Littafan Hausa Novels

Abdul Jalal Hausa Novel Complete

Abdul Jalal Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Abdul Jalal Complete NovelAbdul Jalal Chapter 1 Complete Hausa Novel

Abdul Jalal Chapter 1 Complete Hausa Novel

Aihausanovels9/06/2022

 

 

 

Bismillahirrahmanirahim da sunan Allah me Rahma me jinkai Allah kayi salati abisa shugabanmu annabi Muhammad salallahu alaihi wassalam

 

Bayan haka ban rubuta wannan littafi domin cin zarafin wani ko wataba nayishine domin nishadantarwa dkuma wa azantarwa kubiyoni domin jin me wannan labarin ya kunsa

 

Ina maraba da shawarwari, sharhi, kokuma gyara nagode.

 

 

 

This is my first novel

 

 

 

Misalin karfe biyu na ranaa a cikin garin kaduna, lokacine da rana ta kwalle tayi zafi sosai mutane wasu na hada hadarsu wasu Kuma sun koma gefe suna hutawa, tafiya take a hankali kaman batajin zafin ranar jikinta sanye da uniform take ratsa lungunan anguwarsu harta karaso wani matsaikacin Gida dayake rukunin gidajen layin dayakasance gamayyar masu kudi da masu rufin asiri, a kofar gidansu taci karo da wata hadaddiyar mota baqa, tana ganin mortar tayi murmushi ta shiga Gida da Sauri tundaga tsakar Gida tafara sannu dazuwa kawuna kuma babana, oyoyo da kyakyawar yata kuma ya tagari Cewar wani babban mutum dake zaune a daya daga cikin kujerun wani matsakaicin palour gefensa kuma wata matashiyar matace a zaune a kasa daka ganta kaga mahaifiyar wannan yarinyar saboda kamar dasukeyi, a kasa tazube tana gaida mutumin ya amsamata cikin sakin fuska yata ya makaranta lafiya kalau kawu aniyi mana Hutu yau mungama mock zanshiga ss1, masha Allah Ashe yarinyartawa ta girma shikenan faduwa tazo dai dai da zama kishirya anjima zan koma dake zan tafi muje kimana hutun acan to kawu d fara artata juyo ta kalli mamanta mama yau zan tafi ke Kadai zaki dinga kwana mhmmm Kawai mama tace amma har ga Allah bataji dadi ba batason yarinyarta ta yi nesa da ita amma yadda Alhaji imam yke nunawa yarinyarta so bazata iya cewa a’a ba kasancewar yarinyar yar Dan uwansa ce, ita kuwa murna take koba komai kwana biyu zata huta da fadan mama.

 

Misalin karfe Biyar na yamma sukashigo garin kano ta dabo jalla babbar hausa, rukunin gidajen sharada NNDC quarters ananne Inda gidan alhaji imam yake, gidane babba Wanda akayiwa gini na zamani gidan yyi matukar tsaruwa, yaran gidanne sukafito domin Tarar mahaifinsu suna masa sannu dazuwa ai daganin shida wadda yake tare suka dau murna, murna farinciki ya mamayesu Nana ce tariqo hannunta tana naji dadi JALILAH Hutu zeyi dadi 💃💃 ta rungumeta suka shiga cikin gidan, matar gidan da fara arta take fadin sannunku dazuwa yau munyi babbar bakuwa murmushi JALILAH tayi tazube har kasa tana gaida matar amsamata tayi Nanace tajata dakinta tace shiga ki watsa ruwa kizo musha hirar yaushe gamo,

 

 

karfe takwas na dare iyalan gidan suka hallara domin cin abincin dare, daga bakin kofa sukajiyo muryarsa kai kai kai wanake gani haka kaman wata Yar kauye nake gani cewar wani matashi dabaze wuce shekaru ashirin da biyuba yayin shigowa palourn dariya suka kamayi wuce nan wlh Niba Yar kauye bace, murmushi yayi yace to Yar birni saukar yaushe Nana tayi caraf tace saukar dazu da abbah yaje yataho da ita hakan yayi kyau Cewar matashin haka sukacigaba da hirarsu gwanin sha awa.

