Kalaman Soyayya Na Saurayi da Budurwa Pdf da Kuma Text
FUREN SOYAYYA.
Idan har ya kasance zan ke samun kyautar furanni a dukkan lokacin da na hadu da ke, to kuwa ni zan kasance mai ziyartar dausayi ma’abocin firanni masu kamshi na mallaka dukkan lokacina na wannan rana domin girmamaki. Ina son ki sosai a cikin zuciyata.
NA MALLAKA MIKI ZUCIYATA.
Ina tsananin so da kaunar ki bayan da kika samu nasarar sace zuciyata. Wannan zuciyar da ta kasance mallakina, ina mai farin cikin na mallaka miki ita a matsayin wata kyauta ta musamman. Na zama mallakin ki. Ki kasance mai ririta soyayyar mu kamar yadda na kasance. Na baki amanar kaina ki amince mu damke amanar juna. Ki huta lafiya.
AMSARTA NAKE JIRA.
Duk da Iskar dake kadawa a wajen lokaci bayan lokaci amma kasantuwata a bakin kogin bai hana gumi tsatstsafowa daga cikin fatata ba.
A zaune nake kan daya daga cikin duwatsun da suke gefen kogin ammafa kaina a sunkuye yake tamkar wanda aka bawa aikin irga korayen ciyayin dake wajen, fuskata cike take da damuwa.
Sautin shigowar sako wayata ne ya sanya na zabura na daukota daga cikin Aljihuna, sunan wadda ta turo da sakon da na gani ne ya sanya na yi murmushi cikin zumudi na shiga karantawa kamar haka ” Dan-Hausa ka yi hakuri a bisa jinkirin da na yi wajen turo maka da amsar sakon ka na ganin na amince da soyayyar ka.
Abba a tun ranar da na fara dora ido na a kanka na ji zuciyata ta kamu da son ka, bana iya bacci a kullum idan ban ganka ba, kaine masoyina na hakika tunda har zuciyoyin mu sun aminta da juna.
Ina son ka kaima kana sona ina yi maka albishir din ka samu makullin bude DAUSAYIN SOYAYYAR zuciyata, ina kuma fatan zaka kara shiri domin fantsama a cikin kogin soyayya mai dadi. Ina yi maka fatan samun nasara a dukkan al’amuran ka, daga masoyiyar ka SAFIYYAT.”
ina gama karantawa ban san lokacin da na yi wani tsalle ba na fada cikin wannan kogin dake gabana saboda tsabagen farin ciki tare kuma da sanyawa a raina wannan shi ne kogin soyayyar da take magana a kai, ina cikin kogin bakina na furta kalmar SOYAYYA! SOYAYYA!! SOYAYYA!!! MAI DADI!
Karanta Wannan Littafin Na Soyayya
*Allah ka bani ikon rubuta Abunda zai anfani Al,ummarka,Allah ka kiyaye mani harshe na ka bani ikon rubuta alkairi Ameen summa Ameen.*
1.
*1998*
Wani yaro ne da ba zai ga za shekara tara zuwa goma bah, ya tusa mahaifiyarsa ga ba kuka kawai ya ke saboda irin yadda ya ga halin da take ciki na tsananin labour………..murk’ususu take duk ta fice da ga hayyacinta, fita ya yi karo na babu iya ka tsakar gidan,wani d’aki Ya shiga Ya na kuka.
“Antu lantana ki yi hakuri ki zo ki taimaki Maah kar ta mutu……ga ta can ta na yin irin abun nan kamar na mutuwa………Cikin Wata irin tsawa da tun da ya zo duniya bai tab’a jin irin ta bah……. Tace,
“Idan na sake ganin bak’ar fuskar ka Cikin d’akin nan wallahi sai na yi maka dukan da za, a kasa ganeka…….fita anan shegen yaro Mai shegen naci, nima halin da nake ciki kenan fita.”
Haka ya juya ya na kuka bai koma d’akin ba waje ya fita ya shiga wani gida da ke kallon na Su da kukan sa……tun kafin ya fad’i abunda ya ke so matar ta tare shi cikin kulawa………
“ya a Kai *Areef*?lafiya kuwa? me ya faru gidan naku?maman ka tana lafiya kuwa?.”
Duk lokaci d’aya ta jera masa wad’annan tambayoyi kamar tana yiwa wani babba.
Yana shashshekar kuka muryar ta kasa fita sosai yace,
“Maah…….maah…….za ta mutu…… Ki taho karta mutu…..”
Cikin tashin hankali ta jashi suka fice ko gidan bata tsaya rufewa ba.
Sadda Su ka je har faya ta fashe tana nishin wuya d’an na son fitowa……..waje ta kora shi ta shiga tai makonta Cikin yar dar Allah sai ga jaririya ta fad’o wani wahalallen nishi ta sauke……..dan danan jaririyar ta fara tsanyara kuka asan dai ta iso duniya…. Cikin lokaci k’an k’ane aka gyare su sannan aka d’ora sanwar wanka……….Areef sai tsallen murna ya ke kamar ya anshe ta hannun maah da ke bata nono, d’akin da Areef ya fara shiga ne Wata mata ta fito Cikin tashin hankali tayi waje………duk kiran da Anni ke kwala mata ba ta saurare ta bah, zuwa can ta dawo nan ma Anni sai tambayarta take ta yi mata banza………ita sai ma ta k’yaleta…. Lantana aka fiddo aka Kai Asibiti.
