Wani Uba Hausa Novels Complete
WANI UBA*
Page 1️⃣
*SECRET SUPER STAR
(Tauraron boye )
Wanna labari True life story ne ( wanna labari ya faru da gaske)
A guje tashigo gida tana kiran innanmu innanmu da iya karfinta duka gidan Saida ya amsa kajin gidan sai guduwa suke da awakai suna neman gurin buya saboda yadda tashigo a guje wata mata Naga nafito daga wani daki saida na qaremata kallo Naga kamanninta da yarinyar da tashigo matar bazata wuce shekara 40yrs ba.
Ajiyar zuciyar matar ta sauke saboda inda sabo ta Saba da wannan shirmen na Hafsatu
Innanmu wlh anacan ana danbe da Hajaru da Hadiza Yar gidan malam liman
Saida gaban mamarsu ya fadi saboda tasan fada ba halin Hajaru bane
Bata jira Hafsatu ta qara koda kalma dayaba ta zari Hijabinta tayi waje gurin rabon fada.
Fada suke sosai anyiwa Hajaru taron dangi sun hayeta kamar sun samu bishiyar mangoro dagudu innanmu ta garaso tana daga Hadiza busa Hajaru data gamacin baqar azaba sabo ta daku.
Mutane sosai suntaru domin kallon fada sabuda niyar rabawa saboda ba halin Yan gauyen bane rabon fada saidai su tsaya suyi kallo koda kuwa kisan kai za’a babu ruwansu
Innanmu taja hannun Hajaru ranta a mugun bace ko bokitin dibar ruwan basu tsaya daukaba ta tasa keyarta gaba tana tafe tana mata fada saboda rayuwar ta batason rigima shiyasa Bata shiga sabgar kowa a kauye.
Yan Boarding Hausa Novel Complete
Suna shiga gidan awakai suka fito daga dakin innanmu dagudu
Wani uban salati ta buga inalillahi wa’inna ilaihi rajiun gaba daya awakai sun canye dan garinda ta samo domin tayima yaranta tuwo.
Dagudu Hafsatu tabi awakan da gudan katon iccenta a hannu daniyar duk akuyarda tacinma saita buga matashi
Bazato ba tsammani taji anjawota kamar kayan wanki anjefar saiji kayi timmmm tafadi cikin kasa wani uban ihu ta buga Saida gidan ya amsa saboda yarinyar akwai katuwar murya saboda Kuka datake yawanyi Kuma tamayar dashi abincinta❤🔥
Wata katuwar mata nagani doguwa gata da kiba sosai kamar muta nai Niger farace Kuma tanada kyau ba laifi sai huci takeyi kamar wadda tagama danbe kokuma tayi gudun tseren ~50km~ kedan ubanki akuyar uwarki ce kota ubanki dazaki bita da gudu wlh idan kika kuskura kika karyamin akuya saina kaririyaki shegiya Mai zubin Yan ruwa Mai baki kamar na uwarta dankinga uwarki bata akuya a gidan Nan shiyasa kikeyimin bakin ciki to wallahi kulelenki da awakai na komaiyace ke saidai kici kanki Aheee kinji na gaya miki shigiya baka Mai bakar aniya
Aekuwa kamar Hafsatu jira take matar takai aya itama ta dauka Adin uwata batada akuya amma tanada abunda yafi akuya a gidan Nan saboda tanada gargen shano Kuma tanada mu Kuma Yara Mata Rahma ne eheee kuma Ni ba shegiya bace da uwata da ubana awaki kuma sai naci ubansu idan suka qara shigar Mana dakinmu
Wani gigitancen Mari taji ta sauka a kumatunta har sau biyu Wanda yasa ta Kara wuntsilawa daga tsayenda take baki shiryaba Wanda Kuma yayi sanadiyar hadiye sauran maganar ta takeson qarasawa
Kuyi hakuri da wanna
Manage
Taku harkullun
*SECRET SUPER STAR
(Tauraron boye)
Yar mutan SOKOTO
WANI UBA
Page 2
*SECRET SUPER STAR
( *Tauraron Boye*)
Wanna labari True life story ne
(Wanna labari ya faru da gaske)
Wani zabgegen mutun Nagani tsaye kamarsu daya sakk da Hafsatu kallo daya zaka yi mashi kagane shine mahaifinta amma farine sull dashi masha Allah ga kyau ga tsayi gakuma uwa uban cikar haiba kallo daya zakayi mashi kasan latcizo ne(tsoho) Wanda shekarun shi kobai kai 60yrs ba sai kadan amma fah akwai kyau iya kyau tsofanshi bai boye kyauwonshi bah.