 

 

 

*****************************

 

Zaune yake a cikin parlour yadora qafa daya kan daya yanata busa shisha sekace salansar tifa ta hanci ta baki gefensa mp ce ke fitar da sautin kida a hankali se lumshe ido yake alamu yanayin yayi masa dadi wayarsa ce ta dau ringing yanaji har ta katse be kulaba takuma ringing ya kallah seyaga mum a jiki ya kauda kai yacigaba da busa hayaqinsa karo na hudu wani kiran Yakuma shigowa a fusace yadaga wayar what’s is it ne mum kinkira ban daukaba ai seki hakura kinsan INA wani abunne haba Dan Allah 😱😱😱 jalal kazo yanzu inason ganinka akace daga daya bangaren am having rest now komene let’s meet tomorrow bejira mezata kuma cewa ba ya kashe wayarsa yasata a flight mode yacigaba da babbakar hayaki qaramar wayarsa ce itama tafara ringing yaja wani dogon tsaki ya dakko Dan duba waye jeje ne akan screen din wayar dagawa yai kara wayar a kunnensa be maganaba ya danyi shiru yace karkutafi gani nan…

 

 

 

Download>>> Maciji Ne Complete Hausa Novel Document

 

 

 

Jalilah tawayi gari a cikin garin kano, da garin Allah ya waye tareda Nana suka Shiga kitchen suna hada breakfast sunayi suna hirar makaranta Nana CE ta dubi jalila tace sister dama kiyi zamanki a kano sekicigaba da karatun a an an kinga bani da Yar uwa mace se jimmai house girl din Ummi inajin dadin zama da ita amma ita kullum cikin yawon biki take, hmmm ajiyar zuciya jalila tayi taace idan nadawo kano mama fa in barta ita kadai a Kaduna naana bazan iyaba kam, Dama nasan bazaki yaddaba dallacan matsa kiban guri murmushi kawai jalila tayi, suka cigaba da aikin dasuke, wajenkarfe shadaya suna dakin Nana suna hira jalila take cewa gaskiya Nana garin kano tanada kyau matuka na Dade rabona da kano, ai ba kya ziyara taya zaki Sani ba kya zumunci kullum kina like da mama, kudin zuwa kuke ai hargara ni kuma ai bazuwa kuke ba dalla bari mu tambayi Ummi muje kiga gari Yar kauye kawai wuce nan wallahi kema Yaya jawwad dince ko dariya sukayi sukasa hijjabai suka fito parlour Ummi ta dubesu se INA Ummi zamuje gidansu nusaiba ne jalila ta danga gari kinsan kifin rijiyace, murmushi Ummi tayi tace to adawo lafiya akula da kai kuma karku Dade to Ummi sukasaka kai suka fita sunata hirarsu gwanin sha away Layinn shiru se kukan tsuntsaye dasuke shawagi akan manyan bishiyoyin dasuke cikin wasu daga gidajen dake unguwar suna tafiya suna hira,

 

a guje wata mota ta taho da gudu kaman zata tashi sama se uwar kura datake tashi kwata² tukin rashin hankali akeyi galalala jalila tabi mortar da kallo Nana ta tabota yadai tab amma nana direban motan nan bashi da Rabin hankali in akasamu akasi ya bige wanifa, hmm ko a jikinsa jalila me tukin nan baya ganin kowa da kima a anguwarnan babu me fadamasa yaji haka rayuwarsa take ko iyayensa basu ISA dashiba Yaya jalal kenan abokin Yaya jawwad ne, tab amma ya akayi Yaya jawwad yake abota da irin wannan Sam halinsu be kamaba, jalila kenan kema kyafada anyi2 arabasu abu yaci tira Allah ne yahada jininsu yana matukar son Yaya jawwad, hmmm Allah y kyauta Cewar jalila Nana tabita da Ameen, haka sukaje suka dawo suna ta hirarrakinsu, wayar hannun Nana Ce tafara ringing ta daga tayi sallama jalila bata iya jin abinda ake fada a wayar se dai murmushi da Nana tayi tace sorry mun Dan fitane sister tace tazo muka fita bari mu biyo, ta kashe wayar jalila zomuje wata qawatace tazo kai wannan hutun zemun dadi gaki ga ilham mtseww kekin cika gayyar kawaye wlh ni nagaji gaskiya, Dan Allah kizo muje to shikenan muje sarkin naci.

