Littafan Hausa Novels

Doctor Fadil Hausa Novel

Doctor Fadil Hausa Novel

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*DOCTOR FADIL*

 

 

Story & Writing

By

Smart ‘yar Ahmad

 

 

Free book

Page 26

 

 

 

*HADAKA WRITER’S ASSOCIATION*

 

Doctor Fadil Hausa Novel

 

Gaba daya dai ji ya ke kamar ba dadi don shagon rufe shi ya yi ya dawo gida.

Sallama ya yi ya shiga gidan ya tarar Inna zaune a tsakar gida ta na tsinar shinkafa amsa wa ta yi ita kan ta ta tsorota da yanayin shi amma sai ta dake ta ce “lafiya malam yau ka dawo da wuri?”

Ta fada ta na ta shi tsaye.

“Lafiya lau Maryama wlh yanayin ne ba dadi kuma kai na ke min ciwo gashi baban su Yusuf ya ce za mu hadu da shi” bai karasa magana ba ya wuce dakin shi ya kwanta.

“Anya kuwa lafiya kar fa na kashe miji na da hannu na” ta fada don ta na masifar son Malam isa.

Karanta Littafin Gidan Mu Hausa Novel

Kamar hadda Dije da Fadil haka su kahaddace addu’ar shiga gida da fita.

 

Addu’ar su sukayi a bayyane su ka shiga gidan ba su tarar da kowa ba sai kanin mahaifin su wato malam Isa da har yanzu barci ya ke kamar mashayi.

“Subhanallah yaya Wannan malam min fa ya ce babu kyau barcin la’asar.

*HADAKA WRITER’S ASSOCIATION*

 

 

 

DOCTOR FADIL

Story & Writing

By

Smart ‘yar Ahmad

 

Free book

*22*

 

 

 

 

 

 

Murmushi ya mata hade da daga kai alamar insha Allah ya shiga motar hannu Nihal ta cigaba da daga mishi har motar su ta fita daga harabar makarantar.

Dije dai sai mamakin yadda wannan yarinyar ba ta da ta ido.

 

Yusra ta dauki jakar Dije da ke kan cinyar ta ta ce” yawwa Dije ya maganar assignment din nan ne ? Kin gama kuwa?”.

 

Kafin Dije ta ce za ta yi magana karaf Yusuf ya yi ya ce”ke ma ai kin san Dije akwai kwanya ita kadai na za ta iya”.

 

 

Haka Yusuf ya cigaba da tsokanar Dije ita kuma ta na biye mishi Fadil kuwa ko tanka musu bai yi.

 

Cigaba da jujjuya layoyin ta ke a hannun ta tana tunanin yanzu haka za ta cusa ma Malam Anya ta yi na kan ta adalci.

Ita kadai ta na saka ta na warwara ita kadai.

 

Cusa layun ta yi ta na tunanin yadda za ta janyo hankalin Malam ya kwana a dakin ta don tun da ta kore shi ya yi fushi ya daina kwana a dakin ta.

 

 

Wankan ta tasha cikin wata leshi doguwar riga ta ci dauri zuciyar ta sai zullumi ta ke ta na kai kawo ita kadai a dakin.

 

Dije ce ta shigo bakin ta dauke da sallama hadi da addu’ar shiga gida zuciyar ta fess don ko ba komai ta huta yawon tallah.

Dakin ta kai tsaye ta wuce ta ajiye jakar ta ta hadi da cire safar ta.

Fadil! Dije! Inna ta kwalla musu kira.

Fadil kam shiru ya yi ita kuwa Dije jiki na rawa ta amsa ta fito waje ta na fadin”Inna gani ina cire safa ta ne”.

 

“Ga abincin ku nan ke da Yayan ki kuma idan kun gama ki zo ki yi wanka”.

 

Ba Dije kadai ba har Fadil ya ji mamakin yadda Inna ta chanza sosai haka kawai ya ji a zuciyar shi akwai wani abu don ruwa ba ya tsami banza.

” to” kawai ta ce ta nufi kitchen ta dauka ta kai na Fadil na shi.

 

 

Zama ta yi a gaban shi ta ce”yaya wlh na gaji sosai”ta fada ta na rike bayan ta.

“Ohhh kin fi son tallah kenan koA”

Ya fada ya na bude kwanon dambun zogale a ciki ya ji kuli kuli da albasa.

“Kaii yaya” ta fada a shagwabe.

 

Hannu ta sa za ta diba ya rike ya ce”kin manta ba kiyi addu’an cin abinci ba.

 

Murnushi ta yi ta karanto addu’ar ta fara ci.

Sai da ya tabbatar ta koshi kafin ya ci na shi.

 

Tashi ta yi ta na hamdala ga ubangiji lallai Inna ta iya girki” yaya bari na je na yi wanka ” don ji na ke kamar an mun duka.

 

“Ohhhh Dije ni fa har mamakin Inna na ke ji ke ba kya ganin kamar akwai abun da ta ke shiryawa na mugunta?”.

 

Anya kuwa yaya ni fa gani na ke kamar

 

*Smart ‘yar Ahmad*

Add Comment

Click here to post a comment