Littafan Hausa Novels

Adheenah Hausa Novel Complete

Adheenah Hausa Novel Complete

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

ADHEENAH*

 

 

*(labari mai cike da tausayi,zalinci,soyayya,cin Amana)*

 

Story and writing by

*Beentu*

 

*Dukan yabo da godiya sun tabbata ga Allah madaukakin sarki.*

 

*Wannan Labari ‘kir’kiraran labari ne banyi shi don cin zarafin wani ba ko tozarci,Ina rokan duk wanda yaga ba dai dai ya yi hakuri saboda Dan Adam ajizi ne*

 

 

*Sadaukarwa ga yar uwata Nanah Hafsat Allah ya jikan ki da rahma ya gafarta miki,ina rokan karanta mata suratul Iklas da dukan yan uwan mu da al’umar Musulmi gaba daya Allah ya gafarta muku yasa kuna cikin dausayin Aljanah,mu kuma ka sanya mucika da kalmar shahada kasa muyi karshe mai kyau.*

 

*Wannan page din naku ne Aisha marubuciyar(Sai na aure Marubuci),Allah kara basirah ya kawu miji na gari, tare da Yayata Yar uwa rabin jiki Fatimah Adam,pagin farko naku ne wannan ina muku son so fisabillahi*

Hayar Mace Hausa Novel Complete

Note: Novel din Da na gida(akan cuci gida),ya na nan tafe insha Allahu zanyi kokarin had’a typing biyu sai da banyi alkwarin yin shi kullum ba.

 

*Cigiya:Yayata(Ummu farhan,stylish)ina cigiyar ki ido rufe,Don Allah wanda ya ganu min ita tana kungiyar(First class),Ina kewarki yar uwata*

 

 

1/2

 

Kife kaina na yi,tun daga lokacin da Mijina Mallam Isuhu ya fara jawabi gaba d’aya na ji duk wata gaba dake motsi cikin jikina ta tsaya cak.

 

kowace jijiya da zata taimakawa gabobina gurin bata jini ita din atsaye sake.Yawun bakina ya k’afe,numfashina na kai kawu.

 

Kafe Isuhu nayi da idanuna ina kallonshi babu ko k’iftawa,ga zuciyata dake masifar yi min zafi kamar zata fasa kirjina ta fito don bugawa.

 

“Innalillahi wa nina ilaihi raji’un”.

 

Karanta Luttafin Jiddatul Khair

Dogon sallatin dana ni gaba daya cikin masallacin ya dauka ne ya dawu dani da ga mutuwar wucin gadin dana yi.

 

“Adheenah! Kin ji irrin zargin da mijin ki ke miki?

Shin kina da hujjar kare kanki?

 

To!Mai zance,ban aikata ba,shari yamin ko kuma da gaske ne zargin da ake yi a kaina haka ne?.

 

Tambayoyin dana shiga yiwa kaina da zuciyata kenan.

 

Muryar mahaifiyata na jiyu tana kiran sunana kamar da ga can nesa da ni nake iya ji yu sautin muryarta cike da rauni.

 

Bude idona na yi cike da nauyi ina jin duk ga’bobina sun yi min nauyi da alama na kwan biyu akwance.

“Allhmdllh ta farka Babansu”

cewar Ummata.

 

“sannu uwata,bari na kira likintan ya buba ki”cewar Babana.

 

Sake lumshi idona nayi don ya yi min nauyi sosai,gaba daya abin da ya faru tsakanina da Mallam Isuhu ne ya shiga zuwa min cikin kwakwalwata ,ban san sa’ad da na fashe da kuka ba.

 

Shiguwar Dr ne ya sa ni share hawayen dake bin kuncina”Allhmdllh komai ya na tafiya daidai sai dai a kula da yanayin ta saboda abin da ke cikin ta”

 

”mun gode likita insha Allah zamu kiyaye”cewar Babana.

 

“Adheenah! Ki kwantar da hankalin ki komai yayi farko maganin shi Allah, komai zai wuce ya zama kamar ba’ayi ba Insha Allah,ki manta da komai kodan abin da ke cikin ki”cewar Umma ta.

 

“Umma Allah ya sani ban taba aikata zina ba,Allah ne shaidata”.

 

“Na yarda dake diyata”.

 

Kwana na uku ina jiya kafin jikina ya warware.

Sake neman mu akayi akaru na biyar daga fadar mai gari,cike da jimami da koma tsoro muka nufi gurin da Dangina.

 

Mallam Isuhu zaune da nashi muk’araban sa agefe.

 

Liman ne ya bude taro da adu’ah kafin ya daura da cewa”Allahamdullilah!Kamar yadda muka yi zama da akaru da hudu baya yanzu zamu daura,sanan insha Allah wannan shine karo da karshe da zamu yi zama akam Adeenah tare da mijinta Mallam Isuhu,inda yake zargin cikin dake jikinta ba nashi bane”.

 

Numfasawa yayi”yanzu kam jayaya tashiga tsakanin su mai karfi zamu tsalaka ga mataki na gaba wato zasu rantsuwa atsakanin su”.

 

Ya fad’a yana duban duk wanda ke gurin da kallo.

Sake ‘kasa da kaina nayi ina jin gaba daya kamar na tozarta.

 

Maganar Mallam Liman dana ji ne ta dawu dani daga duniyar tunanin dana fad’a”kamar yadda yazo cikin Hadisin Manzon Allah(S A W),idan har aka samu jayaya tsakanin ma’aurata haka akan d’a ko ciki zasu yi rantsuwa”.

