Wani Haske Complete Hausa Novel
WANI HASKE
_*NA*_
_*UMMI A’ISHA*_
_101-105_
_Assalamu alaikum masoya masu karanta littafin
wani haske kuyi hakuri da rashin ganin posting akan lokaci
wannan ya farune ta sanadiyyar wasu hidimomi da suka
hau kaina sannan kuma kun san wannan littafin abubuwan
da suke cikinsa sun shafi bincike da nazari shiyasa zakuga
Azeemah Hausa Novel Complete
wani lokacin nadade banyi posting ba, yanzunma korafe
korafenku naji shiyasa kawai na rubuto muku abinda ya
sawwaka amma da a manufata zan kawo muku
matsaloline wadanda mata suke fuskanta musamman ma
ta fuskar auratayya tsakanininsu da mazajensu da kuma
hanyoyin warwaresu to amma jin korafin naku yayi yawa
yasa na ajiye wannan batun agefe saboda naji wasu na
cewa ummi ta fiya jan rai akan wannan book din, to kuyi
hakuri wlh ba jan rai bane yanayin rubutun ne haka,
sannan kuma wata baiwar Allah tace ya kamata yanzu
adaina kiran tauraruwar littafin da goodness tunda ta
musulunta ana kiranta da bahijjanta, dan haka yanzu
bahijja zakuji ina ambata, wannan Shafin nabayar dashi
kyauta ga duk wata masoyiyar wani haske._
~~~Duk iya kokarinshi na ganin ya hanata aikata abinda
tayi niyya kasawa yayi dolenshi haka ya rabuda ita taci
gaba da yin yanda take so da bakinsa, rungumeshi tayi
tana murmushi,
“Abbu yau bazakaje office ba ko?” Ta tambayeshi tana
shafar sajensa, bude idonshi yayi yana kallonta kafin ya
bata amsa wayarsa dake ajiye akan bedside drewar tafara
vibration, hannu ya mika ya dauko ya duba mai kiran
nasa,secretary dinsa ne na office dinsa dan haka yayi
saurin dagawa domin yasan tunda ya kirashi to muhimmin
abu zai sanar dashi,
Asanyayenshi ya daga wayar bayan sun gaisa yake sanar
dashi bakin da zasu zo wurinshi anjima domin tattaunawa
akan wata kwangila da zasu samu, wayar ya kashe yana
tunanin dole yayi saurin fita zuwa office before bakin nasa
su zo,
Karanta Lttafin Asp Zahra Hausa Novel
“Dagani naje nayi wanka” yace da ita yana kallon yar
kyakkyawar jar rigar dake jikinta mai yalo yalo marar
nauyi,
“Abbu kana yin azumin ko? Bayan kuma na yi maka
breakfast, ni wlh bazan yarda ba” tafada cikeda shagwaba,
“Binti ai nafasa yin azumin tunda kin rigada kin bata min
shi, idan nayi wanka yanzu zanci duk abinda kika girka
min”
Wani tsalle ta daka ajikinsa tana murna, “yawwa abbu ko
kaifa”
Murmushi yayi ya tashi zaune har lokacin tana kan
cinyarsa azaune, kallo yabita dashi acikin zuciyarsa yana
cewa “ai kuwa zaki sani tunda kika karya min azumina”
Hannunshi ta kama tana kallon fuskarshi “abbu inje in hada
maka ruwan wankan”
“Uhm” yafada ahankali, wani tsalle ta dira ta sauka ta nufi
toilet din yayinda shikuma yabita da kallo har yanzu akwai
kuruciya da yarinta a tattare da ita,
Tana ciki tana sirka masa ruwan zafin data tara acikin
wani babban baho ya turo kofa ya shigo cikin bathroom
din, juyawa tayi ta kalleshi sai ta ganshi da dan gajeren
wando, da saurinta ta juya wadda har tana kokarin fadawa
cikin bahon ruwan zafin bata sani ba,
Da saurinshi ya rikota ta fada jikinshi ya riketa,
“Binti wannan gangancin fa? Saura kadan ki fada cikin
ruwan zafi” yafada ahankali yana rikeda ita,
“Abbu gashinan kayi wankan, bari naje na gyara maka
dakinka kafin ka fito” tafada tana mai sake rufe
idanuwanta,
“Kitsaya binti, ai tare zamu yi wankan yau, ko bakya son ki
samu lada?” Bude idonta tafara yi cikin sauri tareda
yunkurin raba jikinta da nasa,
“Abbu kayi hakuri dan Allah, nidai wlh bazan iyaba
kunyarka nakeji”
Dan murmushi yayi mai kayatarwa gamida dafa bangon
bathroom din da hannuwanshi yayi mata runfa tana jingine
ajikin bango tana neman hanyar guduwa,
“Ai kema wasa kike yi yarinya, ki karya min azumin nawa
sannan kuma kice ba za muyi wanka tare ba, binti ladafa
zaki samu domin babu abinda yafi kyautatawa miji saurin
samun lada, duk umarnin da na baki muddin kika bishi to
lada zaki samu, idan kika yimin wani abu wanda ya sani
farin ciki shima lada zaki samu..!”