 

 

Kofar palourn ya tura ya shiga yanufi kitchen kai tsaye ya Shiga yadakko abinci a Warmer’s yana shirin fita jalal yaji ankira sunansa be waiga ba yatsaya INA ka kwana jiya matar ta jefomasa wannan tambayar yayinda take sakkowa daga kan bene ba magana nake maka ba INA ka kwana jiya juyowa ya kalleta a club yafada kansa tsaye batare da wata shakkaba jalal wato kai ko kimata baka gani kankaa tsaye kake gayamin a club ka kwana ohhh my God mum tambayata fa kikayi nagayamiki shima kuma laifi nayi I don’t want the way u are treating me mum kibarni inyi abinda ya dace dani cikin daga murya da gadara yake maganar Wanda yayi dai² da shigowar su jalila tundaga waje suke jiyo hayaniyar jalal da mahaifiyarsa abin yyimatukar bawa jalila mamaki itakuwa Nana ko a jikinta Dan ta saba jin irin wannan rashin ta idon da abokin yayanta yakeyi yaja wani dogon tsaki yafito waje, mommy INA wuni yawwa sannunku nana, mummy INA ilham tamin waya tazo nuni mummy tayimana da dakinta cikin damuwa ta koma sama, mukuma muka nufi dakin data nuna mana muna Shiga suka rungume juna suna murna, nana wannan sister dinkice kuna kama matuka eh kanwata ce sannu ya sunanta jalila nana tabata amsa hmm nice name thank u kawai jalila tace amma hankalinta na kan abinda tagani yau wannan Sa insa tsakanin da da mahaifiyarsa abin yabata mamaki kuma yadameta,

 

bayan sun koma Gidane jalila ta kalli nana tace nana gidan da mukaje dazu wlh wannan din nan bashi da tarbiyya wallahi wakenan kike nufi oho ban San sunanshiba wannan din nan me dogon hancin nan kaman tattasai tooo dariya nana takamayi tattasai ni banganeba mtseewww is not joke nana y kalli mahaifiyarsa yace mata a club y kwana yana mata shouting haka, mhmmn bakiga komaiba India jalal ne jalal ta maimaita sunan yeahp shine me driving a mortar nan dazu kafin kibar kano zakigane wayeshi bakiga komaiba, amma a haka Yaya jawwad yake abota da shi jalila ta tambaya cikin tuhuma, jalila ba se lallai hali yazo daya ake abota ba soyayya da shaquwa gamon jinine tsakaninsa da Yaya jawwad Allah ne yahada jininsu, Yaya jawwad se yasaka jalal ABU yayi amma mummynsa bata isaba, ga shaye shaye a cikinsa yawon club ba Wanda ba yayi, tabdijan nana wannan abotar bame yiwuwa bace inji jalila kaman yaya, basu dace da abotar ba wannan Sam bashi da tarbiyya Dan haka sena rabasu bashida tarbiyya Nana tirkashi!!!!!!!!!!!

 

 

 

Download>>> Kamanni Complete Hausa Novel Document

 

 

 

Kallonta Nana tayi, ta ce

 

“kaman ya se kin rabasu, ina ruwanki dasu? kinga Jalila ba ruwanki dasu, Maaama ma tayi ta Hakura, Jalal ba ze iya rabuwa da Jawwad ba, bayan abokansa na banza ina ga Yaya Jawwad ne kawai mutumin kirki, kika sani ko Allah ya shiryeshi a sanadin sa? kawai muyi musu addu’ a.”

 

Ajiyar zuciya Jalila tayi ta ce “Nana abotar Yaya Jalal da Ya Jawad sam bata dace ba,

 

barazana ne ga tarbiya da rayuwar Yaya Jalal mutumin dabe ji maganar Wanda suka kawoshi duniyaba ne kike zaton ze wani shiryu sanadin wan?i yau da gobe se Allah yasha giya ya kwana club yayi sa’insa da mahaifiyarsa shi kike tunanin ze shiryu sabodaa wani aboki Sam bashi da tarbiyya Nana .”

 

Jalila Allah shi yasan manufar hada abotarsu duk da banbancin halayensu, kawai muyi musu addua shine mafita mukuma muyi abinda ke gabanmu.”

 

“Nana ni kam nacji amma ban gamsu da bayanan ki ba , zanyiwa Yaya Jawwad magana,”

 

” to Allah yatemaka inji Nana, amma kome zakiyi karki shiga harkar Jalal.”

 

Ajiyar zuciya Jalila tayi ta ce “karki wani damu Yar uwata, ni dai fatana yafita shirgin yayana, bana so yazama irinsa ya lalatamin Dan uwana,

 

tunda shi lalataccene ma tayashi da addu a.”

 

“To Allah ya baki Sa’ a, nima da naso hakan”.

