Soumaya Majnoon Hausa Novel Complete
SOUMAYYA MAJNOON!!*
(The innocentmad)
PAIDBOOK
*Writting By*
Fatymasardauna
*Wattpad*
@fatymasardauna
*FREE PAGE*
*18/11/2021*
*Chapter 1*
#Firstday
*ANNA’S HEALTH COLLAGE ABUJA*
*5:00 pm*
Yamma ci ne mai dadi, haka kuma yau din rana ne da ya kasance na musamman wato Jumma’a, ranan da yake d’auke da albarka da kuma rahamar Ubangiji kala kala.
Wannan dalilin yasa sassanyar iska mai cike da tsananin dadi, da kuma sanya shauki ke busawa, a gaba daya ko wani lungu da sak’o dake cikin shahararriyar makarantar koyon likitanci, dake cikin garin Abuja wacce tayi suna sosai, kana take kuma d’auke da yawan d’alibai maza da mata.
kamar kuma yanda d’aliban suka saba akoda yaushe, haka yau din ma takasance, domin kuwa 5 na yamma na cika, babban k’arrarawan dake sanar dasu lokacin tashi, ya soma bugawa yayinda karansa ya shiga karad’e ko Ina dake cikin makarantar.
K’aran daya sanya da yawan d’aliban dake cikin makarantar farinciki, kasancewar abune da kowani d’alibi ya saba, cewar matuk’ar aka yi Nisan zango acikin makaranta to akwai gajiya da kuma yunwar dake damun d’alibi.
Jin k’aran k’ararrarwan tashi ne kuma, yasa kowanne dalibi dake cikin makarantar, soma d’aukan jakunkunan su suna fitowa izuwa waje dan komawa gida.
Nana Maryama Hausa Novel Complete
*”SOUMAYA!”*
*”SOUMAYA!!”*
Cewar wata matashiyar budurwa dake tsaye, tana me kokarin rataya katuwar school bag din dake hannunta, Wanda kuma ahankali ta dan rank’wafo da kanta, tana me kallon wacce ke zaune agefenta.
“Soumaya wake up kodai bacci kikeyi ne?.”
Matashiyar budurwar ta fad’i haka tana me gyara tsayuwanta, tare kuma dasa hannu ta dan zunguri wacce ke gefen nata, wanda kuma ita d’ince ake kira da suna.
*SOUMAYA*
(Gift of God)
Ahankali ta d’ago kanta wanda ta kifashi akan desk almost 15mn ago.
Sam ba bacci takeyi ba, hasalima duk abunda k’awar tata ke fad’a tana jinta.
Numfashi ta d’an sauke tare da d’ago manya manyan Oily eyes dinta, masu matukar kyau ta kalli abokiyar zaman nata.
Hakan da tayi dinne kuma nima ya bani daman kallon, tsananin kyawun dake kwance akan fuskar matashiyar budurwar, mai suna Soumaya.
Idanunta da suka d’anyi ja ta lumshe, tare kuma da bud’e su alokaci guda.
Cikin unique voice d’inta, mai dadin amo da sanyin sauti, tamkar ana busa sarewa tace.
“What happen NOOR (Light)? ba bacci fa na keyi ba, just I’m tired.”
Ta k’are maganan tana me d’an kwantar da wuyanta gefe.
“What happening kike tambaya, time din tashi yayi, kalla class kowa ya watse sai nidake kawai, oya tashi mu tafi kodai zaman class dinne bai isheki ba?.”
Waccce aka kira da suna Noor ta fad’a, tana me kokarin fita daga roll din da bencin su yake.
Fuska Soumaya ta d’an kwab’e, kana cikin yanayin gajiya, da kuma yunwar dake cinta tasa hannu ta d’auki jakarta.
Domin kuwa zuwa lokacin har Noor ta kai kofar fita daga cikin ajin.
Wannan yasa cikin sauri ta rufa mata baya, tana me kokarin rataya jakanta bisa shoulder dinta.
Atare suka fito compound din makarantar tasu, wacce ke d’auke da tarin d’alibai.
Saidai kuma kamar yanda suka saba, kowani d’alibi harkar gabansa yakeyi, yayinda da yawan wasu daga cikin d’aliban ke tafiya izuwa wajen motocin da suka zo d’aukarsu.
Kasancewar makarantar tasu ta masu kudi ne, shi yasa duk wani d’alibin dake cikinta to babansa wanine, kuma kowa a motar gidansu ake zuwa d’aukarsa,
sab’anin mutum d’aya wato SOUMAYA.
Yarinyar da zuciyarta ke cike da rauni, haka kuma yarinyar da k’addara da kuma k’alubalen rayuwa ke gudana acikin jikinta kamar jini.
Har lau kamar koda yaushe anutse take tafiyanta, yayinda ta sadda kanta k’asa, saidai ahankali take matse lips dinta, da kyawawan teeth dinta.
Ahaka har suka iso babban filin parking space din dake cikin makarantar.
Isowarsu wajenne kuma yasa Noor sakin ajiyar zuciya, saboda hango Musa driver’n gidansu da tayi.
Cikin jin dadi tace.
“Yawwa Soumaya yau musa driver yazo da wuri, kinga har ma zamu samu muyi dropping naki agida, basai kin shiga taxi dinnan da kika saba shiga ba, duk da na fahimci cewa shiga taxi din yana miki dad’i.”
Noor din takai k’arshen maganan tana me juyowa, ga Soumaya wacce ke kokarin ratsa cikin motocin dake wajen ta wuce.
“Soumaya.”
Noor ta kira sunan k’awartata, tare kuma da Dan tsayawa tana kallonta.
Ganin yanda Soumaya’n ke d’an cizon lips dinta kad’an kad’an, yasa ta gyara tsayuwanta tare da cewa.
“What’s wrong Soumaya, na fahimci kwana biyu duk kaman bakya jin dadi but bakyason fad’a meyasa?.”
Noor din ta tambaya cike da kulawa.
Idanunta ta d’an rumtse tare da d’aura hannunta d’aya akan waist d’inta, cikin kuma nuna rashin mahimmancin abun tace.
“No Noor I’m okay fa, kawai dai kinsan period time Dina ya kusa shiyasa, kin kumasan yanda nake shan wahala.”
Ta k’areshe maganan tana me d’an yayyarfa yatsun hannunta, kasancewar tana ovulation period ne, then pain din yakan taso mata time to time.
Kai Noor ta jinjina, cike kuma da tausayawa K’awartata tace.
“Eyyah sorry bestie you’ll be fine insha Allah,Kizo mu saukeki agida.”
Kai Soumaya ta d’an girgiza, tare dasa hannu ta gyara zaman jakan dake shoulder dinta.
Cikin kuma yanayin nutsuwarta na koda yaushe tace.
“I’m sorry Noor karkice wani abu please, Zan fita bakin gate rana tayi sanyi nasan zan samu taxi, then nasan ma ABBOU ya kusa dawowa yanzu.”
Tayi maganan tana me duba, d’an siririn wristwatch din dake d’aure ahannunta na dama.
Noor kuwa saurin juyowa tayi ta kalleta, tabbas idan da sabo yaci ace ta saba da halin Soumaya, domin bako da yaushe ne kakeyi mata tayin abu tayi accepting ba, ta sani Soumaya wata kalan mutum ce, duk da cewar ita din ba y’ar gidan masu akwai bane, amma Ware kanta gefe da takeyi abun yayi yawa.
Sanin halin Soumaya’n da tayine kuma yasa, ta b’ata fuska batare da tasake cewa komai ba, ta shige cikin motar tare da rufo murfin da k’arfi.