Shine Wanda ya zabgawa Hafsatu mari, ke Dan uwarki ubanwa ya daure miki gindin zagin *Larai* sa’ar kice ko sa’ar uwarkice eyeee ba magana nake miki ba kinwani sakomin idanu kamar na uwarki shegiya mai baki kamar bakin zunubi.
Duk wannan abun da akeyi innanmu na tsaye batada ikon magana saboda Mai gaiya Mai aekine ke magana wato mai gida
Saida nagama rera kukana kamar mai rera Waqa kukan da idan na Fara banajin rarrashin ba Yan gidanmu ba har makwafta sai sunji na addabesu anan nayi bacci dana gama kukana wanda shine dabi’ata idan na gama kuka anan nake bacci saidai a daukeni.
Wata Aza babbiyar yunwace ta tashe Ni banshirya ba karfe uku daidai na Rana sai hamma nakeyi kamar zanci Babu, innanmu nagani tana damun fura cikin Wata qatuwar kwarya bansan lokacinda na washe Mata fararen hakorina ba ( teeth) Ina Mata dariya hade na murmushi gaisheta nayi ta amsa tare da cewa natashi na wanke bakina nayi alwala nazo nayi sallah aekuwa kamar jira nake natashi a guje nayi waje har ina karo da kayan dake tsakar gidanmu Saida nayi sallah sannan aka bani hura nasha na koshi fura damun hannu gashi Kuma da kan hannu 😋🤤 Saida nasha na koshi innanmu Ina Hajaru da mairo kosun fita talla ne natambaya Ina kallon innanmu wadda ta tsareni da ido tana bina da kallon suna islamiyya kawai ta kawar dakai kema maza tashi ki wuce ankusa tasowa kisamu koda addu’ar tashi daga makaranta Saida na cinno baki kafin nayi gaban madubi Ina kallon fuskata fauda (powder) nashafa Wanda ake cewa kafin bleaching nadauko jan janbaki nashafa kamar wadda xataje kasuwa ko gurin buki
Nazari kodan Dan Hijabina nayi waje da gudu saboda komi nawa da guda nakeyinshi.
Kuyi hakuri da wannan
manage🙏🏻🙏🏻🙏🏻
Taku harkullun
*SECRET SUPER STAR
( *Tauraron Boye*
Yar mutan SOKOTO
WANI UBA
page 3
*SECRET SUPER STAR
( *Tauraron Boye*)
Wanna labari True life story ne
(Wanna labari ya faru da gaske)
Ina tafe Ina Yan waqe waqe🎶🎶idan kaganni ka rantse ba islamiya nayiba naci uwar kwalliya
Ina tafe Ina addu’ar Allah ubangiji ya hadani da Indo yau sainaci uwarta jiya ta tsokaneni ta gudu gida aekuwa kamar daga sama Nahangota tana fitowa daga gida da tukunyar laka akanta daga gani gurin tallar pure water zataje aekuwa tana gani na takwasa aguje tasaki tukunyarda ke kanta nan take ta watse aqasa duk ta farfashe wata dariya nasheqe da ita harda riqe ciki saboda dariya aekuwa da gudu naje na labe a kofar gidansu ina jiran fitowarta, inajin dakun tafiya alamun mutun nazuwa na kara qafa ta saiji nayi Timmmm abun ya fadi qasa dagowar da zanyi Naga innarsu Indo ce na karama qafa ta Fadi nantake na ari ta kare na zuba da gudu🏃🏻♀️ sai gidanmu inashiga gida ban tsaya ko inaba sai dakin innanmu na kara kutsa kaina sai uwar daka ina sauke ajiyar zuciyar aekuwa saijin sallamar mutane nake innanmu na sallame sallah tayi waje saboda hayaniya datayi yawa Lallabawa nayi naje gurin window (taga) na labe Ina leqawa Naga bakin innarsu Indo yafashe harda jini ido na zaro bakinta ya kumbura ya koma kamar ganda 😂😅 karaff naji an cafkemin hannu Ina dago kaina Naga babanmu ne ya rikeni wani uban ihu na zuba Ina magiyar yasake Ni baitsaya ko Ina Dani ba sai tsakar gidanmu ya wullardani Saida na fadi kasa nantake diyan innarsu Indo sukayo kaina kamar sun samu kayan wanki Saida sunkayimin liqiss suka jiuya suka bar gidan.
