Littafan Hausa Novels

Ba Jinina ba ce Hausa Novel Complete

Ba Jinina ba ce Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Ba Jinina ba ce Hausa Novel Complete

Page 1

 

“Ke Maryam naji wata ’yar matashiyar budurwa tana kira cikin muryar rad’a” da sauri naga yarinyar da aka kira da Maryam ta waigo fatabarakallahu asanulkalik’in shine abinda na fad’a lokacin da idanuna suka arba da zankad’ed’iyar kuma matashiyar budurwar aka kira da MARYAM wani shegen murmushi tasaki tace “ba saikin fad’aba Halima nasan abinda yasa kike wannan kiran sai kace makauniya’ a d’an dame Halima tace “kinsan halin wannan bros d’in nakifa baida mutunci yanzun saiya b’ata mana shiri”

 

 

 

 

Wani d’an iskan kallo Maryam ta sakarwa Halima tace “ke ya dama ni kam banga wanda ya isa hanani abinda naga damar yiba uwata da ubana basu ta kuraniba sai wani can daban, kinga malama aje acigaba da shirya wajen ayi yadda zamufita kunyar abokanmu”

 

 

Karanta Littafin Fitar Rabo

 

kai kawai Halima ta jinjina batare da ta ce komai ba domin tasan halin Maryam da shegen taurin kai idan ta kafe akan abu babu wanda ya isa ya juyata sai YAYA MUHAMMAD daya daneta ya shanye a taurin kai gashi bala e en sojan dana k’asansa suke masifar tsoronsa gashi miskili ne shi na gaban kwantace inba ta k’ureba zai wuya kajishi yana yawan magana hatta abokansa da abokan aikinsa sun saba da halinsa sau tari da ido yake basu umarnin abinda zasuyi kuma su aikata domin sun riga sun saba da halinsa.

 

Al-amarin Zuci Hausa Novel Complete

 

 

Ta juya kenan zata gidan su anwar wani mate d’inta ne yayansu yana d’inki to duk kayan da zata buk’ata shi tabama d’inkinsu, saiga Nasser ya k’araso da gudu yace “Adda Maryam kizo inji Ammyna” wata shegiyar harara ta galla masa tace “kaje kace tazo tajani bazan zoba inkuma zata iya tazo tajani”

 

 

 

Shima hararan ya maida mata dan babu ragayya a tsakaninsu ko kad’an yace “kada Allah yasa kizo d’in banza wacce batasan darajan nagaba da itaba”

 

 

 

Cikin b’acin rai tayi Kansa tace kai dan uwarka ni kake zagi?”

“Anzage kin ni uwata sa ar wasanki ce da zaki zauna kina aikena da wannan banzayen zantukan?”

 

 

 

Kansa tayi da nufin mammake shi ya d’ebi sauri tabishi tana cigaba da gaya masa bak’ak’en maganganu akan mahaifiyar sa, shi kuma koda wasa bai saurara mata ba duk zagin data masa Sai ya maida mata martani acewar sa tunda ita Allah baiyota da ruwan mutunci ba baiga dalilin da zaisa ya kyaleta ba.

 

 

 

 

Yana bud’e get ya hango bros wani shu’umin mirmushi ya saki sannan ya tak’ark’are ya zunduma wani uban ihu har Sai da bros ya to she kunnensa ya juyo afirgice dan jin wannan ihun tayi zaton kunama ne ya d’alleshi ganin shi yai yana nufoshi yana cigaba da kukansa wata uwar harara ya maka masa wadda tasa nan take ya had’iye kukan ya k’araso kusa dashi, da ido yake tambayar shi abinda akayi masa yace

 

 

 

 

 

“Ba Adda Maryam bane kawai dan Ammyna tace na kirata shine ta hau zaginmu nida Ammeyn danna ce badai Ammeyna ba shine ta mareni kuma ta biyoni wai zataje gaban uwar tawa ta takamin kai taga inda abinda ta isa tayi”

 

 

 

 

Kafin yace wani abu saiga maryam d’in ta shigo a fusace kuma har lokacin bata bar fad’ar bak’ak’en maganganun da take fad’awa Nassar ba, abinda ya dad’a b’ata ran bros kenan yayi mata wani mugun kallo wanda sam bata kula daahi ba Sai da tashigo tsakiyar gidan itama had’e rai tayi ta bala in d’auke kai tai kamar batasan da zaman su awajen ba.