 

 

 

********************************

 

 

 

Sanye yake da kananan kaya, wando 3quater fari da Riga T-shirt itama fara, yayi kyau sosai, yasa hannu ya dauki turare ya feshe jikinsa dashi, ya dauki wayoyinsa dake kan mudubi da mukullin motarsa yafito.

 

Kai tsaye ya nufin inda akayi parking motoci, sekuma ya juya ya nufi cikin gidan.

 

yanazuwa kofar parlour ya budee ya Shiga, ba sallama ba komai fuskanan tashi a daure tam babu alamar fara’a

 

parlour shiru se kamshin turaren wuta dana abinci da ya gauraye parlourn, gefe kuma Ilham ke kwance kan kujera 3seater tana kallon Tv.

 

“keee!!”

 

ya fada cike da gadara ,

 

a dan tsorace ta dago Dan batasan ya shigo ba, “Yaya Jal sannu da zuwa”

 

 

 

Download>>> Burin Abbana Complete Hausa Novel Document

 

 

 

Ta fada tana kallon sa tare da yaba kyawun da yayi acikin ranta, be amsa ba yace

 

” Ina matar gidan nan take?”

 

“matar gidan nan kuma?”

 

ta maimaita tana dubansa

 

“ba kiji bane ko kuma tsabar rainin hankaline?”

 

Adan daburce ta ce “ai jinai kace matar gidan nan, wai mummy kake nufi?”

 

” Yaushe raini ya shiga tsakanina dake ne? har nake magana kina maimaitawa, akwai wata mata a gidan nan banda itane?”

 

Mamakinta ne yakasa boyuwa, lallai yaya Jalal abin nasa ya girmama, mummyn tasa ma bata tsiraba wai matar gidan nan? tabdijan, amma ta dake ta boye mamakinta ta bashi amsa da

 

“ta fitane, taje saloon”

 

“mtseww” ya Dan jaa tsaki , “inta dawo ki ce ta kirani a waya, ina da magana da ita.”

 

Bai jira mezatace ba yasa kai yafita,

 

“ohh God ni Ilham, yaushe Yaya Jalal ze fara sakarmin fuska ne yana kulani? kullum mutum fuska a daure Yaya Jalal whyyyy?? ”

 

tafada tana jifa da pillon hannunta,

 

“I must do something!”

 

tafada tare da mikewa tabar parlour.

 

 

 

**********************************

 

JALILA ce zaune akan carfet tana waya da umminta,

 

“masoyiyya nayi missing dinkifa irin sosai din nan ummina”,

 

“bawani nan tunda kika iya tafiya kikabarni,”

 

“ummina kenan kina birnin zuciyata fa”,

 

” ke tafi can ya mutan gidan naku kowa lpy?”

 

“ummi garin kano ya hadu kinsan na dade banzoba zuwan yayi min dadi”

 

“to hakan yayi kyau”,

 

“ke dazu wata kawarki tazo ta bani sako in gayamiki amma wayata babu caji in anjima mayi waya yanzu fita zany”‘

 

“ina zakije kuma ummi?”

 

“inda kika aikeni”

 

“huh ummina ta kaina adawo lafiya anjima zankiraki insha Allah”

 

“to shikenan ki gaida ya’n uwannaki ki gaidamin da halima(Maman su jawwad) kar inkirata tazata dankina gidanne nakirata to Ummi zasuji insha Allah”.

 

“To shagwababbiya Yar gidan Ummi wannan shagwaba haka kinfa girma JALILA Cewar JAWWAD

 

 

 

Download>>> Kishin Bal-Bal Complete Hausa Novel Document

 

 

 

Murmushi JALILA tayi tare da fadin “Allah yatemaki babban Yaya ai ba a girma a gurin iyaye mussaman iyaye mata”

 

Murmushi yayi tare da fadin “kekam halinki yana nan baki canza ba kome mutum yagayamiki kinada amsa dai dai da abinda yace JALILA baki abun magana,

 

dariya sukayi gaba daya

 

“yace ba wannan ba tukuna yanzu dai ya studies dinki komai lafiya dai ko?”

 

“Alhamdilillah Yaya JAWWAD komai lafiya ina karatuna yadda yakamata,”

 

” to masha Allah haka akeso amma kamata yayi kiyi waec a ss2 se Asama miki admission a BUK kidawo kano gaba daya”.

 

“Tab to umminawa fa shikenan in batta acan”

 

” murmushi yayi yace haba JALILA wataran fa aure zakiyi kitafi gidan miji ko me rabawa taraba (MUTUWA!!!)”