Bantashi a gurin ba sai bayan magrif inashiga daki na haye gadon Kara sai bacci mai nauyi yayi awon gaba Dani.
*KANO*
Babban gida ne daya qunshi bangare(Part) hudu Wanda aqalla kowane bangare yana daukar mace 2 harda yara sai gurin ajiye motoci (parking space) Wanda zai dauki motor shida koma fiye da haka
Da sanyi safiyane gidan tsitttt kamar Babu mutane a gidan sai kukan tsontsaye da tumakai daga gani gidan ana kiyon Dabbobi( Domestic Animals)
Karar motar daukar Yara naji fiiiiii wato school bus aekuwa saiga Yara takowane bangare suna fitowa
Can Kuma bayan kamar 20mtns sainaga yan Mata su uku sunfito daga wani parts wata tsohuwa fara tas da ita ta rakosu tana yimusu adawo lafiya tare da musu addu’ar samun nasara dakuma dawowa lafiya
Bayan tsohuwar nabiyo Ina binta da kallo masha Allah tsohuwa ce amma akwai kyau ga fari gakuma uwa uba dukiya data zauna farinta harwani walkiya yake tana sanye da Dan karamin glass (tabarau) a idonta falon data shigo nabida kallo so Masha Allah ya hadu iya haduwa, karamin falo ne Amma yaji kaya na alfarma babban falo ne da kujeru guda biyu 3siter dakuma 2siter sai katuwar carpet maroon colour sai hiluluwa suma maroon colour sai dispenser itama Maroon sai tv dake kunne ankamo tashar *sunnah TV*
Falon yayi kyau sosai gwanin sha’awa komi tsaff tsaff Saida na garewa tsohuwar kallo sainaga daga gani tana cikin damuwa dukkuwa wannan uwar daular datake ciki.
Gakuma wani abu daya dauremin Kai tana bala’in kama da fadimatu (innarsu Hafsatu)🤔
Kuyi hakuri da wannan
Manage🙏🏻🙏🏻🙏🏻
Taku harkullun
*SECRET SUPER STAR🌟*
( *Tauraron Boye*)🧕🏻🧕🏻
Yar mutan SOKOTO
WANI UBA
Page 4
SECRET SUPER STAR
( *Tauraron Boye*)
Wannan labari True life story ne
(Wannan labari ya faru da gaske)
Kishiya a Yau Hausa Novel Complete
Koda na tashi da safe jikina gaba daya ciwo yakemin saboda dukanda nasha jira innanmu Nagani zaune tana sallar walha aekuwa bansan lokacinda na wuntsiloba Saida na fado timm kasa duniya Babu abunda na tsana kamar na Rasa sallar asuba har kuka nake idan bansamu sallah ba wanke bakina nayi tareda alwala nazo a gurguje nayi sallah nasa kodandin uniform Dina riga Fara sai wando green sai farin Hijabina dayasha dinki da allura da zare kwalliya na cancada Wanda kullun nayita sai ansa na gogeta kafin nashiga aji
Ruwan kunu/koko nasha babu ko sugar ina turo baki saboda nafiso nasha fura kokuma abani kudin tara😄(Break) mutafi musha hanjin Ligidi da Dan tamatsitsi😆 saida na duka innanmu tayimin addu’a kafi na kwasha aguje nayi waje ina zuwa baki kofa naci karo da babanmu gaisheshi nayi ya amsa sama sama kafin yabani hanya nayi waje abuna Ina tafe ina Yan waqe waqe Na akwaini dason Waqa
Saida na gama Yan labe labe na jikin bango kafin nayi wuff nashige cikin dalibai saboda har anriga antashi break.Karfe daya 1:00pm daidai aka tashemu daga makaranta kaina na ciwo sosai,tare da kawayena muka jero zuwa gida
Inashiga gida innanmu na tadda tayi takumi hawaye na bin kuncen ta da gudu naje na fada jikinta saboda mutane Dana gani sosai kamar anyi mutuwa aekuwa kamar daga sama naji babanmu nacewa kowa ya tashi ya watse
Bayason munafurci daga Allah ya dauke mishi lalura
Diya mace ko wahala daga Allah ya daukemin nauyi kowa ta tashi tabarmin gida idan ba hakaba nadawo daga gurin sallah duk abunda nayi mata ita ta jawa kanta. Idan kunne yaji gangar jiki ya tsira.
