Littafan Hausa Novels

Samu tsofaffin hausa novels wattpad

Samu tsofaffin hausa novels wattpad

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Samu tsofaffin hausa novels wattpad

Ga jerin sunayen wasu tsofaffin Hausa novels wadanda zaku iya karantawa.

 

BASED ON TRUE LIFE STORY*

 

Da sunan ALLAH Mai Rahama Mai jin Ƙai

GODIYA-: ta tabbata ga ALLAH da ya bani ikon fara rubuta littafin nan cikin,Allah ka bani ikon fadakarwa akan tafarji na gaskia, kada ka bani ikon rubuta É“atan ci,Allah ka bani ikon kamallawa lafiya Amin.

Tsofaffin Hausa Novels

GARGADI- A goji juya labarin ta ko wane tsiga domin mallakin marubuciya ne!!

SHARHI:-wanan labari dai ba Æ™irkirarren labari bane ya faru ne akan wani saurayi mai ji da kanshi,yana fariya da kyau’n da Allah ya mashi ta hakan yan’mata da dama suka fada cikin kogin sonshi ko wace dai burin ta HISHAM NATA NE basu samu nasara ba sai Yan mata biyu ZEENAT DA ALIYAH daya ta samu karbuwa sosai a wurin shi, yayin da yake mugun wulakanta dayar hakan bai saka ta saduda ba”KO WACECE CIKIN SU ZATA MALLAKI HISHAM?

Ku kasance tare dani domin jin yadda zata kaya tsakanin yan matan nan biyu…

 

🅿1-5

 

Motar Ce kirar land cruiser É“aka ta dannu hanci bakin gate É—in FEDERAL UNIVERSITY GOMBE [FUG]yana yin jan motar kadai ya isa ya fahimtar da kai ma mallakin motar natsatsen mutum ne,mai ji da kanshi!!

Tun daga shigowar shi ake bin motar da kallo wanda ya zama d’abi’ar daliban makarantar”musamman mata ko wacee burin ta ta mallaki wanan guy din wanda ya gaji da haduwa.!

Shi kuwa babu abunda ya tsana irin kallo!

STUDENT PARKING SPACE,,ya parker motar,ya jima sosai a ciki domin har takaici yake ji yadda zai fito ayita bin shi da kallo kamar wani baÆ™o…

Agogon dake daure a tsintsiyar hanun shi ya duba 9:30am gashi zuwa 10am yake da leactuers.

Samu tsofaffin hausa novels wattpad

A kasalance ya jawo brief case nashi mai dauke da laptop sai handouts nashi, ya bude ko far motar tare da zuro kafafun shi waje sai da yayi kamar secon biyu sanan ya fito…

Hadadden guy ne dogo sosai wanda za’a iya kira da jient,fari sol mai matsakaicin jiki, fuskar sa na dauke da dogowar hanci, manyan idanu ga saje daya aje wanda ya kara Æ™awata fuskar!

Sumar kanshi kwance take luf tasha gyara sai sheki take!!!

Sanye yake cikin farar yadi mai sulbi wanda ya amshi jikin shi[kasancewa ranar juma’a ce],taku yake cikin natsuwa a hankali kamar mai tausayin k’asa”wanda bai sanshi ba zai dauka yanga ne”wanda kuwa ba haka bane komi nashi cikin natsuwa yake yin shi, hatta magana idan yana yi sai kayi mamaki kamar mai ciwon baki idan ba saurara kayi da kyau ba baka jin mai yake fadi, tsafta kam va’a magana ko wata macen bara ta nuna masa tsafta ba,ga mugun tsandan tsiya”HISHAM B HASHIM KENAN!!!

Kallo kam ya shashi fiye da kullum, kasancewa yau sabbin dalibai suka zo interview…

Mata sai gaishe shi suke babu wacce ya amsawa domin yasan ba saboda Allah ake mashi hakam ba sai don kyau da kudi daya mallaka!!!

Tafiyar minti 30 ya kaishi faculty of medicine “duba da yanayin tafiyar shi”

Building ne mai girma sosai wanda a kalla zai dauki dalibai sama da dari biyu, ga furniture’s birjik, kowa na sha’anin gaban shi….

Wata budurwa dake zaune daga bangaren dama hankalin ta naga system nata da alama abu mai muhimmanci take yi..