Idanunta ta d’an lumshe a hankali kuma sassanyan murmushi ya bayyana akan fuskarta.
Tasan cewa hakan da Noor din tayi alamane dake nuna cewar tayi fushi.
Saidai akoda yaushe bata da wani zab’in daya wuce haka.
Juyawa tayi ta nufi babban gate din fita daga makarantar, yayinda take ta ratsa cikin manya manyan motocin d’aukan d’aliban da suketa wuce wa ta wajen.
Tafiya takeyi amma gaba d’aya duk bata jin dad’in yanayin nata, saboda ajikinta takejin cewa ana kallonta, duk da ta saba da hakan, amma da yawan lokuta kwata kwata batajin dadin, yanda idan ta shiga waje idanun jama’a ke yawo akan ta, domin kuwa kallon da sukeyi mata irin kallon nanne na kurulla.
Wannan dalilin yasa ta dan d’aga k’afanta, saboda batason irin kallon da mazan dake wajen keyi mata.
Lokacin da ta tsinci kanta abakin kofar fita daga cikin makarantar kuwa, wani irin sassanyar ajiyar zuciya ta sauke, domin ko ba komai tasan ta tsira daga irin kallon da jama’a keyi mata.
Daidai fitowar nata waje ne kuma su Noor ma suka fito, harara Noor dake zaune acikin mota, b’angaren gidan baya ta watsa mata.
Wanda hakan yasa ta d’an saki murmushi, tare da had’e hannayenta waje d’aya alaman ban hakuri.
Da sauri Noor din ta kawar da kanta, tare da murgud’a mata baki,, sannan suka wuce.
Again murmushi Soumaya tayi, domin tasan halin Noor fushin nata bazai kai ko Ina ba.
Hango wani taxi da tayi yana zuwa ne kuma yasa da sauri ta soma d’aga hannu tana son tare mai taxi din.
Cikin sa’a kuwa ya tsaya, d’an saukowa tayi daga kan steps din da take, tare da lekowa ta kalla mai taxi din.
“Wuse 2.”
Ta fad’a tana me sake kallon mutumin dake tuk’a taxi din.
“To yarinya zaki biya 200”
D’an dattijon Mai taxi din ya fad’a shima yana kallonta.
Kai ta jinjina batare kuma da ta nemi ya rage mata ba, ta bud’e murfin taxi din ta shiga, saboda dama ahaka ta saba kusan kullum 200 ake kawota, akuma maida ita 200.
Inda tayi sa’a kuma yau din babu kowa acikin taxi din, wannan dalilin yasa ta shiga da confidence dinta, domin dama batason shiga abun hawan da akwai mutane da yawa acikinsa.
Bayan ta rufe murfin motar ne kuma, mai taxi din yaja sukayi gaba.
Hawa titin da taji sunyi ne kuma yasa ta, zare jakanta dake kan kafadarta, tare da zuge zip din jakar.
Tsohuwar naira 500 din dake cikin jakan nata tasa hannu ta ciro tare da damk’e ta acikin tafin hannunta k’am, tana me tuno lokacin da Abboun ya biyota waje ya bata.
Hawayen da suka taru acikin idanunta ta share, tare da d’an kifa kanta akan jakanta, tana me tuno mahaifin da yafi mata kowa da komai.
Wani irin so takeyi masa na musamman, son da yake tafiya da tausayi mai tsanani, bata da kowa aduniyar nan daya wuce mata shi, shine komai nata Garkuwanta haka kuma farinciki agareta.
Sake dunk’ule kud’in dake cikin hannun nata tayi, a hankali kuma ta jingina bayanta da jikin kujeran motar.
*”INASONKA ABBOU NA”*
Ta fad’i hakan acikin zuciyarta, tana mejin tsananin shaukin son mahaifin nata na ratsata.
Uban da takejin babu irinsa aduniya, Uban da take fatan faranta masa akoda yaushe,
Uban da yake matukar son farincikinta fiye da kowa.
Babu wani wanda zata so sama dashi aduniya.
Soumaya kenan innocent girl din da batasan komai ba, sama da soyayyar mahaifinta, yarinyar da babu kunci ko matsanancin damuwa acikin rayuwarta.
Ayanzu farinciki kawai tasani, duk da cewar suna rayuwa irin ta masu k’ananan k’arfi, amma kwata kwata hakan bai kawo mata nakasu acikin rayuwarta ba.
Batasan yawan tunani ko kuncin zuciya ba.
Haka kuma daskararriyar K’addarar dake kwance acikin jininta bata fara motsawa ba.
Hakika akoda yaushe rayuwa tana tafiya da k’alubale.
Haka kuma kowa da irin k’addararsa, amma nata K’addarar B’oyayye ne, kowa da irin na k’asunsa amma nata nak’asun mai tsananin RAUNI ne.
Kamar kuma yanda yake a bayan kowani bakinciki akwai farinciki, haka kuma a bayan kowani kunci akwai sassauci.
Rayuwa mai juyawa ce farinciki ko akasin haka, mummunan k’addara ko zazzafar Soyayya, wannene zaiyi tasiri acikin rayuwar yarinyar da zuciyarta ke cike da buri da kuma fatan tallafawa mahaifinta, yarinyar da batasan komai ba sai Soyayyar mahaifinta? Tayaya zuciyar yarinyar dake da Rauni zai iya jurewa k’arb’an k’addarori Biyu alokaci guda? Meye zaiyi mata shamaki da nutsuwar zuciyarta?
Yaushe ne kuma zata san kanta?
Kiiiiiiiiii!!!
Haka Drivern taxi din yaja burki, saboda wata mota mai azaban gudu da tazo ta gilma ta gabansu.
Wanda K’aran taka burkin nasa ne kuma yasa ta bud’e idanunta, masu cike da gajiya, bugu da K’ari ga kuma yunwar dake tsakalan cikinta.
“Yauwa mun iso anan zan sauk’a.”
Ta fad’a tana me kallon cikin unguwar tasu, wacce take d’auke da yalwatattun gidajen masu kudi.
Lokaci guda kuma ta juyo da kallonta ga mai taxi din, inda ta Mika masa naira d’ari biyar din dake hannunta.
Bayan ya bata canji ne kuma ta bud’e murfin motar ta fito, hannunta rik’e da jakan makarantar ta.
K’ofar gidan dake facing dinta ta zubawa ido, Wanda kuma ya kasance nanne gidansu.
zuciyarta cike da fatan samun mahaifin nata, haka ta nufi gidan dake d’an gefe.
Gidan da aduk layin shine k’arami kuma na mararrsa k’arfi, duk da cewar gida ne na rufin asiri, amma kuma idan aka had’ashi da sauran gidajen dake cikin Unguwar shi ba komai bane.
A hankali ta tura kofar gidan nasu ta shiga, bakinta d’auke da sallama.
“Assalamou Alaekoum!”
Ta fad’a cikin nutsuwar daya zame mata sabo, duk da cewar tasan ba lallaine a amsa mata ba.
Kamar kuwa yanda tayi hasashe hakanne ya kasance, domin babu kowa a tsakar gidan nasu, sai kuliyarta dake ta yawo tana shawagi, ak’asan bishiyan fruit din dake tsakiyar gidan.
“My Cutie.”
Ta fad’a tana me k’arasa shigowa cikin gidan, tare dasa hannu ta shafa kan kuliyar nata.
“Sai yanzu aka tashi daga makarantar?”
