Umaru ya sanya k’afa ya bar garin bai dawo ba har sai da tayi wajen wata biyu da haihuwa sannan ya dawo duk da kuwa yaji labarin haihuwar.
Nan ya bi ya tsani Aliyu ko kad’an baya kaunar yaron, ga zafin talauci da ya kunno mishi kai saboda motar da yake aiki da ita mai shi ya kwace abar shi, sai buga buga da yake faman yi.
Aliyu na da watanni 10 cif, Fatima ta sake samun wani cikin nan Umaru bak’in ciki ya isheshi, a lokacin babu irin cin mutuncin da bai yiwa Fatima daga k’arshe sai da yasan yanda yayi ya zuba mata maganin zubar da ciki a lemo, ya bata tasha babu dad’e wa ciki ya zube nan farinciki fal cikin zuciyar shi, yayin da Fatima bata zarge shi ba ta d’auka kawai 6ari ne tayi nan ta cigaba da rainon Aliyu wanda uban bai ta6a d’aukan shi ba, ko kallon mutunci baya yi mishi saboda tsabar tsanar da yayi mishi kamar ba shine uban shi ba.
Bayan zubewar ciki ne ya dawo da d’an bata kulawa kafin daga k’arshe kuma wani cikin ya sake bayyana a jikin Fatima, wannan karon ma zubar mata da cikin yayi wanda sai a lokacin Fatima ta ankara da hakan, nan tayi kukan bak’in ciki da takaici na abin da mijin nata yake yi mata na mugunta.
Sai da Umaru ya zubar wa mata da ciki sau uku bayan haihuwar Aliyu, ana hud’un ne kuma bai samu nasarar zubar wa ba har aka haifo Suhaima, sai da Suhaima tayi shekara 5 sannan ta sake samun wani cikin wanda har Fatima ta fitar da ran sake haihuwa ganin shekarun Suhaima sun d’an ja, kwatsam ta samu wannan cikin wanda ya sanya Umaru dana sanin auren Fatima a rayuwar shi ga talaucin da yake fama dashi mai tsanani.
Har zuwa yanzu babu abin da ya canja daga tsanar da yake yiwa Aliyu, Suhaima da kuma cikin da yake jikin Fatima, daman abinci ba basu yake ba komai na abin da ya rataya a wuyan shi na hakk’in matar shi da yaran shi baya yi, kanshi kad’ai ya sani idan ya samu kud’i zai ci mai dad’i a cikin shi, wani lokacin agaban su zai ci abin shi sai dai su yi ta had’iyar yawu, amman ko kad’an ne bazai ba su ba, sai dai da dare ya bi ya tak’ura wa Fatima da buk’atar shi, bayan kuma ko abincin kirki baya bata wani lokacin ma tun karyawar safe har zuwa daren ba zata samu cin wani abincin kirkin ba, haka zai bi ya gala6aitar da ita shi yasa kullum sake rame wa take ga jiki babu k’arfi.
Ban da uban dukan da su Aliyu da Suhaima suke sha a hannun shi, don kusan akan su yake huce haushin shi, har zuwa lokacin da Aliyu ya fara fita d’an aikin k’arfi yana d’an samun wani abin wani lokaci ya siyo musu abin da zasu d’an sa a cikin su, ko kuma idan makobcin su idan anyi girki da d’an yawa suna taimaka musu saboda sun san halin da suke ciki, bama iya su kad’ai ba kusan k’auyen gaba d’aya ma sun gane halin da suke ciki.
*** *** ***
*CIGABAN LABARI*
Haka su Fatima suka cigaba da rayuwar wahala a hannun mugun mijin ta uban yaran ta, da ita da yaran nata don gaba d’aya had’a wa yake ya ci musu mutunci son ran shi.
Kamar yau da sassafe suna zaune cikin d’aki, a gaban su garwashin wuta ne a cikin kasko suna jin d’umi, duk sun yi jigum jigum Fatima da Aliyu suna tunanin hanyar da zasu bi don su samu abin da za’a karya dashi, yayin da Suhaima kuma ta fara hawaye saboda yunwar da take nuk’urk’usar ta.
