Littafan Hausa Novels

Gidan Mu Hausa Novel Complete

Gidan Mu Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

DEDICATED TO:*

*Aisha alto(Sisinah)*

*Chubado muhammad(Uwar dakina)*

*Yahanasu Soupnass(Qawalli)*

*Kausar salis(My jika)*

*Rahma Ladingo(Dota)*

*Gabadaya wannan Labarin Tun daga farko Har Karshensa mallakinsu ne*

 

 

 

*p1*

 

 

*KANO STATE*

_Area:Gadan kaya Da misalin karfe 8:30am na Safiyar Ranar Litini_

 

Gidan mu

 

“Cikin Hanzarinta na koda yaushe ta Fito Daga Cikin Wani koridon Dake Yammah da wasu Jerun Dakuna guda uku,Ta bayyana a madaidaicin Falon Lokaci Daya Tana Daidaita zaman Daurin Dakwalinta na Zahra Buhari.

Farar Budurwace Sosai kamar ka Tabata Jini ya fito Doguwa mai Jikin murjewa akallah a shekara bazata wuce ashirin da daya ba 21aduniya ba,yanayin Fuskarta da Zubinta In kayi mata kallo Daya zaka alakanta ta da ita din Jinin Fulani ne gaba da baya Balle ma Data sanya Hannu Tana kara gyara zaman Daurin Dankwalinta bisa kanta wanda yaZauna Daram saman Tilin gashinta wanda ta Daureshi da Band mai girma.

Karanta Littafin Gidan Uncle Hausa Novel Complete

Sanye take da Atamfa mai gold Blue da Milk dinkin Riga da Sikat ,kafarta Sanye cikin wani bakin Takalmi mai Saukakken Tudu sai karamar Jakarta,Saman Daya Daga Cikin kujerun Falon ta Zube Jakar Lokaci Daya Tana Dafe kanta sai data Dago na Fahimci batayi kwalliya ba Domin in Hasashena ya zama gaskiya ko Hoda bata saka ba ammh Saboda Farin Fatarta da yanayinta yasa she is ok ko ahaka taTsaya ma.

Sauri ta kwasa zuwa Cikin Koridon Kafin ta Shiga wani Daki bata jima ba sai gaahi ta Fito da waya a hannunta da wasu Tarin Littafai kamar wacce zata shiga wani Nazari,kan Kujeran ta Sake Zubesu Lokaci Daya tana Duba agogon Hannunta wanda ya kasance karami mai kyau na Fatar Damisa,siririn Tsaki Taja Kafin ta kara Daga kai Tana Hango Barayin Dinning Table din Dake chanta bangaran yammah Mikewa Tayi Da mamaki ganin bata gansa yana karyawa ba,Alhalin Tafi kowa sanin Daga ita sai shi sune masu Tashi da wuri acikin gidan Ita saboda Makaranta tana Shekararta ta Farko a BUK ne suna yawan Lacture din safe shi kuma YA YUSUF saboda Tafiya wajen aikinsa,sannan kuma shi ya kan Kaita ya ijiyeta kafin ya Karisa wajen aikin nashi sai dai in tagama abunda take yi ta hawo adaidaita zuwa Gida.

 

Jikinta ne yayi sanyi Data karisa Saman Babban Teburin cin Abincin mai Daukan Mutum Biyar kachal,Ta Bubbude Kololin abincin Data tashi Tun asuba Tayi shi kafin ta Shirya Saboda Abbanta da yayyin nata Guda Biyu da Bayan su bata da kowa,Daman bata sako Abba ko YA IMU a lissafinta ba sanin basa karyawa da wuri har gwara ma Abba Tasan by Now yana nan Idanuwansa Biyu yana Fama da Tunanen Tunanen da suka zama abokansa ashekarun yanzu Ya Imu kuwa Sai Rana ta Take yake Fitowa,koma ya Fito ba Balle ya iyacin wani abu ba Sanin Halinsa mai Kaifi Daya da Muraddam Hali,bai cika Damuwa da abinci ba Barsa da Shan Tea da kayan marmari Sai kuwa Busar Tabarsa wacce Take Tunanin kila ita ke Cikamai Ciki wamda yasa bai cika Neman abinci To in ba ita ba me yake ci.? Abunda Tunda take dashi bata Taba ganin Lokacin da yayi kyakyawan Minti Biyar bai Busa Hayaki a abakinsa ba!Tun Tana mamakin Taya Rayuwar Mutum Zatatafi ahaka har ta bari ganin Rayuwar ahakam Tana tafiya Kuma Tana kam Tafiya yarda Kaddara ta Fado ma GIDANMU..!