Sautin murya ta fito daga bayanta, Wanda hakan yasa ta saurin juyowa, inda ta sauke idanunta akan wata matsakaiciyar bafulatanan mata, wacce take rike da buta ahannunta, da alama fitowarta daga public toilet din dake tsakar gidan kenan.
“Moudou sannu da gida.”
Soumaya ta fad’a tana me sunkuyar da kanta k’asa, saboda sanin halin Moudou din da tayi.
Moudou kuwa fuska ta d’an ya mutsa, kana cikin halin ko in kula tace.
“Yauwa.”
Daga haka kuwa bata sake cewa komai ba ta wuce, izuwa d’akinta wanda sautin tv keta b’ab’atu.
Da idanu Soumaya ta bita, ganin da tayi ta shiga d’aki ne kuma yasa ta sauk’e ajiyar zuciya.
Tare da sunkuyawa ta d’au cutie dinta, kaitsaye wani d’aki dake can gefe ta nufa, Wanda da alama kuma nannne d’akin daya kasance mallakinta.
Anutse ta tura kofar dakin ta shiga.
Madaidaicin d’aki ne da yake dauke da katifar kwanciya, sai kuma madaidaicin drawer Wanda kayanta ke ciki, baya ga carpet din dake shumfud’e akasan tiles din dake cikin d’akin kuwa, babu komai sai fanka dake ta faman aiki ita kad’ai.
Jakar dake hannunta ta ajiye, tare dasa hannu ta zare Hijab din dake jikinta.
Wani irin azababben yunwa takeji, wannan dalilin yasa batare da ta tsaya cire uniform din nata ba, ta fito daga cikin dakin nata, kaitsaye ta nufi kitchine dinsu, dan nemawa cikinta abunda zata ci.
K’ofar gidan nasu aka turo ahankali, tare dayin sallama da wata irin sark’akk’iya muryar, dake bayyana pain din wanda yayita.
Kyakkyawan farin dattijon da ak’alla bazai haurawa 50 years bane ya shigo, cikin gidan hannunsa rike da bakin leda.
Yayinda d’ayan hannun nasa kuwa ke dafe da kansa, ya rumtse idanunsa wanda yakejin tamkar zasu zazzago k’asa.
“Innalillahi!
Hasbunallahu wani’imal wakeel!!!”
Shine abunda Kyakkyawan matashin dattijon ke fad’a, da muryarsa wacce ke rawa, yayinda kuma yake tsaye cak ya kasa motsa koda y’ar yatsar k’afarsa ne.
Saima wani irin numfashi mai kama da fusga da yake fitarwa.
Kasancewar da k’yar ya iya kawo kansa gidan, domin ayanzu ko ganin gabansa bayayi, saima wani irin duhun da yake gani ya rufe masa ido.
Daidai lokacin kuwa Soumaya dake cikin kitchine ta fito, hannunta d’auke da plate din shinkafa da wake.
Fitowar nata kuma yayi daidai da sakin nishi, da kuma fitan sautin gurnanin numfashin mutumin nan dake tsaye abakin kofa.
Jin sautin fusgar numfashin mutumin ne yasa, Soumaya dake tsaye saurin juyowa.
Take kuwa ta sauke idanunta akansa.
“ABBOU!!!”
Ta fad’a da k’arfi, lokaci daya kuma Idanunta suka zazzaro waje.
“ABBOU!!!”
Tasake fada cikin yanayin kid’ima da rudewa, tare kuma da tsananin tashin hankalin daya bayyana akan fuskarta, ahanzarce batare kuma da ta jirayi komai ba ta nufi inda Abboun ke tsaye.
Saidai kafun tayi taku biyu wanda zasu sada ta garesa.
Tuni ya saki ledan dake hannunsa, take kuma ya zube awajen hannunsa dafe da kansa.
Wani irin k’ara Soumaya ta sa, Wanda har hakan yajawo fad’uwar plate din dake hannunta.
Take kuma itama ta yanki jiki ta fad’i akan guiwowinta.
*Wannan shine Farkon fara bugun zuciyarta, haka kuma farkon fara kukanta, kukan da babu mai rarrashi.*
Hak’ik’a wannan ne K’addararta, k’addarar dake janta izuwa bak’uwar rayuwa.
MAJNOON bakamar yanda kuke tunani bane, ba kuma irin yanda kuke hasashe bane.
MAJNOON acikinsa wani soyayyane mai tsananin zafi.
Meye zai faru? Meye kuma zai rinjayi Zuciyoyi biyun, dake bugawa alokaci guda batare da sunsan da juna ba?.
*6:40pm*
SOUMAYYA MAJNOON!!*
(The innocentmad)
*Writting by*
fatymasardauna
*(This book is mainly for those that pay, If you know you didn’t pay please don’t read it. Here is the Account Number for people that are willing to pay- 0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz Bank. WhatsApp number 07069917168)*
*CHAPTER 2*
*Freepage*
Ta fad’i akan guiwowinta wanda suka riga sukayi sanyi, kana kuma suke b’ari da kakkarwan tsoro da firgicin da ta samu kanta aciki.
“ABBOU!”
“ABBOU!!”
Ta k’ira sunan mahaifin nata cikin muryarta wacce ke rawa, saboda tsananin tashin hankalin daya rusketa.
Tare kuma da rarrafawa zuwa garesa.
Koda ta karisa
Sunkuyowa kansa tayi tana me kallon fuskarsa, da kuma idanunsa wanda suke a rufe ruf basa ko motsi.
“ABBOU! Abbouna!!”
Ta sake kiran sunansa cikin tarin fargaban dake dukan kirjinta, kana tana me girgizasa da hannayenta, zuciyarta cike da fatan ganin ya bude idanunsa.
Rashin ganin hakanne kuma yasa ta, tallafo kansa ta d’aura akan cinyarta, cike da tsananin tashin hankali ta daura hannunta, adaidai saitin hancinsa.
Daidai lokacin kuwa Moudou dake cikin d’aki tana kallo ta fito, da niyar surfa fad’a saboda ihun Soumaya’n da taji, Wanda bisa dole ya taso ta.
Da yake kwata kwata ita din ba mace bace mai damuwa da sha’aninsu, shiyasa cikin fad’a tace.
“Ke Soumaya lafiyanki k’alau kuwa, kodai kin fara haukane?, ko kuwa aljanune suka shiga kanki?.”
Ta fadi hakan tana me kokarin karasowa inda Soumaya’n ke durkushe.
Soumaya ko jin muryar Moudoun abayanta ne, yasa ta juyowa da sauri, cikin tashin hankali da kuma firgicin da ta samu kanta aciki, murya na rawa tamkar wacce aka jonawa shocking tace.
“ Abbou na Moudou, ABBOU ne…..”
Sauran maganan nata ya mak’ale saboda wani irin, matsanancin kukan daya k’wace mata, still kuma tana me jijjiga Abboun da kansa ke kwance bisa cinyarta baya ko motsi.
K’irji da zuciyar Moudou ne suka buga atare, lokaci daya cikin yanayin tashin hankali, ta tsurawa fuskar Abboun dake kwance idanu, zuciyarta cike da fargaban kada hasashe da kuma abun da tajima tana rayawa acikin zuciyarta ya zama gaskiya.
D’an jim tayi, zuciyarta cike da sak’e sak’e kala kala, wani sabon tunani da yazo ranta ne, Kuma yasa ta had’e fuska.
Cikin halinta nako inkula da tasaba yi musu, murya adak’ile tace.
“Shine kiketa kururuwa tamkar wacce ake zarewa rai? Kukan nakine zaisa shi dawowa cikin hayyacinsa?.”
Da sauri ta soma girgiza kanta, still da muryar kuka tace.