Jin da tayi class din yayi tsit ya sa ta daga kai taga menene yasa yan ajin suka natsu, wanda ba’a fi minuta biyar ba da ajin ke hautsine kowa na sha’anin gaban shi…

Guy din data dade tana mafarkin mallaka ne tsaye gaban aji yana raba manyan idanun shi”da dukan alamu wurin zama yake zabe domin mugun tsanda ke gare shi…

Dalibai maza takaicin shi suke ji yadda ya fisu aji, ilimi, iya daukar wanka, kyau, natsuwa da dukiya uwa uba yadda yan mata ke rubibin shi a makarantar amma ko a jikin shi babu wacce yake sauraro tun suna UG1 har zuwa yau din shekaru Uku kenan…

Yan mata kuwa ko wace sai wani fari suke da idanu, suna yanga ko Allah zai sa burin su ya cika ya taya!!

ZEENAT dai ikon Allah take kallo ace namiji da shegen kyankyamin tsiya wurin zama ma kullum yana kashe minti biyar tsaye yana nema!!

Tun yan matan ajin na tsare mashi wuri bai sauraren su har suka gaji suka bari…

Layin da zeenat ke zaune ya biyo a natse yake tafiya har ya wuce ta zuwa last sit wanda kujero uku ke tsakanin su da ita ya ciro farar hand katchef ya goge sit din sosai kafin ya zauna yana yatsina fuska.

System nashi ya fitar tare da mai da hankali sosai akan shi.

Komi na hisham na matukar burgeta!!

ZEENAT alkasim kyakyawar budurwa ajin farko, mai natsuwa, ilimi,bata da hayaniya ko kadan, bara kace ga abokiyarta ko abokin taba cikin makarantar”duk da dalibai da mallamai na yi mata tayin soyayyar su babu wanda taba dama burin ta tayi abunda ya kawo ta shine karatu…

Asalin yar adamawa ce karatu ya kawo ta gombe wanda dama ta kamala NCE,DEGREE PROGRAM tazo yi ta samu nasarar shiga UG2 tare dasu HISHAM wanda tun ranar data fara ganin shi ALLAH ya daura mata ciwon sonshi matuka bata taba gayawa kowa ba haka bata taba attempting sanar da hisham din ba duba da yadda yan mata ke rubibin shi suna neman halaka kansu akan namijin da bai san suna yi ba!!!

Shekara guda kenan tana dakon soyayyar HISHAM…

 

Nanauyar ajiyar zuciya tayi tare da maida hankali ga system nata har leactuerer nasu wanda zai masu test yau ya shigo.

Sanar dasu yayi ya fasa yin writing test din sai oral and practical test da zai grouping nasu ya basu topic…

Class Captain yaba damar raba mutane gida goma[dama su dari da hamsin dabiu ne a faculty din, akwai masu karanta pure medicine mutum hamsin da biu wanda ya hada da hisham da zeenat,, sauran darin kuma pharmacy suke karantawa]

Koda aka kasa mutum hamsin gida goma, aka samu group biyar”saura HISHAM da zeenat

Leacturer yace su biyu sun yi kadan dayin practical dama ka’ida daga mutum biyar ne zuwa sama idan test za’ayi..

sai dai akwai research da zasu yi akan vesico vaginal fistula[watau ciwon yoyon fitsari] su gabatar[paper presentation] ranar monday.

Matan class din wani irin kishin zeenat suka ji ya taso masu dama sun tsane ta wai ta fiya girman kai,bata iya ma kowa magana sai yan ga!!!

HISHAM kan bai so haka ba domin anything dat has to do with mata bai son shi sabida yadda suke nuna maitar su kara ra a kanshi shi yasa yake jin wani tsana da kyamar su, musamman matan makarantan da masu da kamun kai….

ZEENAT a nata bangaren wani iri nake farin ciki ne ya ziyarceta ko ba komi wanan wani golden opportunity ne da zata yi amfani dashi wurin mallakar zuciyar hisham cikin sauki ba tare da mutuncin ta ya zube a saman idanun shi ba!!!

Leacturer na fita kowa ya kama yan group nasu suka fara tatauna yadda abun zai kasance banda HISHAM DA ZEENAT ko wane na jin kanshi yadda zai tunkari dan uwan shi da maganar.

Har aka tashi zeenat ta tatara inata inata ta kama hanyar fita…

Ganin haka HISHAM ma ya hada kayan shi yana zancen zuciya”lallai yarinyar nan yar rainin hankali ce a hada mu tare bata gode ba sai sai wani jin kanta take kamar wata sarauniya!