 

Gaba daya shiru gurin yayi kowa da abin da yake sa’kawa.

 

“Don haka! Zamu zarta kamar yadda ya zo cikin alk’ur’ani cikin suratul ali imran,aya da sitin da d’aya(61).

Inda Allah madaukakin sarki ke cewa Annabi Muhammad(S A W).

 

“To,wanda yayi musu da kai a kan cikinsa a bayan abin da ya zo maka daga illimi,to kace”Ko zo mu kiraue yayanmu da yayanku da matanmu da matanku,da kawunanku da kawunanmu,sa’anan kuma mu ‘kankantar da kai kuma mu sanya La”anar(LI’ANI)Allah akan ma’karyaci”.

 

gaba daya gurin yasake daukan shiru tun sa’ad da Mallam Liman ya fara karantk Ayar Allah har zuwa karshen shi.

 

“To Allhamdullilah kamar yadda ya zo cikin ayar Allah ga danginku nan duk kusa,amma kafin kuyi rantsuwar zan fara da yar nisiha tsakanin ko”

 

“Mallam Isuhu!Kaji tsoran Allah kasan duk abin da zakayi akwai Allah kuma shi Allah ba azalumin bawa bane.Ina so kaji tsoransa da ranar karshe yadda zamu tsaya da kafafunmu rana da dukan mu tana tafasa kwakwalwarmu hata fatar jikinmu tana zagwanyewa,shi baka tsoran kwanciyar kabari.Kwanciya ce da baka san iya tsawan shekarun dazaka dauka ba shin akwai wani tanadi dakayiwa hakan.Yaya arziki ne wanda ba kowa Allah ka bawa ba,Mallam Isuhu kana gani wani ga dukiyar kamar zata kashe shi amma Allah ba azurtashi da d’a,idan har zai bada duka dukiyar don yasamu haihuwa zai bayar amma babu hali,shin kasan wani irrin baiwa Allah ya bawa abin dake cikin yarinyar nan halan baban mallami ne ko wani mai baiwar da zai amfane al’umah da ita.

 

Shin ka tabatar da zargin da ka ke akan ita matar taka kuwa,kasan hukunci ‘kazafi,musanman kazafin zina,Ka tsoraci Allah da ranar karshe kada kasanya ‘Danka/Yarka cikin jirin yayan da asan matsayin daza’a kira su dashi ba Mallam Isuhu”.

 

Babu wanda jikinsa baiyi sanyi ba”Idan har ka aikata haka akwai tarin nadama da kuma da na sani aciki domin kuwa Manzon Allah(S A W)yana cewa”duk wanda rantsuwa irrin ta LI’ANI ta shiga tsakanin sa da matarsa,wannan ‘Dan ko cikin da ake jayayya akai ya haramta ga uban,nasabar sa zata koma ga mahaifiyarsa ne,sanan kuma koda su k’adai suka rage matsayin mace da namiji to aure ya haramta agaresu har abada”.

 

“Mallam Isuhu bazan gaji da nusar da kai da ka ji tsoran Allah da azabar sa da kuma irrin girman rantsuwa musanman irrin wace kake kokarin yi ka fadi gaskiya domin fitar da kanka da kuma danka daga bakin mutane”.

 

Kuka nakeyi sosai ina lisafa yadda rayuwa take tafiya min”Allah gani gareka Allah ka fitar dani,Rabbi ka wanke min wannan bakin fenti ya Allah”abin da zuciyata ke fadamin kenan.

 

Kuka Mallam Isuhu ya fashe dashi”Allah gafarta Mallam kamar yadda nake fada acan baya cikin jikin Adheenah ba nawa bane ban kuma san dashi ba”.

 

Gyad’a kai Mallam Liman yayi kafin ya kai dubansa gun danake zaune”Adheenah”ya kira suna na da kaukausar murya”Adheenah!Ki ji tsoran Allah ki fadi gaskiya lamarin nam kada kiyi duba da kunyar duniya ki lura da kunyar lahira,inda zaki tozali da Allah ranar da babu wanda zai kwace ki baki da gata ko galihu sai abin da kika aikata.

 

Ki tuna ba shi hakki komin ‘kank’antarsa ba abu bane mai sauki.Idan ki ka fadi ki ka mutu da hakkin wani kanki mai zaki cewa Allah.

 

Annabi Muhammad(S A W)yana cewa”lallai babu wani bawa da ya kai Allah kishi,inda zai ga bawansa ko baiwarsa suna.Ya ku al’umar Annabi Muhammad(S A W)da kunsan abin dana sani da kunyi dariya kad’an da kuma kunyi kuka sosai”.

 

“Shin bakiyi tunanin wannan ranar ba Adheenah?.

 

Kiji tsoran Allah kada ki sanya Danki/Yarki cikin jerin yayan da al’umah zata kyamacesu,kijk tsoran Allah da azabarsa ki fad’i gaskiya shin cikin jikin ki na waye?

Waye ubansa?.

 

Ko ina ajikina rawa yakeyi muryata har bata fita don tsanin kukan danayi”Wallahi Mallam cikin jikina ba na kowa bane da Mallam Isuhu ne”.

 

Shiru gaba ki daya gurin ya dauka”To Allhamdullilah! Yanzu kam rantsuwa zata shiga tsakanin ku.

 

*Yadda zaku yi comment hakan zai nuna min irrin kaunar da kuke min da kuma yadda labarin ya karbu agurin ko*

 

*Idan har yayi zamu cigaba*

 

Add Comment

Click here to post a comment