 

” Kaman yadda ta rabani da banana ko ta fada idonta cike da hawaye Yaya jawwad karkamin wannan fatan, idan narasa ummina yanzu wanake dashi daze soni kaman su,

 

abbana yatafi yabarni bana fatan ummina ta barni, nafiso in mutu in barta”

 

“Haba JALILA kinga share hawayenki kinji qanwata bahaka nake nufi ba yanzu idan Abba yaji furucinki na wa kike dashi baze jidadi ba Abba yana matukar sonki ya daukeki kaman yanda ya daukemu ko kinrasa kowa ni INA tare dake kanwata har abada yayanki yana tare dake duk wuya duk dadi zan kasance tare da ke”.

 

 

 

Taji dadin kalaman yayannata mutum ne nagari me kirki tayama zata bari abotarsa ta dore da wancan sakaran yabata matashi baze yiwuba dole tayi wani Abu, “Yaya JAWWAD inason in maka wata magana…

 

Mamansu jawwad kuwa da tazo shigowa parlourn ta riski hirar tasu ta labe tana sauraransu abin se ya kular da ita, me jawwad yake nufi da ze kasance tare da yarinyar nan duk rintsi aikuwa baze yiwu ba, dole tayiwa tufkar hanci bazata taba bari danta ya auri jalila

 

ba in ma sonta yakeyi danko maqiyinta tagani ze aureta tahanashi saboda gudun bacin suna ahaka dai gata kamilar yarinya tagari me da a amma babu asali me kyau ta danyi tsaki

 

( 😱😱😱 tooo wata sabuwa me ummu jawwad take nufi ne

 

Wayartace takama ringing Wanda yasa dole ta fito badan tagama jin hirar tasuba tare da kakalo murmushin yake Yaya da kanwarsa hira akene “wlh kuwa maaamaa, ni zan wuce zan raka JALAL wani gurine,

 

gaban jalila ne yafadi jin ya ambaci jalal ta dago a Dan razane tana kallonsa,

 

“to sekun dawo ka kula da kanka Cewar maaama”,

 

“sisy akwai damuwane” yafada yana kallon JALILA,

 

 

 

Download>>> Raɗaɗi Complete Hausa Novel Document

 

 

 

girgiza kai tayi yace to sena dawo, “safe journey”

 

tafada a takaice yace thank u sisy maaama sena dawo to asauka lafiya Allah yasa ya amsa yafice.

 

Maaamace ta amsa wayarta data cigaba da ringing salamu alaikum tafada ta danyi shiru to shikenan inkin dawo da magariba zan turo su Nana su karbarmin to nagode,

 

 

 

********************************

 

 

 

Banyan sallar magariba maaama ta aiki su Nana tace su shiga gidansu JALAL zasu karbo mata sako gurin mummynsa,

 

da sallama suka shiga suka Tarar zata fara cin abinci, gaisawa sukayi suka fadamata Aiken

 

” tace to bari in dakko muku sakon” “aa tunda kinzuba abinci kigama tukuna Cewar JALILA,

 

Eh momy gama bari muje gurin ILHAM kafin kigama inji Nana to shikenan sekun fito

 

Tana zaune a palour tana cin abinci yashigo yasamu guri ya zauna ya kalleta

 

“ILHAM bata gaya miki saqona ba?” “tagayamin” tabashi amsa a takaice,

 

“meyasa baki kirani dakika dawoba?” nace inason magana dake “ban niyyaba” tabashi amsa

 

Dakin ilham suka shiga ta kwanta rub da ciki tana kallon hotunan JALAL

 

sallamarsu yasa tayi firgigit ta aje wayan

 

“yan matan maama sannunku dazuwa

 

“yawwa sannu” JALILA ta amsa haka kurum ILHAM intaga jalila se gabanta ya dinga faduwa tarasa meyasa,

 

NANA takalli ILHAM “” daddawar daki wannan zuwannaki ba yawone?”

 

” ke dai bari wani abu ke damuna wlh,”

 

” tooo menene inji Nana ”

 

kedai bari semun hadu kawai”, jalila tunawa tayi zasuyi waya da umminta in anyi sallar magariba tabaro wayar a Gida maybe tana can tana kirana, “Nana bari inje indawo inazaki inji Nana yanzu zan dawo tafito da Sauri

 

“Dubai nakeson tafiya next months

 

kudi zaki turamin a account”

 

” mezakaje kayi a Dubai?”