Nikam nace kanka ake ji[lol]

Samu tsofaffin hausa novels wattpad

Tana tsaye a cafeteria sai duba agogon wayarta take, tana jan tsaki akai akai domin tunda ta fito ta kira driver tace yana hanya amma har yanzu shiruuuu!!!

HISHAM ne ya wuce ta yana takun nan nashi na jan hankali a natse kamar wani basarake…

Dauke kai tayi domin babu abunda ta tsana kamar jira har yanzu driver shiru ga rana da akae kwalawa!!!

Motar shi ya bude ya fada amma bai wuce ba yana dane dane cikin wayar shi har babban aminin shi kuma Childhood friend nashi ya iso wurin…

MR B yane?

Fine imran!

Ya naga ranka kamar a bace?

Uhm mr Ahmad ne ya bamu wani reaserch on vesico vaginal fustula da worse thing ma da mace ya hada ni, macen ma mai girman kai ita a dole mai kyau!!!

Daria sosai imran ya sheke dashi hadda dafe ciki domin abubuwan hisham na mugun bashi mamaki kai ba’a ce maka mai yanga ba kai ke kirar wata mai yan ga!!!

Beside ma ai mace ce ko tayi yanga bata fadi ba,, kuma na tabbatar tana da kyawun ne tunda har kayi admitting…

Bana son shakiyanci imran haka naji ana fadi cikn class wai wai wai kyawunta ke rudan ta har take yanga!!!

uhm yanzu sai yaya?

Mtswww she’s on her own babu ruwa na,zan fara research dina yau,ita ta sani idan tayi failing girman kanta ya ja mata…

Kada kace haka MR B,ita mace ce kai ya kamata ka fara mata magana idan ta nuna girman kai ka rabu da ita!!!

Over my dead body imran mata nawa ke neman irin wanan golden opportunity din?

mata nawa ke kawo mun kansu?

Mata nawa ke fada a kai na?

Mata nawa ke sacrificing komi nasu saboda ni?

Uncountable MR B

Amma wanan assure u dat she’s different from them.

Imran mu bar wanan zancen kawai gida zani yau friday!

Dama baka son gaskia, ina da Leacturer’s around 2pm sai mun hadu dai anjima..

Ok kawai yace tare da jan motar shi har lokacin tana tsaye wurin!!

Wuce ta yayi a guje wanda ba dabi’ar shi bace gudu da mota.

Ba’a dau wani lokaci mai tsayi ba driver mal. sani ya iso yana bata hakuri sosai anty ta bashi sako ya fara biyawa kafin ya iso..

Dole ta hakuri ki a banza dai mal. sani ya haife ta,, shiga tayi yaga motar…

 

*MASY KARATU YA ZATA KASANCE TSAKANIN HISHAM DA ZEENAT?*

NIKAM NACE AKWAI JAN AIKI GABAN ZEENAT

 

 

 

*Y’AR GARUWA*

HAWWA M. U[$maHer]

*littafi mai kunshe da dombin fadakarwa, hakika na jima ban karanta littafi mai cike da darusa irin Y’AR GARUWA BA,na jinjina maki c’weety real smasher Allah ya baki ladar fadakarwa, ya kara basira da daukaka*

_congratulations once again my c’weety smasher_

 

🅿10-15

Sir nice zan gabatar da presentation din,shi tambayoyi zai amsa!

As u plan,the more point u present ,the more marks u willl score…

HISHAM wani nanauyar ajiyar zuciya ya sauke”thank goodness ta fanshe shi da yau sai yasha kunya,Allah ma yasa ta iya turanci da zata yi presenting abun kwarai….

Cikin shiryeyen turancin ta ta fara gabatar da kanta da topic din da zata tatauna akai.

Vesico vaginal fustula-:a gagauce yana nufin yoyon fitsari ko wane lokaci a Sanadiyar wani huduwa ko rami a cikin gaban mace wanda ke aukuwa a sanadin doguwar nakuda[prolonged labour for more than 24hours]wanda ya wuce awa ashirin da hudu ko kuma wurin diban gurya[gishiri cord] yana faruwa ne da mata zalla.

Kamar yadda nayi bayani mata zallah yace faruwa dasu, daga yan mata har matan aure, wasu ma tun lokacin haihuwa irin kaciyar nan da ake wa yara mata[diban gurya],wani lokaci kuma ana samu wurin tiyata[caserial section]ko ƙari da ake ma mace wurin haihuwa[episotomy] idan anyi temparing Da wasu organ na gabanta..