Fuuuuuuu kamar iska haka ya wuce daya bayan,Matan gidan suka fara watsewa kowa nayin Allah ya waddarai da hali irinna Amadu
*TUSHEN LABARI*
Malam Ahmad Aliyu Balarabe shine asalin sunan Amadu haifanfen Dan sokoto ne awata karamar hukumar *illela local government* Su hudu mahaifinsu ya haifa kuma rainon ubane mahaifiyarsu ta rasu tun suna yara kuma mahaifinsu bai kara aureba saboda kasuwancin shi daya sama gaba.
Yana kula dasu daidai gwargwadon yadda yake iyawa ya basu ilimin Addini sosai, Shu’ibu shine na farko sai Musa sai Amadu shine na uku mace ce ta hudun su lubabatu, lubabatu dai bata rayuba saboda ciwon sanqarau daya kamata batare datayi wata doguwar jinyaba tace ga garinku rai yayi halinsa,
Sunan Mahaifinsu Aliyu Balarabe Dan asalin garin Yola, almajiranci ya kawoshi garin sokoto yasamo sunan Balarabe ne saboda kwata kwata baya kama da hausawa kuma baya kama da fulani idan ba magana yayiba ka rantse da Allah cewa Balarabe ne.
Yayi karatu sosai ta fannin addini kuma yayiwa musulunci hidima sosai,
Ya fara *Dako* ne a tasha domin samun abun dogaro dakai, daga bisani Kuma yayi kicibiss da Malam Auwalu Wanda hamshaqin mai kudi ne a wancan lokacin shiya daukeshi a matsayin limamin masallacin da ke gofar gidanshi wanda shine sanadiyar Arzikinshi,
“Dadin zama kesa Agola ya koma Dan gida” saboda mutunci dakuma girmama dake tsakanin su yasa malam Auwalu
Aurawa Aliyu yarshi Hauwa’u.
Kuyi hakuri da wannan
Manage
Taku harkullun
*SECRET SUPER STAR*( *Tauraron Boye* )
Yar mutan SOKOTO
*WANI UBA*
Page 5&6
*SECRET SUPER STAR*
( *Tauraron Boye*)
Wannan labari True life story ne
(Wannan labari ya faru u gaske)
Hauwa’u kyaykyawa ce sosai amma fa kokadan bata kamo kafar Balarabe da kyauba saboda ita baqar fatace,
Sunyi zaman aure cikin so da qauna dakuma mutunta juina har Allah ya albarkace su da samun Yara hudu Dare daya Hauwa’u ta tashi da zazzabi Wanda Nan take rai yayi halinshi,tabar yaranta guda hudu masu yimata addu’a,
Shu’ibu,Musa, Amadu dakuma lubabatu.Duk cikin yaran malam Balarabe Amadu yafisu kyau kuma shine gaba daya sak kamannin Mahaifinsu yataso Dan gayu Kuma shine baida sana’a shidai idan yayunshi sunje sunyo bida yayi masu dadin baki su bashi,
Allah ya jarabci mahaifiyarmu Fadimatu da masifar son Amadu saboda Dan gayune Kuma gashi kyaykyawa son kowa qinwanda ya rasa,bashida gurin kushewa ,Amma kwata kwata dangin ta Basu sonshi saboda baida sana’a.