 

” aa meye kuma na tambayata ina daddy yace idan INA bukatar kudi abani to mene na tuhumata kuma”

 

se kajira ubannaka yadawo seyabaka sangartaccen banza yaushe rabonka da makaranta Baka zuwa karewama sokake ka tsallake kabar kasar karatun ko oho ko?

 

“Wait please meye kuma namin fada kibarni in tsara rayuwata yadda nakeso ba ruwanki da abinda nake aikatawa makaranta ko inje ko kar inje ai bada kudinki ake biyaminba duk kin takuramin kin tsaneni ni am doubting ma if u are my biological mother 😱😱😱

 

“Allah wadaran naka ya lalace tur da Dan daze tsaya gaban mahaifiyarsa tana fada yana mayarwa,

 

Anya kana Neman albarka a rayuwarka asara ta tabbata ga me sabawa iyayensa

 

Gaba daya suka waigo domin ganin me maganar……..

 

Gaba daya suka waigo suna kallon inda jalila take maganar, taci gaba da fadin

 

“duk d’a nagari me fatan nasara a rayuwarsa, baya fad’i in fad’a da mahaifiyarsa wannan ba halin d’a nagari bane me neman albarka,

 

wannan ba komaibane kake face tsantsar rashin tarbiyya!!”

 

ta kare maganar tana kallon cikin idon jalal,

 

ta kalli mummyn Jalal tace “mummy seda safe Nana ta taho da sakon”

 

Idanuwansa ne sukayi jawur jijiyar kansa ta daddaga ganin yarinya Karama ta tsaya tana gaya masa miyagun maganganu,

 

Wani yunkuri yayi da nufi ya karasa inda jalila take ya hukunta ta

 

mummy tasha gabansa ta rikeshi gam, duk da ta danji ba dadi da Jalila takira Jalal Mara tarbiyya amma ta dake tare da fadin

 

“Karka kuskura ka tabata abinda tafada gaskiya tafada kadan kagani Indai haka zakacigaba dayiwa rayuwarka, indai zaka cigaba da gayamin maganganunu daka gadama kana wuakantani agaban mutane.”

 

fizge hannunsa yayi da karfi

 

 

 

Download>>> Rabon Kwaɗo Book 1 Complete Hausa Novel Document

 

 

 

“kicikani wallahi sena kakkarya yarinyar nan ni zata gayawa wannan maganganun wallahi sena koyamata darasin da harta mutu bazata mantaba,”

 

Da gudu jalila ta ruga ta fice daga palourn.

 

hannunsa ya fizge daga cikin na mummy ya rufa mata baya a zuciye, amma kash kafin ya fito harta bace kaman walkiya yanemeta yarasa, har bakin gate yafito amma be ganta ba, yanufi dakin me gadi Yakama buga masa kofa iya karfinsa,

 

a sukwane me gadi ya fito babban mutum amma haka ya zube agaban jalal jiki na bari “ranka ya dade….” Begama ba JALAL ya katseshi

 

“kaii yarinyar da ta fita yanzu INA tayi,” jalal ya katseshi

 

“Ranka ya dade sallah nakeyi banga fitar kowa ba”

 

” shut up!!! Useless man Sam bakasan aikinkaba dakiki kawai,”

 

A fusace ya shiga part dinsa zuciyarsa na tafasa, he wish Yakama yarinyar nan da ya nuna mata waye jalal,

 

‘me yasa kika rikeni kika hanani daukar mataki akanta yafada a fili Dan karamin flower base din dake kan side bed dinsa ya dauka yayi jifa dashi yana huci,

 

“Waima Yar uban waye daga ina take”

 

Kaman yataba ganinta amma yamanta a ina ne

 

wayarsa CE tafara ringing, bros jawwad ne yafito akan screen din wayarsa, yadaga wayar yakara a kunnensa, ”

 

“Dan uwana meyasameka tun dazu nake nemanka kazo ka karbi ajiyarka,

 

Wai yanaji kanata hucine me yafarune,”

 

“bari bros bakomai zan fitane inna dawo zamuyi magana wata Yar iskar yarinyace ta zageni kuma idona idonta sena lahira yafita jin dadi” JALAL yayi maganar a hasale,

 

“Subhanallah haba Dan uwana ya kake fadin haka kaifa me hakurine fushi banakabane nasan maybe wani Abun kayi mataa kamanta da ita kawai yanzu dai kana ina”

 

“Bazan mantaba din wallahi sena koya mata hankali” cewar JALAL

 

“Easy bross karkayi fushi Manzon Allah salallahu”

 

“………..alaihi wassalam” Jalal yakarasa masa, “zaka fara Toni fita zanyi semun hadu da anyi magana sekace mutum yayi hakuri ka dauka kowa irin Kane”

 

“Dan uwana ina maka nasiha kaji tsoron Allah Dan an bata maka rai kar in kafita kasha giya Dan Allah kar kasha giya koka aikata abinda ba shikenanba babu abinda zata qara maka se bacin rai,

 

garaka… ..”