“Abbu wlh zaka makara a office gashi ana can anata
jiranka”
Kallonta yayi yana sake bude manyan idanuwansa yana
kallonta, fuskarta ya zubawa ido yana kallonta amma ita
takasa kallonshi idonta yana kasa,
“Binti kinga, dago idonki ki kalleni”
Kasa dagowa tayi har lokacin kasa take kallo, hancinta ya
lakuce “wannan yarinyar kin fiya wayo da yawa”
Ruwan da yake zuba acikin bahonne yafara zuba akasa
domin bahon tuni ya dade da cika,
“Tunda kin ki yin abinda nasaki shikenan bari nayi ni daya
kafin amaryata tazo munayi tare”
Juyawa yayi yaje gaban fanfon yafara kashe ruwan da
yake zuba,
Ahankali bahijja ta bude kofar bathroom din tafita, agaban
mirror ta tsaya tana tunani aranta, tunanin maganar da
jabir ya fada mata yanzu take yi indai kuwa hakane amma
da tasan sunanta gawa domin ayanda take jin zuciyarta
gani take yi indai ya kara aure yanzu to babu makawa
mutuwa zata yi, lallai Ummu al’amin tayi kokari gamida
juriya data iya barinta ta zama kishiyarta,
Bata taba sanin kishi yanada daci ba sai yanzu da take
auren jabir, kasa gyara dakin tayi tana tsaye har lokacin
tana juya maganar da jabir yafada mata acikin kwanyarta,
har jabir yayi wankan ya fito ya sameta tsaye agaban
mirror wadda ita bata ma san yafito daga wankan ba,
Kafadunta ya dafa da duka hannuwanshi guda biyu sai
alokacin ta dawo hayyacinta a sanadiyyar sanyin ruwan da
taji ajikinta,
“Me kike tunani ne binti?”
Fuskarta ta shagwabe ta turo baki tana son yin kwalla,
“Abbu ba kaine ba kace…!”
Sai kuma tayi shiru,
“Nace me? Fadi inji, me nace?” Ya tambayeta yana kokarin
juyo da ita,
“Kaine kace wai, wai, wai…!”
Hawayen idonta ne suka silalo kan kuncinta, hakan yasashi
bude baki yana kallonta cikeda mamaki domin bai san
abinda yafaru ba,
“Binti me nace? Yi shiru ki fada min kinji”
Kamar ya zugata sai tafashe da kuka tareda fadawa
kirjinsa, rungumeta yayi ya fara shafa gashin kanta,
“Binti idan baki fada min ba wa zaki fadawa wanda yafini?
Ni yafi cancanta da ki sanarwa da dukkan damuwarki”
“Abbu kaine kace wai idan amaryarka tazo, wai, wai, wai
tare zaku nayin wanka” tana gama fadin haka ta boye
fuskarta acikin kirjinsa, dariya sosai maganarta ta bawa
jabir domin shi yayi tsammanin wani abune muhimmi
tunda yaga harda kuka tayi,
“Yanzu binti wannan maganar kike yiwa kuka? Ohhh, nifa
nayi zaton wani abune babba yasaki kuka, kishiyar kike
yiwa kuka? So kike ta rainaki tun kafin tazo kenan”
“Abbu dagaske kake?”
Kanta ya shafa yana murmushi wanda har hakoransa sai
da suka fito, kanta ya dago yana kallonta,
“Wasa ne binti, bada gaske nake yi ba dawasa ne amma
indai bakya bani kyakkyawar kulawa to zan yimiki abinda
bakya so, indai bazaki rinka bani farin cikiba to zanyi miki
kishiya”
“Abbu dan Allah kayi hakuri Allah bazan sakeba” tafada
idonta narai narai tana kokarin sake yin wani hawayen,
“Shikenan nahakura, karki sake yin kuka kinji, maza kije ki
kawo min breakfast din kafin na shirya”
Sakinta yayi yana yi mata lallausan murmushi, fita tayi
tabarshi yafara shiryawa ita kuma ta nufi sashenta,
kwanuka masu tsafta ta dauko ta zubo masa doya da
kwan data soya masa ga dan farfesun kayan ciki agefe
sannan ga custard powder data dama sai tea wanda yasha
kayan kamshi aciki,
Kinkimar kayan tayi ta kai masa falonshi ta ajiye sannan
tabishi cikin dakin, lokacin data shiga har ya gama
shiryawa cikin wani bakin danyen boyel mai kyau dakin
gaba daya ya gauraye da kamshin turarensa mai dadi na
special oud.