“Moudou baya numfashi, mukaishi asibiti banason wani abu ya sameshi..”
“To idanu zaki zubamin ko kuma zaki tashi ne kije ki nemo mai taxi ko adaidaita sahu mu kaishi asibiti.”
Moudou ta tambaya tana me watsawa Soumaya’n harara, dan daga ita har baban nata duk haushinsu takeji.
Soumaya ko jin abunda Moudou’n ta fad’a ne yasa ta, d’ago da kanta had’i da idanunta wanda suke tsiyayar da ruwan hawaye tamkar a kunna famfo, ta kalli Moudo’un zuciyarta cike da tausayin kansu, dama kuma halin da suke kokarin fad’awa cikinsa ayanzu.
Tabbas bata da wani zabi wanda ya wuce, aikata abun da Moudou’n ta fad’a, hakan yasa cikin hanzari ta tashi daga durk’uson da take.
Arude ta nufi dakinta dan d’aukan mayafin da zata rufawa jikinta.
d’aya daga cikin lufayunta da take ajiyewa akan y’ar katifarta ta d’auka, batare da ta jira ta gama saka hijabin ba kuwa, haka ta nufi hanyar fita daga cikin gidan.
Hawaye na ambaliya akan fuskarta.
Da sassarfa mai kama da gudu gudu, ta k’araso kan babban tititin daya malale cikin unguwar tasu.
Wanda tsirran motoci ke wucewa jifa jifa.
Koda ta iso bakin titin kuwa babu kowa awajen, musamman ababen hawa na haya babu ko d’aya dake gilmawa akan titin, sai dai manyan motocin masu kudin anguwar dake wuce wa.
Su kuwa ko ka tsaidasu dama ba tsayawa zasuyi ba.
Hagu da damanta ta kalla, rashin ganin abun hawan da zai taimaka mata, yasa ta rumtse idanunta, araunace kuma cikin tsananin damuwa da fargaban ganin mahaifin nata da tayi awannan halin, yasa murya na rawa, cikin sigar neman taimako tace.
“Allahumma La sahala illama ja’altuhu sahala, wa’anta taj alul hazna iza shiyta hasla, Yah Allah Kataimakeni, Yah Allah….”
Ta kare maganan tana kuka, hade Kuma da Ware idanunta, cikin matuk’ar sa’a kuwa ta saukesu akan wani taxi dake fitowa daga can cikin unguwar.
Da sauri tasa hamannayenta duka biyu ta soma kokarin taresa, batare kuma da ta jira ya karaso gareta ba, ita ta soma kokarin karasawa.
Wanda hakan yasa saura k’iris mai taxi din ya kad’eta.
Kiiiiiii..
Haka mai axi din yaja burki saboda ganin da yayi tayo kanshi, harma ya kusa take ta.
Ai ko gama parking din motar baiyi ba, da sauri ya bud’e murfin motar ya fito, fuskarsa dauke da yanayin damuwa, saboda yasan irinsu y’ay’an masu kud’i, idan ya kad’eta to ya kad’owa kansa masifa, Dan bashi da wani abu dazai iya kare kansa dashi, iyayenta sai su d’aureshi har sai igiya ta saura.
“Haba Yarinya bakya gani ne, kike kokarin kawo kanki tsakiyar titi, yanzu da na taka…….””
Shiru yayi tare da kasa k’arasa maganan nasa daya soma, saboda yanda yaga hawaye na ambaliya akan fuskarta, wannan dalilin yasa shi tsayawa yana kallonta, zuciyarsa cike da fargaba da kuma tsoron cewa kada daima ace harya takata baisani ba.
Soumaya’n dake cikin tashin hankali kuwa, Sam ma bata lura da cewar mai taxi din ya kusa kad’eta ba.
Saidai ganin yanda mai taxi din ya tsaya yana kallonta ne, yasa ta karasowa inda yake.
Cikin muryar kukan dake bayyana damuwarta tace.
“Dan Allah Mallam Ka taimakeni, Abbouna bana son wani abu ya sameshi, Dan Allah ka taimaka mukaishi asibiti.”
Tayi maganan tana me had’e duka hannayenta biyu awaje daya, yayinda idanunta dake zubar da hawaye ke kallon k’ofar gidansu.
D’an jim mai taxi din yayi, yana me k’arewa kyakkyawar budurwar yarinyar kallo, saboda saida ya matso kusa da ita, sai yake ganin kamar ba mutum bace.
Wannan dalilin yasa cikin son samawa kansa lafiya yace.
“Kiyi hakuri natashi a aiki, yanzu ma sauri nake na koma gida, saidai ko zaki tari wani, gashi duk asibitotin gari ma yanzu suna yajin aiki.”
Yayi maganan yana me kokarin komawa cikin motarsa, kasancewar lokacin anata shirye shiryen kiran sallan magriba.
Ganin da tayi yana kokarin tafiya ne kuma, yasa da sauri ta rik’o murfin motar nasa, hankalinta amatukar tashe, then still cikin kuka tace.
“Dan Allah karka tafi, Abbouna baya numfashi ka taimakemu Dan Allah….”
Idanu mai taxi din ya zuba mata, bawai saboda yana mamakin yanda take kukan ba, aa kawai dai yana mamakine game da yanda kyawunta yake.
Saidai kuma daga gefe guda kukan yarinyar da yasan bazata wuce, 18 to 19 years ba ya matuk’ar tab’a masa zuciya.
Saboda kuka ne da yaga tanayi nagasken gaske.
Ajikinsa kuma yaji cewa lallai tana bukatar taimako,
Hakan yasa shi bude murfin motar ya fito waje..
“Muje.”
Ya fad’a yana me rufe murfin motar.
Soumaya kuwa da sauri ta juya harta na cin tuntub’e haka ta nufi cikin gidan nasu, yayinda mai taxi din ya rufa mata baya.
Da gudu ta shigo cikin gidan, tare da durk’usawa ta tallafo Abboun nata jikinta.
“Abbouna.”
Ta kiran sunansa asanyaye, tare da tab’a gefen wuyansa, saboda yanda taji jikin nasa ya d’au zafi sosai.
“Barin tayaki mu d’aga shi ko.”
Mai taxi din ya fad’a yana me kokarin sunkuyowa dan d’ago Abboun daga kwance.
Kasancewar kuma Abboun ba mutum ne mai garin jiki ba, shiyasa bayi da wani nauyi, asauk’ak’e mai taxi din ya d’agosa, inda Soumayan ta taimaka duk da bata da wani k’arfi, amma duk rabin jikin Abboun yana nata jikin.
Ahaka suka fito dashi daga cikin gidan, Kaitsaye suka wuce wajen taxi din.
Suna zuwa kuwa mai taxi din ya bud’e gidan baya, suka kwantar da Abboun aciki.
Daidai lokacin Moudou ta fito sanye da mayafinta , bayan tasa dan makulli ta kulle gidan, fuska duk babu fari’a, haka ta k’araso wajen motan.
Gidan baya inda aka kwantar da Abboun ta shiga, Wanda tuni Soumaya ma tana ciki.
Mai taxi din kuwa ganin da yayi duk sun shiga ne, yasa shi jan motar ya nausa izuwa kan titi.
Sanin cewar kuma Ana yajin aiki a k’ananun hospitals dake cikin garin ne , yasa kaitsaye NIZAMIYYE Hospital ya nufa dasu.
Idanunta da har yanzu suke tsiyayar da hawaye ta zubawa, fuskar Abboun nata wanda kansa ke kwance bisa cinyarta.
Bata fatan wani abu ya samu mahaifinta, domin kuwa shine komai nata.