ALAMOMIN SHI:-ya danganta da girman huduwar ko ramin dake gaban mace”idan huduwar bai da zurfi sosai fitsari zai rinka É—igowa ne har ya jiÆ™e maki zani,idan kuma huduwar da zurfi sosai zai rinka zuba É“e da yawa idan kina kwance,zaune,tsaye,da safe ,da rana ko da dare babu control…

Aiki[surgery] shine kawai babban abunda ke maganin wanan lalura”sai dai akwai yanayi da ake dubawa nada ba sai anyi ma mace aiki ba idan anga wurin bai huje ba tsaguwa ce kawai sai a saka mata ruba[catheter]har sai yayi tsawon sati uku a gaban mace kafin a cire, idan an dace shike nan, idan ba’a dace ba sai anyi mata aiki[surgery] ta gabanta domin É—unke huduwar nan ko ramin.

Akwai asibiti na musamman wanda aka bude domin masu lalurar watau[vesico vaginal fistula center] kafin ai aikin ana umurtan mace data yawai ta shan ruwa masu tsafta akal litta hudu a rana,”fa’idar yin gaka zai kashe zarnin fitsarin, idan ma tsaguwa ce zai rufe da kanshi ba tare da saka ruba ko yi mata aiki ba.

Sanan bayan anyi aiki mace ta rinka cin ya’yan itace,ganyayaki da ruwa[fruits,vegetables and alot of water].

Anan na kawo karshen jawabi na idan da mai tambaya ko neman karin bayani kofa a bude take dan uwana zai amsa maku…

Tafi ake raf raf raf raf”domin ta burge kowa cikin ajin musamman maza da suke ganin kasawan HISHAM kuma girman kai ya hana shi tuntubar Zeenat!!!

HISHAM kam sake baki yayi domin ko muryan Zeenat kadai abun burgewa ce, bare turancin ta wanda yake a saukake, a tsare tana fidda ko wane harafi yadda ya kamata gaskia ya yaba ma kwazon ta!! [lol]

Bayan an tsagaita ne”leacturer ya yabawa zeenat sosai akan namijin kokari da tayi wurin gabatar da wanan jawabi tiryan tirya duk da dai yasan ba fanin su bane, [na ganiology’s ne]amma a matsayin ka na mai karatun lafia ya kamata ka samu haske koda kadan ne akan ko wane fani…

Aka bada dama ayi tambaya da neman karin haske”nan mata suka fara jero ma HISHAM tambayoyi kamar haka..

Wai a ina suak samo wanan jawabi[watau reference]?

Tare suka yi research din?

Sun ziyarci asibitin masu lalurar ne tare da zeenat?

ya akayi a matsayin shi na namiji ya bari ta zama speaker?

Kai sai da leacturer’din ya tsawata masu domin wanan tambayoyi basu shafi abunda akayi ba!!

HISHAM ne dai yasan tsabar kishi ne ke cin zukatan su yau an ganshi da mace suna presebtation tare!

Samu tsofaffin hausa novels wattpad
Kuma ya godewa Allah da aka dakatar dasu domin bashi da amsar bayar wa”bai san inda ta samu wanan jawabi ba kuma ba zai iya kunyata kanshi ya tambaye ta ba!!!

Tambaya ta fannin maza kuwa shine…

Shin mace mai wanan lalura idan akayi aiki ana da tabbacin zata warke gaba daya?

Tana iya sake daukar ciki ta haihu da kanta ko dai anyi aiki kuma[CS]?

Bayan ta warke tana iya komawa mijin ta?

 

HISHAM ne yace bai da masani ya akan hakan domin shi ba mace bace babu mai lalurar cikin ahlin su,sanan bai taba cin karo da kowa wanda ke dayke da lalurar ba!!!

Aji ya kaure da hayaniya ana fadin tabbas ya tabata zeenat kadai tayi research din nan girman kai da jan aji na HISHAM ne ya hana shi neman ta suyi tare”duk da leacturer’n ma ya fahimci hakan tsawata ma yan ajin yayi!!!

Zeenat tace a bata dama ta amsa tambayar”aka bata..

