Littafan Hausa Novels

So Ne Hausa Novel Complete

So Ne Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

*So ne*

Page 1

Labari da tsarawa

Maman sharifa ce

 

 

 

Littafi na na kud’i ne

SO NE & TAWAGAR MUTUWA

Ki sai d’aya na baki d’aya kyauta

akan 200

 

Phone nomber

08069167242

 

 

*JARUMAI WRITER’S ASSOCIATION

_{Marubuta masu aiki da jarumta domin wa’azantawa ilimantarwa, nishad’antarwa tare da fad’akarwa da jama’a bisa harshen hausa}_

 

 

©J.A.W

 

 

Bismillahirrahmanirraheem

 

*Da sunan Allah mai rahama mai jink’ai, dukkan godiya ta tabbata ga Ubangiji mad’aukakin sarki da ya bani ikon kammala Nana khadijah kuma ya bani dama na shiga sabon littafi na wato *SO NE* Allah ka bani ikon rubuta abinda zai amfani al’uma, Allah ka tsare mana alk’aluman mu, Allah ka taimaki k’ungiya ta abar alfaharina Jarumai writers association Allah kayi ruk’o da hannayen mu Amin.

 

 

Karanta Littafin Tawagar Mutuwa Hausa Novel

Madaidaicin gida ne irin na wanda yake da rufin asiri wanda ba za a sakashi cikin jerin masu kuɗi ba, kuma baya cikin talakawa,

koda na shiga ciki manyan soraye ne guda biyu irin ginin masu kuɗin nan, sai tsakar gida babba da ɗakuna guda huɗu a ciki ɗaya na matar gidan, ɗaya kuma na yaran ta mata, sai kuma na yara maza na farkon shigowa gidan shi ne na maigidan wanda yake saukar baƙi idan ya yi, kuma a nan ne suke haɗuwa dukansu suna karyawa da safe suna cin abincin dare tare da mai gidan, zan iya cewa gida ne wanda aka ginashi cikin tsantsar ƙauna da girmama juna, yaran gidan sun sami ilimi da tarbiyya shi ya sa na ƙasa yana girmama na sama da shi..

 

Abba shi ne sunan da yaran gidan suke kiran mai gidan da shi, zau ne yake akan wata babbar dadduma yayin da matarsa wadda suke cewa Umma take gefe tana zau ne itama..

 

Wata budurwa ce wadda za ta kai kimanin shekara goma sha tara zuwa ashirin zau ne kanta a ƙasa tana sauraron iyayen nata.

 

 

 

Abba ne ya yi gyaran murya sannan ya ce” Muhasin cikin tattausan kalami wanda ke nuna tsantsar nutsuwa wadda ilimin addini kaɗai ke samar da ita,

Inaso ki kula da kanki nasan kina da kamun kai kuma ina da tabbacin ba za ki bani kunya ba, ki sani university ba kamar secondary ba ce wannan wajene da kowa yake yin abin da ya zab’awa rayuwarsa, ba wanda zaice wani ya bari ki sani ke ba kowa ba ce kuma ba ƴar kowa ba ce, wannan makarantar akwai ‘ya’yan masu kuɗi waɗanda ba karatu yake kawo su ba, saboda koda sunyi ko ba su yi ba suna samun good results wanda kuɗin iyayensu ya ke saya musu, fatana ko kuma ince roƙona a gareki karki biyewa ƙawaye kar ki ga rayuwar wani taburge ki matuƙar ba koyarwar addinin musulinci ba ce acikin rayuwarsa, sannan ki mini alƙawarin riƙe mutuncinki domin shi ne rayuwarki, sannan uwa uba kiji tsoron Allah a duk inda kike, ban yarda ki nema a wajan wani ba matuƙar ina numfashi koda kuwa ɗan uwana ne , idan ki ka yi haka zan yi alfahari dake..”

Yana kaiwa nan ya gyara zama ya kalli Umma ya ce” Idan kina da abin da za ki faɗa mata ki yi sauri karta makara.”

 

Sauke numfashi Umma ta yi ta kalli Abba ta ce “Bani da abin faɗa komai ka faɗa mata sai dai in ƙara jadda kalmar rike mutunci da kuma addini sannan aji tsoron Allah.”

