Littafan Hausa Novels

Na Gama Auren Hausa Novel Complete

Na Gama Auren Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

Na Gama Auren Hausa Novel Complete

 

_BISMILLAHI RAHAMANIR RAHEEM_

 

1️⃣

 

 

Cikin wani irin sanyi na miƙe daga kujerar idona ƙur saman agogon bangon da ta buga ƙarfe goma da rabi, na ɗaga wayata na sake shigar da lambarsa a karo na babu adadi sai dai har ta ƙaraci kukanta ba a ɗaga kiran ba,wasu hawaye masu ɗumi suka yi saurin gangaro min,na ɗaga hannu ina sharewa tare da ƙarfafa wa kaina wani abu ne muhimmi yake tsayar da shi a ƴan kwanakin nan yake dare haka, na haɗiye wani yawu wanda ya busar min da dukkan wata lema da ke bakina. Ƙarfe sha ɗaya ta buga lokacin da nake kai kawo

,ya yi daidai da ƙarar buɗe gate da na ji, ƙwalla ta cika idona na yi saurin matseta ina tausar tsokar ƙirjina tare da kuma shaida mata ta kasance mai uzuri, idona akan ƙofa har ya turo bakinsa ɗauke da sallama, na sauke numfashi take idona ya yi narai-narai da hawaye, ya ware hannayensa alamun na isa garesa na lumshe idona daidai lokacin hawayen da suke kokawar fitowa suka samu nasarar sauka kan kundukukina.

Karanta Littafin Matar Makaho Hausa Novel

“Subhanallahi kuka Nafi!” Ya faɗa yana ƙarasowa gare ni tare da ƙoƙarin haɗa ni da ƙirjinsa, da sauri na ja baya sanadiyyar ƙamshin turaren da nake ji a jikinsa dumu-dumu kwana biyun nan in ya dawo, wani abu ya caki ƙirjina don ko ba a faɗa ba ƙamshin turaren mace ne.

Na Gama Auren Hausa Novel Complete

“Lafiya?” Ya ce yana sake ƙoƙarin kamo hannuna, ban hanasa riƙewar ba haka ban dakatar da ruwan da ke ta gudu saman kuncina ba. “Kin ga daina kukan, kwana biyu lissafi ne yake tsayar da ni,shi ya sa nake yin dare”

 

“Lissafin me?” Na ce ina laluben idonsa.

 

“Kin san ƙarshen shekara ta zo,yanzu ne muke lissafin uwa da riba,don a yi sallama a ga kuma me aka samu a cikin shekarar”

 

“Hmmm!” Kawai na ce ina wucewa,Ni ai ba yarinya ba ce da zai yi min wata kwana na yarda da shi.

 

“Don Allah haɗa min ruwan wanka ki ɗan matsa min jikina, na bala’in gajiya My Nafi”

Na Gama Auren Hausa Novel Complete

“Sannu ” na ce a taƙaice tare da nufa banɗakin na haɗa masa ruwan ɗumi, ko da na fito yana ƙoƙarin rage kayan jikinsa, ina tsaye ina linkewa bayan ya cire wayarsa da ke kan gado ta ɗauki ƙara,cikin wani irin sauri da zafin nama ya ɗau wayar tare da latse sautin ya kife ta yana sauke nannauyar ajiyar zuciya, tsai na yi da linkin ina kallonsa don alamar rashin gaskiya ƙarara ta bayyana kan fuskarsa, ya ɗan haɗe gira ya ja wayar ya yi danne-danne ya ajiye tare da wucewa toilet. Har ya shige kuma sai ya fito tare da kamo Ni yana cewa “mu je ki taya ni cuɗa baya,na ce miki na gaji ko”

 