 

Jikinta a sanyaye ta bar wajen ta Nufi Jerin Dakunan Dake kallonta,Dakin Farko ta Fara Knooking kafin ta Tura jinta a Bude taShiga da karamar sallama abakinta Cikin Takun na na Natsuwa.

 

Wani Farin Dattajo mai yalwar Gashin Kai Fari tas Har zuwa Gemunsa da Sajensa,dake Kishingide saman Gadon Dake Dakin yana sanye da Jallabiya mai Ruwan Madara Kafafunsa suna Sambal Saman gadon Farare dasu duk gargasa,In ka kalleshi Zaka Fahimci ba Shekaru ko Tsufa ne suka sanyamai Farin gashi ba sai Hallitarsa ce haka Duba Daga yanayinsa a Tsarin Shekaru bai wuce 61 ba,Duk da ya kwana Biyu Hasken Fatansa bai DusaShe ba da kuma Tsabar kyan Fuska da Zati idanuwansa suna Lumshe ne Tamkar mai Barci Casbaha ne a hannunsa yana ja Lokaci bayan Lokaci Bakinsa na Motsi kamar mai mgana.

 

Cak taTsaya agabansa ta Zubamai Ido Cikin wani yanayi idanuwanta sun ciko da kwallah suna gabda Zuba sai da na kara Dubawa Dakyau na Fahimci Tsananin kamar da suke da wannan Farin Dattijon ban gama Mamaki ba Naga ta Durkusa agabansa Tana Fadin”Abba ina kwana..”Tafada Lokaci Daya Tana Dafa Hannunsa Dake jan Casbaha.

 

Cikin Natsuwa ya Bude Idanuwansa ya sauke akanta To daman in ba ita bace waye..?itace kadai wacce yake Fara ganin in garin Allah ya waye,Muskuta wa yayi ya gyara Zama yana Fadin”Lafiya lau MAIMUNATU..!yafada yana sakar mata Mirmishi Itama Mirmishin ta maida mai ta Mike Tsaye Tana Fadin”Kayi sallah Abba..? Kur yayi mata da ido kafin yace”Sallar mene Maimunari? Cikin Gyada kai tace”Eh Sallar asuba Abba..”Ido yadan Zaro kafin yace”Ke don Allah..An kira Sallar ne..?Maimuna Dataji kamar ta Fashe da Kuka saboda Tsausayin Abbanta ammh sai ta Dake Cikin Rawan baki tace”Anyi Abba..Yanzu fa Takwas ta wuce har nagama Abun karinmu yanzu haka nazo mu gaisa ne zan wuce makaranta..”Ta karishe Fada wasu Zafafan Hawaye suna Biyo Kuncinta.

 

Abba Dayaji abunda Maimuna tace yasa yayi Saurin Dirowa Daga kan gado kamar zai Fadi har sai data Rikeshi Tana Fadin”Yi a hankali Abba…”Cikin Takaicinsa yace”Wlh Maimunari Bansan anyi sallah ba..Kinga zaman nan da kikaga nayi ina Jiram akira sallar ne fa..Ko dai agogon ki ne yaLalace Maimunari gari bai waye ba..”Yafada yanawuceta Zuwa Window dake Dakin ya Daga Labulen ya leka kafin Taji yana Fadin”Innalillahi…da gaske kike Munari gari yayi Tar..”Yafada kafin ya Juya da Sauri ya Nufi Hanyar Tiolet kamar zai kifa Maimuna kuwa Banda Shesshekam kuka Babu abunda take yi ganin zai Shiga Tiolet din ne yasa tace”Abba Magungunan ka sun kare ne..? Bai juyo ba yace”Basu kare ba..Likitan fa da Mugunta Wlh mgugunar dayawa ya Tulamin sai kace wani Jaki..”Daga haka ya Tura Kofar Tiolet din yaShiga Da Casbaha a Hannunsa ya Rufo Kofa Tana jinsa yanata mgana Shi kadai Nan maimuna ta Duke Tana kuka mai Cin rai da kuma Tsausayin Halin da Gidansu ke Ciki na kuncin Rayuwa Dana Zuciya bata iya Fita Daga Dakin ba Har Abba ya Fito Daga Tiolet dim yana Digan Ruwa da alamu alwala yayi da sauri ta Mike ta isa ga Cikin Makeken Wardrope dinsa Tabude ta Daukomai Darduma ta Shimfidamai Kallonta Yayi yana Mirmishi yace”Allah yayi miki albarka Munari..”Yafada Lokaci Daya yana Dafa kanta Hawaye ta Share tana amsawa da Ameen.