Shine mutumin daya kasance Bango kuma majingina agareta.
Shine madubin rayuwarta, haka kuma shi kad’ai ne wanda yake bata farinciki acikin rayuwarta.
Shin Tayaya zata iya rayuwa babu shi?
Tayaya farinciki zai samu idan babu shi?
Waye zai kawar da duk wani damuwanta?
Tunanin da takeyi acikin zuciyarta kenan, Wanda suka sanya hawayen dake cikin idanunta kara tsananta.
Daidai lokacin suka iso kofar babban asibitin Nizamiyye.
parking motar mai taxi din yayi, tare da juyowa ya kallesu, cike da son taimaka musu yace.
“Bari na zagayo mushiga dashi ciki ko.”
Kai Soumaya ta jinjina masa da sauri.
Take kuwa ya zagayo suka fito da Abboun, da taimakonsa suka nufi can cikin asibitin.
Cikin sa’a kuwa suna shiga suka had’u da wasu Norse’s.
Kamar kuma yanda yake duk emergency patient ana bashi kulawa, before komai hakan yasa suna ganin jikin Abboun, take nurses din suka d’auko irin gadonnan na marassa lafiya, aka d’aura Abboun akai.
Direct emergency room aka wuce dashi, domin duba lafiyarsa.
After 15mn.
Tsaye suke dukansu a k’ofar emergency room din.
Yayinda kowannensu da irin abunda yake sak’awa acikin rai da zuciyarsa.
Saidai banda ita da tunani da kuma nutsuwar zuciyarta suka kau.
Wani irin tarin fargaba takeji acikin ranta.
Sanadiyar hakanne kuma yasa hawayen dake cikin idanunta kasa tsayuwa.
“To nizan wuce Allah Ya k’ara sauki, ya kuma sa zakkan jiki ne.”
Mai taxi din nan daya biyosu har bakin emergency room din ya fad’a, cike da tausayawa.
“To Bawan Allah mungode sosai Allah ya biyaka da alkahiri.”
Moudou ta amsa masa ahanzarce dan dama batayi niyan biyansa ko sisi ba.
Souamaya kuwa idanunta da sukayi jajur ta zuba masa, kana cikin raunatacciyar muryarta mai dauke da tarin damuwa tace.
“Mungode sosai Malam, duk da nasan bazamu tab’a iya biyanka ba, amma nawa ne kudinka?”
Murmushi Mai taxi din yayi, hade da d’an girgiza kansa, cike da tausayawa yace.
“A’a ni Dan Allah Nayi, saboda haka bana bukatar wani abu, Allah Ya bashi lafiya.”
“Amin.”
Soumaya ta amsa, tana me binsa da idanu, kasancewar har ya juya ya fara tafiya.
Moudou dake tsaye kuwa, Soumaya’n take ta watsawa harara, zuciyarta cike da haushin d’agota da sukayi zuwa asibiti da magriban Allah, babban abunda ke sanya bugawar zuciyarta kuwa shine, abunda zaije ya dawo agame da rashin lafiyan Abboun.
6:30 pm.
Izuwa yanzu mintuna 20 kenan da suka d’auka suna tsaye abakin emergency room din.
Haka kuma mintuna 20 kenan da doctors din dake cikin emergency room din, suka kwashe suna mai kokarin daidai ta numfashin ABBOU, amma duk yanda suka so abun yaci tura.
Ganin abun na kok’arin fin k’arfinsu ne kuma, yasa su yanke hukuncin wucewa dashi ICU kaitsaye saboda, acanne zai samu ganin babban Doctor’n su, wato DR Mouhammad Boulama.
K’wararren likita kuma babba wanda yasan aikinsa sosai.
Acan wajen emergency room din kuwa Soumaya ce ke zaune, tayi jigum
yayinda ta manna kanta da jikin bango. Daga cikin raunanniyar zuciyarta kuwa.
Sunayen Allah take ta ambatowa, cike dasa duk wani fatanta akansa..
izuwa yanzu kuwa ta zubar da hawaye masu yawan gaske, har saida cikin idanunta sukayi jajur.
Daga can gefenta kuwa Moudou ce zaune, rike da yar wayarta kirar techno mai keypad, sai faman latsawa take, da alama kuma wani Number take nema.
Motsin bude kofar emergency room din da akayi ne, kuma yasa duk suka d’ago idanunsu.
Musamman Soumaya wacce hakanan taji zuciyarta na bugawa, wannan dalilin yasa ta tsurawa likitoti biyun da suka fito daga emergency Room din idanu.
D’aya daga cikin doctors dinne ya k’araso inda suke, yana me kokarin zare hand gloves din dake hannunsa.
“Likita ya jikin nasa? Ya farfad’o ne?.”
Moudou ta tambaya, cike da fargaban kada agaya mata mutuwarsa.
Ajiyar zuciya Doctorn ya d’an sauk’e, kana cikin son kwantar musu da hankali yace.
“Jikinsa yayi worst sosai, saboda haka dole sai yaga babban Dr dinmu, yanzu haka zamu wuce dashi ICU ne, amma karku damu insha Allah zai samu sauki.”
Ya kai karshen maganan yana me kallon yarinyar da ta tsaresa da idanunta, da sukayi ja sosai.
Duk shiru sukayi gaba d’ayansu, yayinda shi kuwa Doctor’n ya rab’a ta gefensu ya wuce.
Wasu irin zafafan hawaye ne suka gangaro daga cikin idanunta, zuwa kan k’uncinta, cike da raunanta had’i da rashin k’warin zuciya ta koma ta sake jingina jikinta da bango.
Still kofar Emergency Room din ne ya sake budewa.
Inda wasu nurses guda uku suka fito suna tura gadon nan na marassa lafiya, Wanda aka kwantar da Abboun akai.
Ganinsu da tayi ne kuma yasa azabure tayi kansu, saidai kasancewar kuma suna sauri sosai ne, yasa ta kasa cimmusu saboda dakatar da ita, da d’aya daga cikin nurses din tayi.
Bisa dole haka ta tsaya akan k’afafunta dake rawa, daga can nesa ta zubawa fuskar mahaifin nata idanu, duk da cewar baiyi wani nisa da ita sosai ba, amma dishi dishi take kallonsa, saboda ruwan hawayen da suka cika mata idanu.
Hakanan acikin zuciyarta, sai takejin cewa tamkar ta rasa shi ne.
Ya zatayi da irin wannan rayuwar da take shirin fuskanta.
Hakika ta sani cewa ita yarinyace mai rauni da kuma raunannar zuciya.
Wannan dalilin yasa idan wani abu ya samu Abbounta zata shiga cikin gararin rayuwa.
“Soumaya Soumaya!! Me yake faruwa ne meya samu Abboun naki? Yana Ina yanzu?”.
Duk aka jefo mata way’annan tambayoyin, da muryar Malam Musbahu wacce sautin ta ta fito daga bayanta.
Juyowa tayi asanyaye, duk da cewar tasan me muryar amma hakanan taji tanason ganinsa acikin idanunta.
“Soumaya!”
Still Malam Musbahu da isowarsa cikin asibitin kenan, ya kira sunanta fuskarsa d’auke da tsananin damuwan, yanda yaga hawaye cab’a cab’a akan fuskarta.
Asanyaye ta d’an tako kafafunta zuwa inda Malam Musbahun yake.
Cikin muryan kukan dake kokarin fin karfinta, ta kamo hannun Malam Musbahun.
Hakanan takejinsa tamkar d’an uwa ne agaresu, wannan dalilin yasa cikin sigan bayyana tsananin rauni da damuwarta tace.