 

kitt JALAL ya kashe wayar in yatsaya cigaba da sauraron JAWWAD ze kuma bata masa rai,

 

Lamabar Jeje ya nemo bugu biyu ya dauka ya kara wayar a kunnensa

 

“Man where are u now?” Banji me akace daga daya bangarenba

 

“OK I will be there”

 

Ya kashe wayar yafice daga gidan

 

Da gudu ta karasa cikin gidan sukayi karo da Abba a hanyar shiga gidan tanata haki kaman tayi wrestling,

 

“Meyakoromin ke haka diya tagari”

 

“Am..mmm… Maama CE ta aikemu shine nayo gaba wani kare yabiyoni tafada tana maida numfashi”

 

“Shine kike wannan gudun in kika fadi fa matsoraciya kawai ba a yiwa kare gudu inbahakaba wataran seya cijeki” yafada cikin wasa

 

“Tunda kin shigo Gida seki tafi a hankali”

 

“To nadena abbana”

 

“Good girl, kodayake yanzu tazama lady”

 

Murmushi tayi tashige ciki kai tsaye ta tafi dakinsu tana kuma sauke numfashi

 

“Tab daya kamani dana gane kuskurena yadda idonsa yayi ze iya sumar dani fa”

 

Tayi maganar a zuciyarta

 

 

 

Download>>> Abban Sojoji Part 1 Complete Hausa Novel Document

 

 

 

wayarta ta laluba tafara trying lambar Ummi amma taki shiga har tagaji ta aje wayar,

 

ta mike tashiga bandaki tayo Alwala tafara gabatar da sallar isha’i ta idar da sallah ta canza kaya zuwa na bacci ta nashirin kwanciya Sega Nana tashigo

 

“Se yanzu?”

 

“Eh nai ta zaman jiranki baki dawoba nagaji shine na karbi sakon na taho, dama atamfofine maama zata Cuba”

 

“Hmm yayi kyau” cewar Jalila.

 

Can na hango shi yana zaune kan wasu fararen kujeru matasa ne maza da mata suke kaiwa suna komowa daganinsu kaga yayan Hutu masu karancin tarbiyya,

 

fuskar nan tasa a tsuke kansa dauke da wani irin aski ga Suma fal akansa se cika yake yana batsewa da anjima yadan ja tsaki.

 

“Man what’s actually wrong with u tun dazu bakacemin komai ba what’s happening”

 

Jalal ya danja karamin tsaki kawai se yakasa gayawa jeje abinda yabata masa rai

 

“Just forget”

 

Shine abinda ya iya cewa ransa fal takaici

 

“Anyway since u decide not to share ur problem with me Dan ja kaya at least it will help u reduce ur temper”

 

Ya fada tare da tsiyaya masa Wayne a cup ya mikamasa ya Sa hannu ya dauka ya shanye ya kara masa yakuma shanyewa yana shirin kuma zuba masane

 

 

 

“DAN UWANA KAJI TSORON ALLAH DUK INDA ZAKAJE KAR KASHA GIYA KO KA AIKATA ABU MARA KYAU BA ABUNDA ZATA KARA MAKA SE BACIN RAI”

 

 

 

Kalaman Jawwad ne suke dawo masa se yaji haka nan jikinsa ya danyi sanyi.

 

Hannu yadagawa jeje yacemasa”enough ”

 

“Kana nufin ta isheka” cewar jeje”

 

“Yeah” yafada a takaice

 

“Am going ” Jalal yafada yana duba agogon hannunsa

 

“But man kaman akwai abunda yake damunka”

 

“Bakomai ni na wuce Gida”

 

Yafice daga gurin.

 

“Nana dakika baro gidansu jalal kinganshi kafin kifito”

 

“Aa nadai ji fitarsa a mota amma bamu hadu ba, akwai matsala ne”

 

“Aa babu koma”.

 

 

 

***********************************

 

 

 

Washegari da safe Jawwad ya shiga gidansu Jalal, seda ya shiga suka gaisa da mummyn jalal sannan ya fito ya nufi sashen Jalal,.