Tabbas idan anyi aikin ana iya dace wa mace ta warke sumul amma idan tabi ka’idoji kamar haka-:

Dama udan anyi mata aikin za’a saka mata ruba[catether]ta nan fitsarin zai rinka bi, bayan sun sati uku ko hudu za’a cire rubar dai dai aikin ya warke za’a sallame ta lokacin za’a bata shawar wari akan ta rinka yawan shan ruwa masu tafta, cin y’ay’an itace da ganyayaki, ta nesanci mijinta[idan tana da aure]har bayan wata uku,idan ta kiyaye wanan dokoki dai dai zata koma gidan mijinta za tayi tsarin iyali[family planning ]wanda sai da yaddan mijinta, idan kwayoyi take so, alura ko roba har na yan watani yadda wurin zai kara cikowa kuma ya huta da kyau sanan idan ta ciki wana sharuda,bayan ta samu ciki asibitin da akayi mata aiki zata rinka zuwa awo, idan kuma tana da nisa da wurin sai tayi agarin da take idan ciki ya shiga wata na bakwai dole taje tayi hoti[scarnning]ta kawo asibitun da akayi mata aiki suga yanayin da abunda je cikin ta yake ciki, so dai dai ciki ya shiga wata na takwas zata dawo asibitin a rika kula da ita har sai haihuwa yazo ayi mata aiki a cire abunda ke cikinta”IDAN HAR TA SAKE TA HAIHU DA KANTA TA GABANTA AIKIN CAN NA IYA LALACEWA DOMIN TA DUNKIN ZAI WARWARE”kunga yoyin fitsari zai dawo Sai an sake yin wani aiki..

Ina fata kun gamsu!

100% gaskia muna jinjina maki da wanan baiwa da Allah ya baki!

Murmushi kawai tayi domin bata son yawan hayani sai ya kama dole.

Shin kuma goga HISHAM sarkin jin kai ga shegen zuciya kamar koturu nan da nan yayi fushi ai hade gabs da yamma yayi!!!

leacturer ya nemi da suyi submitting presentation din domin ya samu daman dubawa yayi scoring nasu”kuma kowa zai submitting nashi ne!!

Samu tsofaffin hausa novels wattpad
Suna hada ido da HISHAM taji wani mugun tausayin shi ya kamata”sir dama akwai masu son copy shine muke so muyi masu kafin muyi submitting!!

Yace babu ruwan shi ya basu nan da jibi domin shine assesment nasu idan basu kawo ba absent zai saka masu kuma bara su samu nasarar tsalake jarabawar shiba wanda ya zama dole sai kaci kafin ka shiga zangzangona karshe UG4 SO ya basu nan da kwana biyu su kawo individual!!

Masu practical kuma ya basu the whole week su shiga lab su kamala next week zai fara dasu kafin a fara exams…

Samu tsofaffin hausa novels wattpad

Yana fita class ya kaure da hayaniya mata na matukar jin haushi da kishin zeenat, maza kuma na yaba mata suna jin matukar farin ciki yadda HISHAM yasha kunya yau!!

Ko zama bai ba ya fita a class din..

Ita kam sit dinta ta koma tana hada kayanta domin zuwa gida kasancewa sunyi covering duka sylabols din na wanan zango jarabawa kawai suke jira dama wanan lecturan ne kawai bai masu test ba”don haka bata tunanin zata shigo gobe sai bayan kwana biyu domin tayi submitting presentation din, Allah yasan saboda hisham tayi haka idan yazo ya amsa yayi copying ruwan shi, idan bai zo ba shike nan tayi cikin shi…

Gidan Uncle Hausa Novels Complete

Yana fita ya koma cikin mota zuciyar shi na tafasa kamar wuta,marfin swam watar ya bale tare da bulbulewa a bakin shi, ya kwantar da sit tare da jingina kanshi abubuwan da suka faru tiryan tiryan suna dawo mashi yana kara jin tsanar zeenat domin a ganin shi da gangan tayi mashi hakan!!

Yana kwance cikin motar ya hangota tana tafiya cikin natsuwa da alama gida zata”wani uban tsaki yaja tare da dauke kai!

Ita kam bata ma san yana wurin ba sabida bashi da takamamen mota kullum da kalar da yake zuwa da ita..

Koda ta isa parking space driver nasu anty ya iso suka gaisa ta shige motar sai gida!!!

 

Bayan ta yi wanka da cin abincin sallah ta labarta ma anty asiya duka yanda sukayi da HISHAM ne a makaranta yau..