 

Har ya Daidaita Sahu ya Dago yana kallonta Kafin yace”Kukan me kike Munari..? Da sauri ta Goge Hawayenta Tana Fadin”Bakomai Abba..wani abu ne ya Fadamin a ido..”Kai ya girgiza kafin yace”To kije Yayanki Yusuf ko Imram su cire miki mana..Ni kinga idanuwana duk sun Mutu ba wani gani nake yi ba sosai ba..”Yafada Lokaci Daya yana kara Damke Casbahan Dake Hanmunsa ya Tada Salla da Kallon Tsausayi ta bishi Dashi Tana Tuna Wasu Shekaru achan Baya Abbanta ba Haka yake ba ammh yanzu kalli yadda ya koma Depression ya sa ya koma kamar wani mai Tabin kwakwalwa ga Kuma hawan Jini Da suka Hadu sukamai yawa Wai ahakan ma Don Likitan Kwakwalwa na zuwa duk wata ya Dubashi da kila Abba yana Chan Gidan Mahaukata tasan ko zata Mutu Abba bazai ijiye Cashaban Dake hannunsa ba Shiyasa bata wani matsa ma Kanta ba ta Juya ta Fice Daga Dakin Bayan ta jawo Kofar.

 

Tana Fitowa suka kusa cin karo dashi ya Fito Daga Dakinsa Zai Shiga Dakin Abba Baya taja Tana kallonsa Kafin tace”Gud Mrning ya Yusuf…!

Kauda kansa yayi Saboda baya so ta Fahimci yayi kuka yace”Mrning Sisy how was ur Nite..?Yafada Cikin Sanyinsa kamar ko yaushe.

Da kallo ta Bishi ganin yana ta kauda kai sama da kasa karemai kallo Dogo ne sosai mai Dan Jikin murjewa Sannan Shima Fari ne kamar ita sai dai ta Dan Fishi Haske suna Tsanananin kama da juna Kamanin Abba suka Debo kamar an Tsaga kara.

Cikin Zargi da Tantama tace”Ya Yusuf Lafiya..? Domin bata ga yayi wani Shirin tafiya aiki ba kamar yadda aka saba ba,Kansa ya sosa yana Fadin”Lau..Me kike jira baki tafi school ba..”?Maimuna tace”Yaya kaifa nake jira..Har na gama Breakafast baka fito ba..”Hannu kawai ya saka a gaban Aljihun Jallabiyansa ya Dauko 1k ya Mika mata ta karba da mamaki kafin Tace wani abu ya Rigata da Fadin”Ki hau adaidaita kitafi makaranta yau ba zan je aiki ba ina gida..”Yafada Lokaci Daya Yana Kokarin Rabata ya Shige Dakin Abba da Sauri taRiko Hannunsa yakiya waigo sai ta koma ta gabansa ta Tsaya tana Kallon yadda Idanuwansa sukayi Jajir,alamun yayi kuka Cikin Tsausayinsa tace”Meya faru ya Yusuf..?kuka fa kayi..?

Da sauri yace”Kuka kuma Sisy..? Ni ban yi kuka ba..’