Jiki babu ƙwari nake mi shi wankan ina ta mamakin wane irin turare ne haka da ya laƙe masa har a fatar jiki ba iya kayan jikinsa ba. Bayan mun fito duk yadda na so ya ci abinci ƙi ya yi wai ya ci abinci a waje, sai da na saka a fridge ina jin raina babu daɗi. Ko da na shiga ɗaki waya yake, murmushi ya saki sannan ya ce “okay, sai da safe” ya katse kiran. Hannu ya miƙo min alamun na zo, ban je ɗin ba na ƙarasa ɓarin da nake kwanciya na kwanta, ya mirgino inda nake tare da rungumeni yana shafar jikina, Alhaji Sammani ya bala’in iya soyayya, duk wani ɓacin ran da nake ciki minti goma kacal kalaman baki zai sa na sassauto bare ma yanzu da yake sarrafa lungu na saƙo na jikina,sai dai ya cire duk damuwar raina muka sama wa juna nutsuwa, sannan ya ja ni muka yi wanka tare da sake kaya, abincin da ya ƙi ci muka ɗumama muka ci sannan muka koma gado, na kwanta a jikinsa ina ta addu’ar Allah kar ya kawo wani abu da zai yi sanadin raba soyayyar da ke tsakaninmu, don zuciyata sosai ta fara rawa akan Alhaji Sammani, shekara goma sha shida muna zaman aure babu yadda za a yi na kasa fahimtar wannan sauyin da ya fara. Da wannan tunanin bacci ya fara kwasata ina jin yadda yake wasa da jikina kamar kowani lokaci.

 

“Nafisa!” Cikin bacci na tsinkayi muryarsa.

 

“Uhm” na amsa cikin bacci.

 

“Nafi aure nake son na ƙara” ɗif na ji wuta ta ɗauke min. Sai na yi shiru na kasa wani motsi.

 

“Nafi kina ji na?”

Na Gama Auren Hausa Novel Complete

“Uhm!” Na ce don baccin idon nawa tuni ya watssake.

 

“Nafi haihuwa nake so!” Wannan karon sai na ji harsashi ne ma ya fasa zuciyar tawa ba mashi ba, na dai yi shiru ina danne zuciyata da ke ta yunkurin fashewa da kuka.

 

“Nafi ƴar gidan manyan mutane ce, ki taya ni addu’a Allah Ya sa rabona ce,ina da ƴan takara da yawa”

 

“Allah Ya tabbatar da alkhairi” na ce ina jin wani ɗaci da ɓacin rai,ba neman auren nasa ba ne ya ɓata min illa kalamansa. Bacci bai ɗauke Ni ba har na fara jin saukar numfashinsa, kalamansa na ta amsa kuwwa a kunnuwana, wai haihuwa yake so, raɗe-raɗi da maganganun da ake ke nan har da Alhaji Sammani,shi ma ashe kallon juyar yake min, Ni na san haihuwa ba wanda ya isa ya ba wa wani ita sai Allah, duk idan na dungura goshina ƙasa ina roƙon Allah Ya zaɓa mini alkhairi, ina kuma da tabbacin addu’ata ba za ta faɗi ƙasa banza ba. Bacci sosai ya gagari idona sai na raya daren da sallah.

 

Washegari haka na tashi zuciyata duk a cunkushe, na kammala gyaran gidana na shirya masa abinci, ko da ya fito ina zaune kan kujera cikin kwalliya kamar koyaushe,wayar hannuna nake ta juyawa bayan na kashe data, WhatsApp din sam ba ya kaina.

 

“Nafi!” Ya zauna gefena yana kama hannayena,na ɗago na kalle shi na ɗan saki murmushi na ce “ka fito?”

 

“Fushi kike da ni, don na ce zan ƙara aure?” Ya ce cikin rauni. Na girgiza kai na ce “a’a Alhaji,don me zan yi fushi kan za ka ɗabbaka sunnah”

 

“In dai don zan yi aure ne ki gaya min bana son ganinki cikin damuwa, sai na fasa” ya ce yana ɗan matsa hannuna.

 

Na ɗan harare shi cikin wasa na ce “a’a wallahi ka cigaba da neman aurenka,ba wannan ne damuwa ba,kawai bana jin daɗin jikina ne”

 

“Ko na kai ki asibiti” ya ce cikin kulawa.