 

Anty asiya tace lalai kina da jan aiki a gabanki da dukan alamu guy din yana da É—anyen kai,kuma akwai zuciya da saurin fushi ni da zakibi ta nawa ki aje soyayar shi gefe tunda kina da masoya birjiÆ™ a gari!!

Anty adu’a zaki taya ni dashi nesa tazo kuwa in har baya son ya maimaita wanan zango nasan dole ya neme ni ya amshi copy na presentation É—in nan!

Zeenat!akace yaro yaro ne yadda uban shi yayi suna a nigeria kina ganin akwai wanda ya isa ya sashi maimaita wanan zango?

Allah shi ya isa ya saka shi mainaitawa,idan suna taÆ™ama da duniya,mulki ko suna Allah shine sarkin sarakuna,shi ne mai bada dukiya kuma shine ke yadda yaso a lokacin da yaso kuma a inda yaso abu ya tabbata…

Kin gama magana zeeta Allah ya mana jagira amin.

HISHAMna zuwa gida part na iyayen shi ya shiga da’a dadfy na gari, bayan sun gaisa yake fada mashi wai wani lecturer yace dole sai ya kawo copy na presentation vanda bama jin field nasu ba’e…
Dady yace kayi hakuri ka bayar kawai tunda ya bukaci haka mai nema ai baya fushi!

Mumy ta saka baki”aikin kenan alhaji kullum ina masa tuni akan ya rage saurin fushi shi namijine aure zai yi wace mace zata yadda ta zauna dashi sai da wana hali?

Samu tsofaffin hausa novels wattpad
Jin yayi ranshi ya k’ara baci da aka ambaci aure barin part din yayi zuwa nashi ya shiga wanka, yana fitowa yajia sallamar imran!

Mr B ya presentation?

Ba’baa bari kawai ai yau nasha kunya”da yake baya boye ma imran komi nan ya kwashe labari ya fada mashi…

Dariya sosai imran keyi hadda hawaye domin yasan za’ayi haka kuma yaji dadin hakan sosai”yaso ganin HISHAM lojacin da abun ya faru dama bai iya shiga damuwa ba sai ya bi ya rude sosai..

Tsaki HISHAM yayi!

Kai fa matsalar ka kenan da mutum ya kawo maka matsalar shi yana neman mafita sai ka gama dariyar iskanci sanan ka bada amsa!!!

Mr B abun ne da ban dariya kuma da ban tausayi yanzu dai solution guda ne ka nemi yarinyar nan ka amshi copy idan ba haka ba za kayi wa kanka wallahi da Girl even try ma, idan da nine ita sai na tabbatar da nayi disgracing naka to do bastard level!!

Mtswwww waya haife ta wallahi wargi ma wuri ya samu…

 

Ai tayi maka halarci ga research tayi, tayi presentation and sanan babu tayi answering me Questions…

Am serious mu nemi address nata kawai gobe muje ka amsa!

U are a fool imran!

Tunda nake da kai ka taba ganin kafafuna a kofar gidan su wata yarinya kai ko number waya ka taba gani!

Baza a fara akanta ba!

Uhm HISHAM ina guje maka kada kyawunka ya rudeka wata rana ka rasa macen aure kana nema suna gudun ka!!!

Amma kace wani abu bara kaji macen da zan aura ko haihuwarta ba’ayi ba..

Shike nan muna na da kai sai kace na fadi ai!

Suka ci gaba da wani hirar sallah ya fitar dasu daga na ta suka tafi gidan su imran!

Dare nayi HISHAM ne ya kasa bace domin mafita kawai yake nema dole sai ya kunsa ma yariyar nan takaicin da har ta mutu bara ta mance dashi ba…

 

Can yayi wani irin tsadadden murmushi;finally

Waya ya daga can aka dauka!

Hello imran inaso ka nema mana address da contact me na yarinyar nan gobe muje gidan su”da sauri ya kashe wayar yasan halin imran yanzu zai aza mai daria…

 

Da saƙe saƙe iri iri yayi bacci!

Wace gari da misalin karfe goma sha biyu imran ya shigo gidan nan yake sanar dashi ai state low-cost take house number 6..

Yace ya gode kawai!

Babu yaÉ—da imran bai ba ya bugi cikin hisham yasan plan nashi a kanta amma Æ™ememe yaÆ™i sanar dashi…

Da dare kwalliya sosai hisham yayi ya É—au makulin mota sai state low-cost!

Add Comment

Click here to post a comment