Yafada yana kokarin Sakin Mirmishi,itama Mirmishin ta Sakarmai Mai ciwo kafin tace”Kuka kayi ya yusuf..Ko baka Fadamin ba Nasani..”Ta karishe Fadai itama Hawayenta suna zubo mata Da Sauri ya Dafa Duka Kafadunta yana Fadin”Me ye na kuka Sisy..? Bafa kuka nayi ba kaina ne ke Ciwo Shiyasa kika ga kamar nayi kuka..”Kara saka mai kuka tayi Tana Fadin”Bari naje na kira Anty Safiya na gayamata kila ita Zaka gayamata meke damunka..”Tafada tana Kokarin wucewa da sauri ya Rikota yana Fadin”Kada ki kirata Munari

Da sauri ta kallesa jin yadda yayi mgana sai taga kawai ya gyadaa mata kai yana fadin”Domin ko kin kirata bazata zo ba..Itama an Rabamu da ita Sisy..”Ya Karishe Fada Hawayen DayakeBoyewa suka Zubomai,Maimuna Dataji abun Daga sama Taji Jikinta yakarayin sanyi,Cikin wani yanayi tace”Itama din Yaya..? Itama din an gayamata Abban mu Mahaukaci ne,Sannan bamu da uwa bamu da kowa sannan itama an gayamata ya Imran bayajin mgama yana Shaye Shaye..? Itama din Am bata Labarin Gidanmu ko Yaya.. ?Ta ke Fada tana wani Gunjin kuka Da Sauri ya Rumgumeta kamkam Yana Fadin”An gayamata Sisy..An ce ma iyayanta irin kallon da Mutane suke mana Munari..Itama na rasata Munari..”Haka yake Fada yana kuka itama kukan take aka rasa mai Lallashin Daya acikinsu Sai da suka gaji kana suka saki Juna Maimunatu bata tsaya ba ta kwashi Gudu Zuwa Dakin ya Imran Dake gaba Kadan Da Dakin Abba da Ya Yusuf da kallo ya Bita Ita yafi Tsausayi gwarasu maza ne ammh itama fa mace ce,tafi su Rauni,

Hawayensa ya Share da Sauri ya Tura Kofar Dakin Abba ya Shiga da Sallama.

 

Bubbuga Kofar ta shiga yi Tana Kiran sunansa,Yana zaune akan Kujera kwara Daya Tal Dake Cikin Bedroom din nashi Yana Kishingide Taba ne a Hannunsa yana Busawa Hayaki ta baki ta Hanci Bai ma jinta Bugar Kofar Domin ya shigawata Duniya Sai zuwa Chan yaji Kiran sunansa Da Buga Kofar Bude Jajayen Idanuwansa yayi yana mamakin waye yazo zai Dameshi.?ko yace zai katse mai Jin Dadi Mikewa yayi a Fusace Dauke da Taban a Hannunsa ya isa ga Kofar ya Bude yana Fadin”Wai Wayeee…!

Yafada Cikin kakkausan Muryansa Kallon kallon sukayi Tsakanin shi da Maimuna wacce ke Zubar kwallah Sama da kasa yake Kare mata kallo Lokaci Daya ya Karkata kansa gefe ya Saka Tabarsa abaki yayi mata wata Zuka,kafin ya Fesar Da Hayakin zuwa Fuskar maimuna Baya Taja Tana Toshe Hanci Saboda bata kaunar warin Taba.

 

Kara Hade rai yayi ganin Tanawani Toshe Hanci Cikin Muryansa ta Kaushi ba Tausasawa yace”Ke…Ubam wa kike Toshe ma Hanci..?Ni sa”an ki ne..? Yafada yana Nunata da yatsa kafim ya Cigaba da Fadin”Cire hannun ki a saman hancinki..In ba Haka ba kika Tunzurani wlh zan kamaki na Danne ki sai na Karar da Hayakinta a cikin bakin ki..”Ya karishe fada yana Nuna mata Taban hannunsa Dake Kunne tana Fesar da Hayaki Lokaci Daya yana Zare mata Jajayen manyan Idanuwansa kamar na mace.

