Luwadi da Madigo Abinda Ya Kamata Ku Sani
LUWADI DA MADIGO
******
Wani babban Bala’in da ya shigo kuma yake watsuwa acikin al’ummah acikin ‘yan shekarun nan shine Dabi’ar nan ta Luwadi da madigo atsakanin Matasa maza da Mata.
Babban abin mamakin shine yadda matasan da suke yin wadannan Miyagun dabi’u Zuciyarsu ta Qekashe. Basu jin kunyar bayyana ma duniya cewa wannan shine aikinsu.
Zaka ji Matashi yace wani shi haka kawai yake jin sha’awar Maza!! Ko kuma mace tace wai ita bata sha’awar Namiji sai dai ‘yar uwarta mace. Sun samo wannan fahimtar ne daga wajen ‘Yan Kungiyoyin Luwadi da Madigo na Qasashen turawa.
Su irin wadannan Tsinannun turawan suna kokarin nuna ma Duniya cewar wai Allah ne yayi kuskuren sanya musu Jiki irin na Maza, Amma dabi’unsu irin na mata ne. Ko kuma yayi kuskuren sanya dabi’un maza ajikin Halittar mace!!!
Wannan Mummunan Tunani ne na kafirci. Kuma su ‘yan madigon ko Luwadin da suke yin irin wannan tunanin zasu afka cikin kafirci bayan kuma Mummunar dau’dar Zunubin dake tare dasu.
Luwadi da madigo, Miyagun dabi’u ne wadanda ko dabbobi bassu yi ballantana ‘dan Adam. Kuma a sanadiyyar wannan Zunubin ne Allah ya hallakar da al’ummar Annabi Luut (as). Yayi musu irin azabar nan wacce bai ta’ba yiwa kowa ba, domin hakan ya zamanto abin lura ga mutanen baya..
Zauren Fiqhu na jan hankalin masu yin wannan dabi’ar cewa su tuba zuwa ga Allah tun lokaci bai Qure musu ba. Kuma su dena bayyanar ma duniya wannan miyahun aikin da sukeyi. Domin kuwa wannan bayyanarwar tana nuna alamar cewa Allah ba zai gafarta musu bane.
Yazo acikin hadisi cewa Allah zai gafarta kowanne zunubi amma banda na mutanen da suke bayyanar dashi bayan sunyishi aboye.
Ya Allah ka shiryemu ka nisantar damu daga wannan bala’in.
DAGA ZAUREN FIQHU WHATSAPP (1).
Add Comment