Bankad’o labulen d’akin aka yi aka shigo, kamar kullum ba wanda ya kalle shi, cikin sauri ya wuce uwar d’aki ko kallon inda suke bai yi ba, babu jimawa ya fito hannun shi rik’e da jakar kayan shi kaf.
Kallon matar ta shi yayi tare da cewa
“to ni Fatima tafiya zan yi, kuma bansan ranar dawowa ta ba, watak’il na dawo ko kuma na tafi kenan, tun da kin k’i yin abin da nake so, zan tafi zan yi nesa da rayuwar ku, zan bar ki ke da yaran ki.”
Tun da ya fara magana Fatima take kallon shi tana kuka, yana k’arasa maganar shi ya sanya kai zai fice zuwa waje babu alamar damuwa a fuskar shi, da sauri Fatima ta rik’o rigar shi cikin kuka ta fara cewa
“yanzu tafiya zaka yi ka barmu? ”
Babu wata damuwa yace
“tabbas tafiya zan yi, bazan zauna bak’in cikin ‘ya’yan ki ya kashe ni ba, tun kafin lokaci na yayi ”
Cikin tsananin kuka Fatima tace
“Don Allah kayi hak’uri ka dawo mu zauna, kada ka mance ina da auren ka akai na, sannan kuma ga yaran k………”
Kafin ta k’arasa fad’in maganar ta, Umaru ya sanya hannu ya ture ta da k’arfi, ta fad’i da6ar a k’asa, tuni marar ta tayi wani mugun d’aure wa, da sauri Aliyu ya nufi wajen Fatima shi da Suhaima suna mata sannu, cikin hassala da rashin mutunci yace
“kada ki k’ara danganta ne da wad’annan shegun yaran, kuma zan tafi babu uban da ya isa ya hana ni tafiya ”
Yana gama fad’in haka ya kad’a kanshi ya fita, cikin zuciyar shi wasai babu damuwa ko kad’an.
Dakyar Fatima ta iya gyara zaman ta, saboda mugun ciwon da marar ta yake, sakamakon ture ta da mijin nata yayi ta fad’i, wani irin zugi zuciyar ta take lokaci d’aya ta nemi hawaye ta rasa, ta kafe idon ta waje d’aya tamkar wata mara rai don ko motsin kirki bata yi.
Tun motsawar da tayi bayan ta fad’i, a hankali wani abu mai d’umi ya fara zubowa ta jikin ta, sai a lokacin ta motsa idon ta, zuwa kallon jikin nata, sai ta ga jini ne yake zuba sosai, alamar cikin nata yana cikin hatsari, koma yana daf da fita, sai a lokacin taji wani kuka ya zo mata mai k’arfi.
Cikin kid’ima Aliyu yace
“Umma jini a jikin ki, na kirawo miki Babaa lantana? ”
D’aga kai kawai ta iya yiwa Aliyu saboda yanda take jin jikin nata, yayin da Suhaima take kuka sosai, saboda ganin halin da mahaifiyar tasu take ciki, da gudu Aliyu ya fice daga gidan har yana cin tuntu6e da dutse, yana saurin k’arasa wa gidan Babaa lantana mak’ociyar su, domin neman taimakon ta………
Name: | A Sanadin Son Ki Hausa Novel Complete |
---|---|
File Type: | Download Novels as .TXT .PDF .DOC (WPS) .HTML |
Uploaded By: | Hausa Novels Team |
Category: | Hausa Novels Documents |
Novel Author: | Null |
Novel Price: | Free |
Last Modified: | October, 2022 |
Idan kuna bukatar Audio Novels se shiga anan ku danna mana Subscribe
Akwai novels maras adadi a manhajar mu ta Android wadda zaku iya saukewa anan…
Domin samun littafai a saukake su shiga group namu na Telegram
Powered by: www.hausanovel.org.ng
[…] A Sanadin Son Ki Hausa Novel Complete […]