 

“Na haɗiyi panadol ma, mu je ka karya” na miƙe don taƙaita zancen. Dole na ƙarfafi kaina na ba shi abinci sannan ya wuce kasuwa. Wunin zungur bani da wata walwala, da yamma ina kan kujera ina ɗan kallo bayan na kammale komai nawa na ji shigowarsa, da murmushi na tarbesa don shima cikin jin daɗi da farin ciki ya shigo, ya zauna ya ce “Hajjaju kawo min abincina nan” nan ya ci yana ta bani labarin kasuwa. Kafin magriba ya shirya cikin sabuwar shadda dal ya murza hula da agogo, a parlor ya same ni yana ta tashin ƙamshi da ɗan murmushi ya kalleni ya ce “to ya kika ganni Hajjaju”

 

Duk da kishin da ke azalzalar zuciyata bai hana ni sakin murmushi ba na ce “ka yi kyau” har dai ya min sallama cikin barkwancinsa ban da nutsuwa,yana fita hawaye suka fara sauka a fuskata, Ni na ƙarfafi kaina dole tare da tuna duk haƙuri da alkhairan da Alhaji ya yi min, shekara sama da goma ƴan uwansa na hura masa wuta ya ƙara aure amma ya ƙi sai a yanzu,ko ba komai bai cancanci na ɗaga masa hankali ba a yanzun, ya jure!. A ranar bai tashi dawowa ba sai bayan sha ɗaya da rabi,raina ya bala’in ɓaci hakan ya sa da ya dawo na tunkaresa na ce “wani irin abu ne haka,ka barni ni ɗaya ka tafi zance har ƙarfe sha biyun dare,wane irin zance ne ma wannan cikin dare haka” ƙamshin da ya shigo da shi ne yake kuma ingiza kishin da ke cin zuciyata. Ya ɗan saki murmushi ya ce “na gaya miki ina da ƴan takara, wallahi yarinyar ce akwai farin jini ga kyau”

Na Gama Auren Hausa Novel Complete

“Wannan ba matar arziki ba ce,har layi kuke hawa sannan ta gana da ku, a haka take ƴar manyan mutanen?” Na ce cikin ɓacin rai, wannan karon kutun-kutun ya yi da fuska ya raɓe ni zai wuce na kuma cewa “kuma wani irin ƙamshi kake haka,daf da daf kuke zama ko kuwa rungumarta kake da ƙamshinta yake kama ka har haka” a bala’in fusace ya juyo yana “ke kar ki gaya min maganar banza,don ina lallaɓaki ba fa tsoronki nake ba,wane irin iskanci ne wannan Ni za ki kira da ɗan iska?”

 

“Ni ban ce maka ɗan iska ba,tambayarka na yi” na faɗa ina ɗan sassauto da muryata.

 

“Matseni sai na baki amsa” ya ce da jan tsaki ya wuce. Ko da ya shiga ɗaki bayansa na bi ya shige toilet batare da ya kula Ni ba, ina tsaye wayarsa da ke kan mirror ta yi ƙara,ba halina ba ne duba wayarsa amma yau sai na durfafi wajen da ya ajiye wayar.

 

_First love💞_ shi ne sunan da ke yawo kan screen ɗin,tsaye na yi cikin mutuwar jiki yayin da zuciyata ta shiga wani irin bugu har wayar ta katse jikina rawa yake, take kuma hoton wata kyakyawar budurwa ya bayyana a fuskar wayarsa daidai lokacin ya fito, hannu ya sa ya zare wayarsa ganin abun da nake kallo shima sai da ya ɗan sha jinin jikinsa sannan ya sosa kai ya ce “wallahi ita ta sauya fuskar wayar Nafi”

 

Ban tanka shi ba na nufi gado na kwanta, addu’a nake karantawa duk wacce ta zo bakina don na samu zuciyata ta sassauto daga ƙuncin da take ciki.

 

“Abinci fa” ya ce cikin sanyi, ban ko buɗe idona da ke a kulle ba bare na tankasa. Duk yadda ya so mu raya daren ƙin ba sa haɗin kai na yi,haka ya haƙura ya ƙyaleni. Washegari da safe ina idar da Sallah na koma bacci, ban da niyyar gyara ko shirya masa komai,zuciyata a jagule nake jin ta,first love ɗin da na gani ya bala’in ƙona min rai,wato akan ta ya soma soyayya,in na tuna har wani ɗaci nake ji a bakina ba iya zuciyata kawai ba, ko da ya dawo daga motsa jiki bai tanka mini ba musamman da ya ga ina ta cin magani, haka ya yi shirinsa ya fice, rana ta farko da hakan ya kasance tsawon shekarun zaman aurenmu.