“Baffa Ab..b..ouna, ka taimakeni banason rasashi…..”
Yanayin yanda tayi maganan cikin muryar kuka ne, yasa idanun Malam Musbahu ci kowa da hawaye.
Saboda yafi kowa sanin tsananin kaunar dake tsakanin Soumayan da mahaifinta.
Hannunsa yasa ya d’an dafa kafad’anta, cike dason kwantar mata da hankali yace.
“Insha Allahu Abbounki zaiji sauki, zai tashi kuyi rayuwa kamar yanda kuka saba, ki daina wannan kukan kinji Soumaya.”
Kai ta jinjina masa, duk da batajin k’warin guiwa ajikinta, amma tayi believing cewa Allah bazai barsu haka ba.
D’an zame jikinta tayi tare da zama akan wani dogon benci dake wajen.
Sai alokacinne kuma ta lura da kanta, da kuma kayan uniform din dake jikinta, saboda rudewan da tayi ne Kuma yasa, ko takalman dake k’afafunta bata sasu adadai ba, duk da cewar normal takalma ne irin wanda take zaman gida dasu.
Kanta tad’an langwab’ar gefe tare da lumshe idanunta, tana me sauraran yanda zuciyarta ke bugawa da karfi.
Malam Musbahu dake tsaye agefe kuwa shi dinma yanzu zama yayi akan bencin, tare dayin zugum zuciyarsa cike da zullumin abunda zai faru.
Tabbas Tsoro da fargaban abunda zaije ya dawo yake, domin yasan lokaci yayi da dole Soumaya zata San abunda Abboun nata bayaso ta sani, abunda ya jima yana b’oye mata yanzu dole zata sani, lokacin bayyanar abun yayi, abunda suka jima suna tsoron bayyanuwarsa.
Abun dazai dakatar da duk wani farincikin su, tare da maishe da abu guda izuwa rabi.
*Intensive Care Unit*
Dr. Muhammad Boulama ne ke tsaye agaban gadon da Abboun ke kwance, Wanda aka riga da aka sawa wasu na’urori na musamman akansa.
Gyara zaman Na’urar Oxygen din da aka sawa Abboun yayi, kana cikin mamaki da kuma al’ajabin abundake zuciyarsa, yasa hannu ya goge gumin dake tsatstsafowa daga goshinsa.
Duk da cewar sunyi nasarar ceto numfashin patient din nasu, amma akwai sauran aiki mai yawa agabansu.
kasancewar ciwon nasa yayi worst sosai.
“Su waye suka kawoshi?”
Dr. Muhammad Boulama’n ya tambaya, yana me kallon d’aya daga cikin doctors din da sukayi aikin tare.
“Inaga matarsa ce da y’arsa.”
Doctor’n ya bashi amsa, yana me zare hand gloves din dake hannunsa.
“Okay ka fad’a musu su sameni a Office.”
Dr Mouhammad din ya fada cikin hanzari, tare da juyawa ya fice daga cikin dakin.
Kaitsaye babban office dinsa ya nufa, Dan kasancewarsa babban DR shiyasa komai nasa ya kasance na musamman acikin asibitin.
Tura kofar office din nasa yayi ya shiga, Wanda shigarsa cikin office din yayi daidai da shigowar kira cikin wayarsa, dake aje akan babban table dinsa.
Jin kiran ya kusa katsewa ne kuma yasa cikin dan sauri ya karasa inda wayar tasa take, tare da leka screen din dan ganin sunan wanda ke kira.
*”BILLIONAIRE DAWOUD SARAKI”*
Ya maimaita sunan akan harshensa.
Aransa yana me tunani da kuma fargaban abunda zaiji dangane da ciwon.
*MAJEED.*
(Karku manta wannan littafin ba Freebook bane, ga wacce takeson ci gaba da karantashi zata biya 300 naira ne kacal, zata tura kudin ta Account Number 0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz Bank ko kuma MTN card ta WhatsApp’s Number, but banda VTU, then idan kika tura zaki turomin evidence na Payment dinki, ta WhatsApp Number na 07069917168 thank you my lovely fans!)
*2:30 pm*
*MAJNOON!!*
(The innocentmad)
*Writting By*
Fatymasardauna
Wattpad
@fatymasardauna
*(This Book is mainly for those that pay, if you know you didn’t pay please don’t read it. Here is the account number for people that are willing to pay-0002214625 Abubakar Muhammed Sardauna Jaiz bank. AMOUNT 300. WhatsApp Number 07069917168)*
*Chapter 3*
Idanu Dr. Mouhammad ya tsurawa screen din wayar nasa dake ta faman ruri, tamkar me nazartar wani abu.
Duk da cewar yasan Billonaire DAWOUD Saraki. Bazai kirasa haka kawai ba, lallai dole saida wani abu.
Amma yana tsoron ace masa jikin MAJEED ne ya sake tashi.
Hannunsa ya mik’a da niyar d’aukar wayar, saidai kafun yakai ga d’auka, kiran ya katse.
D’an Jim yayi yana me tunanin bin kiran, saidai sanin da yayi cewar mai kiran nasa, zai sake kira ne yasa shi sauke ajiyar zuciya, tare da fesar da numfashi.
Anutse ya koma kan kujera ya zauna.
Yana me tunani acikin zuciyarsa, ta yanda zai sake fuskantar matsalar MAJEED.
Idanunsa da suka dan kawo ruwa, ya lumshe saboda tunowa da wasu abubuwa da yayi.
Acan waje b’angaren su Soumaya kuwa har yanzu babu wani wanda yayi kyakkyawan motsi, daga cikinsu haka kuma babu wani wanda yake cikin yanayi mai dad’i.
Sai Moudou wacce ta k’osa da komawarta gida, saboda duk tagaji da zaman asibitin, gashi kuma har yanzu basu san awani Hali Abboun yake ciki ba.
“Idan ya mutu ne ai sai sufito suce ya mutu.”
Ta fad’i haka acikin ranta tana mejan tsaki kasa kasa, tare da wurgawa Soumaya harara, wacce ta cusa kanta acikin tsakankanin cinyoyinta.
Gaba d’aya jin duniyar takeyi babu dad’i, acikin zuciyarta kuwa, ak’agare take da sanin halin da mahaifinta ke ciki.
K’aran sautin takun takalmin da taji acikin kunnuwanta ne, yasa ta d’ago kanta, tare da kallon inda takejin sautin takun, da kumburarrun idanunta.
Ganin Doctor’n d’azu da tayi yana kokarin k’arasowa garesu ne, yasa ta zuba masa ido, domin hakanan taji zuciyarta na bugawa tamkar zata faso kirjinta ta fito.
Bata fatan jin wani mummunan labari daga bakinsa.
Dan tayi imani cewa jin hakan zai iya sa zuciyarta tarwatse wa.
Ganin da tayi har ya kusa k’arasowa garesu ne kuma, yasa ta sanya hannu ta d’an dafe kirjinta, tare da rumtse idanunta.
Saboda batason ji da ganin wani mummunan abu.
“Likita ya ake ciki dai, kodai har yanzu bai farfad’o bane? Ko kuma ya rasu ne kuke b’oyewa?”
Moudou ta jefowa likitan tambayar, da yasa zuciyar Soumaya rugurgujewa, sannan yasa jinin jikinta daskarewa.
Saboda tambayar da Moudou’n tayi ne kuma, yasa bisa dole ta ware idanunta tana kallon likitan, zuciyarta cike da fargaban amsar da zai bawa Moudou’n.