Dagowa Tayi tana kallonsa Tana kukan Tsausayinsa da Tsausayin kansu shima sai Lokacin ya Lura da kuka take Da sauri ya kwara ware ido yana kallonta,Kamar yadda take kallonsa Dogo ne sosai Har yafi Yusuf Tsawo kuma Shi Faffada ne Da kuma Kirar Karfi da Zafi Jikinsa yana Cure ne Domin baya wasa da Motsa jiki Fari ne shi ammh ba sosai ba Sunfishi Haske,yana da manyan Idanuwa mai Dauke da Doguwar Fuska Sai Sajensa daya Zagaye Bakinsa,wanda ya fara koma baki baki saboda busa taba,kansa Nannade yake Da Askin nam na Dada,kuma ya Dace dashi Domin ya Tafi da bakin gashin Fulanin daya wani Nannade Bisa kansa Daga Shi sai Bakin Dogon wando Ko Riga bai Dashi Faffadan Kirjinsa mai Cike da gargasa duk yanawaje ne.

 

Kukan da Maimuna take yi ya Dakatar dashi Domin shi bai ma Lura da kuka take ba Da sauri ya kariso gabanta yana Fadin”Ke..Kukan me kike yi ne.? Ya fada Cikin Daga murya da Bayyana Damuwa Domin Duk Iskancin Imu yasan Gidansu Baya kaunar yaga wani Daga Cikinsu Cikin Damuwa kasa mgana Tayi har sai da ya Harzuka ya Daka mata Tsawa yana Fadin”U better stop dis Nonsess ki gayamin abunda ke Faruwa…Tun kafin na jimi ki Rauni anan wajen..”Ya karishe Fada Lokaci Daya ya Dukan Bangon Wajen da Hannunsa mai Dauke da Taban Wacce ta Fadi kasa ya sa Kyakywan Farar kafarsa ya Take Wutan ko Zafi bai ji ba saboda Zuciya da Sauri Maimuna taja Baya sanin Halinsa in yayi wannan Bakar zuciya sai ya iya mata Targade ai tun kafin ya juyo tace”Ya imu..Dama..Daman ya Yusuf ne ke kuka..”Ido ya sakar mata Cikin wani yanayi kafin a Hankali ya Furta..”Kuka..? Cikin alamun Tambaya..”

Kai ta gyadamai Cikin Kaushin Muryansa yace”Yana ina..! Da sauri tace”Yana Dakin Abba..”Bai ma Tsaya Sauraranta ba ya wuce Fuu kamar zai tashi Sama da Sauri ta maramai Baya zuwa Dakin Abba.

 

Yusuf na Zaune gefen Abba yana Ballamai mgani yana bashi yana sha Daga Gefen Dirowam gado kuwa Mug ne na Tea da Bread wanda Yusuf din ya Dauko ma Abba yasha Saboda yasha mgani Suna Cikin wannan Halin Imran ya Bango Kofa ya Shigo Cikin Muryansa mai Cike da Amo da Sauti yace”Uban waye ya saka ka kuka Yusuf…!

Ya fada Cikin Sauke Jajayen Idanuwansa kan Yusuf din wanda bai ma dago ya kallesa ba illah Mikama Abba mganin Daya Ballo masa ya karba ya saka abaki yabi da Ruwa Lokaci Daya Yusuf ya karbi Ruwan yana Fadin”Abba ka kwanta ka Huta don Allah..”

 

Abba bai yi mgana ba illah yabi Yusuf da kallo yajuya yabi Imran da Munari da kallo kamar yana so ya Tantance su,Ganin haka yasa Yusuf ya kamashi ya kwantar Lokaci Daya yana Rufamai Bargo Daga kafarsa yana Fadin”Kayi barci..Wannan kuma Daya Shigo Imu ne Abba Mara Hankalin kanin nan nawa ne..”Yafada yana dan Mirmishi sai Shima Abba ya Murmusa yana kallon Imran wanda ke tsayr Kikam yana kallon Abba Yusuf ne ya waigo yana kallonsa kafin yace”Kai wai yaushe ne zakayi hankali ne..? Sai an ce ka gaida Abba zaka gaishe shi..?

