Fa'idodin Dake Cikin Yin Aure

Fa’idodin Dake Cikin Yin Aure

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

Fa’idodin da suke cikin aure ba zasu Kididdigu ba. Amma ga wasu ka’dan daga ciki zamu lissafo kamar haka:

 

1. Yin aure biyayya ne ga umurnin Allah da Manzonsa (sallal Lahu alaihi wa aalihi wa sallam).

 

2. Yin aure yana sanya Manzon Allah (saww) farin ciki aranar lahira. Yace : “Kuyi aure ku hayayyafa. Domin ni zanyi ma sauran al’ummomi alfahari daku aranar Alkiyamah”.

Yadda Ake Wankan Janaba

3. Ta dalilin aure zaka samu wanda Zai fito ta jikinka, har ya girma yana Kalmar Shahada!! “LA ILAHA ILLAL LAHU MUHAMMADUR RASULALLAHI.

 

4. Ta dalilin aure ne zaka samu Zuriyar da zasu yi maka addu’a bayan rasuwarka. Wannan yana daga cikin ayyukan da ladansu ba zai yanke ba har abada.

 

5. Yin aure ya kan zama dalilin runtsewar idanun mutum daga kalle kallen Haramun, sannan ya kare masa al’aurarsa daga Zina.

 

6. Ta dalilin aure ne zaka samu damar taimaka ma ‘Yar uwarka Musulma, ka aureta, ka Kiyayeta kenan daga Zina.

 

7. Ta dalilin aure ne zaka samu cikar addininka, da ninkawar ladanka fiye da wanda bashi da aure.

 

8. Ta dalilin aure ne zaka samu ladan ciyarwa da Matarka, da daukar nauyinta, da ladan samar mata da Mazaunin da zata rayu.

 

9. Ta dalilin aure ne zaka samu damar Qara yawan Musulman duniya ta hanyar haihuwar da zaka samu.

 

10. Ta dalilin aure ne zaka samu damar Karkatar da himmarka daga kan neman biyan bukatarka ta hanyar haram izuwa ga hanyar halal. Da kuma samun ladan saduwa da iyalanka.

 

11. Zaka samu lada mai girma sosai idan Har Allah ya azurtaka da ‘Ya’ya mata guda biyu, kumq kayi hakuri dasu ka kyautata musu, ka kyautata tarbiyyarsu, Su zasu zama Garkuwarka daga shiga wuta.

 

12. Idan kuma har ‘Ya’yanka guda biyu suka rasu, kuma kayi hakuri, to Allah zai shigar dakai Aljannah saboda wannan.

 

13. Ta dalilin aure zaka samu Qaruwar mutuncinka da darajarka acikin al’ummah. Ka shiga sahun mutanen da zasu iya jagorantar lamuran rayuwar al’ummah.

 

14. Ta dalilin aure ne zaka Samu Taimakon Allah cikin al’amarinka. Kamar yadda Manzon Allah (saww) yake cewa: “MUTUM UKU, HAKKI NE AKAN ALLAH YA TAIMAKESU

 

(a) WANDA ZAI YI AURE DON NUFIN KAME MUTUNCINSA.

 

(b). BAWA WANDA YAKE NEMAN ‘YANCINSA SABODA YA SAMU DAIDAITUWA (ACIKIN ADDINI)

 

(c). MUJAHIDI (MAI YAKI DON DAUKAKA ADDININ ALLAH).

 

15. Ta dalilin aure ne zaka samu Qaruwar yawan dangi. Domin duk mutanen da ka auri ‘yarsu ko Qanwarsu, to ka zama nasu.

 

16. Ta dalilin aure ne zaka samu zuriyya tsarkaka wadanda zasu bauta ma Allah kuma za’a baka ladan dukkan aikin ibadar da sukayi.

 

* ZAUREN FIQHU yana kira ga Matasan da suke da ikon yin aure, lallai aje ayi aure. arage burin duniya. Kullum rayuwa tafiya take yi.

 

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (30/12/2014 Modified on 27/10/2018).

Post a Comment

Previous Post Next Post