Wannan shiya janyo sabani tsakanin dangin mahaifiyata da kuma shi maihaifin namu
Wannan shine sanadiyar rugujewar rayuwarmu wannan shiya janyo mana qiyayyar dangin uwa
Suka manta damu, batare da sunsan halinda muke cikiba,basa kawo Mana ziyara, basu damu dasusan halinda muke cikiba.
Kuma kowa yasan yara mata suna fuskantar wannan matsalar most especially idan suka bujirewa zabin iyayensu sukace suga abunda sukeso, shine abunda ya zanyo manah wannan halinda muke cikin kuma Allah ya hadamu da *WANI UBA* Wanda bayason ya’ya Mata yafison Yara maza saboda Yana ganin yara maza kamar liability ne a rayuwaShiyasa bamuda wani amfanin a gurinshi😭
Mahaifiyarmu takasa komawa gurin mahaifiyarta domin kuwa tasana diyarta mahaifinta ya kamu da ciwon zuciya gashin itace kawai mace a cikin yaranshi Yana sonta sosai yayi Mata gata gatanda bakowace Yar mace ke samunsa bah
Tunda bayan aurenta ya rasu suka raba qado suka tattaro haqinta suka kawo mata🙇🏻♀️ tasamu shanaye har guda hudu Sai awakai talatinTunda mahaifinmu yaga wannan dukiyar Saida yaga bayanta gabaki daya saida yazo yayi mata dadin baki ya lallabata tabashi Wai akaima bakyayi (masu kiwon shanu a daji) shanuwa daya kawai tabari cikin shanun saboda. Ciki dake gareta idan ta haihu zamu samu kudin cin abinci, tundaga ranar da tabada dukiyar ta Bata qarajin halinda take cikiba kuma haryanzu maganar ake hasalima idan tajewa mahaifin mu da maganar saidai ya korota da baqaqen maganganu da Kuma zagi,Wannan shine labarin danasani a rayuwar mahaifiyarmu saikuma Wanda nake ganin ana nuna mana yanzu danake da wayau
*CIGABAN LABARI*
Saida nagama kukana na tashi nashige daki nacire uniform na nacanza kaya zuwa atampa Koda na fito gaba daya mutane kowa ya watse sai mahaifiyarmu dake zaune tayi ta gumi duk ta rame ta qara baqi sai hanci da idanuwanta dasuka qara fitowa.
Fuskarta na shafa saboda nakira ta bataji ba murmushi tayimin tareda cewa mamana Allah ubangiji yayi maki Albarka kinji inaji a jikina kamar nima bazanyi tsawon Rai ba ki kula da kanki kiriqe mutuncin ki, kuma kiji tsoron Allah a duk inda kike,kiringa tunawa da Allah kinji ta qara shafa kaina, Kai na girgiza tareda cewa innanmu bazaki mutuba saina kaiki makkka na Gina miki gida babba,amma Banda babanmu bayasonmu… diyan inna larai kawai yakeso da sauri ta girgizamin Kai tare dacewa natashi naje gidansu Gambo idan akwai surfa na karbo Mata tayi gobe ta samu na bamu kudin laraba…
Ina tafe inayan waqe waqe na kamar kullun harnakai inda ta aekeni…. inazuwa nagaisheta nagawa Maya aekeda akayimin, Allah sarki Hafsatu kicewa mamanku yau Babu surfa harmun bayar ayimana saboda munga anyi rasuwa Amma kigaya mata gobe insha Allah zan aeko da ita kigaisheta kinji naji ance Amadu yahana zaman makoki shiyasa bamu zoba Amma kigaisheta kinji,Koda take wannan maganar Ni hankalina bayama gurinta yana can gurin kallon dangali danaga anjera kwanuka sunfi ashirin ana rabawa Masha Allah nace saboda yan gidan sunnunka gidanmu dayawa amma gashinan su Mahaifinsu yana basu abincin Rana kawai naji tsanar Mahaifinmu yaqara shigata hawaye kawai naji zirrr suna zubomin da saurin na goge tareda jiuyawa zantafi kawai naji talatu Kishiyar Gambo nakirana zoki karba hafsatu kinji ina karbowa nayo gida sai dadi nakeji…