Acan wurin da ya kebe domin gudanar da ibadarsa ta
hangoshi yana sallar walaha, tsayawa tayi ta zuba masa
ido tana kallon shi hakika yayi mata kyau domin gayunshi
ya burgeta mutuka, tun daga hular kansa har agogon dake
daure a tsintsiyar hannunsa duk kalar kayansa ne, tana nan
tsaye tasaka zaren gabar rigarta abakinta tana wasa dashi
har ya idar yayi addu’a yatashi ya nufo inda take tsaye
tana jiransa, gabanta ya karaso ya tsaya, hannunsa yasa
yana kokarin zare zaren dake bakinta tana wasa dashi da
hakorinta,
“Binti abin riga kike ci? Kalleki kamar wata baby”
Kallonsa tayi tana murmushi “abbu kayi kyau sosai”
“Nagode binti, yau yarintar ce ta motsa?” Yafada yana
lakuce hancinta,
Murmushi tayi taja hannunsa tana kallonsa, “abbu muje
kayi breakfast, bana son ka makara azuwa office”
Bin bayanta yayi har suka isa wurin da takalmansa ke jere
reras, wani bakin takalmi ta dauko masa na fata half cover
mai kyau, ajiye mishi tayi agabansa,
Falo suka nufa bayan yasaka takalmin, akan kujera ya
zauna ta jawo masa dan karamin stool ta ajiye masa
abincin akai tana kallonsa,
“Binti wannan girkin naki ai sai yasa kunnena ya cire”
yafada daidai lokacin da yafara cin doyar data soya masa,
“Abbu banda tsokana fa” tafada tana murmushi,
“Babu wani tsokana binti, abincin yayi dadi gashi naga
harda wani koko koko, kunu kunu kika hada min”
Murmushi tayi tana tafa hannunta “lah jama’a kunji abbu
bai san custard powder ba, amma abbu idan akaji dariya
za ayi maka”
“To ai gashinan kin fara yimin dariyar”
Hannunsa ta riko na hagu, “abbu bari na gyara maka
agogonka”
Agogon ta kunce ta sake daura masa tana murmushi koda
ta gama daura masa bata saki hannun nasa ba yan
yatsunta tafara ja tana lankwasa masa su suna kara kas
kas,
“Binti kema kin iya mugunta ko?”
“Abbu me nayi maka? Daga gyara?”
Mikewa yayi yana murmushi aranshi yana burin wani
lokaci da yake hasashen zuwansa a daren yau,
“Bari naje binti”
“Abbu, Allah ya kiyaye hanya, Allah ya bada sa’a” tafada
tana kallonsa
“Amin binti” yafada tareda jan hancinta saboda ganin
idonta ya fara kokarin kawo kwalla,
“Meyasa bakya gajiya da kuka ne? Ki rage saurin kuka idan
ba haka ba zaki haifi yaro ruwa ruwa”
Dariya ce ta subuce mata bata shirya ba “abbu nida ko
cikin banyi ba har zaka fara yimin maganar yaro” tafada
tana yi masa murmushi,
“Saurin me kikeyi binti? Zakiyi ai soon”
Murmushi tayi har lokacin tana rikeda hannunsa “abbu ka
taho min da chocolate”
“Muga bakin kwadayin shan chocolate?”
Bakin ta bude tana turo masa dan yagani, kiss ya manna
mata akan lips dinta duka yana murmushi,
Sakinsa tayi ta juya tana murmushin itama, fita yayi yana
mai jin babu dadi acikin ranshi dalilin nisantar ta da zaiyi,
Tana labe tana lekenshi har yabar gidan, kan kujera ta fada
ta kwanta tana tunanin hali irin na jabir.
Tunda ya tafi yabarta taketa kirkirar ayyuka domin bata
son zama kurum saboda idan ta zauna tasan kadaicine zai
dameta gashi kuma tunda jabir yafita take tunaninshi
acikin zuciyarta,
Babu irin aikin da bata yi ba domin ganin ta ragewa kanta
lokaci, kananan kayan jabir duk ta tattare da jallabiyoyinshi
da kayan baccinshi duk ta wanke, bayan ta gama taje ta
dora girki, tuwon shinkafa miyar agushi tayi tahada
lemonta na kwakwa da madara kamar yadda ta saba,
Wayar jabir tafara kira lokacin misalin karfe 1:30 narana,
yana tsaka da aiki a office sai rubuce rubuce yake gashi
files tuli guda akan teburinsa kasancewar ya dade baya
office din shiyasa ayyuka suka tarar masa,
Agajiye ya daga wayar yana murmushi aranshi kuma yana
tunanin ko yanzu da wacce rigimar ta bullo kuma,
“Binti ya akayi?”