 

 

 

.

“Ke zo nan” ya fad’a cikin dakakkiyar muryarshi da babu alamun wasa aciki had’e rai tayi tare da kuma galla masa harara sannan ta saki tsaki tayi cikin gidan abinda yai masifar k’ona masa rai kenan ya kama hannun Nassar suka nufeta ai tana ganin ya nufota ta taka aguje tayi ciki’ mamanta da Ammey suna zaune afalon suna d’an tab’a hirar su dake babu laifi basu cika fad’a da junansu ba saboda hak’urin haj. Amina da kuma tsantsar biyayyar da take wa abokiyar zamanta haj. Lubabatu hakanne yasa ba ajin kansu indai ba Maryam aka tab’owa haj. Luba ba yanzun zakaji ruwan masifar ta da bala I.

 

 

 

 

 

Suna cikin hirar Maryam ta shigo da gudu ta shige bayan mama cikin shagwab’ar daya zame mata jiki tace “mama kinganshi ko zai dakeni ”

 

 

 

“Wa kenan?” mama ta tambaya tana duban hanya ai tana ganin wanda ya shigo tai masifar had’e rai dan a duniya idan da wanda taiwa masifaffiyar tsana to Muhammad ne dan ya riga da ya hana ta sakat ya shige mata hanci da k’udundune tarasa yadda zata fyato matsiyaci ta huta.

 

 

 

 

 

Sosai tai masifar had’rai tace “dan ubansa idan ya isa yazo ya tab’aki tsabar masifa da jaraba abi a hana yarinya sakat to wallahi ni na gaji bari alhajin ya dawo dole yayi mana tsakani dakai dan ‘yata na baiwa bace”

 

 

 

 

Kafin takai ga dire jarabar da take Muhammad ya shammace ta ya fisgo Maryam ya d’auketa da wani gigi yaccen mari wanda yasa nan take ta shid’e numfashinta ya tafi yajin aikin hucin gadi kafin tasaki wata azababiyar k’ara, karar ce ta ankarar da mama ai har mayen ya damk’eta sunan da tasaka masa kenan dan duk inda takai da bala I matuk’ar yayi niyyar mata hukunci babu wanda ya isa ya hanashi sai Baffa wato mahaifinsu

 

 

 

 

Ranta yai masifar b’aci cikin bak’in ciki tace “matukar ka kuma dukanta Allah ya isa ban yafe makaba shege mugu azzalumi ta Allah batakaba munafiki wallahi bari alhaji ya dawo sai yayi mana tsakani dakai tunda kai Allah yayi ka da zuciyar kafurai.

 

 

 

 

Duk zagi da munanan kalaman da take binsa dashi bai saurareta ba saida ya tabbatar ta turarawa Maryam jikinta sannan ya wulla mata ita jikinta ya juya ya fice yana huci yayin da mama taci gaba da zagi tana la antarsa.

 

 

 

 

Rungumo maryam tayi wacce take rusar kuka na fitar hankali domin ba k’aramin dakuwa tayiba jikinta kuwa banda azaba babu abinda yake mata abinka da farin mutum fatar nan tayi jajur tayi rud’u rud’u, suna had’a ido na Nassar tayi mata gwalo ta hayagagar ta tace

 

 

 

” wannan munafikar uwar taka ita kayima gwalo dan uwarka shege mai kama da d’iyan aljanu🤣🤣🤣🤣dole na dara domin duk wanda yaga Maryam yaga Abdul Nassar yaga JINI

 

 

 

 

 

Tana dire zagin bros yana dad’a danno kai daman a bakin k’ofa yatsaya domin ya San da cewa dama bazatayi shiru ba dole zata fad’i wani abun.

 

 

 

 

 

 

Comments and shere

 

 

 

 

 

Maman isi ce

1 Comment

Click here to post a comment