Dr. Hafiz wanda shima yana d’aya daga cikin manyan Doctors din dake cikin asibitin, kallon Moudou yayi cike da mamakin irin tambayar da tayi masa.
Saidai kuma rashin sanin wace ce ita awajen marar lafiyan, yasa shi kawar da mamakinsa, kamar kuma yanda yakasance acikin tsarinsu akwai iya tausasa harshe, da kuma samawa mutane nutsuwa hakan yasa shi, girgiza kai kana cikin kulawa yace.
“Calm down patient dinku zai samu lafiya Insha Allah, domin munyi nasarar ceto numfashinsa, sauran bayani kuma zakuji shi ne daga bakin, Dr. Mouhammad, zaku iya zuwa ku sameshi a office yanzu.”
Ya kai karshen maganan yana me nuna musu, hanyar office din Dr. Mouhammad Boulama.
K’akk’arfar ajiyar zuciya mai tafiya da k’warin guiwa, da kuma sanyin zuciya Soumaya ta sauk’e.
ahankali kuma siraran hawaye masu sanyi suka Zubo daga cikin idanunta.
“Alhamdulillah Allah Mungode ma, yanzu kenan DR. zamu iya zuwa mu ganshi?”
Ta fad’a cikin farincikin daya kasa b’uya akan fuskarta, dan sai takejin tamkar Doctorn cewa yayi Abboun nata ya warke.
Idanu Dr. Hafiz ya zubawa matashiyar yarinyar, da ya hangi abubuwa da yawa atarrare da ita, tabbas ganin farincikinta, yasa shi jin damuwa acikin zuciyarsa, saboda cutar da yasan yana damun mahaifin nata, kwata kwata baisan ya zasu d’auki abun ba.
Amma gudun kada ya karya mata lagon confidence din daya gani akan fuskarta, yasa shi bayyana murmushi akan nasa fuskarsa, atausashe kuma cikin kulawa yace.
“Don’t worry Zaku ganshi amma ba yanzu ba, ki kwantar da hankalinki kinji, yanzu ku fara zuwa wajen Dr. Mouhammad tukunna, dan yace yana buk’atar ganinku.”
Murmushi ne ya bayyana akan fuskarta, najin dadin abunda Doctor’n ya fad’a mata, dan haka cikin fatan samun kyakkyawan labari ta mik’e tsaye.
Dan tuni Malam Musbahu da Moudou sun jima da mikewa.
Dr. Hafiz kuwa shi yayi musu jagora, har zuwa dan corridor din dake gaban office na Dr. Mouhammad din.
Shida kansa ya shige musu gaba, tare dasa hannu ya soma knocking k’ofar office d’in.
“Yes come in.”
Daga ciki Dr. Mouhammad ya amsa yana me gyara zamansa, tare da d’auko wani file dake gefensa ya soma dubawa.
Jin anbada izinin shigowa ne kuma yasa Dr. Hafiz ya Bud’e musu kofar, tare dayi musu nuni da hannu alaman su shiga.
Malam Musbahu ne akan gaba, sai kuma Moudou yayinda Soumaya dake bayansu, duk taji jikinta yayi sanyi, hakanan lokaci daya duk yanayinta ya sanja.
Da k’arfi k’arfi takejin kirjinta na bugawa, sab’anin farincikin da taji a y’an mintunonin da suka wuce, fad’uwar gaba ne ya maye gurbin kowanne dakika na bugun zuciyarta.
Dr. Mouhammad ne ya amsa sallamar da Mallam Musbahu yayi, tare da nuna musu wajen zama.
Kan d’aya daga cikin kujerun dake gaban Dr. Mouhammad din, Malam Musbahu ya zauna, haka ma Moudou wacce take ta faman raba idanu, tana karewa tankamemen office din kallo.
Soumaya kuwa da ita tayi na k’arshen shigowa, abayan Malam Musbahu dake gaisawa da Dr. Muhammad ta tsaya, tare da sunkuyar da kanta k’asa.
Aranta take amabaton sunan Allah‘n da shi yasanya mata, Rauni mai tsanani acikin zuciyarta.
Dr Mouhammad kuwa
File din dake gabansa ya karasa cikewa, kafun ya d’ago kansa ya kallesu.
Gyara zaman siririn farin Glass din dake saman idanunsa yayi, kana anutse kuma cikin kulawa yace.
“Acikinku waye shak’ik’i ko Kuma mafi kusa da marar lafiyar?.”
Shiru duk sukayi, sai Malam Musbahu wanda duk damuwa ta bayyyana akan fuskarsa ne yace.
“Dukanmu shak’ik’aine agaresa, domin ni nakasance amini ne agaresa, sannan wannan matarsa ce, wannan dake bayana kuma y’arsa ce ta jini, ita kad’ai ya mallaka.”
Ya kare maganan yana me nuna Soumaya dake tsaye ta sadda kanta k’asa.
Wanda kuma sai alokacin ne Dr. Mouhammad ya lura da ita, ido ya zubawa yarinyar sosai tamkar mai nazartar wani abu adangane da ita,
Kana daga bisani ya dawo da kallonsa ga Malam Musbahu’n
Kallon Malam Musbahun yayi na y’an wasu sakanni, kafun daga bisani ya maida kansa ga duba wani file dake gabansa.
Hakan ko shi yasanya zuciyar malam Musbahu karyewa.
Asanyaye cikin fargaba yace.
“Lafiya kuwa Likita, kodai wani mummunan abu ya faru ne?.”
Kai Dr. Mouhammad ya girgiza, tare da zare glass din dake idanunsa.
Cikin sassauta murya ta yanda yasan zasu fahimcesa yace.
“Kamar yanda kuka sani kowani bawa yana da irin nasa k’addarar, Allah keda ciwo sannan shike da magani, babu kuma wata cuta aduniya, da bata da magani amma kuma nayi mamaki kwarai ta yanda kuka bari ciwo yayi worst ajikinsa sosai, domin ayanzu yakai wani stage da shawo kan matsalan abune mai matuk’ar wahala….”
D’an Jim yayi tare da soma kallonsu d’aya bayan d’aya, wannan dalilin yasa Soumaya dake tsaye zuba masa ido.
Zuciyarta cike da fargaban sauran abunda zai fito daga bakinsa.
Haka shima Malam Musbahu cikin tashin hankali yake kallon Dr. Mouhammad din, duk da cewar yasan hakikanin zancen, amma yana tsoron abunda zaije yazo.
“Likita kayi shiru meke damunsa ne, wai kodai mun rasa shi ne kuke boyewa?”
Moudou ta jefo masa tambayar, saboda duk ta k’agara dason jin abunda ke damun Abboun.
Kai Dr. Mouhammad ya girgiza hade da gyara zamansa yace.
“Ko d’aya bai mutu ba, har yanzu yana numfashi, amma saidai cutar dake damunshi zata iya zama sanadiyar rasa shi acikin lokaci kad’an, matukar akayi wasa to tabbas za’a rasa rayuwarsa, saboda yana d’auke da cutar nanne ta BRAIN CANCER, wato Cancer’n kwakwalwa!!”
Hakika Maganansa daidai yake da saukan aradu, acikin kunnuwan Soumaya, haka kuma maganar sa daidai take da tsayawar bugun zuciyarta na y’an wasu sakanni.
Saurin fusgo numfashinta dake kokarin kwacewa zuciyarta tayi, ta hanyar furta kalman.
“Innalillahi Wa Inna Ilaihirraju’un!!!”
da sauri, saurin dake tafiya da gudun bugun zuciyarta.
“Likita Cancer’n kwakwalwa fa kace?”