 

 

D’ago kanta ta yi ta kalli iyayen nata ta ce” Naji duk abin da kuka ce kuma in sha Allah zanyi ƙoƙarin kiyayewa, ba za ku yi kuka dani ba.” Albarka suka shiga saka mata tana amsawa cikin nishad’i,

Suna cikin haka mai napep ɗin da Abba ya ɗaukar mata ya yi horn a ƙofar gidan, tashi ta yi suna yi mata

addu’a ta fice ya ja suka kama hanyar B U K..

 

Tun da suka fara tafiya take jin nishadi a ranta tare da addu’ar samun nasara a cikin karatunta, sai da ya kaita newa site sannan ya ajiye ta ya juya, ta fara tafiya tana kallon ko’ina na cikin makarantar, komai ya yi mata , aranta tanaji cewa yau ita ce a bayero university, tabci gaba da tafiya cikin nutsuwa har ta kai inda hole ɗin makarantar yake ta d’akko wayarta ta fara kiran number wanda Abba ya ce ta kira idan tazo, bugu biyu ya ɗauka da sallama bayan ta gaishe shi ta sanar masa ta zo, kwatancen inda yake ya yi mata bata sha wata wahala ba wajan samun inda yake ,

tana zuwa ya yi mata jagora zuwa inda za ta dinga ɗaukar lecture ya gabatar da ita ya fice,

haka ta zauna cikin bak’unta har aka gama lecture ta fito..

 

Wurin da ɗalibai suke zama ta samu ta zau na tana nazarin abin da aka koya musu a class..

 

Gefen ta wani group ne na matasa su biyar mata biyu maza uku shugaban tawagar mata shi ne da bazai wuce shekara ashirin da biyar ba Kyakykyawa ne sai dai ba ajin ƙarshe ba yana da haske amma ba za’a kirashi da fari tas ba dogo ne sosai me matsakaicin kyau..

 

 

Kamar ance ya kalli gefen sa ya juyo ya yi arba da wata halitta, rass gabansa ya faɗi abin da bai taɓa ji akan wata y’a mace ba, saurayin da ke gefen sa ya kula da inda Abokin nasa ya karkata idon sa, shima sai yabi wajan da kallo, sannan ya dawo da kallonsa zuwa ga abokin nasa , da ido ya yiwa wani alama cikin sauri wanda aka yiwa alamar ya tashi ya je inda take…

 

Tsaye ya yi akanta ya ce “Barka da hutawa y’an mata.” Bata kalleshi ba bare ya sa ran zata amsa ganin haka yasa shi saurin ce wa” Ki yi haƙuri Ms ne yake kiranki.”

 

Ɗagowa ta yi tanuna kanta tare da cewa “Ni?” Ɗaga mata kai ya yi alamar eh, a hankali ta miƙe ta nufi inda ya nuna mata tana kiran sunan Allah a ranta, tana zuwa ta yi musu sallama ta tsaya kanta a ƙasa, nan fa ragowar mutanen wajen suka fara rige rigen amsawa, banda Ms da ya kafe ta da ido,

sai da na kusa da shi ya zungure shi da ƙafa sannan ya yi ajiyar zuciya ya kalle ta ya ce” Sabuwar ɗaliba ko? “Eh kawai ta ce sai da ya jinjina kai sannan ya kuma cewa” Wane cors,?” Kanta a ƙasa ta ce” jonorlist.” taɓe baki ya yi ya kuma cewa “Suna.” ta gaji da tambayar rainin hankalin da ya ke mata don haka a taƙaice ta ce” Muhasin”. Ihu abokansa suka saka har suna haɗa baki wajan cewa “”macth” kallonsu ya yi kowa ya yi shiru sannan ya maida kallon sa gareta ya buɗe baki kamar anyi masa dole ya ce” Sunana Muhsin Sale Bako inkiya Ms Bak’o.” Ok zan iya tafiya shine abin da ta ce cike da Jin haushin Ms Bak’o..