Imran ya wani Dage Hanci yana Fadin”Indai banyi hankali at age of 30 ba Kila sai age of 36..”Yafada lokaci Daya yana karisa ga Abba Hannu ya bashi Suka Tafa yana Fadin”Abba kana Hutawarka fa..!Kaji Dadinka Allah ya baka lafiya..”Ya karishe fada yana Shafa Gemunsa Abba yayi mai Dariya kafin yace”Allah yayi muku albarka..”Yana Fadin haka kuma sai duk sukayi wani iri Yusuf kuwa Hanyar fita ya kama Bazai iya tsayawa ba Fita yayi Daga Dakin Maimuna tabi Bayansa Imran kuwa Durkusawa yayi gaban Abba Idanuwansa ya kara Kadawa yace”Allah ya baka Lafiya Abba..”Yake Fada yana Rike da Hannunsa Kansa Abba ya Dafa Yana mai Mirmishi Cikin Muryan Barcin Daya Fara Fuzgan Abba yace””IMRAN…..!

Bai karisa ba barci ya Tafidashi Dayake mgangunan akwai na Barci Imran Dake kallon Fuskar mahaifinsu yaji kamar ya Kurma Ihu Kai ya girgiza kafin ya mike Dakyar ya iya Sabule hannun Abba ya gyaramai kwanciya ya kuma Rage mai karfin Sanyin Dakin kafin ya Fice Zuwa Falo anan ya iske yusuf da Maimuna suna Zaune mgana suke suna ganinsa sukayi Shuru,bai damu ba yana zuwa gaban Yusuf ya tsaya yana Fadin”Kukan me kake yi ne kamar wani mace..?kasa wannan Shagwabbiyar kanwar naka itama tazo Tana Damuna da kuka..”Ya fada Lokaci Daya yana Tura Hannunsa Cikin aljihun wandonsa sai ga Taba ya Fito da ita da Lether ya saka abaki ya kunnata ya Zuka ya Fesa musu Hayakin yana Fadin”Ina Tambayarku kumin Shuru..Kada ku bari na Harzuka fa..Mahaukaci kuka maidani ko me..?

Ya karishe Fada yana Fitar da Hayaki ta Hanci Dukkansu kallonsa suke ba wanda yayi mgana Daga kafa yayi ya Buga Jikin Kujera Cikin Tsananin Fushi yace”Nace waye ya saka ku kuka ne..?Yau yagane ba wanda ya isa ya saka wani Daga Gidanmu Zubda Hawaye..”

Yusuf dai baice komai ba Maimuna ce ta Tsorata taja Baya Tana Fadin”Safiya ce..!

 

Cak yaTsaya yana kallonta ganin haka yasa tace”Eh Anty Safiya Budurwan Ya yusuf…Itama..Itama..”ITAMA ME NE.! ya katseta Cikin Tsawa da Bala”i Yusuf ya kalleshi ganin yadda Munari kerawan Jiki yace”Kai fa Sakarai ne..Itafa macece kayi mata ahankali mana..”Jajayen Idanuwansa ya sakarmai kafin ya Bushi Hayakim Taba ya Fesamai yana Fadin”Ai tama fika Jarumta malam..’Yafadamai yama kallonsa karamin tsaki yaja ya Mike yana Fadin”Kada ka sake naji ka taka kaje gidansu Safiya kaji ma nagaya maka..”Daga hakaya juya zai tafi Imran ya Daki Kirjinsa Har sai da yayi kara Lokaci Daya yana Fadin”Itama sunce baazasu baka ba saboda muna Rayuwa agidamu bamu da Mace aciki..? Abban mu ya Haukace ni kuma ina Shaye Shaye ko..? Itama sun kara hanaka keman duk da Tarin Nasabarka Kafa fini Hankali Da Tunani meka rasa da zaka Dinga Neman aure ana hanaka..?

Yusuf ya tsaya Cak yana Jin wani Kukan Zucci Cikin Sanyinsa yace”Bamu rasa komai ba Face KWARIN ZUCIYA..”