Fuska ta shagwabe kamar yana kallonta, “abbu sai yaushe
zaka dawo?”
“Binti aiki yayi min yawa, sai 5 zan tashi may be ma yau sai
nayi over time saboda inada ayyuka dayawa”
“Abbu kar kayi over time dan Allah, kadawo 5 din”
“Kina son ganina ne binti?”
“Ehh abbu”
“Me zaki bani?”
“Abbu sai kadawo dai, yanzu dai ka turo min mal idi driver”
“Ina zaki aikeshi?”
“Wurinka abbu, dan Allah karka manta”
“Bazan manta ba”
“Yawwa abbu nagode, ayi aiki lafiya”
Wayar ta tsinke tana jin wani irin dadi acikin ranta,
Shima jabir wayar ya ajiye yana murmushi ko me zata aiko
masa kuma oho,
Lokacin da mal idi driver yazo dama tuni ta gama harhada
masa kayan acikin kwando babba, komai da zai bukata ta
zuba kama tun daga filet da cokula da cups da tissue
domin goge hannu, dan haka yana zuwa bashi kawai tayi
takoma sashenta,
Lokacin da sakon ya riski jabir ba karamin mamaki yayi ba,
domin abincine wanda akalla mutane biyar zasu ci ya
ishesu gashi harda hadadden lemon kwakwa,dadine yake
ratsashi tako ina dama meeting zasuyi shida directors
dinsa Wanda duk lokacin da sukayi meeting din abincin
sayarwa ake siyo musu amma shi baya ci saboda gaskiya
yanada tsananin kyankyami,
Wannan abincin da bahijja ta aika musu shi sukaci sukayi
kat Suna santi kowa sai yabawa yake yi, shikuwa jin
bahijja yake har acikin zuciyarsa saboda yasan ta damu
dashi sannan tana kiyaye duk wani abu wanda zai sakashi
cikin damuwa, ranar har 6yakai a office sai 6:30 ya nufi
gida, duk ya gama kosawa burinsa kawai yaje gida yayi ido
hudu da ita.
Tana falonta tana kallon wani American film ya shiga yana
gyara babbar rigarsa,
Tashi tayi tana murnar ganinsa yayinda shikuma yayi
mutuwar tsaye yana kallon kyakkyawar shigar da tayi
domin wata rigace orange colour mai wasu fararen
duwatsu ajiki, iya cinya rigar take sannan bata da babban
hannu, hannunta dan karamine, ga wani wando baki fela
tasaka, kanta ta daura bakin dan kwali,
Gabansa taje ta tsaya tana kallonsa,
“Abbu sannu da zuwa”
Hannu ya mika ya kamo nata hannun yajata ya hadata da
barin jikinshi ya nufi sashensa da ita,
“Yawwa binti ya gida? Natafi nabarki ke daya ko?”
Daga kai tayi “abbu ai gobe sai nabika”
Murmushi yayi yana mai tuno al’amin dinshi domin shima
kusan kullum haka yake cewa sai ya bishi office lokuta da
dama sai yayi masa dabara sannan zai samu ya zare
jikinsa ya fita,
Har cikin falonshi ta rakashi tana shakar kamshin jikinsa,
cikin bedroom dinsa ya shiga yayi wanka ya fito yayi shirin
masallaci, gaba daya kamshine ke tashi daga jikinsa,
Har inda take yaje ya kamo hannunta ya yatasheta daga
zaunen da take ya rike yan yatsunta yana kallon kwayar
idonta, sunkuyar da kanta tayi ta kasa kallonsa,dago
habarta yayi yakai bakinsa kan goshinta yayi mata
kiss,yana murmushi,
“Binti zanje masallaci kinji? Sai nadawo”
Kai ta daga masa sannan ahankali tace “adawo lafiya
abbu”.
Fita salla yayi ita kuma ta koma sashenta tayi tata sallar,
anan ta zauna tafara yin azkar irin wanda jabir ya koya
mata, dab da sallar isha ta tashi takoma sashensa tana
sanye da zumbulelen hijabi mai hannu wanda ya saukar
mata har kafafunta domin yanzu jabir ya kawo mata
hijabai manya kala daban daban.
