Gyaran Jiki Littafan Hausa Novels

Yadda Zaki Magance Tusar Gaba

Yadda Zaki Magance Tusar Gaba

 

 

 

 

 

 

 

 

 

MAGANIN TUSAR GABAN MACE ( BUDURWA KO MATAR AURE ):

 

 

Me Ke Janyo Tusar Gaba?

 

Yan Uwana Mata barkan mu da sake saduwa daku a cikin wannan shiri namu mai matukar farin jini, Wato Sirrin Iyayen Giji..

 

 

 

Kamar yadda ku ka sani shi wannan shiri a na yin shi ne don matan aure zalla domin ba su shawarwari ta ko wane bangare na rayuwarsu ta yadda za su samu su gyara zamantakewarsu da mazajen su da Mu’amalar su ta auratayya da ta bangaren girki, tsafta, gyaran gida da gyaran jiki da ma ko wane bangare da ya shafi rayuwar ’ya mace, da fatan ku na amfani da abubuwan da ake gaya muku. Ga cigaba da amsar tambayoyinku:

 

 Kalolin Farjin Mata Uku Da Suka Fi Yawa

 

Assalamu Alaikum. Tambayata a nan ita ce, me ke kawo fitar iska daga gaban mace, wacce na ji wasu su na ce mata tusar gaba?

 

 

 

Dalilan Da Suke Kawo Tusar Gaba:

 

Zama a kasa cikin na’urar AC ba wando kuma a kan tiles.

 

Yawo ba takalmi, musammam a AC kuma kan tiles.

 

Kwanciya ki kunna fanka kuma ba wando a jikinki.

 

Rashin yin tsarki da ruwan zafi.

 

Rashin yin tsarki bayan gama jima’I, wato barin maniyyi ya kwana a jikinki ba tare da yin tsarki ba.

 

Yawan yin maganin mata ba gaira ba dalili.

 

Cushe-cushen kayan matsi na mata barkatai. Ba ki san da me aka yi maganin ba kawai ki kama cusawa cikin gabanki.

 

Matsanancin ciwon sanyi (infection), sai kaga ya cinye mace ta ciki ba tare da ta farga ba.

 

Rashin iya ‘positioning’ na kwanciyar aure da miji.

 

Zama da kamfai guda daya tun daga safe har dare. Sai ka ga mace ta bar shi tun safe har dare ya na jikinta tsabar kazanta.

 

Rashin daure zani da karfi a ciki ga matan da suka haihu.

Barin ciki da yunwa a lokacin da a ke al’ada ko lokacin da a ke Jego.

 

Wadannan kadan daga cikin Manyan abubuwan da ke kawo wa mata matsalar lalacewar gaba har ka ji yana ta kara yana fitar da iska Fut! Fut! Fut! kamar tusa.

 

 

 

Hanyar Magance Wannan Matsalar Ita Ce:

 

Ki nemi ganyen Magarya da Gabaruwa, da ’ya’yan Hulba. Sai ki hada su gu daya ki na dafawa sai ki debi gishirin cikin tafin hannunki ki zuba chiki. Sai ki dinga shiga kina seatbirth da shi na tsawon 20 minutes. Kina fitowa zaki ga wani bakin Abu yana fitowa daga cikin farjinki.

 

Za ki gan shi a kasan ruwan maganin sannan bayan kin tsane ki nemi farin muski sai ki dangwala da auduga me tsafta ki yi matsi da shi.

 

Sannan ki dinga kiyaye wadancan abubuwa guda goma 12 da na fada a sama. Inshaa Allahu za ki kubuta daga cikin wannan matsala. Kuma ki nemi angurya, ’ya’yan auduga ki na turara gabanki da shi.

 

 

 

Ga wani maganin, amma ya na rage ruwan ni’ima kadan:

 

A kan iya amfani da ganyen Tumfafiya, sai a samu kamar guda bakwai a dora shi akan garwashin wuta inyayi zafi se mace ta gasa gabanta dashi kuma ba’a bada tazara ana cire wannan anasa wannan haka har sukare. Haka har kwanaki 3 Insha Allah zata rabu dashi *wannan yana maganin har irin ‘infection’ da ke taruwa acikin Mace taji abu na yawo acikinta kaman mai dauke da juna biyu.

Add Comment

Click here to post a comment