Karanta Littafin Babu So
Alhaji farouk haifeffen garin Katsina ne,ne man Arzik’i ya kawo sa gari Abuja. Alhamdulillah an same shi kuwa don yanzu ya na zuwa Dubai da Sudan sarin kaya,matansa biyu Saudah ita ce mace ta farko da Allah ya bashi wacce A kullum ya ke Alfahari da ita, saboda aurenta shine Abun da ya d’aukaka shi har ya samu rufin asirin Allah,ya na masifar son matar sa sai dai matsalar farko da suka fara fuskanta, ita ce matsawar danginsa akan rashin haihuwarta da wuri, don alokacin sai da suka shekara goma da Aure Saudah ba ta yi ko b’atan Wata ba…….tsegumi dacece kuce ya ringa tashi akan wannan lamarin Idan ta shiga mutane an ringa harararta kenan, gashi Saudah ba mafad’aciya bace za ka jima ka na mata abu ba za ta tab’a tan ka ma ba,sai dai ta sha kukanta idan ya na kusa ya lallasheta ya ba ta hakuri, don idan ba shi ya bata ba bai San me zai ce mata ba, ana Cikin hakan tafiya ta same shi, bai saurari kowa bah ya d’auki matarsa suka cana Dubai…………wannan tafiyar ta tun zura mahaifiyarsa.
“tace Don nayi ma ka Maganar k’arin aure shine ka gudu kaida matarka ko, to kaje ko inane ka dawo Ina nan Ina jiranka.”
Basu dawo ba sai da suka shekara biyu.
Abun mamakin shine ganin Saudah da su Kai da yaro, Areef Kenan.
nan ma wata maganarce tai ta tashi, matar farouk ta haihu saboda bai d’auke mu bakin komi ba shine babu Wanda ya sanar ma.
………..hakan bai hana wannan auren ba Saudah tayi kuka kamar idon ta zai fita saboda bak’in Cikin halin da ta ke ciki, me ta yi masu su ke mata irin wannan k’iyayyar haka mai zafi.
Haka saudah ta ci ga ba da zaman hakuri da dangin mijinta, ta na ci gaba da kulawa da yaronta Areef wanda ta ke ma wata kalar soyayya, Wanda idan so samunta ne ko k’uda karya ta b’a mata shi………….wata biyu da da wowarsu akai bikin Alhaji farouk da d’iyar k’awar mahaifiyarsa……..ko kad’an ba ya son lantana, ba ma lantana kad’ai ba shi duk wata mace kallon na miji ya ke mata idan ba saudar sa ba, jinta ya ke har Cikin *RUHINSA* kuma ya yi alkawarin har abadan ita ce *ABIN CIKIN RUHINSA* bai tab’a cewa ba ya son lantana ba,Ya barwa ransa don Annabi Muhammad [S A W ] Ya yi hani akan furta k’iyaya ga wanda baka so.
Zaman lantana da Saudah kamar zaman doya da manja,ko misk’ala zarratin lantana ba ta Kaunar ta,haka ko ya Areef ya rab’eta sai dai duka shi yasa Saudah ke kaffa kaffa da Yaronta…….Areef na da shekararsa hud’u Saudah ta sake samun wani Cikin, y’an uwanta sun ta ya ta murna da mijinta, mace da namiji ta haifa aka sa ma macen *SHAHIDA* namijin kuma *SHAHID* zan iya cewa wannan haihuwar ta janyo ma sauda wata irin kauna wajen dangin mijinta,
Aka fara juya ma lantana baya, yayin da su ka ta so ta gaba kan cewar bata iya komi ba sai dai taci ta yi kashi.
wasa wasa sai da lantana ta shekara biyar ko b’ari ba ta yi ba, nan fah kuma tsanar da ake ma Saudah ta dawo ga lantana,saboda daman ko kad’an ba ta ganin girman innah mahaifiyar Alhaji farouk,sai ta yi wata uku ba ta je ta gaida ta bah, idan gidan ta zo a wulak’ance ta ke kallon ta……….su ma sauran dangi duk haka take masu……. Kan Ka ce me sun dawo da kulawarsu A kan Saudah wadda Su ke ganin da can zalintar ta Suke.
……yanzu kuwa kamar su goye ta su ke ji………..haka lantana ta ko ma saniyar ware saboda bak’in halin ta,wanda hakan da ta ga su na mata bai sa ka ta canza hali bah……….haka rayuwar ta ci gaba da tafiya Areef ya na ji da y’an uwansa nan mak’otansu akwai matar abokin Alhaji farouk……..lawisa yaran ta biyu, namijin sa,an Areef ne Macen kuma sa,ar Su SHAHIDA,tun da aka auri Saudah su ka kulla k’awance,don Mazajen su ma aminnan juna ne shiyasa su ma su ka had’a kansu abun gwanin sha,awa………wanda takai har dangin Saudah sun san da lawisa,ita ma lawisa danginta sun san Saudah,
Akwana A tashi ba wuya wajen Allah, lantana su ka samu Ciki kusan lokaci d’aya da Saudah…………wanda shine yanzu sauda ta sauka, ita kuma ta na kan hanya da sauran Aiki tukun……….Alhaji farouk ba yanan ya je Dubai akan wani kasuwanci da yake Fatan ya tabbata, Wanda idan hakan ta samu ba karamar nasara ya yi bah,don arzikin sa zai linka na da fintinkau……….da zai tafi twins suka matsa akai Su wajen ummin Dubai [yayar saudah ce d same father d same mother]
Dole ya tai da su don ganin halin da Saudah ke ciki na haihuwa yau ko gobe, koda akai ma Areef tayin zuwa yace Aa shidai ya na tare da Maah d’insa………….
Add Comment