Moudou da tasa hannu ta dafe kirji, ta sake tambaya tare da zazzaro idanunta waje.
Malam Musbahu kuwa hannu yasa ya soma share gumin dake tsatsafo masa, dan duk da cewar yasan tuntuni ABBOU’n na d’auke da cutar Cancer, amma baiyi tunanin abun zai iya kawosu ga haka ba.
Soumaya kuwa kai ta soma girgizawa, yayinda acikin sakanni kad’an wasu sabin hawaye suka b’alle daga cikin idanunta.
Hakanan takejin tamkar k’arya kunnuwanta sukayi mata, wannan dalilin yasa.
Araunace ta matso kusa da kujerar Dr. Mouhammad, tare da zubewa akan guiwowinta.
Cikin matsanancin damuwa hadi da sabon tashin hankalin da tasa mu kanta aciki, ta fa she da kuka mai tsuma zuciya.
Kukan da yasa Dr. Mouhammad dasu Malam Musbahu zuba mata idanu.
Ita kanta tsananin tausayin kanta takeji, saboda tasan cewa farinciki bazai cika mata ba, matukar babu mahaifinta, wannan dalilin yasa araunace, kana murya na rawa tace.
“Kataimakeni Dr Bana da kowa aduniyar nan sai Abbouna, rayuwa bazata yiwu ba idan babu shi, banason rasa shi, dan Allah kayi wani abu Abbouna ya samu lafiya, ka taimakeni, kada kacemin Abbouna bazai tashi ba, kada kacemin bazai sake motsi ba…”
Maganan nata ya sark’e saboda matsanancin kukan daya kwace mata, sanin bazata iya sake cewa komai bane kuma, yasa ta had’e duka hannayenta biyu awaje d’aya, tana kuka mai Alamana roko, da neman taimako.
Idanu Dr. Mouhammad ya zuba mata cike da tausayawa, dan yasan da ace tasan yanda ciwon mahaifin nata yayi worst, to da tayi kuka fiye da haka.
Saidai yanda yaga tana yin kukan da duka karfinta ne, yasa shi sauk’e ajiyar zuciya, tare dayi mata alama akan ta tashi.
Then amatsayin sa na Babba kuma wanda yasan aikinsa, yasa murya atausashe yace.
“Stop crying tashi kinji ki daina kukan nan, Insha Allah he will be fine, bashi ne mutum na farko daya fara facing thesame issue ba, akwai mutane masu fama da brain cancer da yawa, kuma suna warkewa matukar akayi musu abunda ya dace, saboda haka ki daina kuka.”
Ya kare maganan cikin lallashi, da kuma fatan daina kukan nata, saboda yasan yanda yawan kuka ke illa ga lafiya.
Bazata tab’a iya daina kuka ba tasani, har abada way’annan idanun nata bazasu daina zubar da hawaye ba, matuk’ar cutar Cancer bata har jikin Abbounta ba, saboda kasancewar ta d’alibar likitan ci, yasa tasanin yanda Cancer ke cutar da duk wanda ta kama.
“Yanzu Likita meye abunyi?”
Malam Musbahu ya tambaya, cikin matukar damuwa hadi da karyewar da zuciyarsa tayi.
“Babu damuwa insha Allah komai zaiyi daidai, saboda akwai gwajin da zamuyi mishi gobe, daga nan ne kuma zamu tantance abunda ya kamata, yanzu nasa akaishi d’aki na musamman saboda yana tsananin buk’atar kulawa, kasancewar baya iyayin numfashi da kansa, har saida muka sa mishi oxygen kafun nan, baya ga haka kuma akwai na’urorin da muka sa akansa, Wanda suke lura da brain din nasa, ahalin yanzu dai Hutu kawai shine abunda yake buk’ata.”
Kai Malam Musbahu ya jinjina, kafun duk gaba d’ayansu sukayi shiru, saboda kowannensu da kalan irin abunda yake sak’awa acikin zuciyarsa.
Saidai banda Soumaya wanda tunanin ta ya tsaya cak.
K’aran knocking din k’ofar Dr. Mouhammad din da akasoma yi, shine ya dawo da ita hayyacinta.
“Come in.”
Dr Mouhammad dake zaune ya bada izinin shigowa.
Ahankali Nurse Estha dake knocking kofar ta bude ta shigo, hannunta rike da wani file.
K’arasowa wajen Dr. Mouhammad din tayi, arusune cikin kuma girmamawan da suka saba baiwa na sama dasu tace.
“Sir komai ya kammala munkai patient din dakin da kace.”
Kai kawai Dr. Mouhammad ya jinjina,
tare da karban file din hannun nata ya ajiye.
Bayan ya mike tsaye ne kuma ya dawo da kallonsa garesu, murya atausashe yace.
“Zamu iya zuwa ku gansa yanzu, saidai kaman yanda na fad’a yana bukatar hutu, saboda haka dole acikinku zaku bar mutum d’aya wanda zai kwana dashi, domin yawan hayaniya zai iya causing masa wani sabon problem.”
Ya kai k’arshen maganan yana me kokarin wucewa gaba, dan tuni dama ya mike tsaye daga zaunen da yake.
Ganin hakanne kuma yasa duk suka mik’e suma, suka rufa masa baya.
Koda suka fito daga office din nasa,Kaitsaye wani dogon corridor wanda yake acikin part na musamman suka nufa.
Bayan sun d’anyi tafiya mai nisa ne kuma, suka iso wani babban falo, dake d’auke da wasu d’akuna, masu k’ofofi da windows na glass.
Irin dai kofuna da windunan nan wanda kana daga waje zaka iya hango wanda yake kwance aciki.
Hannu Dr. Mouhammad yasa ya bud’e d’aya daga cikin k’ofofin, wanda anan cikin dakin Abboun ke kwance.
Bud’ewar kofar kuwa yayi daidai da sauke idanunta akan Abboun da tayi.
Cak kuwa ta tsaya da tafiyan da takeyi, yayinda atake, wasu irin hawaye masu zafi suka gangaro daga cikin idanunta.
hawayen dake bayyana tausayi da kuma Rauni’n da yayi tasiri acikin zuciyarta.
Idanu ta zuba masa, kasancewar daga inda take tsayen tana iya hango na’urorin da aka jona masa.
Hakan yasa taji sabon kuka na kokarin kwace mata, yayinda zuciyarta kuwa ke sake raunata.
“Brain Cancer.”
Ta maimaita sunan ciwon da Doctor’n ya shaida musu cewar Abboun na dashi.
Kanta ta shiga girgizawa tare da soma takowa ahankali harta k’araso gaban gadon da Abboun ke kwance.
Tana isowa kuwa kanta ta kifa akan hannunsa, tare da fashewa da wani irin sabon kuka mai tsuma zuciya.
Shiru gaba d’aya d’akin ya d’auka, kowanne daga cikinsu yana sauraran sautin kukan ta.
Yayinda Kowa da irin tunanin da yakeyi acikin zuciyarsa, saidai banda Dr. Mouhammad wanda tunanin nasa ya banbanta da nasu.
Domin jin kukan yarinyar wani abu yake tuna masa daban, haka kuma wani abu na daban ne ke yawo acikin tunaninsa.
Duk da bashi da tabbaci amma yanaji ajikinsa cewar hakan dama ce Babba, damar da zata sauya rayukan mutane biyu, damar da zata juya baki izuwa fari, damar da zata maida baya izuwa gaba.
Duk da yasan hakan abune mai wahala, ko kuma ace abune wanda bazai yiwu ba, amma idan K’addara ta had’a fa?.
Add Comment