Asashensa tayi sallar isha, tana idarwa tafara karanta
hadisin da ya koyar da ita adaren jiya wanda aka karbo
daga baban hurairata Allah ya kara masa yarda wanda
annabi Muhammad sallallahu alaihi wassalam yake cewa
“yaku mutane ku yada sallama, kubayar da sadaka, kuyi
sallar dare alokacin da mutane suke bacci, idan kukayi
haka hakika zaku shiga aljanna da aminci”
Shigowar jabir ce ta katse mata tilawar karatun da takeyi,
kafadunta ya kama ya mikar da ita tsaye,
“Tashi muyi salla binti”
“Abbu ni nayi sallata yanzun nan na idar”
Dan malalacin murmushi yayi mata “binti wannan ai daban,
wannan ta nafila ce zamuyi, sannan ina son ki dage ki
rinka yin sallar shafa’i da wutr domin tanada tsananin
falala mai tarin yawa”
“Abbu zan rinka yi kaga shikenan basai nayi ta tsakar
dareba irin wacce kake yi”
“Waya fada miki? Koda ace kinyi shafa’i da wutr to zaki iya
tashi da daddare kisake yin sallolin nafilarki kuma zakiyi
shafa’i,wutr ne kawai bazaki yiba domin sau daya ake
yinsa idan mutum ya sake to yazama shafa’i, nasan
mutane da dama suna son tashi yin sallar dare to amma
idan har sukayi shafa’i da wutr sai su zaci Cewar shikenan
babu damar yin wata sallar tunda sun rufe da wutr to ba
haka bane mutum zai iya yin wasu sallolin acikin dare koda
kuwa yayi shafa’i da wutr kawai dai ba ason ya sake yin
wutr ne domin wanda yayi afarko ya wadatar”
Kai ta kada masa tafara gyara masa abin sallar yanda zai
ishesu,
Limanci yayi yajasu sallar suka gudanar da sallolin nafila
wanda hadda shafa’i da wutr, addu’o’i sosai jabir yayi
musu wadanda ba zasu faduba,
Bayan ya shafane ya jiyo yana kallonta, “binti idan kin idar
akwai kaya acikin babban falo kije ki dauko, ina fata dai
bakiyi wani girkin ba? Saboda yau naga kinsha aiki da
yawa”
Addu’ar ta shafa tana kokarin cire hijabin jikinta “hmm
abbu banyi ba dama yanzu nake tunanin dafa mana
indomie”
“To na hutar dake basai kin dafa ba”
Hijab din ta ajiye ta fita taje ta shigo da kayan da yazo
musu dashi,
Kaza dukekiya ta gani guda biyu gasassu ga chocolates
dinta kala kala sannan ga kayan marmari suma daban
daban,
Baje kayan tayi tana kallon jabir “abbu yau ka hutar dani
nagode da yanzu sai nasake shiga kitchen”
Yan yatsunta ya kamo “babu komai binti, ai naga sakonki
ya sameni har office, me yasa kika bini dashi har can?”
“Bana son ka zauna da yunwane shiyasa kuma nasan kai
ba cin abinci zakayi ba haka zaka wuni da yunwa nikuma
bana son haka”
“Nagode binti, ga abinci nan kici nakine ke daya”
Idanuwanta ta ware “abbu wannan sunyi min yawa, bazan
iya cinyesu ba”
Kankana ya dauka yakai bakinsa “ni kinga iya abinda nake
sha’awa kawai, ita kadai zansha”
“Abbu kazar fa?”
“Takice yarinya, kici kayanki kinji”
Kai ta girgiza tafara yagar kazar tana ci har taci rabi nan
taji tafara koshi,
“Abbu yau zaka doramin karatu ko sai gobe?”
“Duk yanda kikeso binti, amma karatunmu na yau daban
yake dana ko wacce rana, karatun yau na musamman ne”
Cigaba tayi da shan chocolate dinta domin bata fahimci
inda maganar tasa ta dosa ba, har ta kammala yana zaune
yana kallonta, kanta ta dora asaman cinyarsa,
“Washh abbu cikina nakoshi da yawa”
Kanta ya fara shafawa yana yi mata lalube acikin gashinta
“Kinyi irin koshin da ba aso mutum yayi, annabi yace idan
dayanku zaici abinci to ya raba cikinsa gida uku, kashi
daya abinci kashi daya ruwa, kashi dayan kuma iska
saboda gudun kada ya cutar da jikinsa”
Zaune ta tashi “hmm abbu komai dai a musulunci ana
bashi hakkinsa, Allah abbu musulmai sunji dadin
rayuwarsu”
“Tashi muje nasaki aiki a kitchen”
Tashi yayi yaja hannunta suka fita zuwa kitchen, shayin
na’a na’a ta dafa masa da kayan kamshi sannan suka
dawo sashensa, tana kwance akan cinyarsa akan doguwar
kujera shikuma yana shan shayinsa ga tv kuma yana kallo,
Wayarshi ce tafara kara, yana dubawa yaga ummu ce,
“Ummu al’amin kin dawone daga siyayyar?”