Zanshiga soron gidanmu kenan naji Kawo (Uncle) shu’ibu Yana cewa babanmu ae wallahi Amadu kawai katattarasu kawai ka tura Birni aeyara Mata Arziki….. Kaga idan katurasu Birni basaikaje bidaba Lagos saidai duk Wata(month) aringa turoma kudin aekinda sukayi kaii Ina nai tabbatar maka idan sukayi sa’ar gidan aekin Mai kyau…..Hmmm saikaga sunzama jari kadai Kane minake nufi,kaga jibi saude zata tafi Kano kaiwasu yara kawai saika hada da naka Basu uku suka rage bah yanzu kaga saika tura biyu kabar daya koya kaga amma fah shawara ce na baka…. Aa gaskiya yaya nidai nafiso natafi bida kawai,banaso nadauki haqqinsu na rabasu da uwarsu Kuma kabarni kawai na tafi,aedana nasan ba daukar shawarata zakayi ba saikayita. Zama cikin wahala ana nunama Annabi kana rufe ido furrrrrrr saigashi yafito daga gidan karo mukaci dashi gaba daya Dan dankalin Dana samo saida ya zube kotsayawa kallo na baiyiba ya wuce abunshi ajiyar zuciya na sauke cikin Raina nace Ashe babanmu nasonmu Allah sarki…..
Gida nashiga banma damu dana tattara dankalin da bareba kawai nashiga gida…… innanmu nazauna tayi tagumi tana jiran dawowata mamana Ina kika tsayane kinshanyani Saida na turo baki sannan nace innanmu ke kayan wankice dazan shanyaki…….sunce yau babu surfa saboda anyi rasuwa saidai gobe zasu aeko dashi innanmu ina Hajaru ne tudana dawo ban gantaba…batada lafiya zazzabi kinganta can kwance zazzabi Saida nazaro ido danaji tace zazzabi kinwani zaro ido kina kallo na zokije gidan malam ki karbo Mata rubutu Tasha kotaji sauki kinji….waike innanmu kowane ciwo saikice mutun yasha rubutu kawai kice Baba ya bada kudi kikaita asibiti (hospital) Amma komi sai kuce malam malam….Mamana nikike gayama magana rashin kunyar Kuma yau akaina zata gadane nizan aekeki kice bazakije bah Saida na qara turo baki kafin nace nifa innanmu ba rashin kunya nayi miki ba yanzu zanje amma saina shan fura kawai nayi shigewa ta daki… Kai kawai ta girgizamin kafin tace Allah ubangiji yashiryamin ke Mamana bansan lokacinda Zaki Dana wadannan halayen nakibah naji metace Amma nayi shigewa ta ina amsawa da Ameen Kwance na tadda ita ciwon kwana daya kawai duk yasa ta fada tayi wani haske kamar Mai ciki kamar yadda Naga wasu masu ciki sunayi…. Saida na sauke ajiyar zuciya kafin na qarasa inda take Ina taba jikinta zafi kamar wuta idonta suyi yellow hakama tafin hanunta bansan wane ciwo ba ne wannan Amma gaba daya yayuna dasuka rasu da wayau na haka nake ganin jikinsu yana komawa kafin su mutun…..A guje nafito daga dagin nayi gidan malam kamar yadda innanmu ta umarce ni inazuwa na taddashi zaune a soro ya shinfida tabarma yana rubutu a Allo kamar kullun……Dan tsoho mairan qarfe malamin soro,,, Na’am matar Dan tsoho.
Kuyi hakuri Da wannan
Manage🙏🏻🙏🏻🙏🏻
Taku harkullun
*SECRET SUPER STAR*🌟
( *Tauraron Boye* )🧕🏻🧕🏻
Yar mutun SOKOTO
#share plz
Fisabililla🙏🏻
Add Comment