Tawagar Mutuwa Hausa Novel Complete
TAWAGAR MUTUWA Hausa Novel
Page1
Mallakar
Maman Sharifa ce
ARUMAI WRITER’S ASSOCIATION
_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa’azantawa ilimantarwa, nishad’antarwa tare da fad’akarwa da jama’a bisa harshen hausa
Bismillahir’rahmanir’raheem
A wani k’arni can da dad’ewa anyi wani mashahurin birni a kudancin k’asar Aseya wanda akewa lak’abi da Zaurul junn,
Anya Baiwa Ce Hausa Novel Complete
Birnin Zaurul junn ya bunk’asa ya cika da mutane da ‘aljanu birni ne wanda ya tara manyan matsafa, tare da manya manyan sadaukai,
Sarkin dake mulkin wannan birni ya kasance wani basamuden k’ato ne wanda ya kasance matsafi ne na hak’ik’a yana da tsagwaron k’arfin damtse, koda babu sihiri zai iya k’arar da manyan sadaukai gari guda ba tare da ya gaji ba,
Shiyasa mutanen birnin da ‘aljanun ciki suke matuk’ar tsoron sa, sunan wannan sarki Huzubul azab, yana da y’a guda d’aya tilo wacce yake matuk’ar k’auna mai suna Larisat,
Larisat ta kasance Kyakykyawa ta gaban kwatance, tana da wata baiwa a jikin ta wacce matsafan duniya suka kasa sanin ta, shikan sa sarki Huzubul azab yayi iya k’ok’arin sa wajan gano baiwar da gimbiya Larisat keda ita amma ya kasa, hasali ma idan ya matsa sai mudubin tsafin ya tawar watse,
Tin daga lokacin yake b’oye gimbiya Larisat baya bari ta fito koda k’ofar fada , iyakar ta cikin fada daga nan bayin ta su rakata cikin turakar ta,
Sarki Huzubul azab ya ci gaba da bincike a halarar tsafin sa tsawon shekara goma daga nan ya gane cewa, gimbiya nada karfin sihirin da ko shi ba shi da shi sannan tana da baiwar mallakar duniya,
Binciken sa ya tabbatar masa da cewa duk wanda ya’ auri gimbiya Larisat kuma ya rayu da’ita matsayin matar sa to tabbas zai mallaki duniya.
Sarki Huzubul azab yayi bak’in ciki mara misaltuwa lokacin da ya gano mijin ta ne kad’ai zai mallaki sirrikan tsafin dake jikinta,
Gimbiya Larisat tin tana k’arama mahaifin ta ya ba to horo da dabarun yak’i kala kala, zuwa yanzu gimbiya ta haddace da barun yakin sarki tsaf lokuta da dama idan suna gwabzawa takan sami nasara akansa, yana matuk’ar mamaki yadda take kai naushi Kuma zafin naushin ya wuce na sadaukai,
Yanzu gimbiya nada shekara a shirin cif a duniya, kuma wannan lokacin ne manyan sarakai da matsafa da attajirai suka bijiro don neman auren ta, domin ko zuwa yanzu labarin ta da baiwar da ke tattare da’ita ya shiga duniya , duk wani wanda ya shahara a duniya burin sa ya mallaki gimbiya Larisat, domin ya mallaki duniyar gaba d’aya,
Kamar kullum yauma gimbiya ta fito fada, yayin da bayin ta ke rik’e da rigar ta ta baya, fuskar ta ‘ a rufe idanun ta kad’ai ake gani, lokacin da ta shigo saida kowa ya mik’e tsaye don girmamawa,shikan sa sarki Huzubul azab saida ya mik’e ya rungume gimbiya Larisat suna murmushi sannan suka zauna a ta re,
Kujerar gimbiya Larisat tana kusa da ta sarki Huzubul azab kuma ta re suke gabatar da mulkin k’asar,
Sarki Huzubul azab ya kasance azzalimin sarki ne kwata kwata ba shi da imani sab’anin gimbiya Larisat wacce ta kasance mace mai tausayi, wannan yasa duk sanda sarki Huzubul azab zai yanke wani mummunan hukunci a kan wani sai ya bada umarnin a kaishi gidan duhu, amma duk da haka gimbiya tana k’ok’arin dakatar da wani zalincin sadai idan batasan an yanke hukuncin ba,
Bayan an tashi daga fada kowa ya watse ya rage daga sarki sai dogarai dake tsaye sai kuma boka Baharul junn ibn Rak’k’as,
Kan boka Baharul junn a k’asa ya kasa d’agowa ya fuskanci sarki Huzubul azab,har saida sarki ya dube shi ya ce””” ya kai amintacce na tabbas naga alamun damuwa a ta re da kai menene ya hana ka sanar mana, koda jin wannan batu daga bakin sarki Huzubul azab nan take jikin boka Baharul junn ya fara rawa cike da tsoron abinda zai biyo baya, boka Baharul junn ya matsa kusa da karaga yakai goshin sa k’asa alamar girmammawa ga sarki Huzubul azab,
Bayan ya d’ago kansa a k’asa ya ce “”ya shugaba na ka sani cewa tinda nake bincike a halarar tsafina bantab’a ganin abinda ya dugunzuma hankalina ba sai yau, koda boka Baharul junn ya zo nan a zancen sa sai yaja baki yayi shiru,
Saida Sarki Huzubul azab ya gyara zama ya d’aga kansa sama ya sauke alamar yana buk’atar jin abinda ya d’aga hankalin boka Baharul junn,
Boka Baharul junn ya ci gaba da cewa “”” a yaune na gano wanda zai mallaki gimbiya, saidai ba kowa bane face wani saurayi wanda na kasa ganin fuskarsa, abinda na sani a kansa shine, ya kasance ma’abocin wani bak’on addini kuma zai mamayi duniya,
Ba ta re da ya k’arasa maganar ba sarki Huzubul azab ya d’aga masa hannu sannan yayi masa alama da ya fita, kafin k’iftawar ido boka Baharul junn ya b’ace b’at tamkar bai tab’a wanzuwa a fadar ba,
Mik’e wa sarki Huzubul azab yayi a matuk’a fusace ya fara zagaye a fadar fuskar sa a murtike, cikin d’aga murya ya fara magana da wani irin sauti wanda saida ya razana dakarun dake gadin sa yace””bazan tab’a barin wani ya mallaki sirrikan tsafin dake jikin y’ata ba, ni Huzubul azab saina mallaki duniya, yana gama fad’in haka ya yi hanyar d’akin tsafin sa …
Mrs.Shariff
Comment & share please
[…] Karanta Littafin Tawagar Mutuwa Hausa Novel […]