Tana jin ya ambaci sunan ummu tafara kokarin mikewa,
cup din shayin ya ajiye ya riketa ya mayar da ita jikinsa
yaci gaba da wayarshi daga karshe sukayi sallama yana
tambayarta al’amin tace yayi bacci tun jimawa,
Wayar ya kashe yana kallon bahijja bayan sunyi sallamar
da ummu,
“Abbu bacci, zanje nayi wanka” tafada tana mutsusstuka
idonta,
“Bari nagama nakaiki kiyi” bata sake magana ba ta zauna
tana jiransa, kasancewar komai nashi cikin sanyi yake
yinsa shiyasa ya dade bai gamaba,
Yana gamawa ya kama hannunta zuwa cikin bedroom
dinsa,
“Ki shiga kiyi wankan” ya nuna mata bathroom dinsa,
“Abbu brush dina da kayan baccina fa”
“Duk zan baki binti, ai na tanadar miki komai saboda
zuwan wannan ranar”
Sabon brush ya dauko ya mika mata hadeda babban towel
sabo fil,
Karba tayi ta shiga bathroom din amma duk tana cikeda
mamaki da al’ajabi,
“Binti yau bazaki bar kofar bathroom din abude ba? Ko yau
babu tsoro?” Yafada cikin tsokana,
Batayi magana ba tasaka key ta kulle kofar, mayukan
wanka ta gani masu kamshi dayawa kala kala, duk sai da
tayi amfani dasu ta wanke jikinta tas sannan tayi brush ta
tsaftace bakinta bayan ta shaftace jikinta da shaving stick,
hatta bayan kunnuwanta sai da ta tsaftacesu kasancewar
wurine dake rike kazanta dan haka dole sai ana kulawa
dashi,
Sai da ta dauki tsawon lokaci tana gyara jikinta sannan ta
fito duk a tsure take da jabir sai muzurai take yi.
Acikin dakin tasameshi kishingide agefen gado yana
kallonta, irin kallon da yake binta yasata jin kunya,
“Abbu nafito” tafada adirirce,
“Ga rigar baccinki nan kishirya sai kisa”
Towel din jikinta ta gyara,
“Abbu to ka fita daga dakin”
“Tofa, wata sabuwa” tashi yayi yana kallonta yafita ya
koma falo, gaban mirror ta karasa ta fara shafe jikinta da
man shafawarsa na touch me mai dadin kamshi,
turarurrukansa ta fara dubawa har ta samo wani guda
daya mai suna taibah, shi ta dauka ta feshe jikinta dashi
sannan ta feshe rigar baccinta,
Bathroom ta koma ta tsaya tafara duba rigar, tabbas rigar
ta hadu sai dai kuma zatasha kunya yau domin rigar za a
iya kiranta da shararatu, banbancinta da gidan sauro kawai
ita rigace amma net shine yanayinta,
Rigar bata bukatar bra domin akwai ajiki sannan tanada
dan karamin pant,kalarta pink colour,
Daurewa tayi tasaka rigar, tana gama sakawa ta juya
tafara kallon jikinta ajikin mirror din cikin bayin, tayi kyau
iya kyau abunka da yar duma duma sai kace oh oh, jin
alamun za a bude kofar yasata saurin janyo towel ta
lullube jikinta, jabir ne ya leko ya jawota waje,
“Haba binti me kika sake komawa yi acikin bathroom
kuma?”
Towel din yafara ja yayinda ita kuma ta rike kam, dakyar ya
janye towel din hakan ya sata saurin rufe fuskarta da
tafukan hannayenta,
“Masha Allah, binti irin wannan kyau haka?”
Sake damke idonta tayi tana doddoka kafafunta akasa,
“To jeki ki kwanta kinji”
Hannunta ya kama ya rakata har inda ta saba kwanciya ya
saketa ya juya, cikin bathroom din shima ya shiga yayi
wanka bayan ya tsaftace kowanne lungu na jikinsa,
Fitowa yayi yanata faman kamshi, gaban mirror yaje ya
fara shafe jikinsa da mayuka masu kamshi,
Kayan baccinshi ya dauko yasaka ya karasa gefenta ya
kwanta gamida janta jikinsa,
“Binti ko har kinyi baccine bayan ba muyi hira ba yau?”
Yarada mata ahankali yana wasa da zip din rigarta, tana
jinsa tayi shiru tayi luf,
“Nasan idonki biyu, jiyo kiji”
Yafada ahankali, jin shiru yasashi jiyo da ita tana
fuskantarsa, cakulkuli yafara yi mata cikin sauri ta rike
hannunsa bayan tafara dariya,
“Abbu kabari dan Allah”
“Au dama kina jina shine kikayi min shiru?”
“Bazan karaba yi hakuri abbu”
“Yawuce binti, shikenan saura karatunmu da muka fara
rannan ko?”