 

Na Gama Auren Hausa Novel Complete

 

2️⃣

 

Tun daga ranar ya shiga min ɓoyon komai nasa duk ya sauya,ƴar hirar da muke in ya dawo ya daina, illa ya cika cikinsa ya sauya wanka ya fice ba zan kuma ganinsa ba sai bayan sha ɗaya,Allah Ya sani ko kusa bana cikin mata masu kishin jahilci,amma tun kan zuwan kishiyar sai na ji na bala’in tsanarta saboda rawar kan da yake ta yi,ga babu magana mai daɗi da kuma na yi ƙorafi ya balbaleni da masifa,gani nake kamar an sauya min shi, Sama’ila mai shiga tashin hankali da ya ɗan ga sauyi na rashin jin daɗi a fuskata yanzu tsakiyar kaina yake juye kashin kajinsa, sai dai na yi kuka na gode Allah,ga shi ni Allah bai yi Ni da fitar da sirrina ba,duk wasu shawarwari shi yake bani,sai abin ya yi mugun dukana babu inda nake jin sanyi,na yi bala’in zabgewa cikin kwanakin da ba su gaza goma sha biyar ba.

 

Yau wani zazzaɓi nake ji tun rana, sai na kasa yin kwatakwes a gidan, da ƙyar na yi wankan yamma na saka sassauƙar doguwar riga, tun da aka yi sallar magariba nake kwance kan doguwar ina jin yadda ƙafafuna da duk wasu gaɓoɓi nawa suke ragargaza, bakinsa ɗauke da sallama ya turo ƙofar, na amsa, kamar yadda ya sabar mana a ƴan kwanakin bai ce da ni ƙala ba ya wuce ɗakinsa jim kaɗan ya fito cikin doguwar jallabiya da alama wanka ya yi, ya nufi dining amma da ya je sai ya ga wayam babu komai. Hakan ya sa ya dawo kamar ana masa dole ya ce “ina abinci”

 

Cikin yanayin ciwo na ce “ban samu yi ba”

 

“Don me?, Tun safe na fita amma ki kasa yin abinci don rashin mutunci, na kula Nafisa neman raina Ni kike yi, wane irin kishin hauka ne wannan da zai sa ki fara wasa da abincina,ke yanzu ba ki ji kunya ba, duk shekarun da na kwashe ina haƙuri sai yanzu da na ga wacce ta dace da ni na ce zan aura,za ki tashi hankalinki, don mugun hali kin takuri ranki kullum cikin baƙin rai, to wannan ya zamana na farko kuma na ƙarshe da za ki ƙi min abinci, ko ba zan ci ba a ajiye min, washegari a zubar tunda Ni nake kawo komai har kayan sarrafawa don me za a ƙi bani abinci” ya wuce yana huci,gabaɗaya ji na yi wuta ta ɗauke min, a tsawon shekarun da muka yi da shi ranaku ɗaiɗaiku ne ban yi masa girki,ciwo, lalura,uzuri sai na yi sai jefi-jefi, amma yau don ban yi ba bai ko saurereni ba ya hau min balbalin bala’i, ƙwalla ta surnano min na ɗauke da faɗin “Allah Ya kyauta” jim kaɗan ya fito cikin galleliyar shadda yana zuba ƙamshi kamar kullum,ban samu arzikin kallo ba bare ya ce “na fita” kamar yadda ya saba, yana fita na sauke ajiyar zuciya ina kuma share hawayen da ke ta neman kufcemini. Ana yin sallar isha’i na haɗa shayi na sha,cikin nawa babu komai tun safiya, sanin ba yanzu Alhaji zai dawo ba ya sa na saka wa ƙofar sakata wai na ɗan rintsa don bacci na ji ya fara kwasata, kamar jira yake kuwa wani nannauyan bacci ya sure ni ina aza haƙarƙarina saman gado.

 

Cikin bacci na ji wayata da ke gefe ta ɗau ruri, na jawo tare da ɗagawa cikin bacci

Na Gama Auren Hausa Novel Complete

” Wane irin shashanci ne wannan Nafi za ki kulle wa mutum gida saboda kishin hauka,tashi maza ki buɗe masa gidansa wawuya kawai,wannan ai hauka ne” na ji muryar Anna ta daki kunnena. Ina sauke wayar na dubi lokaci ƙarfe ɗaya har ta gota,ƙirjina ya wani irin doka da mugun ƙarfi,da sassarfa na sauka a gadon na nufi ƙofa na buɗe, ya shigo yana wani min mugun kallo,kallon da bai taɓa jifana da shi ba tsawon zamanmu,zuciyata na ji ta wani irin tsinkewa na ɗan raɓe na ba shi hanya ina cewa “sannu da dawowa

