Addinin Mu Littafan Hausa Novels

Wasu Daga Cikin Girmamawar Da Allah Yai Ma Fiyayyen Halitta Adaren Isra’i Da Mi’iraji

WASU DAGA CIKIN GIRMAMAWAR DA ALLAH YAI MA MASOYINA (ﷺ) ADAREN ISRA’I DA MI’IRAJI

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

 

1. Ita kanta tafiyar da akayi dashi ba tare da ya nema ba. anyita ne domin girmamawa gareshi tare da rarrashinsa bisa abinda mutanensa (Quraishawa) sukayi masa ﷺ.

 

2. Turo masa da mafi girman daraja acikin Mala’iku domin ya zama mai rakiya gareshi ﷺ. Wato Mala’ika Jibreelu (alaihis salam).

 

3. An turo masa dabba mafi daraja daga cikin dabbobin gidan Aljannah (Buraaqah) domin ta zamo abin hawansa awannan tafiyar, har ma dabbar ta nemi cetonsa, kuma ya lamunce mata. (Kamar yadda yake awasu riwayoyin).

 

4. Kafin su isa Baitul Maqdis, tun tuni har Allah ya tattaro masa dukkan Annabawansa guda 124,000 domin su taryeshi. (wannan ma wata girmamawa ce wacce wani Annabin bai sameta kafinsa ba. ﷺ.

Tarihin Annabi Muhammad SAW  A takaice

5. Limancin da yayi ma Dukkan Annabawan Allah (alaihimus salam) bayan sunyi sahu-sahu har da Mala’ika Jibreelu alaihis salam.

 

6. Manyan Manzannin Allah (alaihimus salam) tare da Manyan Mala’ikunsa sun tsatsaya acikin dukkan sammai domin jiran isowar SHUGABA ﷺ.

 

7. Gaisuwar girmamawar da ya samu daga dukkan Mala’iku da Annabawan Allah (alaihimus salam) .

 

8. Limancin sallar da yayi musu akowacce sama daga cikin sammai bakwai.

 

9. Ya shiga har cikin Gidan Aljannah, ya zagaya, yayi kallo. yaga ni’imomin dake cikinta. Harma ya bada labari ga al’ummarsa.

 

10. Ya shiga cikin wuta ya lekata ya ganta tare da azabar da take kunshe dashi, kuma yaga mazaunan cikinta.

 

11. Ya gaisa yayi zance na musamman da Manyan Mala’iku irinsu Maliku, Ridhwanu, Israfeel, Mika’il, da kuma Mala’ikan Mutuwa.

 

12. Yaje magaryar tikewa (Sidratul Muntaha) ya wuce har gaba da nan.

 

13. An cudanyashi acikin kogunan haske, Kuma ya keta hijabai yaje inda babu wani wanda ya taba zuwa daga cikin halittar Allah.

 

14. Ya hau shimfidar girma, ya kusanta da Ubangijinsa (SWT) irin kusancin da babu irinsa.

 

15. Ubangijinsa ya girmamashi, yayi zance dashi. Har yau babu wanda ya san zancen da sukayi. Alqur’ani dai yace mana *”YAYI WAHAYIN ABINDA YAYI WAHAYI ZUWA GA BAWANSA”.*

 

16. Ubangijinsa ya sanar dashi ilimin halittun farko da halittun Qarshe, kuma ya Qara masa da wani ilimin. (wanda wata halitta bata sanshi ba).

 

17. Ubangijinsa ya bashi Sallah dashi da al’ummarsa.

 

18. An dawo masa da idanuwansa cikin zuciyarsa kuma yaga Ubangijinsa (SWT) kamar yadda yazo a riwayar Ikrimah daga Sayyiduna Abdullahi ‘dan Abbas (radhiyallahu anhuma)kamar yadda Imam Tabary ya kawo acikin Tafseerin Ayah ta 11 acikin Suratun Najmi)

 

19. Yaga Mala’ika Jibreelu abisa ainihin siffarsa wacce Allah ya halicceshi akai tare da fuka-fukansa guda dari shida (600).

 

21. Yaje ya dawo cikin Kankanin lokaci tare da busharori da baiwa daga Ubangijinsa (swt).

 

Salatin Allah da amincinsa su Qara tabbata bisa mafi girman darajar halittu baki daya, Limamin Mala’iku, Cikamakin Annabawa, kuma Jagoran Manzanni tare da iyalan gidansa da sahabbansa da dukkan salihan bayin Allah baki daya.

 

DAGA ZAUREN FIQHU 07064213990 (10/22/2022).

Add Comment

Click here to post a comment