Bata iya yin magana ba hakan ya sashi kashe wutar dakin
bayan ya lalubi bakinta cikin nashi.
***
K’arfe 8 daidai ta bude idonta, dakin shiru babu motsin
komai aciki,sama ta daga kanta take kallo take abubuwan
da abbu yayi mata suka fara dawo mata, hawayen farin
ciki tafara yi fuskarta dauke da murmushi domin wannan
rana ta jiya da yau ranakune masu mutukar muhimmanci
acikin rayuwarta,
Dakyar ta juya jikinta daga barin da take kwance nan taga
tsakiyar gadon tamkar an yanka kaza,
“Hmmmmm abbu kenan” shine abinda kawai tafada
ahankali tafara kokarin tashi, lallabawa tayi ta shiga toilet
tana dingisawa, ruwan zafi ta tara mai mutukar zafi amma
bata saka dettol aciki ba kasancewar ta taba jin wani likita
yana bayani kan illolin dettol ajikin mace shiyasa ba ason
ayi sit bath dashi amma babu laifi ayi wanka dashi ko
kuma awanke kaya domin yana da karfi yana kashe
bacteria kowacce iri ciki harda mai amfani da marar
amfani, gishiri kawai ta zuba acikin ruwan zafin ta shiga ta
zauna domin shi gishiri har maganin kaikayin dake damun
mutum yake yi haka kuma yana riga kafin ciwon cutar
sanyi,
Ta dade acikin ruwan har sai da ya huce sannan tafita tayi
wanka tayi brush amma duk agaggauce take yin wadannan
abubuwan saboda bata son jabir ya shigo ya isketa bata
shirya ba kuma haka ya kamata ga kowacce mace domin
lokacin da aka tashi daga bacci agaskiya lokacine dake
bayyanar da munin mutum kasancewar daga bacci aka
tashi zaka samu wata ma launin fuskarta ya sauya idonta
yayi ja wata harda kwantsa, sannan ita kanta yanayin
fuskar wani iri yake zama har sai anyi wanka,
Fitowa tayi daga cikin bayin tayi maza tafara bincikar
kayan sawarsa, wata farar t shirt ta zaro mai layi layi ajiki
mai dogon hannu da maballaye ajiki, cikin sauri ta saka
rigar sannan ta zaro jeans blue shima tasaka sai dai kayan
tsayinsu yayi mata yawa kasancewar jabir dogone ajin
farko,
Hijabinta ta dauka tayi salla tana idarwa tayi musu addu’o’i
musamman ma kan samun zuri’a tagari duk da cewar jiya
taji jabir ya dade yana yi musu wannan addu’ar lokacin da
abubuwa zasu faru,
Cire hijabin tayi ta tashi bayan ta kammala addu’ar,gashin
kanta taje gaban mirror ta fara tajewa amma kuma sai
kamshin man datayi amfani dashi wurin wankewa yake,
domin ita ba zata iya kwarawa kanta ruwa kawai tabarshi
ahaka ba har sai tasaka man wanke gashi ta wankeshi
domin idan aka zubawa gashi ruwa kawai aka kyaleshi to
zakaji yana wani irin tashi marar dadi har maigida yaji
babu dadi,
Cure gashin tayi ta daureshi ta nufi hanyar fita, akofa
sukayi kicibus da jabir yana kokarin shigowa yasha wando
iya gwiwa da yar shirt dinshi bashida banbanci da samari
irin yan makarantar nan,
Da sauri ta juya masa baya tayi niyyar komawa cikin dakin,
a tsakiyar dakin ta tsaya tana karewa royal bed dinsa kallo
wanda yake a hargutse,
Jinsa tayi ta bayanta ya rungumeta ya zagayeta da
hannayenshi gamida ziro kansa ta kan kafadarta,
“Binti kin tashi?” Yafada acikin rada,
“Abbu good morning”
“Morning bintin abbu, how was your night?”
Shiru tayi tana yamutsa fuskarta,acikin ranta ta tace “too
harsh”
“Binti ba zaki amsa ba?”