 

Bai ko tankani ba ya wuce ni, na bi bayansa,tun da na yi mai maganar turare ban kuma jin sa a jikinsa ba dumu-dumu sai kaɗan haka wani lokacin ma babu, banɗaki ya shiga ya fito,gabaɗaya sukuku nake ji na,tabbas ban kyauta ba wallahi ban san zan kai haka ba da ban kwanta ba ma gabaɗaya, yana fitowa wayarsa na ɗaukar ƙara,wallahi duk ɓacin ran da yake ciki sai da ya murmusa, ban ji me aka ce ba amma na ji ya ce “e, ta buɗe”, sai ya kuma saurarawa sannan ya ce “okay. Na gode, sai da safe” ya kuma saurarawa ya yi dariya sannan ya ce “me too”, wani irin kishi na ji yana taso min amma sai na yi ƙoƙarin dannewa, na nufi gefensa na zauna na ɗan langaɓar da kaina yadda nake masa a baya in na yi laifi na ce “mijin Nafi don Allah ka yi haƙuri wallahi zazzaɓi nake tun safe,bayan na yi isha’i ne bacci ya ɗaukeni ban san ka dawo ba sai da Anna ta kira Ni”, fuska a turɓune ya ce “duk dukan ƙofar da nake yi ba ki ji ba?”, Na gaji da zaman da muke yi,na bala’in takura, cikin mugun kaɗaici nake ji na, ban san lokacin da na fashe da kuka ba ina cewa “ban san lokacin da ka zama mara min uzuri ba, mijina ko kaɗan yanzu bana ganin ƙaunata a tattare da kai,don zaka ƙara aure sai ya zamo tsanin da ni zaka muzguna min,ban cancanci haka daga gareka ba,don Allah ka daina nuna rashin kulawarka da tausayi da uzuri a kaina,ban taɓa rufe maka ƙofa, akan za ka ƙara aure ba zan taɓa aikata hakan ba” na ƙare ina goge fuskata,sosai na hango sassauci a fuskarsa. Ya kama hannuna ya matse cikin nasa ya ce “to ya isa haka Nafi,raina ne yake ɓaci in na ga kina ƙunci duk akan abin nan,bayan ban tauyeki ta ko ina ba, don Allah ki sassauto da zuciyarki a yi abin nan cikin kwanciyar hankali ba tare da zukata sun taɓu ba,kin ji Nafisatuna” ya ce. Ɗan murmushi na yi na ce “in sha Allahu”

 

“Yanzu ya kike jin jikin naki?” Ya tambaya cikin kulawa. Sai na ji wani sanyi a raina na yi murmushi na ce “da sauƙi” a daren sai da muka faranta ran juna kana muka kwanta rungume da juna.

 

Kiran da ya shigo wayarsa ne ya tashe ni amma sai na yi lamo ban buɗe ido ba don bana jin ƙarfi,gani nake ma asubar ta yi sauri, cikin ƙasa da murya ya amsa yana cewa “Fari na har kin tashi?”

 

Cikin wata iriyar narkewar murya da shagwaɓa ta ce “ba kai ne ka hana ni bacci ba,sai tunaninka nake” ta ƙare da kukan kirsa, wani irin bugawa zuciyata ke yi da bala’in kishi, sai na rasa gane iskanci ne ko kuwa rashin hankali ya sa shi ɗaukar wayarta yayin da nake rungume jikinsa.

 

Ya yi dariya mai sauti cike da jindaɗi ya ce “lallai da alama ni zan amshi kambun” ta ƙyalƙyale da dariya ta kashe wayar, yana ƙoƙarin zame jikinsa na tashi ina jifansa da wani irin kallon takaici,ya bala’in shan jinin jikinsa ya shiga sosa kai yana cewa “dama kin tashi Farida?”

 

“Nafisa! Nafisa sunana ba Farida ba Malam” na ce ina jin wani tuƙuƙi a raina.

 

Cikin borin kunya ya ce “to da me na ce in ba Farida ba, me ya sa kike…” Bai ƙarasa ba na daka masa tsawar da ban san na iya ba na ce “Nafisa! Nafisa! Nafisa sunana ba Farida ba” …

 

#SHARE

1 Comment

Click here to post a comment