 

Sai da ya Gama ƙare mata kallo sanan ya ce “jeki.” Da sauri ta juya tana tinanin wannan waye shi dahar zai yi mata wannan rainin hankain gurin da ta tashi ta koma ta zau na ta juya musu baya tana ci gaba da tunanin ta..

 

Sallama taji a kanta , koda ta ɗago kanta sai taga wata matshiyar budurwa wacce bazata wuce sa’ar ta ba “Zan iya zama budurwar ta ce. “Murmushi Muhasin ta yi ta ce” Wa’alaikissalam bismillah zau na.” Ok na gode” shi ne abin da budurwar ta ce, bayan ta zau na ta kalli Muhasin da murmushi a fuskar ta ta ce “Na ga Ms ya kiraki ko? “”Eh kawai Muhasin ta ce tana kallon budurwar. Itama kallon ta take sannan ta gyara zama ta ce” Nima sabuwar ɗaliba ce kamar ke sai dai na rigaki zuwa da sati uku, yadda naga Ms. yana nuna isa da tak’ama da kuma iko akan ɗalibai abin ya bani mamaki, kowa yana son mu’amala da shi ba maza ba mata , a yadda aka bani labarin sa yana da girman kai sosai ,shi ba kowa bane a makarantar nan fa ce zak’ak’urin dalibi wanda ake ji da shi a fannin ƙoƙari , a yanzu dai shi ne lamba ɗaya, bayason halɗa da mace, sannan yana da wulak’anci, y’ammata da yawa suna son sa amma baya kulawa, kin san abin da yake bani mamaki?”

 

Ajiyar zuciya Muhasin ta sauke sannan ta ce “A’a saikin fad’a.” Waɗancan y’ammatan guda biyu da suke rayuwa tare , tare suke zuwa kuma tare suke tafiya,duk da ance baya hulda da mace..

 

 

Gyara zama Muhasin ta yi sannan ta ce” Me ya sa kika damu da al’amuransa ? ko dai kema kina cikin masoyan nasa?” Dafe ƙirji ta yi ta ce ni!!? rufamin asiri karatu ya kawo ni ba soyayya ba, kawai naga ya kiraki ne bansan me ya sa ya yi kiranki ba , kuma ina tsoron karsu cutar da ke.” Murmushi Muhasin ta kuma yi ta kalle ta ta ce” Me ya sa bakya so ya cutar da ni?” Haka kawai hankali na be kwanta ba da suka kiraki, da fa kafaɗar ta Muhasin ta yi sannan ta ce” Manzon Allah (saw) ya ce idan duniya da abin da ke cikinta za su taru da nufin su amfanar da kai da wani abu, to ba za su amfanar da kai da komai har sai abin da ya kasance acikin ƙaddarar ka, kamar yadda basu isa su cutar da kai da komai ba sai abin da Alƙalamin ƙaddarar ka ya rubuta, ina so kisa a ranki cewa babu wani abu da bawa ya ‘isa yabyi miki har sai Ubangiji ya ƙaddara faruwar haka a gareki sai dai akwai sila…

 

 

 

“Allahu akbar ashe da malama nake tare, gaskiya na ji daɗin haɗuwa da ke fatan za ki karb’e ni matsayin y’ar uwa..

Murmushi Muhasin ta yi ba tare da ta ce komai ba.

 

Sai da budurwar ta tashi tsaye sannan ta kalli Muhasin ta ce” Sunana Fatima Abba Ahmad amma ana kirana Ummulkairi.” Itama miƙewa ta yi cikin fara’a ta ce” Sunana Muhasin Ibrahim Abubakar..”

 

“Wow Ummulkairi ta ce amma sunanki akwai daɗi sai dai ina ganin murage tsawon suna yenmu, kallon rashin fahimta Muhasin ta yi mata…

 

“Sorry sis ina nufin kidinga kirana da Khairee ni kuma zan dinga cemiki M I ina fatan sunan ya yi miki. “Ya yi sosai Muhasin ta ce tana kallon agogon hannunta kafin ta ce “muje muyi salla lokaci ya yi.” Ok muje Khairee ta ce ta na jan hannun MI suka wuce…

 

 

Mrs Shariff

Comment &share please🙏🏻

Add Comment

Click here to post a comment