YADDA ZAKU RABU DA GISHIRIN FUSKA
Yadda za a rabu da gishirin fuska:
Shin mene ne gishirin fuska? Gishirin fuska dai ana kiransa da suna white heads a Turance.
Abubuwan da ke kawo shi su ne, yawan gumi a fuska ko maikon fuska. Idan muka yi gumi, fuskarmu takan fitar da maiko.
Idan ba mu damu mun wanke fuskarmu a lokacin da ta yi gumi ba to hakan yakan taru ne sai ya zama gishirin fuska.
Yakan fari a kan fuska. Idan muka yi kokarin cire gishirin fuskar da hannu, hakan kan janyo kurajen fuska.
Saboda haka na kawo mana hanyoyi da dama da za mu bi don rabuwa da gishirin fuska.
Karanta Yadda Zaki Gyara Nonon Ki A Sati Daya
Idan muna son rabuwa da irin wadannan kurajen fuska da gishirin fuska, amfani da hadin gargajiya irin namu na saurin warkar da cututtukan fata. Za mu iya amfani da daya daga cikin wadanda na lissafo don magance gishirin fuska.
A rika wanke fuska akalla sau biyu a rana da ruwan dumi da sabulu. Yin haka na rage da fesowar gishirin fuska. Kuma yakan hana su fitowa.
A zuba tafasasshen ruwa a kwano ko roba. Sannan mu rufe kanmu da tawul sai mu sanya kanmu a saman ruwan zafin domin fuskar ta tiriru na tsawon minti 10.
Yin haka na narkar da maikon fuskar (gishirin fuska).
A samu baking soda.
Za mu iya samunta a shagon da ake sayar da kayan kek sai mu kwaba a ruwa sannan sai mu shafa a fuskarmu. Bayan haka, sai mu jira ya bushe. Idan ya bushe, sai mu wanke da ruwan dumi.
Idan kuma ba za mu iya tirara fuskar ba, za mu iya sanya tawul dinmu a ruwan zafi, sannan mu matse kafin mu kai fuskarmu.
Shan ruwa kamar kofi 8 ko 10 a rana na wanke maikon fuska kuma yana hana fitowar gishirin fuska.
Lemun tsami na busar da maikon fuska. Za mu iya shafa ruwan lemun tsami a auduga sannan sai mu guge fuskarmu da shi.
Zuma na taimakawa wajen rage gishirin fuska da kurajen fuska. Mu shafa zuma a fuskarmu.
Sai mu bar ta na tsawon minti 10. Sannan mu wanke da ruwan dumi.
Sirrin Rike Miji
+2348037538596