Jiyo da ita yayi sai ta rufe idonta sai ga hawaye sharrr sun
fara zuba akan idonta,
Baki bude ya kalleta dama a banza ma tana yin kuka inaga
yanzu da dalili ya samu,
“Kiyi hakuri binti kinji, nine ko? Yi hakuri”
Hadata yayi da jikinsa yafara rarrashinta har ya samu ta
daina hawayen, hanmunta ya kama ya zaunar da ita akan
wani dan karamin stool yaje yafara gyara mata gadon,
kallonshi kawai take yanda yake da sanyin nan to komai
ma nashi a sanyaye yake gudanarwa dan haka ya zame
mata dole ta nemo mafita duk da tasan ba ita kadai bace
mai irin wannan matsalar ba mata da dama suna
fuskantarta,
Hannun nata ya sake kamawa ya rakata kan gadon ta
kwanta, agefenta ya zauna ya fara jan yan yatsun kafarta,
da haka ya ware ya fara yi mata tausa ajikinta, kamar
wacce take jira sai bacci, zama yayi yana kallonta acikin
ranshi yana tunanin irin banbancin dake tsakaninta da
ummu domin yagane akwai banbance banbance masu
tarin yawa bawai kasancewarta budurwa kawai ba ko a ta
fannin ni’ima ni’imarta tasha banban data ummu, kodan ita
bahijjan tana shan kayan marmari ne da sauran abubuwan
datake hadawa da kanta,
Haka yayita yan tunane tunanensa yana zaune yana
kallonta, drewar din gefen gadonshi ya bude yafara bincike
har ya binciko abinda yake nema, wani dan kyakkyawan
zobe ne na gold mai kyau, dan yatsanta na hagu ya kamata
ya saka mata zoben, ya kwanta agefenta yana makale da
hannunta,
Sun jima suna baccin kafin jabir ya tashi yana kallon
bahijja wacce keta faman baccinta tana fitar da numfashi
ahankali, ahankali yafara kokarin zare hannunsa daga cikin
nata, yana gama zarewa ta tashi firgigit,sai kuma tafara
kallonsu shida ita, sunkuyar da kanta tayi tana kallon
kayan jikinta,
“Abbu kagani kayanka sunyi min yawa ko”
Murmushi jabir yayi ya matsa kusa da ita “amma ai sunyi
miki kyau binti”
Kallonshi tayi tana tuna wani abu acikin ranta wanda ita
kadai tasan ko me take tunawa,
“Abbu yunwa nakeji” tafada tana turo baki,
“Zakici abinci yanzun nan binti, ai nasan bakya wasa da
abinci shiyasa kike da karfi sosai kusan ma kinfini karfin”
“Haba abbu wanne karfi nafika? Tayaya kasan haka alhalin
nida ba dambe muka yi dakai ba”
Sakin hannunta yayi yana murmushi tare da kokarin sauka
daga kan gadon yana cewa “dambe na nawa kuma binti”
Falo ya fita ya shigo mata da kayan Karin kumallon da ya
shirya mata shida kansa, akasa ya ajiye mata ya kamota
ya sauko da ita,
Kazar jiya taga ya dumama mata sannan ya soya mata
kwai ya dan soya mata dankali da plantain, sai ruwan tea,
“yau zanci girkin maza kenan” tafada aranta,
Dankalin taci da plantain din tasha tea ta tashi tana mik’a,
“abbu natafi dakina sai ka taho”
Kafin ya dago yayi mata magana har takai bakin kofa
hakan ya sashi yin shiru, fita tayi ta koma dakinta tana
zuwa tafada gado ta janyo katuwar teddy dinta ta rungume
sai alokacin duk abubuwan da suka wakana tsakaninta da
jabir suka fara dawo mata, idanuwanta ta lumshe tana jin
wani irin farin ciki har cikin ranta, tana nan kwance har
jabir ya shigo kunnensa makale da waya yana magana
amma daga yanda ta fuskanta da al’amin yake wayar
domin ta jiyoshi yana cewa
“Al’amin antyn naka ai sai kayi mata sannu saboda bata
dan jin dadi”
Wayar ya mika mata yana shirin zama akusa da ita gamida
zare teddy din dake makale ajikinta,
“Ni ni nidai lafiya ta kalau” tafada tana turo baki, dan
yatsan da ya saka mata zobe ya kamo yafara ja yana cewa
“yanzu ni zaki rinka rungumewa ba teddy ba binti, wayar ta
kara a kunnenta tafara magana,
“Al’amin, yakake?”
“Anty fine” yanda yayi maganar sai taji tamkar mahaifinsa,
sama sama ta biyeshi suka danyi shirmensu da suka saba
amma yau bata bari sunyi nisa ba saboda wani iri takeji
ajikinta sannan gashi gabanta sai faman faduwa yake yi,
“Abbu bazaka fita bane office?” Ta tambayeshi bayan ta
ajiye wayar,
“Yau ina gidan nan tare dake binti, ko bakya son in zauna
natafi?”
Kanta ta kwantar ajikin kafadarsa, “inaso mana abbu
amma tunda natashi nake jin gabana yana faduwa”
“Kina yin wasa da addu’a binti, bakya son yin addu’a”
“Abbu wlh inayi”
Kafin ya sake yin magana wayarta tafara kara, cikin
hanzari ta daukota tana duba sunan wanda yake kiran.
Add Comment