Da mamaki Imran da Maimuna ke kallonsa bai waigo ba ya Cigaba da Fadin”Mun rasaa kwarin Zuciyan da zamu karbi kaddaranmu mu Cigaba da Rayuwarmu Tamkar kowa..Tunda Kaddaran nan ta Fadamana muka rasa komai Abba ya Koma haka Imran ka koma yadda kake ni kadai ne nake kokarin Tsayuwa da Kafafuna din ma na gaza Domin Kune kwarin gwiwata da komai nawa Domin ku kadai ne ahalina anan Duniya..”Ya karishe Fada Yana Sharan kwallah

 

Imran ya Busa Taba mai tsawo Har sai da Hayakin ya Cushemai Zuciya ya Fara Tari da Sauri Yusuf ya Nufeshi yana Fadin”Kagani ko..?kaga irin Sakarcin ka ko..?baka da Lura ne ka rika Zuka a hankali mana Tunda ta zama ibadarka..”Da hannu ya Dakatar da Yusuf kafin ya Bude Manyan idanuwansa da suka kara zama Ja saboda Hayakin Daya taso mai Daga kai ya Nuna kansa yana Fadin”indai Ni IMRAN wanda ABUBAKAR MALAMI ya Diga kwansa ZUWAIRA Ta Haifeshi adoron Duniyanan sai na Aura maka Safiya..Ko Ubanta ya yarda ko bai yardda ba don Uwatai..”Yafada yana kara Nuna kansa da kuma Dukan Kirjinsa kafin ya Take Taban Hannunsa ya Murjeta da kafansa ya wuce yana wani Tafiyar Takama yusuf ya Shiga kwalamai kira yana Fadin”Imu..? Imu me zakayi kada ka kaje ka Karya mata Uba kamar yadda kayi ma Kawun Asmee fa..!

Imran na jinsa Mirmishi kadai yayi a Hankali ya Furta”Ka bani Shawara ya yusuf Tanque..”Yafada Lokaci Daya yana Shigewa Dakinsa Yusuf ya Dafe kansa yana Fadin”Munari meyasa kika gayamai..? Kin fi kowa sanin zai je yayi act din sa Stupit kamar yadda ya saba..!

Marairaicewa Tayi zatayi mgama ya Dakatar da ita da Fadin”Muje mu karya na kai School kin makara..”Da sauri ta Mike tana Fadin”Nayi missing din Lecture din Dr Sa”idu..”

Dinning suka nufa ya zauna Tayi Serving dinsa Tea kadai ya sha da Soyayyan Dankali itama haka basu jima ba suka tashi Daki ya koma ya Dauki key din Mota Ita kuma ta kwashi Littafanta da Jakarta da mayafinta suka Fito Haraban gidan Sun Shiga Motar kenan Yusif zai yi Rivers sai ga Imram ya Fito ya Tsuke Cikin Riga da wando Duka bakake ya saka P.Cap ga wani Bakin katon Gilashi Daya kwafa fuskarnan ba Annuri Kafarsa Sanye Cikin wani Bakin Booth din Takalmi yana ganinsu yayi kamar bai gansu ba,Bakar mashin dinsa Roba roba Dake fake a Haraban gidan ya Hau Lokaci Daya yayi mata Key ya Tada ita yana Zuba Hon Iro megadi Dake Tsaye Daman Tuni ya wangale get din sanin Hali Yanzu sai yasha mari Imran bayason Jira sai da ya Fice Daga gidan kana suka Fita suma suna Tafe Yusuf na Tunanin kada Imran yaje gidansu Safiya yayi musu Haukanshi har ya sauke Munari bai da walwala Daga nan Gida ya Dawo saboda Abba,ammh Gabadaya Zuciyarsa bata Natsu da Fitar Imran ba yasan sa Kaifi Daya ne in yace Zai yi Abu sai yayi shi yaso kiran Safiyan yaji ko yaje..?Sai kuma ya fasa Domin Cin Zarafin Da babanta yayi mai Jiya bai fatan ta sake ma ganinsa Har Abada.

 

 

 

*Ya kukaji salon wannan Mikakkiyar Tafiyar tamu..? Bamu ce komai ba bamu Fara Wannan Tafiyar ba har yanzu..Ku yi Kyakyawan Sharhi bayan kun yaba kun kuma danna min Kararrawar Voting ni kuma nayi alkawarin Sanya ku nishadi da wannan Labarin mai amon Sautin tafiya da Zuciyar mai karatu..*!

 

 

Add Comment

Click here to post a comment