 

Kofar bedroom dinsa ya bude ya shiga yana kwance yanata bacci, agogo Jawwad ya kalla 9:30am amma Jalal be tashiba, girgiza kai yayi.

 

Ya taba Jalal ” bross wake up gari ya waye fa kalli rana tayi sosai ”

 

Dan motsawa yayi kaman baze tashi ba, sannan ya tashi zaune yayi mika yana Dan yatsina fuska

 

“Jalal anya kayi salla kuwa?”

 

“Banyi ba”

 

yafada hankalinsa kwance

 

“Haba Jalal sekace ba musulmi ba quarter to 10 fa amma bakayi sallar asuba ba why?”

 

“In kai zanyiwa innayi kar ka karba” yafada yana shirin mikewa

 

“No am sorry jekayi sallar kazo muyi breakfast”

 

 

 

Download>>> Jarababben Namiji Complete Hausa Novel Document

 

 

 

Yafita yakoma palour yana jiransa

 

Mikewa yayi yayo wanka tareda alwala yazo yayi salla itama dai sallar gata nan wata kilama badan Jawwad yazoba bazeyi ba,

 

(Sallar karfe 10am Jalal kai lefunka naka sunyi yawa Allah ya yafe mana)

 

Bayan ya idar ne yafito ya tarar da Jawad a palour yasamu guri ya zauna a kujerar datake fuskantar Jawad

 

Jawad yayi gyaran murya yace “Jalal wai me akayi maka jiyane meyafaru”

 

Yayi shiru kaman ba zece komai ba

 

“Wata yarinya CE jiya da daddare ina magana da mummy kawai ta fito ta tsoma baki hadace min Mara tarbiyya”

 

Dan zaro ido Jawwad yayi aransa yace ai batayi karyaba abokina watakila ma rashin mutuncin kakewa mahaifiyarka agaban mutane amma a fili seyace

 

“Wace yarinyar CE”

 

“Toni ina nasanta naga dai kaman na taba ganinta amma namanta inda nasanta,

 

Amma tabbas duk ranar dana ganta sena mata abinda bazata manta dani ba zan tabbatar mata bani da tarbiyya sha³ yarinya”

 

“Yi hakuri bros yanzu taso muje gidanmu muci abinci tunda yanzu dai baka ganta ba kamanta kacigaba da harkokinka kawai”

 

Ya janyo hannunsa suka fita daga gidan, zuwa gidan su

 

Bayan sun kammala cin abincin ne Jawwad yayi gyaran murya yace

 

“mutumina Jalilana fa tazo yau kwananta hudu a kano”

 

“Wace hakan?” Jalal yafada cikin ko in kula

 

” kaifa kafiye wulakanci kanwata fa danake gayamaka ta Kaduna”

 

Murmushi Jalal yayi “to shine kake wannan fara ar haka?”

 

“Bazaka ganeba Jalal irin yadda nakesonta, ba iya son yan uwantaka nake mata ba Jalal ina kaunarta ne sonake in kasance tare da ita har karshen rayuwata ganinta kawai yana Sani farinciki Ina kaunar Jalila matuka zan iya komai akan farin cikinta”

 

Kyakyacewa Jalal yayi da dariya tare da kunna sigarinsa ya fesa hayakin sama tare da wani kasaitaccen murmushi,

 

“Gaskiya ka faller over bross irin wannan bege haka ina mamakin me akeji a soyayya ni har yanzu banga macen dazata Sani wannan sambatun ba”

 

ya karashe maganar da wata irin,

 

dariya

 

“Jalal irinkune soyayya bata muku ta dadi wato dariyama nabaka ko hmm rai dai Allah yabamu rai da lafiya”

 

“Yaya Jawwad barka da Sadiya INA fatan katashi lafiya, Abba yace kazo yanason ganinka,”

 

Daram kirjin Jalal ya buga muryarta ce!!,

 

“Yar halak taki ambato barka da safiya kanwata,

 

Jalal gata fa Jalila kenan danake gaya maka kanwata juyowa yayi suka yi ido hudu da ita

 

Kallonta yayi tabbas itace, yarinyar da tazageshi agaban mahaifiyarasa jiya da daddare nan da nan annurin fuskarsa ya dauke yafara zaro idanu,

 

Cikinta ne ya duri ruwa tafara rarraba idanu zuciyartace take bugawa da karfi yau kam ta shiga uku

 

(Marar kunyar karya kin debo ruwan dafa kanki)

Add Comment

Click here to post a comment