Littafan Hausa Novels

Senior Bachelor Hausa Novel Document

Senior Bachelor Hausa Novel Document

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Senior Bachelor Hausa Novel Document

 

1-5

Yan mata ne haddadu kusan yan shekaru ashirin suka shiga garden na gidan da gudu kaman an koro su, sai haki sukeyi suka zube a gaban wadda yake zaune akan doguwar kujeran, tsawa ya daka musu” kai ku shashashun ina ne, duba yadda kuka ta da kura sai kace wasu dawakai…. Nonsense

Karanta Littafin Babu So Hausa Novel

Bakin su yana rawa alaman suna so suyi magana amma sun kasa, sai daya daga ciki ce tayi kokarin saita kanta cikin rawar murya tace Yayah Hafcy CE, Hafcy muka gani, a dari Yayan ya tashi yana jujjuya idanu yace a ina, ina take, a ina kuka ganta? Sai a lokacin dayar ta amsa da yanxu muka ganta tazo gidan Antyn ta a wancan line in, ta fada tana pointing da yatsa.

 

Cikin zafin nama ya suri key na mota ya fita daga wajen, sai daya danyi nisa ya juyo yace ga wancan container ku duba akwai recharge card Ku dauka na 2k each of u, da sauri ya juya ya fita.

Wani mugun dariya suka kwashe suna tafa hannu, daya mai suna Mooner tace mai na fada miki sis, ai in baki da card a waya kawai ga logic na kawo haka zamu ringa mishi, Rookie ta juya ido tace kuma haka fa, ai shikenan senior bachelor ya shigo hannun mu, amma wat if ya kamo mu, Mooner tace ai kullum we gat to form some new deals tunda mun gane ba karamin so yake ma beb in nan ba. Cikin fuskan tausayi Rookie tace amma har ya ban tausayi ki duba yadda ta rude alhali karya mukeyi, Mooner tace to sannu mai zuciyar tausayi don’t even start, tashi muyi abin gaban mu joor.

Tashi sukayi suka fara barnan kwashe recharge cards kaman na sayarwa sunayi suna dariya har suka gama.

 

Shi kuma yana barin garden na gidan ya nufi parking space na gidan yayi wa Motar shi kirar lexus key ya fita. Sai dai ko alama bai ga wani abu da yayi signifying Hafcy ba, haka dai ya cigaba da duba ta a layin amma shiru babu ita, dafe goshin shi yayi ya daki steering motar sannan ya juyo ya nufi gida.

 

Yana parking ya fito jiki a sanyayye ya ci karo da Alhaji Jibrin Daddy’n su kenan, tsugunawa yayi yana gaishe shi, Daddy bai amsa gaisuwar ba ya shiga sababi kamar ko yaushe in sun hadu “kai kenan ba za kayi wa kanka fada ba kullum kana yawo a kan kwalta, sa’anin ka duk sun aje ya’ya amma kai ko alamar niyya babu, to wlhi na fada maka ba zaka mun arba’in a gida ba, shi dai senior bachelor kan shi yana a kasa bai ce uffan ba, a haka tsohuwa Dada ta fito tana yafa gyale tare da daura na ta comment in, tace to in ni kake jira ma a kul dinka dan ni sai sabon jini irin galadima. Murmusawa senior bachelor yana yi musu a dawo lfy ya shiga ciki.

 

Yana saka kafan shi a parlour Mami ta danna mishi kira IBRAHIM…….

 

Eesha en Nana fa’ad

Add Comment

Click here to post a comment